Sashe 40
Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yau ta kama ranar jumma'a satin baban Zainab bakwai kenan da rasuwa, Hauwa da Maman Haidar suna zaune a parlour suna hira kamar wasu ƙawaye, a yanzu suna shiri sosai, Hauwa ta yi masu mage mai kwanciyar ɗaukar rai, da biyu ta yi shiri da su, akwai abin da take hara ne yasa ta kwantar masu da kai suna zaman lafiya.
Hajiyarsu kuma tana cikin É—aki tana kwance, fama take yi da ciwon zuciya, ga hawan jininta ya taso, so bata da lafiya sosai, ko magana bata iya yi, sai an kwantar sai an tayar, rasuwar baban Zainab ya jefata cikin wani halin da baki ya yi kaÉ—an ya faÉ—esa, Hauwa da maman Haidar basu wani damuwa da halin da Hajiyar take ciki, maman Haidar dama sai abin da Hauwa ta ce take yi, shiyasa bata kula da mahaifiyar tasu, kullum maman Hanif ce take zuwa tana jinyarta, a gida likita yake zuwa ya dubata, maman Hanif ita take zuwa ta bata magani da duk abin da ya dace.
Har yau Hauwa da Maman Haidar basu nemi Khadija ba, Hajiyarsu kuma bata magana a yanzu bare ta ce ina yaran suke, Maman Hanif kam ta san komai, dan har asibitin da Zainab ɗin take kwance ta je wajen ta dubata yafi sau a ƙirga, yadda aka yi tasan komai kuwa shi ne, tun ranar da suka yi kaca kaca da maman Haidar ta tafi bata sake zuwa gidan ba har sai da Hajiyarsu ta kwanta jinya, a ranar ta zo suka je asibiti dan a lokacin jikin ya tsananta sai suma Hajiyar take yi tana farfaɗowa, shiyasa suka je hospital. Bayan sun je anyi duk gwaje gwajen da zasu yi ne aka basu magunguna haɗi da nurse guda ɗaya suka dawo gidan, a nan ne ta shiga ɗakin su Zainab da nufin ta dubasu, sai bata gansu ba dukkansu biyu.
Hankali a tashe ta fito ta tambayi Maman Haidar ina su Khadijah? Maman Haidar ta ce bata sani ba tun da dama ba'a bata ajiyarsu ba. Nan fa ta shiga tashin hankali ta fara tunanin waye zata kira ta tambaya ina suke?.
Can sai Sadiq ya faɗo mata cikin tunaninta, shi ne ta nemi numbersa ta kirasa, da farko har ya ɓoye mata gaskiya, daga baya kuma sai ya tuna cewa ita da maman Haidar akwai banbanci, dan haka sai ya gaya mata gaskiyar abin da yake faruwa.
Tsabar shiga tashin hankali jikinta har kerma yake yi, nan take ta ce ya bata address na hospital ɗin gata nan zuwa, to kunji yadda aka yi tasan batun ɓatar Khadija da rashin lafiyar Zainab, ita kam maman Haidar ko nemansu ma bata yi ba ita da take da alhakin kula da su ma bare Hauwa gayyar tsoɗi.
Sai hira Hauwa da Maman Haidar suke zubawa maman Hanif ta koma gidanta, kamar daga sama suka ga an banko labule an shigo masu cikin parlourn.
Saboda sun tsorata miƙewa tsaye suka yi cikin sauri. Ganin Haidar ne yasa mamar tasa ta ce. "Kai lafiyarka zaka shigowa mutane ɗaki babu sallama? Daga ina ma kake ke? Ina ka fito? Yau fa wajen wata biyu ban sanyaka a idanu na ba, ina kaje!".
A maimakon ya amsa mata maganar da ta yi É—in sai ya ce. "Ni mama ba wannan ba, ina Khadijah? Kin san cewa lokacin aurenmu ya yi ko? Satin nan za'a É—aura auren".
"Ina kaje tukun nan? FaÉ—a mun naji kafin na gaya maka in da Khadijah take".
ÆŠaure fuska sosai ya yi. "Wani waje na je ni da abokaina da nufin mu yi sati biyu, shi ne muka yi wata biyu, dan wajen ta yi daÉ—in, to ina Khadija da kawu suke? Kawu ya zo yau idan an sauko daga sallar jumma'a ya É—aura mana auren kawai". Yana magana kamar yana baiwa mamar tasa umarni.
"Haidar maman Zainab ta kashe maka kawunka, Khadija kuma ina jin cewa tana É—akinsu".
Wani irin ihu ya kurma irin na ƴan daban nan, muryarsa ƙato ya ce. "Kutumar ubancan, lallai yau akwai durun uwa, A'isha ce ta kashe kawu? To akan me? Meyayi mata? Tukun nan ma kisan gaske ko ma wasa?".
Charap Hauwa ta caɓe zancen da cewa. "Tsabar mugunta ce kawai, ta kasheshi mana shi har lahira". Ta kai karshen maganar tare da fashewa da kukan kinibibi da munafurci.
Wani irin kallon rainin wayo ya wurga mata kafin ya ce. "Ke kuma daga ina gayyar soɗi? Kaji munafuka, kina da wani haɗi da kawun ne da zaki tsaya wani ƙaƙalo kukan munafurci? Ke daga ganinki fuskar bakaken munafukai ne da ke, ni mama ki bani amsata me yake faruwa ne?". Cikin bokarewa ya yi maganar babu respect ko kaɗa.
Tsit Hauwa ta yi, ta haÉ—iye kukan gulmarta, dan Haidar dai bata ga alamar mutunci a tattare da shi ba, jahilci cike da kai yanzu zai yi mata mummunar aiki, tasan matasa irinsu sarai, dan haka sai ta kama bakinta ta yi shiru.
Mamarsa bata ɓoye mashi komai ba ta zayyana mashi yadda abin ya faru kamar yadda makira Hauwa ta zayyana masu, da karya da gaskiya duk ta kwasa dama ta gaya masu, dan haka ita ma Maman Haidar haka ta kwasa ta gaya mashi.
Wani irin buga center table na tsakiyar parlourn ya yi da karfi, cikin fusata da É—aga murya ya fara zazzaga jajjagen masifa. "Kutumar uban can, wlh in na yarda Allah ya tsinemun, kamar yadda A'isha ta kashe kawu nima sai na kasheta, wai wace shegiya ko shegen ne ma ya kaita kotu? Ai barin mun ita zasu yi na zo na feÉ—e shegiya, wlh na rantse da Allah sai ta fito daga prison É—in nan na yi mata yankar rago, su ma su Khadijah É—in ba barinsu zan yi ba, Æ´an iskan banza, su ma mugun iri ne sosai, basu da amfani a cikin al'umma, kashe su shi yafi". Yana kai karshen maganar ya nufi É—akunan gidan yana tambayar ina su Khadijah zai kashesu dan basu da amfani, ya fasa batun aure.
Kun ga kaɗan daga cikin aikin jahilci kenan, Allah da kansa baya hukunta wani da laifin wani, laifin wani baya shafar wani, amma shi Haidar saboda jahilci da ya yi mashi katutu shi ne yake neman su Khadija ya kashe su dan mahaifiyarsu ta yi laifi bisa kuskure. Kai Allah ka buɗa mana ƙwaƙwalwarmu ka bamu ikon neman ilimi ka rabamu da jahilci.
Sai kiransa mamarsa take yi a kan yazo kada ya taɓa su Khadija, amma ina ya yi gaba sai faman banke kofofi yake yi yana shiga cikin ɗakuna shi a dole sai ya fito da su ya kashesu.
Ganin basu cikin É—akun nan sai kakarsu dake kwance kamar gawa ne yasa ya fito ya dawo parlourn ya fara tambayar mamar tasa me ya samu kakarsu kuma?.
Nan fa ta sake gaya mashi ai saboda mutuwar baban Zainab ne yasa hawan jini da ciwon zuciya suka kamata. Sake haukace masu ya yi yana faÉ—in ai ga irinta nan, wlh ba zai bar gabaÉ—aya dangin maman Zainab ba, duk sai ya kashe su kamar shi ne dama ya kawosu duniya.
Sai tausarsa mamar tasa take yi, amma ina sai kara haukace masu yake yi, har da wani cewa zai kwashi abokansa su tafi Kaduna su je su farwa maman maman Zainab É—in su kasheta, sannan ya kashe Sadiq kafin ya san ta yadda zai yi ya fito da maman Zainab daga prison ita ma ya kasheta.
Hauwa kam abin nema ya samu, daɗi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, ita gani take yi idan ya kashe mata Khadija and Zainab shikenan ta ci dukiya, ita dai matsalarta abin duniya.
Suna tsaka da wannan hayaniya kwatsam ba zato ba tsammani suka ji sallama a bakin kofa. A tare suka kai kallonsu wajen, ba kowa bace face Khadija.
Binta da kallo suka fara yi, dama can su basu san bata nan ba, basu san da ta ɓace ba bare su yi mamakin dawowarta, kallon tuhumama suke binta da shi, tuhumanta suke yi a kan ina kuma ta je? Da a tunaninsu ai suna ɗaki basu fitowa sai in zasu girka abin da zasu ci ko makancin haka ne suke fitowa, kuma basu haɗuwa da su ko a kitchen amma basu damu da su san wani hali suke ciki ba bare har su je ɗakinsu su dubasu.
Sanye take da doguwar riga abaya maroon color mai matuƙar kyau da tsada, riga ce mai tsadar gaske, takalmar dake kafafunta ma masu tsadar gaske ne, ta yafa gyalen rigar a kanta, hannunta na riƙe da irin school bags ɗin nan mai matukar kyau, bata goya a back ɗinta ba sai ta riƙe a hannunta, ta ƙara kyau ta kuma yi haske sosai, ta yi ƙiba matuƙa, kamar ba Khadija ba, gabaɗaya ta canza.
Kanta Haidar ɗin ya yi da nufin ya aiwatar da kudurinsa na kashesu dukka, da sauri mamar tasa ta yi ƙoƙarin riƙesa dan kada ya ɓallo masu ruwa, ba hankali ne da shi ba, kada ya jajumo masu abin da ba zasu iya ba.
Hauwa kuwa cewa take Maman Haidar É—in ta kyalesa ai gaskiya ya faÉ—a, su Khadijah mugun iri ne, sun tsotsa a nono, dan haka su rabu da shi.
Maman kuwa ta ce a'a bata shirya É—anta ya tafi prison ba, dan haka ita bata yarda ya kashe kowa ba.
Kin yarda ya yi shi kuwa, ya kafe sai ya kashe su, marika ya fara kaiwa Khadija É—in kamar an aikosa, bata ko motsa daga in da take tsaye ba, da alama zuciyarta ya rigada ya bushe, da alama ita ma mutuwar take da muraÉ—in ta yi.
Dukan gaske ya fara kai mata tana tsaye tana kallonsa ko gezau, sai ƙoƙarin riƙesa mamarsa take yi. Kwashe kafafun Khadija ɗin ya yi da nasa kafafun ta zube ƙasa, still dai kallon face ɗinsa take yi ba tare da ta ce mashi ko uppan ba, kuma bata motsa ba, sai dai ruwan hawaye da take yi saboda zafin dukan da yake yi mata.