← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 211

Sashe 53

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shi kansa Abbie sai da ya ji wani irin tausayin maraicinta ya soki zuciyarsa, bayin Allah suna da zuciya mai kyau suna kuma da zuciyar kaunar marayu, nan take suka ji kaunar Leesharh É—in ya kamasu, shi kuma Bilal da hankalinsa baya kan hiran nasu sai bai ji komai ba, gabaÉ—aya hankalinsa kacokam yana kan Ramish.

Riƙo hannun Leesharh ɗin Abbie ya yi tare da zaunar da ita a ɗayan gefen nasa, wlh Abu Abdussalam sarkin kaunar yara ne, duk ƴaƴan King Zuhair da ya tattare suka dawo gidansa bai ishe shi ba, har Auta Zunaira son ɗauketa yake yi King yaki yarda, shi fa bai ki ace gidansan nan a cike yake da ƴaƴansa ba, sai kuma Allah bai bashi aihuwa dayawa ba, ƴaƴansa uku ne kawai a duniya, shiyasa ya kwaso ƴaƴan King, bai ma ki a ƙara mashi wasu ba.

"Rizwan bani handkerchief a wajen kan nan". Cewar Abbien. A hanzarce ya ciro daga aljihunsa ya miƙa mashi, gogewa Leesharh ɗin hawaye ya karɓa ya fara yi yana bata hakuri, nan take ya ji yana kaunar yarinyar, ji ya yi gaskiyar saboda maraicinta shi zai maye mata gurbin mahaifinta, dan gaskiya yana son ƴaƴa mata sosai, amma Sharifat kawai Allah ya bashi, dan haka yanzu a ransa ji yake bayan Sharifat ya samu Leesharh.

A ɓangaren Ummie kuwa haka kawai ta ji wani irin tsanar Leesharh ɗin ya kamata, ko me dalilinta Allah kaɗai masani komai da komai na fili da na ɓoye. Shi ma Rizwan da yake yana da saukin kai sosai sai ya ji yana kaunar Leesharhn, sai ya ji ta bashi tausayi sosai, ƴar yarinya da ita ta rasa iyayenta, Allah sarki ita da ya kamata a ce yanzu tana tare da iyayenta tana jin ɗumin jikinsu, amma saboda babu su gata a in da ma bata sani ba ta zo aikatau, to daga yau gaskiya ta bar yin aikin komai duk da dama ba wani aikin kirki take yi ba, amma daga yau ta zama ƴar gida ita ma, kuma zai riƙeta matsayin kanwa kamar yadda ya riƙi Sharifat, haka yake tunani a cikin ransa.

Shi kuwa Guyson da ya fisu zuciyar tausayi sosai har da hawaye ya yi mata, shi dama already tausayi take bashi, tun da ya ganta an kawota gidansu da sunan aiki tun kafin ma yasan ita marainiya ce yake tausaya mata, dan a cewarsa ƙaramar yarinya kamar wannan ta zo aiki ai akwai tausayi.

Shi kuwa Omaid sarki bakar zuciya yana fita waje harabar gidan ya nufa, kai tsaye in da Obaid yake ya nufa, haushin da ya ji a cikin gida zai je ya sauke a kan criminals É—in nan......... Tab ni kam na ce criminals kunga ta kanku.

Yana shiga ya samu Obaid yasa jami'an Swat guda biyu sun ɗaure mashi criminals ɗin a jikin wasu kujeru da suke ɗaure masu laifi su yi masu tambayoyi, yasa an ɗaure mashi su kamar wani babban mutun ya ɗauko chair ya zauna a gabansu, kai daga ganin yadda ya zauna a gabansu zaka fahimci lallai suna samun horo a makaranta yadda ya kamata, waɗan nan yara wlh idan aka yi wasa sai sun fi Ramish ɗin da ya kaisu school ɗin ma sanin aiki yadda yakamata, dan su baiwarsu ta musamman daga Allah ce, idan suna yi abu sai ka rantse da Allah sun haura shekaru 25, suna karatu ne yadda yakamata, duk wani dabaru da zasu yi wa mai laifi ya faɗi gaskiya sun san shi, gasu da iya zaƙulo mai laifi a cikin dubban jama'a, da ido idan suka ga maras gaskiya suna iya ganesa, kai yaran Momma ba dai ƙwaƙwalwa ba, sun gada baiwa daga iyaye, kada kuso ku ki ganin Guyson a class, bai taɓa tsalleke first class ba, gabaɗaya ƴaƴan Momma a school ɗinsu da su ake kwantance ta kowace halaiya, idan karatu ne da su akeyiwa sauran student kwatance, idan ma da rashin ji ne da su ake kwantance, mugunta da su ake kwantance, kyan zuciya da iya kyauta dukka dai su ne, su fa ba abin da basu iya ba idan sun ga damar yi, in basu ga dama ba ba uncle ba ko uban waye a school ɗin nan bai isa ya sakasu yi ba, ga su kuma tun daga farkonsu har zuwa kan Auta Zunaira shegen mugun shiga rai ne da su, ga ɗan banzan farinjini kamar su suka bawa kansu, komai muguntar da yaran momma zasu yi maka ba zaka dai'na sonsu ba, saboda shegen shiga ransu, kamar ba lafiya ba, haka ita ma Mommar take.

Tambayarsu Obaid yake yi a kan waye ya turosu su kashe masu yayansu? Yadda kuka san da gaske kaunar Ramish É—in suke yi, kawai tsabar iya mugunta ne, amma ba wani kaunar Ramish da suke yi, hasali ma haushinsa suke ji, dan yana takura masu.

Chair shi ma Omaid ya ɗauko ya zauna, jami'an swat dake gadin room ɗin sun zuba idanu suna kallo yara masu aiki da cikawa, gani suke yarannan kamar sun fi su sanin aikinsu wlh, abin har mamaki yake basu, yadda kuka san wasu manya general's na ƙasa baki ɗaya.

Shiru criminals ɗin suka yi suka ki amsa masu tambayarsu, sake maimaita masu tambayar Obaid ya yi a karo na uku yanzu kenan. Habawa Omaid da ya kwaso ɓacin rai daga cikin gida ne ya miƙe tsaye tare da sanya kafarsa da karfi ya taƙa ɗayan criminal ɗin a kirjinsa, ai kuwa baya baya ya yi shi da kujerar tasa suka zube ƙasa, wani irin belt na kaca ya ɗauko, jikin belt ɗin duk kifitoyi masu zafi.

Kansu ya yi da belt ɗin, cikin fusata ya fara zabga masu shi a jiki, ba bu imani bare tausayi, yadda kuka san su fa aka kawowa su hukuntasu, duk in ya zabga masu wannan belt ɗin sai waɗan nan kifiyoyi sun caku har cikin namar jikinsu, amma duk da hakan bai sa tausayi ko mai kankantar ta bayyana a saman face ɗinsu ba, sai ma miƙewa da Obaid ɗin ma ya yi ya je ya tattaro wasu kayan hukunta masu laifin da ya yi.

Jami'an dake wajen ne suke faÉ—i a ransu cewa zaku yi ku gaji ne dan har shi kansa Bilal ya yi iya yinsa criminals É—in su buÉ—i baki su yi magana amma sun ki, da alama irin criminals masu sayar da rayukansu a kan aiki ne, kun san akwai waÉ—an da su idan kuka É—aukesu su yi maku aiki to fa idan aka kamasu asirinsu ta tonu ko kashesu za'ayi ba zasu buÉ—i baki ba bare ma har su tonawa wanda ya sanyasu aikin asiri, su sai dai a kashesu, amma ba tona asiri, to irinsu ne waÉ—an nan, daren jiya saura kaÉ—an Bilal ya harbesu da bindiga saboda bakincikin sun ki yin magana.

Sosai Omaid ya farfashe masu jiki jini yana ta zuba, sun galabaita iya galabaita, sun wahala, amma duk da haka babu alamun zasu buÉ—i baki su yi magana.

Sai da ya ji ya gaji ne ya rabu da su ya koma saman chair É—insa ya zauna yana mayar da numfashi, shi kuma Obaid cewa da jami'an dake wajen ya yi su zo su É—aga masu criminals É—in su mayar da su su zaunar da su.

Ba musu suka zo suka É—aga masu su tare da kujerar tasu suka zaunar da su. Zama suka yi suna fuskantar juna, sai wani irin numfashin azaba sama sama criminals É—in suke yi tamkar ba zasu rayu ba, sun ci bakar wahala Æ´an banza, daren jiya Bilal ya jibgesu, sassafe kuma su twin's su É—aura nasu.

Plastic and cotton Obaid ya ɗauko, miƙewa ya yi ya koma ta bayansu, da karfi ya damki gashin kan ɗaya, jan gashin ya yi baya da karfi dan dole guy ɗin ya ɗaga kansa sama, babu alamar tausayi ko kaɗan a saman face ɗin yaran nan, yadda kuka san ba rai suke azabtarwa har haka ba. Cutton ɗin ta cusa mashi a baki kafin ya bi da plastic ɗin ya manne mashi baki, shi ma ɗayan haka ya yi mashi.

Bayan ya kammala ya koma saman chair É—insa ya zauna, yana zama ya dubi Omaid ya ce. "Me and you zamu ga waye zai fara sanya nasa criminal É—in ya buÉ—e baki ya yi jawabi". Yana kai karshen maganar ya sanya hannunsa ya fara fito da wasu mugayen makamai daga cikin box É—in da ya É—auko.

Small silent pistol gun Obaid É—in ya É—auko, saita babban yatsar criminal dake gabansa na kafa ya yi, fasa mashi yatsar da bulle ya yi ko a jikinsa, sai gani kake jini ya tallatsa. Wani irin sama da kai criminal É—in ya yi yana son ya yi ihu ba hali, dan bakar muguntar Obaid ya toshe mashi bakin nasa ba halin yin ihun.

Bai kula shi ba, sai ma sake fasa É—ayar babban yatsar na kafar hagu ya sake yi. Wannan mai laifi dai yau ya ji azaba, girgiza kai ya fara yi idanunsa sun yi jajir kamar jan gauta, alama ce ta yana cikin azaba. Tsabar mugunta irin na Obaid sai ya É—auko chimical mai suna plutonium-239 É—aya daga cikin wanda ake haÉ—a atomic booms da shi, chemical ne mai bala'in zafi, ko da yake ku daga jin boom ai kun san wuta ce, ba chemical ce ta wasa ba, haka ya É—auko chemical nan ya zuba mashi a kafar tasa, dai'dai in da ya fasa da bindiga.

Azaba kan azaba, wannan mutumin kamar zai mutu, idanunsa sai sun baka tsoro saboda yadda suka yi ja sosai. Kallonsa cikin ido ya yi tare da cewa. "Zaka bada bayanai ko dai har yanzu baka niku ba?". Girgiza kai mutumin ya yi alamar a'a shi ba wani bayanai da zai bada sai dai ya mutu.
Chapter 53 · 0% Book details