← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 119 OF 211

Sashe 119

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nenne ma bata yi barci ba, kwana ta yi tana tsinewa tunanin gwaggo na ce wa a haɗa Mahnoor and Jaish aure, ga shi yanzu tun ba'a je ko'ina ba ya fara tare masu faɗa, a kan Mahreen ya daki Faisal da safe, to ina ga kuma Mahnoor da take matsayin matarsa? Zai iya kisa a kanta kenan?. Abin ya tsaya mata a rai matuƙa, duk sai ta ji kamar ta kashe kanta, sai tunanin ta yadda zata bi ta ruguje wannan aure take yi, ta yi wa kanta alkawarin ko ana ha maza ha mata wlh sai ta ruguje wannan aure ta mayar da yarinya ƙaramar bazawara ko 15 years bata cika ba, sannan ta ƙuntatawa rayuwarta, shi ne next plan ɗinta.

Washegari da safe daga bappa har Nennen idanunsu a kumbure suka wayi gari, saboda rashin samun barci, gara ma shi bappa a kan dadduma gaban Ubangijinmu ya kwana, ita kuma fa? A tawagar shaiÉ—an ta kwana?

Idanun sun yi jajir. Mahnoor da bata samu barci daren jiya bane na asuba ya É—auketa bayan sun yi sallah, kun san shi fa barci ba'a cin bashinsa, idan ka ci sai ka biya a time É—in da baka yi zato ba, aikuwa tana sallah tana gyangyaÉ—i, da kyar ta iya samu ta daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallarta dai'dai.

Daga nan ta ɓige da barci, tana tsaka da barcin ne ta ji saukar duka a jikinta ta ko'ina da bulalar itaciyar gwaiva.

A razane ta miƙe, bama ta yi ihu ba dan tasan wanenen mai dukan nata, waje kawai ta fita da gudu. Nan take hawaye suka cika mata idanu tab da kwallah. Aikinta ta fara yi tana sharar kwallah da ya fara bin saman ƙuncinta.

Karfe shidda ne dai'dai a lokacin. Tsintsiya ta ɗauka ta fara ƙoƙarin share gidan tas. Ita kuwa Nenne ta koma ɗaki bata ko kalli in da Mahreen take ba, saboda ƴarta ba ƴar wahala bace a cewarta, ƴar gata ce ta sha barcinta.

Bayan ya gama sharar sai ta kwashe dattin cikin wani marfin langa ta nufi bayan gida zata je ta zubar a can wani rami wajen dabbobinsu bayan ta gama sharan kenan, dama a nan suke zubar da shara kullum, tana yi ma tana kuka baiwar Allah, ga yunwar safe da take ji, idanunta ita ma a kumbure saboda rashin barci jiya, jikinta duk babu kuzari, zuciya a raunace, tana tafiya tana jan kafafu kamar zata kifa ƙasa. Garin yana haɗe bakin kirin da hadari, yau da alama ruwa zasu sha ba kaɗan ba.

Tana zuwa ta juye sharar a ramin, juyowarta ke da wuya ta ci karo da shi a in da ta buga kanta a saman kirjinsa, baya kaÉ—an ta É—an yi dan ta samu damar ganin face É—insa.

Ko yaushe ya tashi barci har ya fito ya zo cikin dabbobin zai tatso nono? Ta jefa wa kanta tambaya. Ƙasa ta yi da kanta tare da cewa. "Hamma ina kwana?".

Bai motsa ba bare tasa ran ya jita, hannunsa riƙe da bokiti wanda ya tatsi nonon a ciki. Kyawawan yatsun hannunsa ya ɗago ya ɗaura a saman kumatunta a in da ya nuna hawayen face ɗinta tare da yi mata alama da hannun na meyasameta da sanyin safiyar nan take kuka haka?.

Ta gane me yake nufi, dan haka yake tambayar Mahreen ma idan ya ganta tana kuka, dama dayawan lokuta tana kukan yunwar safe idan ba'a gama abinci da wuri ba, ai Mahreen manyan ƙasa ne.

Girgiza mashi kai ta yi alamar babu abin da ya sameta.
Zuciyarsa ce ta zarga mashi Nenne, dan yasan ita ce mai sanyata aikin sassafe kuma tana zazzaga mata masifa. Wucewa ya yi izuwa cikin dabbobin ba tare da ya sake bi ta kanta ba.

ÆŠan binsa da kallo ta yi tana mamakin hali irin nasa, wani irin mutun ne a murÉ—e haka? Abin dai sai a hankali, shi baya tambaya sau biyu, idan ya yi É—aya ba'a amsa ba shikenan kai ka jiyo, gaskiya yana da abin mamaki.

Sa kai ta yi ta wuce, a hankali take tafiya tana goge hawayen nata. Tana shigowa ta sami Nenne a tsakar gida, a lokacin kuma bappa ya tafi gidansu Hamma Faisal ya je duba jikinsa.

Wani irin tsawa da Nennen ta daga mata a kan ta je ta jima ne sai da yasa ta ji duk wani kasala da yunwa da take ji sun gudu, nan take jikinta ya soma kerma.

"Uban me ya tsayar dake daga zuwa zubar da shara?!" Shi ne tsawar da ta daka mata.

Murya a sarƙafe ta furta. "Hamma na tsaya gaisarwa". Har lokacin hawaye suna cigaba da gudu a saman face ɗinta.

Gadan gadan ta tinkarota da nufin ta fara aikin da ta saba na jibgarta, dan a cewarta wato yanzu ta yi girman da har zata iya bata amsa idan tana magana, kuma dai kuna ji ita ta tamnayeta me ya tsayar da ita, ta bata amsa kuma abu ya zama bala'i, wato dai idan mutun mugu ne kawai ka barsa, dan kome zaka yi mashi sai ya gallaza maka.

Wani tray irin na kwano na mutanen da É—in nan ta rarumo a fujajan zata maka mata a kai dan tsabar bakar zuciya irin na matar nan, ga jikin tray É—in duk a farfashe ya yi lamba, wanda kuma kun san lambar jikinsa tsartse ne da yana iya fasa fatar jikin mutun ya shiga cikin nama, yana yi wa mutum illah sosai.

Amma tsabar mugunta sai ta rarumo shi zata rafka mata a kai, ita kuma tana tsaye baiwar Allah, da yake tasan ko ta gudu ma ba tsira zata yi ba, sai dai ta kara wa kanta wani bala'in, dan idan ta gudun ma dole a gidan zata dawo ta kwana, idan ta dawo kuma ninninka mata azaba zata yi, so is better for her to stay kawai.

Da iya karfinta ta É—aga trayn zata buga mata, runtse idanu ta yi gam tare da sanya hannu ta tare kanta da fuskarta tana jiran saukar trayn a kan nata.

Shiru bata ji an rafka mata ba, hakan yasa ta É—an motsa zara zaran eyelashes É—inta tana son buÉ—e idanun ta ga me yake faruwa bata ji anfasa mata kai na?.

Aikuwa tana buɗewa cak ya riƙe hannun Nenne da tray ɗin gabaɗaya. Tsabar tsoro yasa Nennen ta yi suman tsaye, yau ga aljani ya riƙe mata hannu ko in ce maye da suke ce mashi.

E lallai ba shakka yau Nenne taga bone, maye ya riƙe mata hannu ba kanta, me kuke tunanin zai faru a wannan ƙauye? Ya kuke ganin zamansu zai kasance a yanzu? Shin Nenne zata iya samun nasarar raba wannan aure kamar yadda ta shiga ta fita ta haɗa kuwa? Me makomar Jaish? Shin zai yarda ya zauna da Mahnoor matsayin mata kuwa? Dan ni dai ban ga alama ba!. Akwai cakwakiya fa sosai, yanzu muke ƙoƙarin afkawa cikin littafin mu gadan gadan, ku gyara zama akwai......... Ba sai ma na faɗa ba, muje dai zuwa.
________________________🔥🤯

FRANCE🔥🌹

Hakimce yake cikin katafaren office ɗinsa, ya ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya, sanye yake cikin shigar ƙananan kaya wandon jeans milk color and flannel shirt coffee color masu bala'in kyau da tsada, ya ɗaura denim jacket a saman kayan nasa, dan kowa yasan ƙasar faransa suna da balai'n sanyi mai dusar ƙanƙara, mai daskarar da abu, sai da jackets manya manya ma kuwa.
Ya fito a ainahin Smart É—insa, ko mai kiyayyarka da shi sai ka amincewa ranka shi É—in smart ne, komai ya yi guy É—in nan dai'dai take tafiya da shi.

Jiga jigan jami'ai ne ta ko'ina suke ta shawagin shige da fice, wani irin sanyin Ac da kamshin office perfume ne yake tashi a office É—in. A ainahin office É—insa yake ba'a ma'aikatan haÉ—a nuclears É—insa ba, nan yana bakin aikinsa ne.

Wayarsa dake saman desk É—in gaban nasa ne ta fara ruri alamar shigowar kira. Yana tsaka da yin aiki ne ba kama hannun yaro.
Jajirtattun jami'ansa guda ɗai ɗai ɗai har guda shidda ƙasar America ta kama masu a matsayin ƴan leƙen asiri ƙasa da ƙasa, kuma hakance, leƙen asiri suka je yi Allah ya bawa American dama suka kamasu, sun jima suna yi mata leƙen asirin kamar yadda ita ma take yi masu, sai dai Smart hege ne na karshe, maye ne a basira, duk wasu ma'aikatansa ya zuba masu matakan tsaro na na'urori, harta na'urar ɓadda kafa yana da shi wanda shi da kansa ya ƙirƙireta, amfaninta shi ne ba'a isa a bibiyesa a lamuransa ba, komai bala'in ƙasa haka zata gansu ta barsu.

Da su da America fa ana mugun tare, kawaye sosai, amma dukkansu basu yarda da juna ba, suna leƙar asirinta ita ma tana leƙar nasu, kunga duk suna munafurtar juna ta ƙarƙashin ƙasa kenan, a fili kuma idan suka haɗu sai kuga kamar zasu cinye juna saboda so, amma American ce ta fara leƙar asirinsu shiyasa suma suka koya, sai dai America ɗin ko ta leƙi asirin nasu bata samun komai, duk min karfin na'urar da zata yi amfani da shi bata iya hango komai daga sararin samaniyarsu, har tauraron setline system suka sanya dan su leƙi asiri amma ina basu iya ganin komai, hege Smart ya juyar masu da kwakwalen kai.

Hankalinsu ya gaza kwanciya dan suna ganin kamar tabbas yadda Allah ya baiwa Smart wannan basira daddynsa ba zai barshi haka ya tafi a banza ba, suna zargi lallai lallai yana amfani da ƙwaƙwarar nan tasa suna gina ƙasarsu, shi ne yasa suke leƙe leƙe ko zasu iya ganin ko da ɓirɓishin makami ne haka irin abin zargin nan.

Sai dai basu san Smart ya wuce tunaninsu ba, duk ya rufe komai abinsa.

Sau da dama jami'an Smart ɗin suna zuwa laƙar asiri ba'a taɓa kamasu ba sai yau, dama ai ba kullum ake kwana a gado ba.

Yau dai an kamasu shi ne ya É—aga hankulan sauran jami'an, dukkansu jira suke yi suga matakin da zata É—auka a kan jami'an nasu, kansa ya É—au zafi, sai aiki yake yi tukuru dan ya yi amfani da basiransa wajen kwato jami'an sa cikin sirri, baya son maganar ta baza duniya.
Chapter 119 · 0% Book details