Sashe 48
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk yadda yaso ya cigaba da daurewa hakan ya gagare sa, duk yadda yaso nuna 'karfin hali sam yakasa aikata hakan, yaso sake ziyarar kotun ko sauraren shari'ar ma yayi amma ya kasa, taya zai iya zuwa ya zauna ya zuba musu idanu bacin bashi da hanyar basu kariya ko ta wacce hanya, sam bazai iya ba, fita ma ya kasa, ba zai iya shiga cikin mutane yana fuskantar zafafan kalaman su kan 'Dan Maliki ba, bazai iya jure ganin yaddar da ada yake gani a idanu da kalaman jama'ah game da mahaifin nasa na sulalewa ba.
Ranar da za'a yanke hukuncin 'karshe ma yaso zuwa amma sam hakan be yiyuba, zama yayi gida amma natsuwa ta kasaa zuwan masa gaba 'daya tayi masa 'kaura.
Lokacin da labari ya riske shi rasa ina zai sa kansa yayi, shin farin ciki zai yi ko ba'kin ciki.
Kotu ta wanke Zaitun lallai hakan yai masa da'di ya kuma yi farin ciki amma mahaifin sa fa?
kotu cewa tayi zata 'daure shi har na tsawon shekaru goma sha biyar ban da tara da zai biya masu matukar nauyi...taya zai ji kwanciyar hankali har farin cikin sa ya bayyana a duniyar nan.
'Karshe sai da aka dangana Adam da asbiti saboda tashin farat 'daya da ciwon sa yayi, hankalin Hajiya Talatu ba 'karamin tashi yayi ba ta yadda baki ma bazai iya fasaltawa ba, haka yake ga Hafeez ma dan bayan 'dimbin amanar da ya kar6a game da Adam Shaheed, shi 'din abokin sane kuma amintacce da ba zai so ganin gazawar sa kan komai ba, a hakan ma yasan yana matukar 'kokarin yin tawakkali da danne abubuwa da dama ya kuma san matsayin kaddara ga bawa.
Amma irin yadda rayuwa take walagigi da rayuwar sa abin a tausaya masa ne, yadda jarrabawa ke ta riskar sa 'daya bayan 'daya yana ganin da shi ne ma da tuni raunannar zuciyarsa ta samu matsalar da baza'a so afkuwar ta ba.
Ita kanta Hajiya Talatu sai a lokacin ta samu labarin ciwon zuciyar sa ta kuma yi mamaki 'kwarai da gaske, musamman da taji cewa ciwon ya dade yana damun sa har ya kai wani mataki, me Adam ya aikata haka? meyasa ya 6oye mata duk wannan?
Lokacin da ta tuhumi Hafeez da maganar ta fahimci tamkar ya san da batun tuntuni batasan lokacin da ta sau'ke mishi zazzafan mari ba tana kuka take fa'din sun cuce ta shi har Adam 'din gaba 'daya, basu mata adalci ba me yasa zasu 6oye mata irin wannan lamari, taya zasu yi wasa da rayuwar Adam 'din.
Duk yadda Hafeez yaso kwantar mata da hankali abin gagarar sa yayi, kuka wiwi Hajiya Talatu ta zauna tana yi tamkar ranta zai faso 'kirjin ta ya fito, ashe ta kusa kashe 'dan ta da hannun ta bata sani ba, ashe lokacin da ya 6oye kansa sbd raba shi da Zaitun da tayi har take ganin in ya gama fushin zai sauko ne ashe duk jinyar zuciyar sa yake bata sani ba sai yau da Hafeez yake sanar da ita.
Danasani marar misaltuwa tayi 'kwarai da gaske, danasanin abubuwa da dama, ciki harda raba shi da Zaitun da tayi, ta 'kudurta kuma a ranta tunda kotu ta wanke laifin Zaitun 'din dole sai ta nemo masa ita, badan ta raba shi da ciwon gaba 'daya zata yi hakan ba dan tasan abu ne mawuyaci tunda ba dalilin ta ya kamu da ciwon ba dalilin mahaifin sa ne kuma bata da ikon samar masa da farin ciki ta wancan 6angaren duba da abinda ma ya riga ya faru, amma ko da duk abinda ta mallaka zai 'kara wajen neman Zaitun ne ta 'dauki alwashin nema masa ita dan ganin yayi farin ciki ko da 'kan'kani ne, tasan har gobe yana 'kaunar yarinyar dan ko bayan da aka kamata ma ta fahimci hakan musamman daga camzawar yanayi da walwalar sa, zata dawo masa da Zaitun cikin rayuwar sa ko hakan zai rage masa ra'da'din ciwon ta wani 6angare ya samu ragin damuwa dole ne ta bada gudunmuwa wajen farfado da soyayyar sa.
*Toh fa masu karatu, ga Hajiya Talatu tayi alwashin neman Zaitun ga kuma can Zaitun a hanyar Kano...yaya kuke ganin zata kaya ne...?*
_Ku cigaba da biyo ni dan jin dukkan amsoshin ku._
*Comment nd Share to other groups*
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...30*
.........Ido ta waro sosai ganin irin girma da kyan gidan da suka shigo bayan an bude gate din gidan, sosai jikin ta ya fara rawa saboda tsoro, sake rungume Mufee tayi tana me dawo da kallon ta ga Hajiyar da ke zaune gefen ta, magana take son yi amma yadda bugun zuciyar ta ya rinjayi duk wani 'kwarin gwiwa da take ikirarin tana da shi haka ya rinjayi harshen ta ma yayi mata nawi.
Dagaske tsoro da fargaba ya tsarga mata nan take, tuni ta raina kanta ta jinjinawa rashin wayo irin nata, sai lokacin ta fara nadamar yadda da tayi ta biyo matar nan.
Tsayawar motar yayi dai dai da tsayuwar wasu mutane har guda biyu sanye da kayan da take kyautata zaton na aiki ne..." Alhamdulillah"!
Hajiyar ta furta a fili gami da sakin ajiyan zuciya ga dukkan alamu bata tare da wata damuwa sa6anin Zaitun da ta raku6e ta kasa ko da motsin kirki.
Wa'dannan da suka zo tar6ar Hajiyan ne suka bu'de motar batare da 6ata lokaci ba matar nan ta fara kokarin sanya 'kafafun ta waje.
Ganin haka yasa Zaitun tai saurin ri'ke mata hannu idanun ta da kullum suke nan ruwa- ruwa ta 'daga ta dube ta da shi wanda take wasu sabbin hawayen suka taru cikin idanun ta.
Kai ta fara girgizawa batare da ta saki hannun matar ba yayin da 'daya hannun ta ke rike dam da Mufeeda tamkar za'a 'kwace ta.
"...Dan Allah Hajiya ki sa a maida mu inda aka 'dauko mu, wlh tsoro nake ji sosai...".
murmushi tayi tana duban hannun ta da Zaitun ta ri'ke sannan ta dubi fuskar ta " Karki damu daughter, kar kuma kiji tsoro nan gida na ne...sauko mu shiga ina sauri ne....".
Hawayen Zaitun tuni ya gangaro, sau 'daya ta dubi matar sai ta mayar da duban ta ga sauran matasa dake tsaye wajen motar..ita dai haka kawai sai taji hankalin ta bai kwanta da gidan nan ba.
Bu'de mata 6angaren da take akayi bata zaci hakan ba dan haka da sauri ta dubi wajen ganin wani ne sanye da bakaken kaya kamar sauran ya bude ya sa da sauri badan ta so ba ta bi bayan matar ta inda ta fita, dan ji take tamkar zasu kamata bata manta farkon haduwar ta da Dr Rasheed ba, haka ta gansu duk sanye da bakaken kaya.
Da gudu- gudu sauri- sauri ta fara bin bayan ta har yanzun kuma hawayen ta bai daina sauka ba..." Easy madam.. kar ki fa'di..".
Taji an fa'da daga bayan ta, hakan sai ya 'kara mata sauri, matar nan murmushi kawai tayi batare da ta sake duban Zaitun ba, bata damu bane dan tasan tana nan biye da bayan ta har suka ratso cikin tsakiyar 'dakin da duba 'daya Zaitun tai masa ta fahimci Palor ne irin ma wanda ya amsa sunan san nan.
A iya yawon da ta yi ta san faluka iri- daban daban sai dai wannan 'din yasha bambam da kowanne, girma da tsarin sa na musamman ne, wani ni'imtaccen 'kamshi yake fiddawa da duk yadda kake jin zuciyar ka da ka ratsa palon nan sai kaji 'yar nutsuwa ta shige ka.
Wata mata ce ta shigo tsab da ita sai dai, rissina tayi fuskar ta cike da fara'a take fa'din "..Barka da dawowa Ammi...an iso lafiya...?"
" Lapia 'kalau Alhamdulillah Raleeya ina Hajja Ladi fa...?"
" Tana kitchen".
" Kice ta same ni dan Allah..."
Hajiya tayi maganar tana me hawa saman stairs tare da bawa Zaitun umarnin samun wajen zama.
Ita har wacce aka 'kira da suna Raleeyan bb wanda yayi ma 'dan uwan sa duba sau biyu.
Zaitun banda bin parlon da kallo da tunanin makomar ta bb abinda take yi.
Lokaci lokaci takan gyara rikon da ta yiwa Mufeeda da har yanzu ke bacci tamkar wacce wani abu ke tsikarin ta haka take yawan gyarata.
Sau 'daya tak in ka kalle ta zaka fahimci cewa a matukar tsorace take.
Haka kuma ta kasa bin umarnin matar na cewa da tayi ta zauna.
Ta ina zata iya zama a wannan wajen, ta zauna ma tayi me..?
Tana nan tsaye kallo mai kyau bata iya bin parlorn da shi ba sbd wasi wasin da zuciyar ta ke ciki...
Wata mata ce ta sake bayyana da take kyautata zaton itace Hajja Ladi da Hajiya tace ta same ta dan bata yi kama da matar gidan ba ko a yanayi, ta fahimci hakan ne musamman dan ganin hanyar da Hajiyan tabi itama shi ta bi sannan cike da sassarfa ta bi hanya ga dukkan alamu kuma cikin zakuwa take wajen ganin ta cika umarnin Hajiyar.
Tsawon wasu mintina sannan matar ta sake sakkowa, har a lokacin kuwa Zaitun na nan tsaye ledan kayan ta da wani ya shigo da shi na nan gefen ta.
Da wani mugun kallon ta fara cin karo daga Hajja Ladi da sakkowar ta kenan daga sama, kuma tun kafin ta 'karasa sakkowar ta fara aika mata da kallon da ke nuni da zallar tsana da jin haushin ta.
" Ki biyo ni...".
Haka kawai ta ce ga Zaitun bayan ta 'karasa sakkowar tana me nufan wani 6angare daban daga kasan stairs din.
Ke gezau Zaitun batayi ba, sai ma mamakin Hajja Ladin, tabi ta takaita ina kenan bacin ba 'kofan fita taga ta nufa ba.
Wani tunani da ya zo ranta yasa tayi saurin duban Hajja Ladin da rawar murya tace..." Ina zamu...dan Allah ki fitar da ni daga gidan nan...".
Turus Hajja Ladin tayi tana mata wani banzan kallo.