← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 211

Sashe 167

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ya ce maki amarya tana fita? Ki kawo in kai masu". Cike da mamaki ta yi maganar, dan dai ita tasan amarya sai ta yi wata bakwai a al'adarsu kafin ta fara É—an kaiwa iyayenta kawai ziyara, sai ta yi shekara guda zata fara zuwa gidan sauran Æ´an uwa kuma, amma ita kwana uku kenan yau da auren nata ta wani ce zata fita, abin dole ya bawa Jumma mamaki, dan bata saba gani ba.

"A'a Jumma ki bari zan kai masu da kai'na". Ta faÉ—a a É—an takaice.

ÆŠan zaro idanu Jumma ta yi kafin ta ce. "Mahnoor ko dai baki son na je na kalle maki angonki ne? Baki son na kai mashi abinci ko?".

Dan turɓune fuska kaɗan ta yi. "Ni Jumma baki ji na faɗi hakan ba, kada ki zo ki mun sharri, kuma ni ce maki aka yi shi zan kaiwa abinci ne ma........?".

Ai bata gama rufe baki ba Jumma ta hau kirga kwanikan da suke hannunta. Ganin guda uku ne yasa ta ce. "Mahnoor, yanzu idan zaki ɓoyewa kowa komai a garin nan har da ni zaki ɓoyewa?"

"Me na ɓoye maki ɗin?".

"Ba ga shi kwanika uku kika ɗauka ba, bappa ɗaya, Mahreen ɗaya sai shi kuma ɗaya, amma kike ɓoye mun ko?".

"Ni ba abin da na ɓoye maki Jumma, ɗayan kwanon nawa ne ba na Hamma ba, ai nima ban ci abinci ba". Ta faɗa tana ƙara turɓune fuska.

Dariya sosai Jumma ta kwashe da shi. "Amma Mahnoor Allah ya nuna mun ranar da zaki canza hali ki dai'na wannan kunya taki maras amfani, gara maki ma ki saki jiki ki ware ki kula da mijinki, idan ba haka ba kina ji kina gani zaki rasa shi!".

Wani irin zaro idanu ta yi. "Zan rasa shi kuma Jumma? To meyasa zan rasashi? A kan wani dalili?".

Dariya ne mai É—an sauti ya sake kubcewa Jumman, kun san ita fa ta É—an waye, dan haka bata kunbiya kunbiya, komai gar take yinsa a faranti, amma tana É—an sakayawa idan a gaban Inna Rabi ce, sai kun ganta a cikin kawayenta ne zaku gane Jumma Æ´ar air ce.

"Su Mahnoor kenan, wato jin zaki rasa shi har kin tsorata ko? Eyes soyayya ruwan zuma, to dai shikenan ni dai na gaya maki in dai baki kula da shi tsab zaki rasa shi, dan kuwa ƴan'matan kauyen nan dik yanzu sun fara yarda shi ba aljani bane kuma ba maye bane, shi ɗan adam ne kamar mu, dan haka yanzu har gona suke binsa su je suna leƙansa suna jin daɗi, ni kai'na a da na yi tashen zuwa kallon kyansa, amma yanzu da ya zama mijinki gaskiya na dai'na, da ina fatan samunsa a matsayin miji, amma yanzu gaskiya na daina, kuma bana fatan na rinka haɗuwa da shi ma, dan haka idan kin saki jiki kin kula da shi kina iya cin riba, idan kuma kinki kula da shi to wlh zaki rasa shi, dan dai kinsan tu Fatu kam ba kanwar lasa bace, suna ji da kansu sun waye a birni, kina ganin yadda nima da nake zuwa birnin suke yiwa kallon ƙasƙanci da rai'nin wayo, to wlh tun wuri gara ki riƙe mijinki hannu bibbiyu". Ta kai karshen maganar tana jan numfashi.

Kamar zata yi kuka ta ce. "To yanzu ni Jumma ya zan yi?".

Kamar zata yi mata dariya sai kuma ta fasa, yadda ta marairace murya sai abin ya so bata dariya.

"Sai kin gaya mun da gaske kina sonshi ne ko bako son shi? Idan kika gaya mun ni kuma zan gaya maki yadda zaki kula da shi sosai ta yadda ba zai taɓa kula kowace mace a garin nan ba, dik da nasan ma da wuya hakan ta faru, saboda yanayinsa dama baya kula kowa, amma fa ki sani zuciya bata da ƙashi, yana iya canzawa bana yi maki fatan hakan".

Narai narai ta yi da ido kamar zata sa kuka. "Jumma ni ban sani ba, abin da nasani kawai shi ne ina son Hamma Faisal, shi kuma Hamma ina jin dai kamar bana son ya tafi, bana son ya rabu damu, kuma yana bani tausayi haka kawai".

Sosai Jumma ta fahimci akwai soyayyar Faisal sosai a cikin zuciyarta, amma da alama soyayyar Jaish da yake samun gurbi a zuciyar tata a yanzu zai iya tunkuɗe soyayyar Faisal ɗin. Ita Jumma tana sonta a tare da Jaish ɗin ne, ba dan komai take sonta a tare da shi ba kuma face tana zargin Jaish ɗan birni ne, kuma tsayayen namiji ne mai karfi, tana fatan ya cetota daga ukuban da Nenne take gana mata, dan har ga Allah Jumma tana jin ciwon cutar da ita da Nenne take yi, sau da dama tana yi mata kuka, shiyasa ta kafe take son yi mata wayo ta sanyata yin wasu abubuwan da zai sanya soyayyar Jaish ɗin zai shiga ranta ba tare da ta sani ba, dan a ganinta ko ba jima ko ba daɗe Jaish zai koma in da ya fito, sai take tunanin idan zai koma tabbas in suna son juna zai tafi da Mahnoor ɗin, daga nan kuma ta huta da bala'in Nenne, shiyasa take son koyawa Mahnoor ɗin yadda zata sanya shi kansa Jaish ɗin in baya sonta ya fara dan dolensa, Jumma akwai ƙoƙari, lallai kin ɗauko aiki kuwa, baiwar Allah bata son ganin Mahnoor a cikin damuwa.

"Mahnoor Allah ina gaya maki wannan Hamman naki ko in ce mijin naki sau miliyan yafi Hamma Faisal, dan haka ki manta da shi ki rungumi mijinki, kuma ina gaya maki ki dai'na tunanin Hamma Faisal, dan ke É—in yanzu matar aure ce, idan kuma kina son shiga cikin tsinuwar Mala'iku kuma tom shikenan ki cigaba da zancen Hamma Faisal". Ta kai karshen maganar tana É—aure fuska sosai, irin Mahnoor ta É—auki zancenta serious.

"In Sha Allah daga yau na dai'na zancen Hamma Faisal, kuma na dai'na tunaninsa, ki tayani da addu'ar jure hakan kin ji?". Murya a marairaice ta yi maganar, gwanin ban tausayi!.

"In Sha Allah zan tayaki da addu'a, da izinin Allah daga yanzu da muke tsayen nan ma alfarman Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kin dai'na tunaninsa kenan".

Da Allah yasa ta amsa mata, sannan ta ce. "To Jumma ki gaya mun ta yadda zan yi da Hamma É—in".

Hannu ta kai ta karɓa mata kwanikan dake hannunta tare da cewa. "Muje in ɗan rakaki kaɗan sai in yi maki hiran a hanya, amma dai banso ace kin fita a yanzu ba, mutane zasu yi ta surutu idan suka ganki, sai dai ni a wajena ba komai bane tun da wajen mijinki zaki je kai mashi abinci, kuma yanzu zaki yi yaki ne a kansa".

"Yaki kuma Jumma?". Ta faɗa tana miƙa mata kwanikan.

Karɓa ta yi suka jera a tare tana faɗin. "E yaki mana, ai yanzu dole ki yi yaki a kansa dan kada a kwace maki shi, kuma kema dan kin san ba zaki taɓa samun irinsa ba".

Jinjina kai ta yi suna mai cigaba da tafiya. Wasu irin shawarwari masu kyau da amfani Jumma ta rinƙa bata irin na ƴan birni ƴan gayu. Ƙawa ta gari kenan, su yayin cin amanar juna bai shigo garesu ba tukun nan.

Sai da suka kusa isa gonar ne ta miƙa mata kwanikan tare da faɗin. "Dan Allah Mahnoor ki daure ki yi amfani da shawarwarin nan da na baki, sannan ki kula sosai kin ji?".

Da to ta amsa mata tare da karɓar kwanikan tana zuba mata godiya, ta wuce izuwa gonar ita kuma Jumma ta juyo izuwa gida.

Tun daga nesa Mahreen ta hangota, da gudu ta taso ta nufota dan ta karɓa mata kwanikan.

Da farko bappa ya ce ba zasu fita kiwo ba yau, sai bayan kwanaki, sai yaga dabobin suna jin yunwa, sun yi yawan da ba'a isa a ciyar da su a gida ba, dole a fita neman masu abinci, hakan yasa suka fita.

Bappa baya wajen, daga Mahreen sai Jaish É—in ne suke zaune a wajen zaman nasu, shi bappa ya fita da dabbobin dan su É—an yi kewaye su samu wadatatcen abinci.

Karɓa mata kwanikan Mahreen ta zo ta yi tana bata labarin Hamma ya ciro mata gwaiva da mangoro ta sha, kuma ya ajiye mata nata ita ma, Mahreen sarkin labari, wato faɗi ba'a tambayeka ba kenan.

Da to kawai Mahnoor ta bita sa shi har suka ƙarisa wajen da yake. A saman tabarman nasu ta ajiye abincin tare da tsugunnawa da kyau ta ce. "Hamma ina wuni".

Yana kallon face É—inta ya amsa da. "Lafiya lou Alhdulillah".

Wani ajiyar zuciya ta sauke wanda yasa shi cigaba da kallonta, dama zai kawar da kallon nasa ne, jin wannan ajiyar zuciya da ya sauke yasa ya fasa kawarwan.

"Lafiya?". Ya tamnayeta.

"Babu komai". Ta faÉ—a cike da fargabar abin da zata aikata wanda Jumma ta bata shawara a yanzu, shi ne ya tsaya mata a ranta sosai.

"Adda Mahnoor me kika dafa mana?". Cewar Mahreen.

Shiru ta yi bata amsa mata ba, dan ita ba wani juriyar biye surutun Mahreen ta ke da shi ba.

"Me kika dafa mana?". Jaish ya jefa mata tambayar idanunsa a kanta, ta wani sunkuyar da kai kamar tana gaban malaminta zata kai haddan Alqur'ani mai girma.

Jin shi ya yi tambayar yasa ta yi saurin É—ago kai ta kallesa, wato ganin taki amsawa yar rigimarsa Mahreen yasa shi ya tambaya ko? Wato yana son sanyata bawa Mahreen amsa ne.

A ranta ta ce dama haka yake? Dama dan baya magana ne yasa bai cika shigarwa Mahreen surutunta na banzan nan ba! Wato shi ma baya iya jure maganar kurma kurman nan bawan Allah, shiyasa baya biyewa Mahreen sosai, yanzu kuma yana da bakin magana, Allah sarki.

"Ba zaki gaya mana me kika dafa bane?". Ya sake jefa mata tambayar.

Ɗan tsorata ta yi na jin sake tambayar tasa da ya yi, sai kuma a lokacin ta farga ashe ta tsaresa da idanu ta afka duniyar tunani bata sani ba, a hanzarce ta zare idanunta daga cikin nasa tare da yin ƙasa da kai.

"Tuwo da miyar kuka na yi". Ta bashi amsa ƙasa ƙasa.
Chapter 167 · 0% Book details