← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 211

Sashe 14

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hasbunallahu wani'imal wakil ta furta saboda bugawa da kirjinta ya yi na ganinsa a kwance haka, juyawa ta yi da sauri da nufin ta fice daga ɗakin, dan ba zata iya yin wannan gyaran ba, har ga Allah face ɗin Jaish yana tsoratata, ita ba ta yarda mutun bane. Mahreen kuwa da yake ba tsoro a ranta tana kwance saman katifar Bappan tana zuba barci, sam bata ji tsoronsa ba, ta dai yi mamakin ganinsa, amma har da taɓa fuskarsa ta yi dan ta tabbatar ba face ɗin ƴar tsana bane, dan a cewarta fatarsa ta yi mata kama da irin fatar ƴar tsana da Bappa ya taɓa saya mata lokacin da ya je gembu wajen kakansa, da zai dawo ya saya mata kyakkyawar ƴar tsana fara tas, to shi ne take ganin fatar jikin Jaish ɗin kamar na ƴar tsanan, bata yarda ba har sai da ta taɓa shi ta ji, sannan ne ta yarda ba ƴar tsana bace, dan tasan ƴar tsana roba ce, shi kuma ta ji nasa fatar da laushi sosai.

Yana a wannan hali da basu tabbatar yana raye ko ya mutu ba, haka Mahreen ta rinƙa mulmula mashi kumatu wai akwai daɗin taɓawa...........😅

Kumatunsa ya yi mata laushi, kafin ta yi barci har da wani cewa Bappa kumatunsa laushi kamar breadi. (Ni kam nace ina Yah Jawad ya zo yaga yau yadda mace take mulmulawa Jaish sarkin kunya kumatu😅 wlh idan ka biye Mahreen sai ka mutu da dariya 😅 Jaish dai yau yaga ta kansa, ya faɗo hannun Mahreen sai yadda kuma hali ya yi😅)

Na fara yin wani tunani fa, idan Allah yasa yana da rai ya farfaɗo ma kenan haka zata rinƙa taɓa mashi kumatu tana mulmulawa ta ce kamar breadi? Tab hmmmm.....🤔

MAHNOOR.

Tana juyowa suka yi ido huÉ—u da bappa da yake tsaye a bakin kofar shigowa. "Ina zaki je Mahnoor?". Ya faÉ—a tare da shigowa cikin É—akin.

Muryarta har kerma yake yi saboda tsoro ta furta. "Bappa Allah tsoronsa nake ji, ni har yanzu gani nake yi kamar aljani ne, dama Nenne ta taɓa gaya mun cewa akwai aljanu a kogin nan mu dai'na zuwa wajen ba Bismillah, to yau wlh na manta ban yi Bismillah ba ina ga shiyasa naga wannan aljanin, dan Allah Bappana kada ka ce na share ɗakin nan ka ji? Allah ba zan iya ba".

Da yake ya san halinta da tsoro sai ya ce to ta bashi tsintsiyar bari ya sharo ɗakin ya fitar mata da dattin sai ta share tsakar gidan. Ai a dubu ta miƙo mashi tsintsiyar tare da fita waje da sauri. Shi dai Bappa bai ga abin tsoro a tattare da Jaish ba, ba karya yana da kyau sosai, jinin larabawa, amma da yake shi Bappan yana shiga garuruwa da dama a faɗin Nigeria da Niger har ma da Cameroon, so wani lokaci yana haɗuwa da turawa da larabawa, ya sha ganin kyawawa sosai, har Nigerians kyawawa masu kama da larabawa da turawan ma ya sha cin caro da su, so kyan Jaish bai ɗaga mashi hankali ba, haka ita ma Mahreen. Ko da yake wannan yarinyar kam me ma zai bata tsoro? Ina ga sai idan ta ga aljanin gaske kila ta tsorata.

Sharo ɗakin ya yi ya fito mata da dattin, sannan ya bata tsintsiyar, da sauri ta karɓa ta fara sharar tsakar gidan. Wata yar yarinya da bata wuci sa'ar Mahreen bace ta yi sallama a kofar gidan tare da yaye labulen buhun ta shigo. Amsa mata sallamar Mahnoor ɗin ta yi tare da ɗagowa ta kalleta.

"Adda Mahnoor gwaggo Rabi ta ce in zo in tambayi meyasa baku zo karatun ba?"

Islamiya ce suke zuwa a gidan maƙota kullum daga karfe uku zuwa shidda ake tashi, wata mata ce wadda suke cewa gwaggo Rabi ita ce malamar, naira 50 ake biya duk sati idan ta zago, shi ne kuɗin islamiyar.

"Mahreen ce ta yi barci, ni kuma yau Bappa yana aiki sosai, bai zo wajen kiwo ya karɓeni ba sai yanzu na dawo, shiyasa bamu zo ba, amma zamu zo karatun dare In Sha Allah". Ta bata amsa tare da duƙawa ta cigaba da yin shararta. Tom yarinyar ta amsa mata tare da juyawa da sauri ta koma islamiyar, dan ana can ana ta karatu.

Share gidan tsab ta yi kafin ta fito da wanke wanke ta wanke tas, da alama tana da tsabta sosai, ga nutsuwa. Bayan ta kammala wanke wanken ne ta nufi kitchen, sai da ta share shi tsab, sannan ta hau hura wutar itace ta ɗaura tukunyar ƙasa mai ɗan girma tare da sanya ruwa rabi a cikinta, ta tada wutar sannan ta fito.

Tana fitowa Mahreen ma ta fito daga cikin É—akin Bappa tana zuba uban hamma kamar zata ci babu. "Adda Mahnoor ina abincina?".

"Kai Mahreen daga tashi? Ba batun yin sallah bare ki tuna yau bamu je islamiya ba, bare kuma wanka, ke dai abinci kawai daga tashi? To ga shi a rufe a cikin kitchen, idan kin gama ci sai ki zo mu je gidan ArÉ—o mu duba Nenne".

Tsalle ta yi ta dire kafin ta ce. "Wlh ni dai ba zan je ba, wai ke Adda Mahnoor bama zaki yi murna da Nenne ta tafi ba sai ki ce mu je mu dubata dan ta dawo? Ke wato ma baki damuwa da shegen masifarta ko? Tom ni ban son ta dawo, da sassafe ta tashi mutum da faÉ—anta da awaki, sai ta yi ta zagin awaki da karfi karfi kamar sun ce mata suna jin magana, duk ta bi ta tashi kowa daga barci, ni babu in da zanje, gara ma da Bappa ya kawo wannan aljanin, kinga yanzu dole ta koma gidan ArÉ—o da zama ai, ni kam ma aljanin kyau ya yi mun".

Baki Mahnoor ta saki tare da gwalalo ido tana kallonta, tasan halinta sarai fin hakan ma zata aika, amma abin da ya bata mamaki ta saki baki tana kallonta shi ne cewa da ta yi aljanin ma kyau ya yi mata, wato ya burgeta, ko tsoronsa bata ji ba.

Tana tsaka da tuna Mahreen ɗin ta katseta da cewa. "Adda Mahnoor wlh kumatun aljanin nan kamar irin breadin da Bappa yake kawo mana idan ya yi tafiyar nan, idan kina taɓa kumatunsa zaki ji daɗi".......... Hasbunallahu wani'imal wakil, Mahreen zata kashe mutun da dariya.

Zaro idanu sosai Mahnoor ta yi. "Kumatun nasa kika taɓa? Ke Mahreen ina kike son ki tsaya ne wai? Ai dolema kanki ya rinƙa rawa, aljanu wasa ne, daga gani sun shiga kanki shiyasa baki tsoronsu, dole zan gayawa gwaggo Rabi idan muka je karatun dare, dan ta yi maki addu'a, yanzu dai zoki ci abincin ki je ki yi wanka sai muje wajen Nenne". Ta yi maganar cike da tsoron jin cewa Mahreen ta taɓa kumatun aljani.

Sake yin tsalle ta yi ta dire. "Wlh Adda Mahnoor ni ba zan je wajen Nenne ba, ke ni fa banson ta dawo nace maki".

"Mahreen kina da hankali kuwa? Wato duk nasihar da gwaggo Rabi take yi mana a kan bin iyaye ke bakya ji ko? Kina son Allah ya la'anceki ne? Mahaifiya fa? Wlh tun wuri ki yi istigifari sannan kizo ki wuce ki yi abin da nace maki mu gama aiki mu je wajenta, da take yin masifa da akwaki dake take yi ne? Ba shegen kunnenki na jin gulma yasa kike iya jiyota ba? Ni meyasa bana jin faÉ—ar safen nata da awakin?".

Turo bakin nan ta yi kamar zata sa kuka, cikin kuncin rai na bata son Nenne ta dawo ta nufi cikin kitchen É—in dan ta É—auki abincinta, yadda kuka san Nennen nan kishiyar mamarta ce ba mahaifiyarta ba, wai ta cika masifa.

Cigaba da aikace aikacenta ita kuma Mahnoor É—in ta yi, sai sauri take yi dan ta gama suje wajen mahaifiyar tasu a gidan kansu ArÉ—o kenan, shi ne mahaifin mahaifiyar tasu, kuma shi ne sarkin wannan ruga, kawu yake wajen mahaifinsu kuma, duk dangi ne.

Ita kuwa Mahreen abincinta ta É—auko ta zauna a saman kujera irin na zaman tsakar gidan nan ta fata ci tana turo baki dan bata son zuwa gidan kakan nata, kuma kakan nasu fa yana kaunarsu sosai, dan su kaÉ—ai ne jikokinsa, amma da yake ita Mahreen bata son gaskiya, bata son ayi mata faÉ—a yasa ta tsanesa, dan kawai yana yi mata nasiha a kan ta nutsu.

🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Yau kwana uku kenan da kai baban Zainab makwancinsa, wato gidansa na gaskiya.

Khadija dai shiru babu ita babu labarinta, su kuma dangin babanta basu ma bi ta kanta ba, bama su san tana nan ko bata nan ba, kuma basu damu da su sani ba, sun mayar da hankulansu kan zuwa station da hanyar kotu wai lallai dole sai an biyasu jinin Baban Zee da maman Zainab ta salwantar, sun kafe sam ba zasu ɗaga kafa ba. Sadiq ya ji duk abin da ya faru, amma ya ɓoye ya kasa iya gayawa mamarsu saboda tana da hawanjini haɗe da ciwon suga, yasan in ta ji me ya faru da maman Zainab zata iya haɗiyar zuciya ta mutu, ko hawanjininta ya tashi, shiyasa ya ɓoye mata.

Ya zo Kanon amma an hana shi ganawa da ita, almost kafa uku yana zuwa cell ɗin, amma sun hana ya ganta, tashin hankali iya tashin hankali ya shiga, wannan ba maganace da zai ɓoyewa mamarsu ba, amma ya rasa ta yadda zai iya gaya mata, ko dan ta sanya maman Zainab ɗin a cikin addu'a yakamata ya gaya mata, amma ya rasa hanya, bawan Allah ya rasa mafita.
Chapter 14 · 0% Book details