Sashe 66
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shigowa ya bawa Mahnoor buhun hannunsa a kan ta je ta wanke fruits ɗin ta kawo mashi. Shi kuma ya matso ya kama Jaish ɗin yana yi mashi faɗa a kan ya dai'na tashi kada ya je ya faɗi ya jiwa kansa ciwo, ya bari zuwa gobe ko jibi idan ya ƙara samun karfi sai ya rinƙa fita. Ko kallonsa bai yi ba, hasalima ba jin yarensu yake yi ba, dan haka bai ji me bappan ya ce ba, shi dama yare biyu ya iya, daga larabci yaren iyayensa sai kuma turanci yaren masu jajayen kunnuwa.
A wannan karon sam Jaish ɗin bai yi wani yunkuri ture bappa ko wani abin magamancin hakan ba, saboda bashi da wani karfi, yana ji yana gani bappa ya ɗan rungumosa suka koma cikin ɗakin, zaunar da shi bappan a saman tabarma ya yi, sannan ya janyo mashi kwaryar namar da Mahreen ta kawo cikin ɗakin ta ajiye da suka gama suya, bayan ya janyo mashi kwaryar namar ne ya sake janyo mashi kwaryar dake shake da ruwan sha mai sanyi na randar taɓo, ya kuma yi sanyi tamkar a fridge aka ɗauko shi.
Buɗe mashi paipain dake rufe da kwaryar namar ya yi tare da tura mashi gabansa. Habawa azababben yunwar da yake ji yasa ya mance da cewa ma ana yin brush a duniya, ai hannu kawai yasa ya fara ɗaukar namar, ya mance da cewa yana jin kyamarsu. Haba ai yunwa ba kanwar uwar kowa bace bare ta tausayawa bawa, kowa ta kama kifar da shi take yi ta nukurkushesa har sai ya zama abin tausayi, duk wani iyashegen mutun da tsiyarsa duk sai yana ƙoshe yake yi, komai ji da kan mutun yunwa tana sanya shi ya yi ladab ya miƙa wuya, to yau dai ga Prince Jaish yunwa ta kifar da shi ta nukurkushesa har ya zama tamkar ba shi ba....... Allah mai iko yau Jaish ne a Nigeria, a Nigeria ma a Adamawa, a Adamawan a rugar fulani zaune yana cin abincin da suka girka da hannunsu, rayuwa kenan ba ta yadda bata juyawa bawa, ina son ku kara tunawa da cewa yau idan kai ne gobe ba kai bane, duniyar ma gabaɗaya nawa take? Wuni guda ɗaya fa take a wajen mahaliccinmu, Allah kasa mu cika da kyau da imani haɗe da kalmar shahada!!.
A bakin kofa Mahnoor ta tsaya ta miƙawa Mahreen kwayar fruits ɗin da ta wankosu tas, sun yi fresh da su. Ɗan satar kallon Jaish ɗin ta yi yadda yake cusa namar nan a bakinsa tamkar wani ya ce zai kwace mashi, bawan Allah yadda kuka san shi da wasu zakunar da suka shekara basu ci abinci ba yake ci, sai cusawa yake yi a cikin bakinsa, irin kada su cinye su barshin nan, bai gama cinye na bakinsa ba zai sake ɗauki wani ya cusa a bakin masa, shi da yake cin abinci cikin class mai ɗaukar hankali, cikin nutsuwa da jan aji, yau sai ga shi yana cin abinci tamkar almajirin da ya kwana uku bai ga idanun abinci ba, har ya karyar mun da zuciya, shi ma aya ce mai zaman kanta a garemu, yau da gobe sai Allah, yau da gobe ta wuci wasa, dan haka kada ki ga Allah ya baki wani matsayi a rayuwarki ki ce zaki walaƙan wasu, a kowani lokaci Allah na iya canza abubuwa ba tare da ya nemi shawarar kowa ba, Allah na iya kwace abinsa ba tare da neman shawararki ba, dan kuwa lokacin da ya baki ma ai bai nemi shawararki ba, dan haka ina fatan Jaish ya zamar mana aya ku ɗauki darasi........ Ni dai bari na leƙa wani ɓangaren.
___________________________🔥💔
KHADIJAH 💔😥
A hankali ta juyo dan ganin wanene?. Wani matashi ne da ba zai wuci shekaru 25 zuwa 27 ba. Ƙarisowa in da take ya yi, murmushi ya sakar mata yana ƙoƙarin buɗe baki ya yi magana ta rigasa da cewa. "Ina wuni malam?".
"Lafiya lou Alhdulillah Khadija Ahmad, ya gida yasu mama?".
A takaice ta amsa mashi da lafiya lou Alhdulillah.
Shiru suka ɗan yi, shi ɗin malaminsu ne na islamiya ɗinsu. Katse masu shirun ya yi da cewa. "Khadijah Ahmad duk abin da ya faru da ku na samu labari, Allah ya jiƙan baba da rahma ya kuma sanya mama ta iya cin wannan jarabawar tata".
Shiru ta yi ta kasa iya amsawa da Amin É—in, saboda wani irin tukukin bakinciki da ya taso mata, yanzu kenan labarin abin da mamarsu ta aikata ya baza ko'ina? Yanzu duk in da zasu wuce nunasu za'ana yi kenan ana cewa ga waÉ—an da mamarsu ta kashe babansu? Innalillahi wainnailayhir rajiun! Hasbunallahu wani'imal, wannan wace iriyar musifa ce?!.
"Kiyi hakuri Khadija komai mai wucewa ne, sannan ko wani bawa da irin tasa ƙaddara da jarabarwar, fatana dai Ubangiji Allah ya baku ikon cin jarabawarku, ki cigaba da addu'a".
Ɗan dakatawa ya yi da maganar yana kallon face ɗinta, duk da ba wani hasken kirki ne a wajen ba amma suna iya ganin juna, shi da kansa yasan ta yi kiɓa kuma ta yi haske, ta ƙara kyau sosai, dama kun san Zainab ta fita haske, to yanzu har ta kusa ɗara Zainab ɗin a hasken fata.
Cigaba ya yi da cewa. "Dama naga kun jima baku zo islamiyya bane yasa na ce bari na zo na duba meyasa baku zo É—in ba? Allah yasa dai kuna lafiya?". Daga yadda yake magana da ita cikin mutunci da girmama juna zaku iya fahimtar kaunarta yake yi, ba shakka akwai soyayyarta a zuciyarsa ga kwayar idanunsa ma ya nuna hakan.
Wani irin wahalallen ajiyar zuciya ta sauƙe, murya a karaye kamar zata sa kuka ta ce. "Malam muna nan lafiya, sai dai islamiyyar ce ba zamu iya cigaba da zuwa ba, duk fa yanzu kowa yasan abin da ya faru da mu, kasan dama can ƴan islamiyyan namu ba kaunarmu suke yi ba saboda bamu kula kowa muna yin rayuwarmu ne kawai, yanzu idan mun je islamiyya ai kanmu muka jawa bakinciki, dan dai babu wanda zai hana yaran islamiyyar nan tsokanarmu a kan mamarmu ta kashe babanmu, dan haka mu ba zamu sake zuwa ko'ina ba". Ta kai karshen maganar siraran zafafan hawaye na bin kuncinta.
Hakika shi kansa yasan da haka, kuma yana matuƙar tausaya masu, saboda zasu zama abin tsangwama a cikin mutane, amma hakan ba shi ne zai sa su ki neman imili ba, a zamanin yanzun nan ka nemi ilimin ma idan aka ƙunsa maka wani bakinciki in ba ka kai zuciya nesa ba sai ka aikata saɓon Allah bare ace kuma baka nemi ilimi ba ai sai abin ya kwaɓe maka, amma hakika ya matuƙar tausaya masu na irin rayuwar da zasu fara fuskanta a wajen al'umma a yanzu.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Nasan da haka Khadijah, amma ba hakance zata sa ku ƙi neman ilimi ba, kin san da cewa ilimi yana da matuƙar mahimmanci sosai, dan haka ku kawar da kanku a kan duk abin da zaku gani kuma zaku ji, ku daure ku nemi ilimi, kada ki manta babanku bashi da burin da ya wuce ya ga kun yi karatu mai zurfi, to meyasa ba zaku kokarta ku cika mashi burinsa ba? Ki yi tunani a kan hakan mana". Ya kai karshen maganar yana mai da kallonsa a kan mutumin da yake fitowa daga cikin shagon da ta fito a yanzu.
"Tom shikenan malam zamu yi shawara da ƴar uwata da kuma kawunmu Sadiq, kowani hukunci ya yanke mana shi zamu karɓa tun da shi ne mamarmu kuma babanmu a yanzu". Tana magana zafafan hawaye ne suke cigaba da bin ƙuncinta.
"Dan Allah Khadeejerh ki daina kukan nan haka ya isa, addu'a kawai zaki rinƙa yi, addu'a makamin mumini, kada ki zama kamar baki da tawakkali sannan wadda bata yarda da ƙaddara ba mana! Dan Allah kukan ya isa haka, Allah ya gani ba zan iya jurar ganin kukanki ba........."
Wani irin É—augo kai haÉ—e da kallonta a kansa ta yi na jin kalamansa na karshe in da yace ba zai iya jurar kukanta ba. ÆŠan kawar da kallonsa daga kanta ya yi ya mayar da kallon nasa a kan mutumin da É—azun ya fito daga cikin shagon, so ya tsaya ne a ta bakin shagon yana making call.
"Kamar yadda kika ji na faɗa ne Khadeejerh, ba zan iya jurar ganin kukanki ba, zuciyata tana sosuwa sosai saboda ba zan ɓoye maki ba ina sonki, ba kuma tun yau na fara sonki ba, ya kai shekara biyu ina dakon sonki, ban samu damar furta maki bane sai yanzu, ki sani aurenki nake son yi".
Wani irin zaro idanu waje ta yi, kirjinta ta ji ya bada dukan uku uku, bata taɓa zaton hakan daga garesa ba. A dai'dai wannan lokacin kuma wannan mutumin da ya fito daga shagon tun ɗazun yake tsaye yake waya ya zo wucesa ta kusa da su.
A É—ari ta wani irin toshe hancinta da hannunta saboda wani irin bala'in warin da kamshin turaren bawan Allahn nan ya yi mata, duk da ta toshe hancinta nan take cikinta ya murÉ—a zuciyarta ya fara tashi, kan ta yi wani yunkuri amai mai karfin gaske ya kwace mata....... Tashin sense.
Bata iya matsawa daga in da take tsaye ba ta fara tikar aman, hakan yasa ta ɓatawa malamin nata jikinsa da aman, da yake yana kusa da ita ne. Ƙasa ta tsugunna ta cigaba da sharara amanta. A ruɗe shi ma ya tsugunna yana tambayarta lafiya me yake damunta. Ina ai bata iya bashi amsa ba amai kawai take yi.