Sashe 31
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau dai gabaɗaya hankalin kowa a matuƙar tashe yake, Guyson ma ya sha kuka, da yake shi da Sharifat akwai saurin kuka, Obaid and Omaid kuwa idanunsu a bushe, shi Obaid ma cewa ya yi bari ya je ya yi wanka da kafar ciwon nasa, yaran nan sam sam babu wani tausayin kirki a ransu, abin kirkinsu ɗaya dai shi ne kaunar juna da suke yi, amma kome zai faru zuciyarsu bata karaya sam sam.
A haka dai yau gidan ta kwana hankali a matuƙar tashe, kowa yana cikin damuwa, amma King Zuhair bai da kabari, sun ki sanar mashi abin da ya faru.
Da Abu Abdussalam, Rizwan, Bilal sai Dr Raj sune suka kasance a tare da Ramish É—in, sai fama Dr Raj yake yi a kansa dan shawo kan matsalar, Guyson ma ya kasa iya yin barci, sai shige da fice yake yi daga room nasa zuwa wajen Æ´an uwan nasa.
Ba yadda su Rizwan basu roƙi Abu Abdussalam ba a kan ya yi hakuri ya je ya kwanta dare ya yi, amma ina ya kafe ya ce in sunga ya fita daga ɗakin nan to fa ya san a wani hali Ramish yake ciki, dan yanzu su dukkansu har Dr Raj ɗin basu san a wani mataki yake ba.
Sharifat da ta tare a saman dadduma tun karfe 10 sallah take yi tana kuka, addu'a take yi Allah yasa kada ya mutu, bata damu da son jin meyafaru har aka harbesa ba, ita dai burinta kawai ya farka. Ita ma Leesharh ta ji tausayinsa sosai, kuma tasha kuka, duk sai ta ji tamkar É—an uwanta aka harba, ta shiga damuwa sosai, hakan yasa ta yi mashi addu'a sosai kafin ta kwanta, sai dai ko da ta kwanta bata iya yin barci ba, tunani ya hana ta rintsawa, sai kuka take yi masu nikaf basu haÉ—ata da babanta ba, bama su sake kiran ta ba, tun da suka yanke call É—in É—azun, basu cika alkawari ba.
A ɓangaren Obaid and Omaid kuwa, suna cikin room ɗinsu dake part na su Ramish ɗin, dama idan sun zo gidan a nan suke zama, ko a jikinsu suka yi shirin kwanciya Obaid kafa ta dai'na zogi, shirin kwanciya abinsu suka yi, dan a cewarsu ai ragonta ne dan an harbi mutun da bindiga su wani tsaya ɗaga hankalinsu, Yah Ramish ai jarumi ne, ba rago bane, sun tabbata da Yah Bilal aka harba haka Yah Ramish ba zai tashi hankalinsa har haka ba, dan shi ɗin jarumi ne baya son harkar ragonta, dan haka su basu ga wani abin ɗaga hankali ba, Allah ne yake riƙe da ransa, idan ya tashi fine, idan ma bai tashi ba fine, kowa ma zai mutu, su basu son shirmen banza, ba zuciyar mata ne a kirazansu ba da zasu tsaya yin kuka ko su hana kansu barci, dakakkun maza suke shiyasa suka yi kwanciyarsu basu sake leƙawa wajen Ramish ɗin ba!.
Yo su dama ta ya za'ayi su damu? Kada ku manta suna da tsama tsakaninsu da Ramish ɗin da kuma Mama, duk cikin kingdom of power Ramish ɗin ne kawai yake iya nutsar da su su nutsu, shi ne mai ci masu ƙaniya dai'dai gwargwado, ba wanda suke shakka da tsoro sai shi, shiyasa ba wani kaunarsa suke yi ba, kunga kuwa fin haka ma zasu faɗa, ga maman Ramish ɗin ta sako Mommarsu a gaba, ta takura mata, kunga ai dole su ce su ba ragwaye bane. Amma fa da yake jini ba wasa ba har cikin ransu abin ya yi masu zafi, sun ji babu daɗi, kuma sun ji a ransu da zasu kama wanda ya harbesa tsab zasu kashe banza, yaran nan baka iya gane masu sam sam.
Haka suka yi shirin kwanciya suka kwanta abinsu, kafin su yi barci ma sai da suka sha hira tare da cewa gobe da safe zasu bar gidan nan dan basu son wani koke koken da shirmen banza, jibi zasu wuce school, zasu koma gidam King Badeen su ƙarisa shirinsu a can.
Obaid ne ya fara yin barci ya bar Omaid, shi kuwa Omaid É—in har wajen karfe 3 yana latsa waya bai kwanta ba.
Washegari da safe, shiryawa sosai suka yi kafin su fito, kai tsaye palace na Abu Abdussalam suka nufa, dan su yi mashi sallama. Sai dai ko da suka je baya nan, hakan yasa suka dawo wajen Ramish. A nan suka sami family gabaÉ—aya.
Allah sarki Sharifat idanu sun kunbura luhu luhu sun yi jajir kamar mai ciwon ido saboda kuka da ta kwana yi, shi ma Guyson idanu sun kumbura saboda kuka da rashin samun barci, yau gabaɗaya kowa da yake cikin gidan Abu Abdussalam sai da yasan ba lafiya, jami'an special weapons sun yi tururuwa zuwa gidan, kaki sun ƙaru a cikin gidan sosai, tamkar ba lafiya ba, sai kai komo manya manyan motocin kaki suke yi, waɗan nan su shigo waɗan nan su fita, babu wanda ya sami damar ganin Ramish ɗin.
Harta air force, wato ma'aikatan Bilal sun cika gidan, sai up and down suke yi suna wani muzurai kamar zasu cinye mutun É—anye, ga su mafiya yawancinsu idanunsu jajir, sannan ga wasu jiga jigan bindigu a hannunsu wanda ko baka yi laifiba ka fito tsakar gidan nan ka gansu sai ka razana ka ruÉ—e ka rasa ina zaka sanya ranka, idan ma kana da zuciya a kusa yanzun nan zaka haÉ—iya ka mutu saboda razanar da zaka yi da ganinsu.
Yadda kuka san ɓarayi ne suka hauro gidan suka yi ɓarna, sai wani kaiwa suke yi suna komowa haɗe da gyara bindigunsu kamar masu jiran kiris su saki wuta.
Abu Abdussalam suka fara gaisarwa kafin su gaida Ummie, sannan suka bi sauran Æ´an uwan nasu dukka suka É—aga masu gaisuwa. Da yake yau kowa yana cikin tashin hankali sama sama suka amsa gaisuwar tasu. Cikin girmamawa suka ce da Abu Abdussalam zasu koma gidan King Badeen dan gobe zasu koma school.
Ba musu Abu Abdussalam ya ce okey Rizwan ya rakasu waje yasa a É—aukesu a cikin motan jami'ai, sannan jami'ai kamar guda 10 su rakasu har gida dan tabbatar da tsaro.
Da okey Rizwan ya amsa kafin ya wuce gaba su rufa mashi baya. Kowa dake cikin É—akin banda Ummie duk suna tsaitsaye ne cirko cirko sun zubawa Ramish dake kwance kamar gawa idanu. Ummie kuma tana zaune a bakin bed É—in da yake kwance ta tsare shi da kallo, Guyson kam ya kifa kansa a jikin bangon É—akin yana ruwan hawaye.
Kai tsaye Rizwan ya je ya faÉ—awa securitys dake bakin gate umarnin Abbie, yana gaya masu kuma ya juya izuwa cikin gida, dan suna tsaka da aiki ne.
Nan take jami'ai 10 cif kamar yadda minister Abu Abdussalam ya faɗa suka shirya tare da fito da mota har izuwa gabansu in da suƙe tsaye, sannan suka buɗe masu kofar motar a kan su shiga a mayar da su.
Obaid ne ya fara ƙoƙarin shiga. Basu kai ga shiga cikin motarba jiniya ya ƙaraɗe ko'ina a cikin gidan.
Dakatawa daga shiga suka yi, Obaid ya ce su jira bari yaga su waye kuma suka zo? Ba yadda jami'an suka iya dole su jira, haka suka tsaya cirko cirko suna jiransu, yarana kanana sai sakawa manyan mutane ciwon kai.
Wasu daga cikin Jami'an Swat ne suka danno hancin motocinsu guda uku cikin gidan, yau gidan minister ya zamana tamkar filin yake, ko'ina ka juya kaki daban daban ne suke kai komo.
Wasu jiga jigan jami'ai guda biyu ne suka fito daga cikin mota ta tsakiya, suna fitowa wasu matasa guda biyu suka fito suma. Damko matasan suka yi suka nufi hanyar discipline room dake cikin gidan ta kusa da apartment na jami'an dake cikin gidan gabaÉ—aya, a nan É—akin discipline room É—in nasu yake, wannan É—aki wlh da'a kai mutun ciki gwara mashi su harbe shi da bindiga kawai ya mutu ya huta.
Wlh idan suka shiga da mutun wannan É—akin da wuya uwar da ta haife shi ma ta iya ganesa a lokacin da zasu fito da shi. ÆŠaki ne katafare gaske, babu kalar nau'in azaba da babu a cikinta, kayan azabtar da bawa birjin suka tara a ciki, ko É—an'sanda or soja ko dai swat or wani kaki dai idan ya yi laifi, shi da yake da horo a jikinsa ma kuka yake yi idan aka ce a kaisa wannan É—akin a bashi punishment bare kuma wanda bai da kaki bai da horo a jiki, sam babu imani a wannan É—akin.
Dama tun da motocin suka shigo cikin gidan Obaid and Omaid ɗin suka nufesu dan su ga su wanenen? Su da zasu tafi amma sun tsaya ganin gulma, jami'an da zasu raka sun ɗin kuma sun tsaya kamar wasu tsaƙaguna suna jiransu.
Sun zo dai'dai tsakiyar harabar gidan suka ci karo da jami'an swat ɗin guda biyu suna riƙe da mutane guda biyun da suka fito dasu daga cikin motan, sun riƙe masu kunkumin wandunansu kamar dai yadda suke damke criminal.
Kallon Omaid Obaid ya yi kafin ya furta. "They looks like a criminals". Jinjina kai Omaid É—in ya yi alamar e zancen Obaid dutse tamkar wani babban mutun. Ga Æ´an rakiyansu a can suna jiransu sun zo yin abin da ba'a aikesu ba.
Da sauri Obaid É—in ya dakatar da jami'an tare da tambayarsu me waÉ—an nan kuma suka yi? And su waye su?.
Cikin girmamawa É—aya daga cikin jami'an ya buÉ—e fasasshiyar voice É—in nan nasa kamar na adawa ya furta. "They're criminals, we're suspect that they are one of those who shot sir Ramish with gun, Sir Bilal told us to bring them home because he cannot go out today".
Da sauri suka juyo suka kalli juna kamar abin haÉ—in baki, zaro idanu suka yi a tare, da alama yaran nan sun saba magana Æ´ar kurma kurma da ido haÉ—e da É—an motsa lips É—in bakunansu, duk wata kafa ta munafurci sun santa kusfa kusfa, kana zaune ka saki baki zasu yi cinikinka su saidaka ko su haÉ—ama boom da zata yi maka mummunar fashewa ta hanyar yin magana da ido baka sani ba.