Sashe 111
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Habawa kan kace me sai jini ya ɓarke, duka ta ko'ina take sauke mata tamkar wadda aka yi wa wahayin duka.
Lallaɓawa Khadija ɗin ta yi ta miƙe tsaye, baiwar Allah har wani irin jiri jiri take gani.
Kai tsaye kitchen ta wuce tana É—an dafa bango, ruwa ta É—ebo a bowl ta zo ta fara yayyafawa Æ´ar uwarta, bata sake bi ta kansu maman Hanif É—in ba.
A ruɗe Zee ta farka, kuka ta shiga yi hawaye bibbiyu haɗe da sambatu wadda sai ka yi zaton yaren China take yi, ko ita kanta bata san me take faɗa ba, surutu kawai take barƙate da yaren da bana mutane ba, kamar wadda ƙwaƙwalwarta ya samu matsala.
Rungumota Khadija ɗin ta yi a kirjinta, wani irin tausayinta ne ya kamata, ji take tamkar ta fasa ihu mai sautin dode jin kowa ko zata huta, wannan shi ne rana zafi inuwa ƙona.
"Zainab dan Allah ki daina waÉ—an nan surutan haka ya isa, dan Allah kada ki bari wani abin ya sama mun ke, kada ki manta ke kaÉ—ai ke gareni, ko kina son wani abin ya sameki zuciyata ta buga na mutu ne?". Tana magana tana matsar kwallar da suka cika mata idanun, abin gwanin ban tausayi.
Ina ai Zainab kamar ta samu matsala fa a ƙwaƙwalwarta, dan kuwa duk bata jin me ƴar uwar tata take faɗa ba, cigaba da sambatunta kawai take yi. Abin idan ka gani sai ka matsa masu kwallah.
Khadija ta rasa ina zata sanya ranta ta ji sanyi, rarrashinta ta shiga yi tana ruwan hawaye tamkar ruwa ya fasa hanya ya ɓallo.
Ita kuwa maman Hanif da zuciya ya ɗebeta sai da ta ga Hauwa ta daina wani motsin kirki ga jini da yake bulbula daga bakinta, bakin ya sunduma sum, sannan ne ta kyaleta tana sauke numfashi da sauri sauri, haki ta shiga yi yadda kuka san wadda ta tiki uban gudu ta ƙoshi.
Kan su Zainab É—in ta koma, kama hannun Zee É—in ta wajen shoulder É—inta ta yi, É—agota ta yi suka koma saman sofa.
"Khadija jeki ki kawo mata magungunanta da sauri". Ta yi maganar har lokacin tana haki sosai, dan fa ba karya ta jibgi Hauwa iya jibga, wannan shi ake cewa dukan huce takaici.
Da gudu ta watsa cikin É—akin, jikinta sai kerma yake yi ta kwaso magungunar ta fito.
"Zainab É—in ta ci abinci ne?". Cewar maman Hanif.
Girgiza kai ta yi, tana kuka sosai ta ce. "A'a bata ci komai ba".
Shiru maman Hanif É—in ta yi tana tunanin ya zasu yi kenan? Dan babu komai da ya danganci abinci a cikin wannan gida, ga shi ita bata da ko sisin kwabo.
"Gwaggo dan Allah ki bata maganin mana". Cewar Khadija da voice baya fita.
"Khadija ba ta yadda za'ayi ta sha magani ba tare da ta sanya komai a cikinta ba, maganin ba zai yi mata wani amfani ba, dan haka dole mu nemo mata wani abu mai É—umi wanda zai É—umama mata ciki ta ci".
Zaro idanu ta yi, jikinta sai kerma yake yi, ta gaza tsayuwa waje guda, kamar zata faÉ—i tana ta tangal tangal. "Na shiga uku na ni Khadija, Zee dan Allah kada ki mutu, kowa sai mutuwa yake yi yana barina, baba ya tafi ya barmu da kewa, yanzu kuma Hajiya ta tafi, ke kam Zee ki tsaya da ni, ko kuma ni gara na tafi na barki". Tana magana tana mai cigaba da tangal tangal.
Ba kara É—aga hankalin maman Hanif suka yi ba, ga abin tausayi marayun Allah. Ta ruÉ—e sosai a in da take ta faÉ—in. "Khadija ya isa kukan nan ki yi shiru, Zainab ki yi wa Allah ki daina sambatun nan, kinga kin jefa Æ´ar uwarki ita ma ta fara sambatu ko? Kin É—aga mana hankali sosai, dan Allah ki yi shiru". Ita kanta da take maganar kwallah ne a cike tab a idanunta, dan kuwa dole su bawa mutum tausayi.
Kamar daga sama suka tsinkayo muryarta tana faɗin. "Gwaggo wlh na yarda ciki Khadija take da shi, tana yawan yin amai a toilet, ga yawan barci da faɗa, idan na yi mata abu kaɗan zata hau zagina abin da a baya ko da sunan wasa bata taɓa yi mun ba, sannan ga kukan da take ɓuya tana yi, na sha kamata tana yi a cikin toilet, innalillahi wlh tun da ta dawo gidan nan dama na ƙasa gane mata". Cewar Zee mai sambatu.
Jin zantukan Zee ɗin yasa maman Hanif da tashin hankali ya kusa yin ajalinta ta miƙe tsaye, a razane take kallon Khadija dake tsaye tana layi.
Ƙurawa cikinta idanu ta yi, duk da hijabi ne a jikinta amma tabbas cikin ya bayyana, ga alamar ya fara girma. Ai maman Hanif bata san lokacin da ta ɗaura hannu bisa kanta ta kurma ihu mai sautin gaske wanda ita kanta bata san ya aka yi ta yi shi ba.
Ihun ya yi sanadiyar buɗewar idanun Zee ɗin. Wani irin bugu da karfi karfi zuciyarta ya fara yi, ita ma da take gwaggonsu kenan, yau da ace babansu yana raye ina da tabbacin wannan mummunar labarin ce zata zama ajalinsa, dan kuwa yana da kishin familyns matuƙa.
Zubewa ƙasa ta yi a saman gwiwowinta, dan kafafunta ya kaza iya ɗaukar gangar jikinta, ita ma maman Hanif ɗin zubewa ta yi a saman nata gwiwowin tare da rushewa da kuka mai sauti, tamkar wata ƙaramar yarinya ta shiga rera wi wi wi gwanin ban tausayi.
An rasa waye zai rarrashi ɗan uwa, Hauwa dake kwance magashian tana numfashi sama sama ne kunnuwanta suka tsinkayo mata wanna bakin labarin. Ai bata san lokacin da ta waro idanunta waje ba, faɗi take a cikin zuciyarta ta samu damar korarsu daga cikin gidan, a cewarta yanzu maman Hanif ɗin ce kawai ta rage ta yi maganinta shikenan komai ma baban Zee ya zama nata, yanzu dai shirin korarsu daga gidan zata yi, dan dama ta jima tana tunanin hanyar da zata bi ta aiwatar da hakan, ta ƙasa iya kashesu.
Abin da baku sani ba, sau biyu tana shirya masu gadar zare Allah yana tsaratar da su, taso salwantar da rayukansu, ko kuma ta turasu waje mai nisan da ba zasu iya dawowa ba, amma duk haƙarta bai cinma ruwa ba, to yanzu dai da alama ta sami abin da take so, a tunaninta zata iya cinma burinta..... To fah!! Akwai matsala, amma dai mu je zuwa ni ina ma zarginta a kan mutuwar Hajiya, dan wannan Hauwar a kan duniya babu abin da ba zata iya ba.
"Khadijah wanenen ya yi maki wannan abin? Waye ya cuceki ya kashe mu innalilahi wa Inna ilahir rajiun........". Cewar maman Hanif. Yadda take magana wlh sai ta É—agawa bawa hankali, saboda wani irin kuka take yi mai tsuma zuciya, tamkar ranta zai fita take ji, hmmmm da mamaesu na nan ta sami wannan labari da sai yaya kenan? Ina ga ita ma shi ne zai yi sanadiyar rayuwarta. Zata gwammaci gara mata zaman prison É—in.
Kuka ita ma Khadijah ɗin take yi tamkar ranta zai fita. Da kyar ta iya faɗin. "Gwaggo nima ban san shi ba, ban sansu ba, kawai ɗaukata suka zo suka yi a kofar gidan nan, daga nan suka wuce dani ƙasar Brazil, a can na yi wata ɗaya da sati biyu cikin wani irin gida da ban isa in fita ko nan da parlonsu ba, kuma wlh gwaggo daga ni sai shi ne kaɗai a cikin gidan, ko parlonsa bana iya kai kaina saboda yanayin tsarin gidan, kofofin gidan dukka sai da password suke buɗuwa, kuma shi kaɗai yasan password ɗinsu, bana fita ɗakin da ya ajiyeni, haka na shafe wannan lokacin, daga nan kuma sai ya ɗaukeni muka je wani gari ne ko wace ƙasa ce ban sani ba, sai da dai muka hau jirgi........."
Dakatawa da yin maganar ta yi tana tari mai sauti, irin tarin nan mai kwarzane kirji, mai zafin gaske.
Sosai ta yi tarin, tun tana tsugune kan gwiwonta tana yi har ta zauna dirshan mai gabaɗaya. Maman hanif bata da zaɓin da ya wuce ta matso ta riƙeta dan ta tallafa mata, ita ma Zee da sauri ta sauƙo ƙasa daga saman sofar, rungumarta ta zo ta yi.
"Zee kawo mata ruwa". Cewar maman Hanif É—in.
A guje ta miƙe, sai dai kuma ta ƙasa yin gudun, saboda ba lafiya ne da ita ba, dan dole ta hakura ta ja kafafunta a hankali ta nufi kitchen, gaɓoɓinta duk ciwo suke yi mata.
Ruwa ta ɗebo a cup ta kawo. Karɓa maman Hanif ta yi ta sanya mata a saitin bakinta, a hanzarce ta karɓa ta fara sha ba kakkautawa, Allah sarki har maƙoshinta ya bushe ne saboda tashin hankali.
Tas ta shanye ruwan kafin ta cire kai, kifa kan nata a saman shoulder ɗin gwaggon nata ta yi tana mai cigaba da kuka ƙasa ƙasa.
"Ban san ƙasar da ya sake tafiya dani a karo na biyu ba, shi ma Brazil ɗin abin da yasa na san a ƙasar nake shi ne, a lokacin da jirginmu da ya ɗaukomu daga Nigeria ya sauƙa a airport ɗinsu, a nan ne na ga kasar da muke, to ɗayan ƙasar da muka je ɗin kuma lokacin da muka sauƙa ina barci, sai dai buɗe idanuna na yi na ganni a wani ɗaki na daban, babu kowa a cikin ɗakin, sai dai hayaniya da na ji a wani ɓangare na cikin gidan, hakan yasa na miƙe da nufin in je in ga su wanene? Ko da na fito na rasa hanya, haka na yi ta bin daga in da sautin hayaniyar yake tashi har Allah ya kaini main parlon ƙasa na gidan..........". Ɗan dakatawa ta yi tana mai jan numfashi, kuka yana neman cin karfinta.
"Wanene shi Khadijah?". Cewar gwaggon nasu, a ƙage da son jin amsar ta yi tambayar. "Kin san shi ne? Aina kuka haɗu? Meyasa zai ɗaukeki? A ina yake yanzu?". A cikin tsananin fargabar amsar da zata ji ta jefa mata tambayoyin nan.