← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 211

Sashe 8

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfi ta sanya wajen sake gwada buÉ—e kofar, amma ina abin ya ci tura, tun daga nan ta fahimci ba lafiya ba, tun daga nan hankalinta ya yi mugun tashi, tasan koma waye mai wannan ihun yana tsaka mai wuya, kuma ba lafiya. Sautin ihun ne ya kara dokan dodan kunnuwarta a karo na uku, hakan yasa hankalinta ya kara tashi, jikinta har tsuma yake yi, burinta kawai ta je taga me yake faruwa saboda karfin hali, babu tsoro a tattare da ita.

Da sauri ta juya ta koma wajen bed ɗinta, wayarta ta ɗauko jiki na kerma, har wani tsuma take yi. A hanzarce take daddanna numbers ɗin da take buƙatar kiran, bayan ta gama shigar da number sunan my world ne ya bayyana. Kira ta danna mashi, amma ina kirar taki tafiya, sai wayar ma ya nuna mata sam babu network, da ta matsa ma sai wayar ta ɗauke gabaɗaya.

Wurgi da wayar ta yi a saman gadon, a hanzarce ta juya ta koma bakin door É—in, jikinta na kerma ta fara karanto duk adduar da ta zo bakinta, da karfi ta sanya hannu tana jan handle É—in kofar tana rero addu'a.

Cikin ikon Allah kofar ta buÉ—e, kamar wadda bata da cikakken hankali haka ta nufi waje. Kai tsaye É—akin Auta ta fara nufa, tana buÉ—e kofar ta hangota kwance a saman gado, wutar lamp ya haske kyakkyawar face É—inta, sai sharara barci take yi cikin kwanciyar hankali.

Da sauri ta janyo kofar ta rufe mata tare da nufar É—akin Chuchu. MurÉ—a kofar ta yi domin ta buÉ—e, amma sai kofar taki buÉ—uwa, tamkar yadda kofar É—akinta ya yi haka shi ma wannan ya yi. Kofar a datse gam.

GabaÉ—aya jama'ar gidan barci suke shararawa kamar gawarwaki, duk abin da yake faruwa basu ji ba, shi kuwa King da bai yi barci ba yana saman dadduma part É—insa yana da É—an nisa da nasu, akwai ratar da ba zai iya jiyo su ba, hakan yasa bai ji me ake yi ba.

Ganin kofar a rufe kamar yadda nata ya yi ruf ne yasa ta gane cewa lallai lallai akwai matsala, ya fahimci daga É—akin Chuchun wannan ihun yake fitowa. Addu'a ta fara yi tana tura kofar da karfi karfi!.

Ta É—auki almost 5 mins a wajen kafin ta samu kofar ta buÉ—e, kasancewar da karfi karfi take tura kofar sai yasa da kofar ta buÉ—e ta kusa faÉ—uwa kasa, da karfi ta shiga cikin É—akin a tare da kofar.

Jujjuya fararen idanunta ta fara yi tana bin ko'ina da kallo. Tsit É—akin ya yi kamar babu kowa, a hankali hankali shesshekar kukan Chuchun yake tashi, tana kwance a saman gadon, ta yi ruf da ciki, kayan barcin jikinta duk an yagesu kamar wadda ta yi faÉ—a da damisa, fuskarta gabaÉ—aya ya yi jaga jaga da hawaye baiwar Allah, har da majina.

Mamaki da al'ajabi ya hana Mommar motsawa daga in da take tsaye, ta rasa me zata yi, ganin abin take yi kamar a mafarki, ga shi dai bayan Chuchun babu kowa a cikin É—akin.

Ni kam na ce toh ina Yah Jawad É—in?.

Ta jima a tsaye tana bin É—akin da kallo, sai jujjuya idanu take yi, jin sautin shesshekar kukar Chuchu yana kara karuwa ne yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta afka. A hankali ta É—aga kafarta ta fara takawa. Kai tsaye wajen bed É—in ta nufa. Cak ta tsaya a tsakiyar É—akin sakamakon motsin da ta ji kamar mutun ne a bayanta. Fargabar juyawa ta ji gudun abin da zata gani, ga shi kuma tsakar dare ne sosai, a lokacin almost karfe É—aya da minti talatin.

Wani irin kasala da tsoro ne ta ji ya rufeta, a hankali ta fara jiyo sautin kuka kamar na mage a kunnuwarta ta baya. Ajiyar zuciya ta sauke tare da furta Hasbunallahu wani'imal wakil.

Nan take ta ji kwarin gwiwa da kwarin zuciya ya ziyarceta. Da karfi ta juyo domin ta ga me yake motsi a bayanta?. Sai dai ko da ta juyo bata ga komai ba. Sake sauke wani ajiyar zuciyar ta yi tare da É—aga kafafunta ta cigaba da tinkarar gadon.

A karo na biyu ba ta ƙarisa isa wajen bed ɗin ba ta sake jiyo takun sahun mutun a bayanta yana biyota. A wannan karon cikin sauri ta juya.
Ai kuwa tana juyowa wani irin haske ne ya kashe mata idanu, yadda kuka san an dalla mata wutar fitillah mai bala'in haske. Karfin hali irin nata yasa bata datse idanunta ba, cigaba da zarosu ta yi a cikin wannan haske.

Wani irin idanu ta gani a cikin haske, green eyes irin masu hasken nan ta gani, ga idanun dara dara suna bala'in kyalli, idanu kawai ta iya gani, sam bata ga mamallakin idanun ba, bata ga face É—insa ko face É—inta ba, idanu kawai ta gani suna yawo a cikin wannan hasken.

Da yake akwai ta da karfin hali da jajircewa sai ta kara zaro idanunta tana kallon wannan idanun ido cikin ido, babu ko tsoro a ranta, da alama ta saba da irin waÉ—an nan masifun sosai, gidan King zama cikinsa sai masu karfin imani da kuma karfin hadda dan faÉ—a da shaiÉ—anu, idan ba haka ba kana cikin gararin, dan idan ka yi ba dai'dai ba da daddare ba kai ba barci............

A takaice dai duk yadda aka yi a tsoratar da ita ta gudu abin ya ci tura, ba su san da jinin Modarawa suke tare ba, ai Modarawa basa gudu kuma basa ja da baya, duk wuya duk daÉ—i, komai bala'i sai sun isa in da suka tinkara matikar Allah ya basu tsawon kwana, so basa ja da baya bare gudu, bare kuma ita Momma da take da shegen karfin hali kamar Akka ce ta haifeta, ko da yake babanta ai yayan Akkar ce, Husaininta ne, so fin haka ma zata aikata.

(Ni kam my people's zan so ganin Akka na yaki😅 wato tarihin Akka a lokacin ƴanmatantaka fa zai bada citta 🤔🌝 dan haka kada ku ga laifin su Omaid, sun gada ne har ya yi masu yawa, ta gefen uwa da uba dukka ba sauki, kun ga su Chuchu ai suna da mix, dan mummy ba jinin Akka ba ce, ba jinin Modarawa bane, amma su twin's fa? Gaba da baya jinin Akka ce ke gudana a jikinsu, uwa ba sauki haka uba ma, sannan kakarsu ta gefen uba, ta gefen uwar ma duk tsatso ɗaya ne da gefen uban, ai kunga su kam sai shirin Allah kawai, sai abin da kuka gani, Zunaira ce kawai ta fita zakka a cikinsu, ita ce mai sanyi hali sai Guyson da sai ka taɓo shi yake faɗa, su twin's kuwa ba sai ka taɓosu ba, idan baka burgesu bama sai sun maka azaba😅)

Da dai suka fahimci ba zata tsorata ba, sai suka yi ƙoƙarin canza salo ta hanyar sanya mata kuka da muryoyi kala kala dan su doɗe mata kunne ta dai'na jin sautin komai. A nan ne ita kuma ta fara rero masu karatun Alkur'ani mai girma na duk wata sura da ta zo bakinta.

Ai kuwa ko aya ɗaya bata gama karantawa ba wannan haske ya ɓace ɓat, nan take ɗakin ya yi wani irin tsit, sai a lokacin ita ma Chuchun ta iya ɗago kanta daga kifuwar da ta yi a saman gadon.

A zabure ta miƙe zaune, jikinta sai kerma yake yi, wani irin razana ce bayyane a saman face ɗinta, da alama ta tsorata sosai, a ruɗe take bin ɗakin da kallo kamar mai neman wani abin. Tana sauke idanunta a kan Mommar ta saki wani irin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro, da gudu ta diro ƙasa daga saman gadon. Tana zuwa ta faɗa jikin Mommar tana kara tsananta kukanta.

Ita kuwa Momma ta yi shiru tana ƙoƙarin fahimtar wani abin, sai da Chuchun ta faɗa jikinta ne ta sauke ajiyar zuciya tare da rungumeta. Cike da al'ajabin abin ta fara tambayarta me ya faru?.

Kuka take yi sosai ta kasa iya yin magana, ganin haka yasa Mommar ta kara rungumeta sosai tana ɗan bubbuga bayanta, a haka suka nufi room ɗinta. A saman gado ta zaunar da ita, sannan ta janyo bargo ta lulluɓeta da shi.

Har lokacin jikinta na kerma, gani take kamar Yah Jawad ɗin yana nan. Da kyar Mommar ta iya lallaɓata ta yarda ta kwanta, bayan ta kwanta ne Mommar ta miƙe ta ciro mata wasu kayan barcin Auta da suke ɗakin nata. Da kanta ta sanya mata su sannan ta tofa mata addu'oi, bayan ta kammala sai ta haye gadon suka kwanta tare.

Ba jimawa barci ɓarawo ya yi awon gaba da Chuchun, ita kuma Momma kamar yadda taga rana haka ta ga dare, sai tunani take yi a kan to me yafaru? Waye ya yi yunkurin yi wa Chuchun fyaɗe? Ga shi har an rabata da kayan jikinta gabaɗaya saura pant kawai, sosai ta afka duniyar tunani a kan wanenen? Meyake faruwa? Dan dai ita bata ga mutun ba a ɗakin da ta shiga, ko dai da ya ji motsin fitowarta ne ya gudu? Ko kuma ya ɓuya a cikin toilet ko wani wajen?. Haka dai ta rinƙa tunane tunane har asuba.

Washegari da safe da zazzaɓi mai zafi Gimbiya Chuchu ta farka, jikinta zafi kamar wuta, da alama zazzaɓin firgici ne, ta ƙasa iya tashi ma, ko sallar asuba a kwance ta yi bayan Momma ta yi mata alwala kenan.

Sai kuka ƙasa ƙasa take yi saboda zazzaɓin, da alama bata da juriyar ciwo, tana da raki sosai. Sosai momma ta rinƙa rarrashinta, da kyar ta samu ta yi shiru, miƙewa ta yi da nufin ta je ta sanar da King batun zazzaɓin.

Zata fita kenan a bakin kofa suka ci karo da Auta tana shigowa, gaisuwa ta É—aga mata, cigaba da tafiya ta yi tana amsa gaisuwar.

Ko da ta je part É—in King sai ta isko shi a tare da Mummyn Chuchun da kuma Yah Jawad sai Aunty MieMie suna hira, gaisuwa ta É—agawa King, bayan ya amsa ta gaishe da mummyn ma, sannan Yah Jawad da Aunty MieMie suka É—aga mata nasu gaisuwar.
Chapter 8 · 0% Book details