← Book details Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 211

Sashe 1

Rawanin Zalinci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

❤️🤍 RAWANIN 🔥 ZALINCI ❤️🤍

𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥

❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 16/9/2024.....✍️📚🌹

For more information 08161390581 Whatsapp me only!!.

اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️

💘STEP TWO....✍️📚🔥

E__________________1🔥

GIDANSU KHADIJAH 😥💔

Daga Zainab har mamanta an ransa wanda zai kalli ɗan uwansa ya ce ya yi shiru, sun shiga tsananin tashin hankali. Basu ƙara tsorata bama sai da suka kalli baban Zainab ɗin ya dai'na motsi, ya yi tsit alamar rai ya yi halinsa.

Wani irin ihun da Maman Zainab ɗin ta kurma mai sauti sai da yasa Zainab ta tsorita sosai ta miƙe tsaye. Daga wannan ihun da ta kurma bata sake yin kwakkwaran motsi daga in da take ba, kawai ta sulale ƙasa ne, kan ka ce me ta dai'na numfashi, numfashinta ya ɗauke diff alamar ta sume.

Da gudu Zainab da diro ƙasa daga saman gadon, har lokacin kuma jini na cigaba da malala daga cikin babanta, yadda kuka san hanyar ruwa ta fashe, kuma babban abin takaicin ma faɗuwar da ya yi yana murkusoso sai ya kwanto a kan wukar dake cikin nasa, hakan yasa wukar ta kara lumewa a jikinsa, shiyasa jinin ya yawaita sosai, dan ba ƙaramin ciwo ya ji ba, ga shi a tsakiyar cikin nasa ta caka mashi wukar, abin ya munana sosai!!.

Waje Zainab ta nufa domin ta duba Khadija, ta rasa me zata yi wa iyayen nata ne yasa ta bi bayan yar uwarta.

A takaice dai maman Zainab bata tashi farkawa ba sai da ta É—auki awa uku masu kyau a sume, an zuba ruwa an zuwa ruwa, amma shiru bata farfaÉ—o ba, daga karshe suka kyaleta suka zubawa sarautar Allah ido.

Lokacin da ta farfaÉ—o kuwa sai ganin kanta ta yi a wani irin É—aki mai kama da cell na Æ´an'sanda. A hankali ta fara bin saman celling da kallo, idanunta sun kumbura luhu luhu, sun kuma yi jajir kamar jini ne kwance a cikinsu.

Tunanin baban Zainab ne ya faɗo mata a ranta, hakan yasa ta yunƙura zata miƙe da zafinta kuma a ruɗe. Sai dai kash ta kasa iya miƙewar, sakamakon jikinta duk ciwo yake yi mata, gaɓɓanta sunki koda motsawa.

Hakura ta yi ta cigaba da kwanciya a saman tabarman da take ɗin. A hankali ta fara sauko da kallonta da kallon celling da take yi izuwa ƙasa dan taga a ina take a kuma wani hali take! Wasu irin siraran hawayen takaici haɗe da danasani mai girma ne suka fara zirara daga idanunta izuwa saman ƙuncinta.

Kwatsam ba zato ba tsammani tana sauke idanun nata ƙasa sai saman kofar shigowa wanda yake kofa ce ta burglaris, wato kofar cell kenan.

Zaro idanu ta yi a tsorace, jikinta har kerma ya fara yi, cike da mamaki take tunanin ina su Khadija da baban Zainab ɗin? In da take ɗin babu kowa bare ta yi tambaya. Sake yunkurin miƙewa ta yi a karo na biyu, cikin tashin hankali da ruɗani take. Jikinta sai kerma yake yi, idanunta sun cicciko da kwallah sosai ga kuma wasu na zuba.

A wannan karon ma kasa miƙewar ta yi, saboda jikinta duk a mace yake, ga bala'in ciwo da yake yi mata. Tunani ta fara yi a kan me ya kawota cell kuma? Me ta yi?.

Rasa mai bata amsa ta yi, hakan yasa bata gaji ba ta sake yunkurin miƙewa a karo na uku, sai a lokacin ta fahimci cewa kafarta na ɗaure da wani sarka irin na ɗaure manyan ɓarayi. Kara zaro idanu ta yi tare da fara ƙoƙarin tunawa ko zata iya tunano abin da ya faru a baya?!.

A can gida kuwa sai kuka Zainab take ta yi, ta ƙunshe kanta a cikin ɗaki tun bayan da ƴan'sanda suka tafi da mamar ta su.

Abin da ya faru shi ne, fitar da Khadija ta yi domin zuwa kiran mutane su zo su taimaka masu, tana fita bakin gidan nasu bata ga kowa ba, babu mutane, dukka mazan unguwar tasu sun tafi masallacin jumma'a, dan lokacin an fara sallar jumma'a.

Ganin hakan yasa a ruɗe ta nufi hanyar fita daga unguwar nasu izuwa bakin titi ko zata haɗu da wasu su taimaka mata, basu da nisa da titi. Bata ƙarisa fita ba wata dankareriyar mota kirar Bugatti la voiture noiro baka kirin sai kyalli take yi ta faka a gabanta.

Tana ƙoƙarin kaucewa motar ta raɓa gefenta ta wuce sai gani ta yi an buɗe kofar motar. Wasu maza biyu kyawawa farare tas tas masu sanye da suit ash color ne suka ɓalle kofar motar suka fito. Daga ganin mazan nan ba Nigerian mens bane, daga gani daga ƙasashen masu jajayen kunnuwa suke, dan kuwa jajir suke kamar ka taɓa jini ya fita, ba irin farin Nigeria bane, ga kyakkyawan gashin kai bakin kirin, sannan idanunsu tas kamar an ɗiga zaiba, kwayar idanun kuma bakin kirin har wani ɗan kyalli yake yi, suna da kyau kam masha Allah, matasane da ba zasu wuce 25 years ba a duniya.

Sai dai da kallo É—aya zaka yi masu ka san basu da imani, saboda fuskokinsu babu alamarta ko kaÉ—an, a turnuke fuskokin nasu suke sosai. Ga su dai dirarrun maza ne sosai sosai, kira kamar su suka yi wa kansu.

Da yake tana cikin ruɗani da tashin hankali sai bata ma bi ta kansu ba, hasalima bata ɗaga idanun ta kalli koma su waye bane, kai tsaye ta raɓa gefensu zata wuce, kamar wata mahaukaciya haka ta zama.

Bata kai ga wucesu ba suka damketa suka wurga cikin motar tasu, ga motar da tinted a jikinta. Ihu ta fara kurmawa da karfi karfi. A hanzarce suka faÉ—a cikin motar suma, suna shiga kuma bayan sun rufe kofar ji kake tsit Khadija ta dai'na wannan ihu, kamar waÉ—an da suka yi mata wani abin...... To fa, su waye su?.

Cikin kwanciyar hankali suka yi reverse na motar tasu, a hankali suka takata suka bar unguwar, suka miƙi hanya.

Abin da yasa kenan su Zainab suka ga ta jima bata dawo ba, ita kuma Zainab É—in bayan mamarta ta suma sai ta fito a guje kamar mahaukaciya, dan ta nemo jama'a da kuma Æ´ar uwarta.

Kasancewar ta fito a guje kamar mahaukaciya yasa ta shiga gaban wani mai mashin da ya ɗauko wata mata, ai kuwa bata ankara ba sai jinta ta yi a ƙasa. Ko kaɗan bata wani damu ba, da yake Allah ya takaita mashin ɗin bai ji mata ciwo sosai ba, tureta kawai ya yi ta faɗi ƙasa, ƴar kwarzanewa ta yi a hannunta sakamakon wani dutse da yake a kusa da ita ta faɗa kansa.

Baiwar Allah hankalinta baya a jikinta, sai ta miƙe cikin kaɗuwa da tashin hankali. Da gudu ta nufi bakin titi. Mai mashin da yake ƙoƙarin banka mata ashariya saboda shiga gabansa da ta yi, kafin ya buɗe baki ma ta miƙe da gudu ta barshi da baki a buɗe, bai san me take ji ba, bai san bala'in da yake kanta ba.

Bata ƙarisa isa ga bakin titi ba sai jin jiyar motar ƴan'sanda a gabanta ta yi, birki ta ja ta tsaya da nufin idan sun wuce sai ita ma ta nufi bakin hanyar, kasancewar hanyar fita daga unguwar tasu zuwa bakin titin babu wani faɗi sosai.

Ganin Hauwa a gaban motar Æ´an'sanda ne yasa Zainab É—in bata san lokacin da ta juya ta fasa isa ga bakin hanya dan neman mutane ba, ta juya ta bi bayansu, dan tasan cewa definitely gidansu wannan mota ya nufa tun da ga Hauwa a ciki....... Ashe Æ´an'sanda Hauwa ta je tattarowa.

Suna isa bakin gate ɗin suka fara dirowa ƙasa daga saman bayan motocinsu, ba tare da ɓata lokaci ba suka nufi cikin gidan, ƴan'sanda shidda ne cif suka zo, sai Hauwar da ta kirasu, shegiya ko ɗan'kwali babu a kanta.

Ita ta yi masu jagoranci har izuwa ɗakin nasu in da maman Zee ta kashe baban Zainab ɗin. Suna shiga suka sami maman Zee a sume, duk da take a sumen kuma bai hana sun tafi da ita ba, hands gloves suka sanya a hannayensu kafin su taɓa baban Zainab ɗin, sai da suka ɗauke shi a hotuna kala kala ma kafin su taɓa shi. A takaice dai wannan shi ne abin sa ya faru.

Zainab tana kuka kada su tafi mata da mamarta, amma haka suka wuce da ita tana sume bata san me yake faruwa ba, sannan suka tafi da Hauwar ma, dan kara gudanar da bincike, shi kuma baban Zainab wasu Æ´an'sanda ne na daban suka zo suka É—auki gawarsa izuwa asibiti, dan a yi gwaje gwajen da za'ayi.

Hauwa a police station É—in ne da suka je ta kira Hajiyarsu baban Zainab da wayar baban Zainab É—in ta sanar mata da cewa maman Zainab ta kashe baban Zainab, gawarsa tana police hospital, dan haka su zo.

Ai kuwa babu ɓata lokaci sai gasu sun hallara a station ɗin bayan Hauwar ta gaya masu a division ɗin da suke.

Ƴan'sanda sun yi sun yi maman Zainab ta farfaɗo daga sumar nan da ta yi sun ƙasa, sun yi ta zuba mata ruwa, amma bata farfaɗo ba. Hakan yasa suka yi duk gwaje gwajen da zasu yi ɗin tana sume.

Shatin zanen hannunta ne a jikin wukar dake lume a cikin baban Zainab É—in, suna gwajin farko ya tabbatar masu da hakan, hakan yasa suka gasgata dukkan zantukan da Hauwa ta gaya masu, sun yarda, duk wani bincike da zasu yi ya tabbatar masu da lallai maman Zainab ce ta yi wannan kisan kan, wannan dalilin yasa suka jefata cell tun kafin manyansu su iso kan case É—in.
Chapter 1 · 0% Book details