Sashe 99
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai yanzun ya tsuke fuska tamau bayan fahimtar abinda Fawwaz 'din ke nufi..ganin haka yasa shi jinjina kansa yana cire hanglove a hannun sa yake fadin" Gakiya baka da kirki Rayyan abin ya ban mamaki sosai wallahi..da farko nayi tunanin ko Babyn Sistern ka ne ko wani relatives 'din ka sai kuma naga ai idan ya kasance hakan nasan da kanka bazaka jagoranci zuwa asbiti ba dan nasan halin ka sai dai ka turo hakan yasa na fahimci wannan 'din ta musamman ce..bayan fahimtar tsantsar kama da ke tsakanin ka da ita musamman ma tsohuwar matar ka...."
Saurin duban sa Rayyan yayi yana 6ata fuska, bai ta6a jin mummunar magana irin wannan daga bakin Fawwaz ba sai yau 'din, har gani yake kamar ma Fawwaz 'din ba cikin hanakalin sa yayi maganar ba sai kace mai shafar aljanu, erh mana aljanu, baya ga haka mai yasa babu wanda ya ta6a ganin kammanin su sai shi, babu wanda ya ta6a fa'da hakan sai shi, meyasa shi ma da kansa bai ta6a ganin wani kama tsakanin su ba..a hankali ya zamo Moopy dake baccin ta peacefully ya kwantar saman cinyar sa wai ko zai ga kamannin amma bai ga ko 'dis 'din kama tsakanin sa da ita ba banda ma shirmen Fawwaz da wannan kumburarran fuskan har ya wani ga kama tsakanin su in banda kawai ya 6ata mai ransa abanza ba menene.
" Wai ina kamar?"
Ya tambaya yana duban Mufeeda.
" Ga ta kuwa gaban ka, wlh Rayyan ko rantsuwa nayi nasan bazan yi kaffara ba akwai kama ta jini tsakanin ka da yarinyar nan.
Baki ya kya6e a fili ya furta raba ni da Allah Fawwaz banson shirme ina wani kama anan in ba sharri ba, kasan wace ita kuwa..hmm ban da wata ala'ka da ita Ammi ce ta yimin aikan dole..."
Kai Fawwaz ya jinjina cikin ransa ma jinjinawa 'karyar Rayyan yayi, dan kuwa ko makaho da idanun sa suka bu'du yau 'din nan idan yaga wannan yarinya ya kuma ga Rayyan take zai fahimci suna da ala'ka da juna, badan yasan ahalin Rayyan banda Bassam basu da wani 'karamin yaro ba cikin kannen sa kaf ba da zai ce kila yar 'dan uwan sace ko 'dan uwan sa domin kamar har ta 6aci ma.
Amma da kansa yasan Sultan ne mijin Marwa kuma basu haihu ba, Safaa ta rasu haka ma Yah Kabeer da matar sa har ma da 'diyar sa Zamrud, Anty Madeena kuma Allah bai taba bata haihuwa ba..Raihana kadai ke da yaro Bassam duk yasan wannan, sannan matar Rayyan Nadia yanzu shekaru biyu ake nema da rasuwar ta da tsohon cikin ta bai manta komai ba domin kuwa dashi aka sha fama akan Rayyan kafin ya dawo rayuwar sa normal.
Yayin da Amrah yasan yanzu hakane ma take da juna kuma na farko dan ko kwana biyu da ya wuce Rayyan ya kawo ta scanning.
Sam tunanin sa ya kasa bashi amsar da ta dace da lamarin, dole cikin abu biyu 'daya ne daidai, inma ta kasance 'diyar 'yan uwan sa ko kuma 'kila Rayyan yana 6oye wanzuwar yarinyar ne saboda abubuwan da suka ta faruwa abaya, kila sbd magauta dake bibiyar rayuwar su ne, in hakane kuwa sam bai ga laifin sa ba, kuma ya bashi gaskia, sosai ya goyi bayan sa kan hakan, domin yafi kowa sanin halin da Rayyan ya shiga lokacin da aka akashe masa mahaifi anan asbitin nasu ya rasu a hannun Rayyan, ba 'karamin tashin hankali Rayyan ya shiga ba, haka na Yah Kabeer da Safaa sbd kiyayya, kuma har yau 'din nan an kasa samun wanda ke da hannu ko guda, tuno hakan yasa yaja bakin sa yy shiru...sai dai zuciyar sa cike fal da tunanin yaushe aka haifawa Rayyan yarinyar.
Magunguna Fawwaz ya rubuta ya basa saboda zafin zazza6an da kuma kumburin fuskar ta, still zuciyar sa na kissima masa abubuwa da dama.
Rayyan bai ce komai ba ya juya yana godiya yayi gaba abinsa, dan shi tuni ma ya watsar da batun cikin zuciyar sa bai wani bashi muhimmanci ba.
Can gida kuwa Ammi da 'kyar ta lallashi Zaitoon tayi shiru domin kuka sosai take yi cikin zuciyar ta take 'kissima irin muguwar tsanar da Rayyan yayi wa Feefy da har zai iya yi mata irin wannan muguntar batare da ya dubi 'karancin shekarun ta ba, yarinya ce 'karama 'kasa da abinda zai iya haifa a cikin sa amma yake yi mata irin wannan muguntar, idan ganin su ne be so ai kamata yayi yace su bar musu gidan su amma ba wai ya dinga cutar mata da yarinya ba, yanzu kam ya kaita ma'kura sam bazata sake juran irin hakan daga wurin koma wanene ba.
Sosai take ganin mutuncin Ammi domin ita a fili take bayyana 'kaunar ta gare su musamman ma irin kulawa da kaunar da take yiwa Mufeeda shiyasa ta bata wani matsayi babba, matsayi na daban cikin zuciyar ta wanda kaf 'din rayuwar ta mutun 'daya ne ya taka wannan matsayi kuma har abada tana jin babu wanda zai taddo sa cikin ranta, akwai mutum biyu bayan wancan amma tana jin duk sun biyo bayan Ammi ne sai na ukun su itace Marwa, hatta Rayyan albarkacin su yake ciki yasa har take iya 'dan 'daga masa lokuta da dama tana kawar da kai ga wasu abubuwan da shi da matar suke mata indai ba sun kure hakurinta bane bata tankasu.
Amma badan hakan ba sam mancewa zatayi da taimako da suke mata ta fito masa a mutun ta nuna masa kuskuren sa na takurawa yarinyar ta da yake yi.
Irin kukan da take yi har na bawa Ammi mamaki, aganin ta indai akan dan Mufeeda ta fa'di ne ai wannan normal yake ga yara, ko kuwa dan jini da ta gani ya fitowa yarinyar nan, ko dai wani abun daban ke damin ta sam Ammi ta rasa amsa guda da zata bawa tambayoyin ta.
Gashi har a lokacin Zaitoon bata bayyana mata asalin yadda abin ya kasance ba ta 6oye mata cewa Rayyan ne silar komai.
Sai da tayi kukan ta ta gaji da kanta sannan tayi shiru a hankali ta sau'ke numfashi tana goge hawayen ta ta mi'ke zaune Ammi kam sai binta da kallo ta kae cike da mamakin ta.
Shin wannan 'din duk 'kaunace ko kuwa menene..?"
Ammi ta sake tambayar kanta...
Tun lokacin da ta gudo dakin ta tura kuka take har ta kai yarinyar ga Rayyan ta dawo bata daina kukan ba, ita kanta Ammin yanzu ta sahfe kusan rabin sa'a zaune tana lallashin ta amma ta kasa yin shiru 'karshe dole ta haukra da lallashin ta zubawa sarautar Allah idanu.
Tana so ma ta bar dakin.zuwa saman ta dan 'kiran Rayyan taji halin da suke ciki amma mamakin Zaitun ya hana ta.
Irin duban da taga Ammi na mata na tsantsan mamaki ne ya sa jikin ta yin sanyi, a hankali da sanyin murya tace" Kiyi ha'kuri Ammi na daina kukan...bari inje in bata ko Panadol ne ma kar zazza6i ya shige ta"
Murmushi Ammi tayi sannan tana gyara zama tace" Kwantar da hankalin ki ai na tura su asbiti can za'a fi bata kulawar da ta fi dacewa..amma wai kukan duk na menene haka Zaitoon..?"
Ammi ta 'karashe maganar da tambaya.
Sam Zaitoon bata bi ta kan zancen Ammi na 'karshen ba tamkar ma bata ji abinda ta fada ba, maganar ta ta farkon ne yafi yi mata yawo aka, jin cewa har asbiti Ammi ta tura akaita yasa ta sau'ke ajiyan numfashi, gefen Ammin ta koma ta zauna tana mai sunkuyar da kanta sosai taji sanyi cikin ranta dan hk a hankali ta furta" Nagode sosai Ammi...Ubangiji Allah ya saka mk da mafificin Alkhairi..."
Batun yau ta fahimci cewa Ammin zuciyar zinare gare ta ba sai gashi kusan kowani lokaci gaskata tunanin ta actions din Ammin keyi.
" Ameen Zaitun...Ameen Ameen"
Hannun ta kamo cikin nata sannan ta cigaba" amma daga yau bana son wannan doguwar godiyan kinji ko har yau baki 'dauke ni matsayin mahaifiya bane ?"
" Matsayin ki kamar hakan take a waje na Ammi, domin ke ka'dai kk bani wannan gatan tun tasowa ta...".
" Yauwa 'diya ta, so ki saki jikin ki kinji, ki saki ranki Insha Allabu Mufeedah zata samu lafiya babu abinda zai samu yarinyar ki kinji..."
Kai ta jinjinawa Ammin cike da jin dadin kalaman ta.
Bata ma bari Ammi ta kai 'karshen maganar tata ba ta tare ta da fa'din" Insha Allah Ammi, amma Ammi waye ya kaita asbitin..?"
domin hankalin ta taji kamar bai kwanta ba daga can kasan zuciyar ta.
Shiyasa tayi tambayar.
Batare da wata damuwa ba Ammi tace" Rayyan ne ya kaita ina jin ma ba da'dewa zasu yi ba".
Taso ta 6oye tashin hankalin ta amma sam hakan ya gagare ta...idanun ta da taji suna tara sabbin ruwa tayi saurin kawar wa kar Ammi ta gani.
Baya ta juya mata ta koma ta kwanta ta 6oye fuskar ta a hankali idanun ta ya cigaba da tsiyayar da ruwa...itafa tsoro take, tsanar Feefy da take gani tattare da Rayyan gani take komai ma zai iya yiwa Moopy na cutarwa, a gida ma a gaban ta a kuma gaban Ammi ya aka 'kare ballantana inda babu idanun kowa.
Ammi da bata san me ke faruwa ba ganin kamar hutu take bu'kata ya sanya ta tashi ta fita tana fa'din" barin inje in 'kira shi inji ko suna hanya.
Ko 'kala zaitun bata ce da ita ba har ta 'karasa ficewa daga 'dakin...abu guda kawai ta sani ta kuma dasawa ranta shine matu'kar aka cutar mata da yarinyar ta bazata ta6a 'kyalewa ba...a lokacin ne kowa zai fahimci asalin wacece ita, ita kanta bata iya kissima abinda zata iya aikatawa idan aka cutar da yarinyar nan amma tasan abin bazai yi kyau bane kawai.