← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 211

Sashe 5

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saukar wani irin gigitattacen mari da ya ji a saman ƙuncinsa ne yasa ya dawo daga duniyar tunanin da ya afka. Nan take ya kai hannunsa ya dafe kumatun nasa tare da sauke kallonsa a kanta, tun da yake da ita ko da sukan wasa bata taɓa dukansa ba, wannan mari da ta yi mashi ya kara tabbatar mashi da abin da yake zargi na cewa bata da gaskiya ne yasa take ɓoye rayuwarsu ga kowa, rashin gaskiya ya bayyana karara a tatare da ita, in dai kuwa haka ne yau sai ta gaya mashi wanenen shi wanene babansa? Wani ɓangare na zuciyarsa ce ta amsa mashi da yes kada ya yarda sai ta gaya mashi wanenen shi?.

Cikowa tab idanunsa suka yi da kwallah saboda zafin marin da ta dalla mashi, marinta ba wasa ba, akwai tsananin zafi. Da yake fatarsa akwai haske hakan yasa shatin yatsunta biyar da Allah ya bata suka fito ɓaro ɓaro a saman face ɗin nasa. Wani irin raɗaɗi zuciyarsa take yi mashi, ji yake tamkar an ɗaurata a saman wuta. Dannewa ya yi tare da furta.

"Mamma please ki barni na je na cece rayuwarta, idan ta mutu me zan cewa ƴar uwarta Sweetie? Idan mum ɗinsu ta bayyana ta tambayeni amanar da ta bani me zan ce mata? Ni kai'na nasan idan ta mutu nima ba zan rayu ba, in dai kina sona da gaske to ki barni na je na nemota!". Yana kai karshen maganar wasu siraran hawaye suka fara ganganrowa a saman ƙuncinsa, ba kukan marin da ta yi mashi yake yi ba, kukan rashin Pretty ya fara yi, idan mamma bata barshi ba da alama zai iya mutuwa, da alama Pretty ce rauninsa dan ga shi duk jarumtarsa yau a kanta yana kuka!.

"Kamran ba in da zaka je, kenan dama kullum wajensu kake zuwa? Who're they? Har amanarsu kenan aka baka? A ina kasan amana? Who told you this word?".

"Mamma ki bari idan na je na nemota na dawo sai mu yi magana, please kada mu tsaya magana a yanzu ta yi mun nisan da ba zan iya ganeta ba, duk wani lokaci da zamu ɓata a nan ki sani rayuwar Pretty ce taka cikin haɗari, kin fa san yadda Forest ɗin nan yake, please mamma........."

Tsawar da ta daka mashi a kan babu in da zai je ne yasa ya haÉ—iye sauran maganar dake bakinsa bai amayar ba.

"Kamran kamar yadda na gaya maka tun farko babu kai babu mutane to hakance har yanzu, babu ruwanka da mutane, ko mutuwa mutun zai yi a gabanka ka tsallake ta kansa ka wuce, babu ruwanka da kowa, ni kaÉ—ai ce kake da shi a duniya, haka kuma zamu cigaba da rayuwarmu, dan haka babu in da zaka je, ka wuce mu tafi!!". Cikin É—aka murya ta yi maganar, da alama ta fara hasala sosai.

"I can't go anywhere without seeing my Pretty! Mamma meyasa kike yin hakan? Kenan nima kina son idan wasu suka ganni ina bakin mutuwa su tsallekeni su wuce ba tare da sun taimaka mun ba?..........."

Katse shi ta yi da cewa. "Kai ba zaka mutu ba! Kai daban kake da mutane, babu wanda ya isa ya kasheka, ba mutun kake kamar sauran mutane ba, dan haka kamar yadda na ce babu in da zaka je to babu in da zaka je, ka wuce mu tafi, babu mutuwar da zaka yi da har mutane suki taimakonka!!". Yanzu ma a kausashe ta yi maganar, da alma ranta ya fara ɓaci sosai.

"Mamma na gaya maki ni ba zan je ko'ina ba sai naga Pretty, amanatace, bazan taɓa bari rayuwarta ya salwanta ba, dan haka ki tafi kawai ni zanje nemanta, she's my wife my everything, mum ɗinsu ta bani aurenta, ita ce bugun numfashina, idan har kina son na cigaba da yin numfashi a duniya to ki barni na je na nemota kada ta yi mun nisa, please mamma ki fahimceni, nasan halinta sosai, yanzu haka tana can tana gudu tana kara afkawa cikin daji, kada ta je ta afaka wani wajen, please ki tausaya mana.....".

Katse shi ta sake yi da cewa. "Waye ya gaya maka aure? Waye ya baka wannan kalmar? Wanenen ya gaya maka me mata yake nufi? Yaushe kasan soyayya? Wani maci amanar ne ya gaya maka dukka wannan?". A karo na biyu mamaki ya bayyana a saman fuskarta.

Gyara tsayuwarsa ya yi, ido cikin ido ya kalleta, babu ko shakka, duk wasu shakkarta dake cikin kwayar idanunsa sun kau, cike da rashin tsoro ya furta. "Okey mamma daman kenan da gangan kika ɓoye mun dukka waɗan nan abubuwa da kika tambayi waye ya gaya mun su? Kenan kin san komai kika reneni cikin duhun kai?! Sai kika koya mun ilimin da ba amfanata zai yi ba, wanda zai amfaneni kuma sai kika ɓoye mun kika ki sanar da ni, to amma kin tabka babban kuskure da kika koya mun reading, na iya karatun da zan karanta storys, sannan kin yi kuskuren ajiye litattafai a ɗakinki da har na gani na karanta, ni yanzu dukka bama wannan ba, ki gaya mun ina babana yake tun da kin san komai......."

Tashin hankali, wani irin zaro idanu ta yi, bata taɓa zaton abin zai kai masu haka ba, wani irin bugawa da zuciyarta ya yi ne yasa cikin hanzari ta dafe saitin kirjinta, kanta har juya mata yake yi jin ya ambaci ina babansa? Nan take ta ji jiri na ƙoƙarin ɗibarta.

"Ki bani amsata! Where's my father? Yau ina son sanin wanene ni?!".

"Kamran ni kake yi wa magana haka?". Babu ko shakka ya gyaÉ—a mata kai. "Yes Mamma ke nake yi wa magana haka, kawai amsa my questions...."

Wani irin zufa ne ya fara tsastsafo mata a gefe da gefen face ɗinta, ji ta yi duniya ya yi mata zafi, nadamar hanashi tafiya neman Prettyn da ta yi ta fara yi, yanzu ga shi allura tana ƙoƙarin tono mata garma.

"Kamran baka da wani baba sai ni, ni ce kaÉ—ai kake da shi, dan haka kada ka sake yin magana a kan hakan......"

"Mamma i knew everything now! Mace bata taɓa haihuwa ita kaɗai! Dole sai da namiji! Dan haka tell me where's my father?!".

Shiru ta yi ta kasa iya sake buÉ—e baki, ta rasa me zata ce da shi.

"Mamma ki bani amsar ina babana!!......". Ya faÉ—a da karfi.

Katse shi ta yi cikin É—aga murya. "Idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu, zaka mutu Kamran....."

ÆŠan zaro idanu ya yi yana kallon yadda ta yi maganar cikin tsarguwa da alamun rashin gaskiya ya bayyana sosai a tattare da ita.

"Mamma koma me zai faru ni dai ki gaya mun ina babana? Wanenen ni? Ina familyna suke! Yanzu duk nasan komai".

"Kamran wai wani maci amanan ne ya gaya maka dukka wannan? Wani azzalumi ne yake son raba uwa da É—anta?! Wani bakin mugu ne wannan?! Waye ya ce maka kana da baba? Waye ya koya maka wannan karatun?! Ka gaya mun shi!". Cikin tsawa ta yi maganar.

"Mamma ni kawai ki faÉ—a mun ina babana? Idan kika faÉ—a mun zan faÉ—a maki daga baya sai ki yi duk tambayar da zaki yi, yanzu dai ina babana? Wanenen ni".

To fa yanzu an bar maganar zuwa neman Pretty ma, abu ya ɗau zafi kenan, mamma ta tonawa kanta bala'in da yake ƙoƙarin fin karfinta, saboda kafiya da kafurar zuciya irin tata ga shi yanzu ta ja wa kanta yaronta na cikinta yana jayayya da ita, abin da bai taɓa yi ba, bata taɓa yin magana ya tsaya yana mayar mata da martani ba sai yau, yau ɗin ma ya tsaya yana kallon cikin kwayar idanunta yana faɗa mata magana dai'dai gwargwado, Hasbunallahu wani'imal wakil, duk abin da ya faru ita ta jawa kanta, ai yaro ba'a yi mashi kafiya irin haka, barema shi da ya girma har haka? Ai yama yi kokarin na danne son sanin wanenen babansa da ya yi na tsawon lokaci, kowani ɗa zai so ace ga babansa a tare da shi suna zane cikin farinciki, amma saboda biyayya da kaunarta da yake yi yasa ya danne bai buƙaci lallai sai ta faɗa mashi in da baban nasa yake ba, ya hakura ga shi yanzu ta ja yana fito na fito da ita a kan hakan.

Wani irin yawun wahala ta haɗiye, ji take maƙogoronta ya yi wani irin bushewa da jin tambayoyin ɗan nata, yawun bakinta ya kafe kamar mai yin azumi, da kyar take iya kakalan yawun ta haɗiye, da kyar ma yake wuce maƙogoronta, ji take maƙogoron nata kamar an toshe mata shi ne.

"Kamran idan ka sake magana a kan babanka zaka mutu nace maka, mutuwa kuma mafi muni a rayuwa, kamar yadda ka taso baka san kowa ba, sai ni, to haka zaka riƙe ka manta da duk wasu tunanin banza".

"But Mamma why? I want to know my father ko da kuwa hakan ce zata zama sanadiyar numfashina na karshe, just tell me where's he? Ni zan je in da yake koda kuwa ya fi wuta zafi dole na tinkaresa!! Na kusancesa!!".

Tsawa ta daka mashi mai sauti, cikin fusata, idanunta sun kaɗa sun yi jajir, jijiyon kanta har wani mimmikewa suka yi, da alama ranta ya kai kololuwa wajen ɓaci, har wani huci take yi kamar zakanya. "Kamran ina gaya ma zaka yi mutuwar walaƙanci in dai ka sake yin magana a kan babanka! Kai ba mutun ne kamar kowa ba! Kai ba kamar sauran mutane kake ba! Kai na daban ne, farautarka ake yi kamar yadda ake karautar ruwa a sahara mai tsananin zafin rana! Zaka mutu idan ka fita! Zaka! Dan haka ka tsaya a in da na tsayar da kai!!".

"Mamma i can't! I can't gaskiya! Idan kuma kina son na bi maganarki so tell me who I am?! Where's my father and my family?! Why are you hiding our life anytime?! Am tired! Am tired Mamma! I want to see my father and my family, cos I can't stay with you again! Tafiya zan yi na nemo babana and Prettyta even wannan shi ne ganina dake ta karshe!"......... Tashin hankali.
Chapter 5 · 0% Book details