← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 218

Sashe 15

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar dai yau din da be samu zuwa wajen abokin nasa ba kawai ya tsaya wajen sana'ar tasa sai dai duk ilahirin hankalin sa baya tare da shi, shi bai ma san wani irin so Allah ya jarabce shi da shi ba, ya riga yasan abu ne mai wahala su Hajiya su amince masa batun auren Zaitunan amma a shirye yake ya fuskanci ko wani irin kalubale matukar hakan zai kai shi ga nasarar da ya jima yana sakawa.

Zaman sa ba da jimawa ba arean wajen ya fara dinkewa saboda tahowar wasu shegun motoci bakake masu masifar daukan hankali.
Da gudu suka ringa wucewa 'daya bayan daya kimanin su shida cif.

Yaron dake kula masa da kayan ne ya saki murmushi yana duban motocin da fadin" Yau 'Dan maliki yazo gari kenan ina yin ka mutumi na.".
Ya fada yana me bayyanar da tsantsan farin cikin sa a fili.
Wata guntuwar tsaki Adam ya saki da shi kadai yasan ma'anar kayan sa da alamu dai zancen da yaron yayi ne bai samu shiga wajen Adam din ba.
Karshe ma tashi yayi yai tafiyar sa baiko yi masa Sallama ba.

Daga masallacin da yayi sallar Maghrib bai zame ko'ina ba sai kofan gidan su Zaitun ya aika yaro aka yi masa kiran ta.

Dama tasan dole yau din sai yazo shiyasa ta kasance a shirye dan farin sani ta yiwa halayyar Adam, tasan yadda yake damuwa da duk wani damuwar ta canjin fuska idan yaga tayi sai ya nemi ba'asi.
Tasan abu ne mai wahala idan bai zo yau din ba, dole sai yazo yaji matsalar da take ciki tun bayan ganin da yai mata a shago da safe.

Tun faruwar lamarin nan jiya bata sake kuskuren barin kofar ta a bude ba, ko bathroom zata sai ta kulle kirib.
Ko yanzun ma da zata fita wajen Adam sai da ta kulle shi kafin ta fita.

Kanta a kasa ta isa wurin sa daga sallama kuwa ko gaisuwa bai bari sun yi ba yasa hannu ya kar6i Mufeeda dake hannun ta yana fadin.." Yau duk baki barni na yini cikin natsuwa ba sosai kika tada min hankali Zaitun.."

Ido ya tsura mata jin bata ce da shi komai ba illa wasa da yatsun hannun ta da take faman yi tsawon wani lokaci, ganin da gaske ba fa zata yi maganan bane ya sanya shi a hankali cikin sanyin muryar sa mai dadin sauraro yace" Pls Zaitun ki fa'da min me ke damun ki?"

Salmerh😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...9*

" Zaitun dan Allah ki amsa ni, u don't have idea about yadda nake jin zuciya ta..ko har yanzu bani da wannan matsayin da zan iya sanin matsalar ki..?"
Shiru Zaitun tayi illa kai da ta girgiza masa kwalla na sauko mata, ba karamin kokari take cikin ranta wajen har hado amsar da zata bashi ba.
Adam da bai fahimci hakan ba ajiyan numfashi ya sauke mai nauyi..." Well!..bazan tilasta ki fadin abinda baki yi niyya ba Zaitun ki rike damuwar ki tunda hakan kika ga yafi miki, amma ki sani ni Adam ina tsananin kaunar ki, ban damu da sai nasan kullin da ke cikin rayuwar ki ba tunda baki yi ra'ayin sanar da ni ba, abinda kadai na sani shine _INA SON KI!.._ I love u Zaitun with all my heart, a shirye nake da kar6ar ko wacce irin kaddara dake tare dake cikin ko wani irin yanayi ina tare da ke".
Duban sa ya maida kan Mufee da ke wasa da agogon hannun sa wani choculate ya ciro cikin aljihun sa ya sa mata a hannu.
Bai dubi inda Zaitun take ba ya cigaba da fadin" Zaitun bana fata zuwa na ya zam miki tamkar takura ne duba da yanayin dana sameki.."
Sai yanzun ya juya ya kalli fuskar ta dake kallon kasa illah hawayen da ke sauko mata" Damuwar ki a zuciya ta nake jin sa Zaitun, kuncin ki, farin cikin ki, walwalar ki ko akasin hakan duk tafiyar su dai dai yake da nawa in baki sani ba yau in fada miki...zan wuce yanzu amma duk lokacin da kika shirya sanar dani damuwar nima a shirye nake in saurare ki.."
Daga haka ya juya ya fara tafiya da takun sa mai birgewa.
Taku uku yayi bai kai ga yin na hudu ba Zaitun ta mike tsaye daga dakalin dake shinfide a kofan gidan.
" Yah Adam.."
Ta kira sunan shi da raunin murya mai raunin amo, bai yi kasa a gwiwa ba ya waigo.." Dan Allah kayi hakuri Yah Adam, ba nufi na in 6ata ranka ba..."
" Na san hakan Zaitun karki damu"
Ya fada yana mai kokarin cigaba da tafiyar sa.." Yah Adam!!".
Ta sake kiran sa a karo na biyu.
Tsayawa ya sake yi amma bai waigo ba" Kar kayi fushi da ni dan Allah".
Maganar tata ma dariya ta bashi amma da yake baya cikin yanayi mai dadi madadin dariyar sai yayi murmushi kawau...sai da ya juyo sosai ya dube ta kafin yace" Me kuma zai sa inyi fushi da abar kaunata..baki min laifin komai ba ai da zai sa inyi fushi da ke".
Mufee dake rungume da kafafun ta tun ganin mikewar Zaitun din tasa hannu ta dago ta sama ta rungume ta sosai.
" Zan fada maka abinda ya faru".

.......*****

" Kika ce shine wanda jiya na ganki tare da shi..?"
Adam yayi tambayar bayan Zaitun ta gama bashi labarin kaf yadda lamarin ya faru tun a farkon zuwan ta gidan.
Da kai Zaitun ta amsa shi tana duban gefen sa lokaci lokaci take sa hannu ta share hawaye yayin da Mufee tayi luf cikin jikin ta kamar me fahimtar abinda suke tattaunawa.
" Meyasa baki ta6a sanar dani hakan ba toh..?"
Shiru tayi..." Yanzu da wani mugun abin ya faru dake fa? a tunanin ki zan iya dauka ne? kinsan halin da zan iya shiga ne...?"
" Kayi hakuri..!"
" Mtheew..."
Ya fada yana sake mikewa tsaye dafe da kansa.
Kai kawo ya fara daga gabas zuwa yamma yana tunanin mafita.
Dole ne sai yayi wani abu a wannan ga6ar gudun abinda kan iya zuwa ya dawo...ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi, ga dukkan alamu ya samo mafita ne.
Gaban ta ya dawo ya duka kamar me shirin neman tuba.
" Kinsan yadda za'ayi Zaitun? dole ne sai kin bar gidan nan, bana so ki kara cikakken sati guda a cikin sa in so samu ne ma kafin satin ki kasance karkashin ikona amma duk hakan ba zai faru ba sai da amincewar ki kinsan hakan ko...?"
Da kai Zaitun ta bashi amsa tunanin ta na rarrabewa sashi zuwa sashi.
" Zan yi magana da Hajiya amma kafin hakan dan Allah banaso ki sake komawa wajen aikin kin nan ki zauna a gida, kuma ki kula da kofar ki duk inda zaki ki ringa kulleshi hatta bathroom bana son kiyi kuskuren sake barin kofa a bude in zaki shiga, dama ni tun farko mutanen gidan kun ba kwanta min suka yi ba amma zan san abinyi, dole zan yi magana da Hajiya ta..tashi ki koma gida...".
Ya karasa maganar da mikewa tsaye hadi da matsawa baya kadan daga gaban ta.

Ko da ya koma gida bacci kaurace masa yayi throughout daren, sake sake yake ta inda zai fara fuskantar Hajiya da maganar.
Shi da ake shirin turashi cigaba da karatu matakin masters shine kuma zai zo musu da wannan sabon batun..yasan sai sun sha drama da Hajiya kafin ta amince.

'Bangaren Mmn Abdul kuwa tsananin kunyar Zaitun ne ya hana ta sakewa, ji tayi sam bazata iya hada idanu da ita ba sai aka yi sa'a ita ma Zaitun din aranar ko bi ta kansu bata yi cikin gidan ba.

Mmn Abdul kadaice tasan duk abinda ya faru daren jiyan domin taji duk maganganun mijin nata da Zaitun.
Dama ita bata ta6a zargin Zaitun ko makamancin hakan ba dayake tasan shaidanin, sai ma tsananin kunyar ta da ya cika ta a yanzun.
Rabon da magana ta hada ta da Bbn Abdul tun jiya kafin faruwar lamarin duk ta dauke masa wuta har da kansa ya fara zargin ko dai tasan abinda ya faru tsakanin sa da Zaitun ne..kai anya kuwa? taya ma hakan Zai faru bacin time din daya dawo tuni baccin ta yy nisa.

Wannan tunanin duk yayi su ne bayan dawowar shi gida daga sabgogin sa ya tadda gidan bb kowa, Mmn Abdul ta tattara yaranta kaf sun bar masa gidan..ga Hajja ma bata nan kishiyar Mahaifiyar marigayin Maigidan ta ta rasu tana can, in bai manta ba ko a safiyar yau din gaisuwa wannan bai shiga tsakanin sa da Mmn Abdul ba.

Zaitun kuwa da bata san wainar da ake toyawa cikin gidan ba dakin ta ta shige bayan rabuwar ta da Adam, duk da taji gidan shiru tun dawowar ta daga aiki zuwa yanzun amma bata wani sa akanta ba da yake ba sune gaban ta ba a yanzu...
Cikin rashin sani daga ita sai Bbn Abdul ranar suka kwana cikin gidan Zaitun duk bata san hakan ba..bcuz da tasani hankalin ta ba zai kwanta ba.

Sai da ta kwashe kimanin kwanaki uku ras bata leka ko kofan gida ba haka kuma bata sake jin 'duriyar Adam ba wanda zuwa lokacin ta jima da fahimtar Mmn Abdul bata a gidan amma abinda yadan kwantar mata da hankali shine ganin Hajja ta dawo.
Chapter 15 · 0% Book details