← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 218

Sashe 116

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanun sa ne ya sau'ka akan na Ammi dake kallon sa.
" Ammi shi ka'dai ma fa ya ishe ni ban jin abinci ne yanzu...."
" Hmm".
tace tana daidaita zaman ta.

" Sultan ma fa kwana biyun ganin sa yay min wuya duk kun je kun ha'de kanku kun hana kawunan ku sukuni saboda wai Company ko?...naga dai INFINITY da ku ko ba ku babu abinda zai dakatar da ayyukan sa indai har za'a biya ma'aikata hakkin su yadda ya kamat..."

" Hakane Ammi but inda mu din ai kin san komai yafi tafia bisa tsari kuma babu danne hakkin wani, sa6anin haka nan da za'a barshi sai dai manager kawai ai kinga kowa zai yi abinda yaga dama ne..".
" Da wannan ma, amma dai kuna dan sassautawa ko dan saboda iyalan ku suma ku dinga basu lokutan ku kuna zama da su, musamman kai ka ga ka fara tara iyali, dole ne abubuwa zasu bambanta da yadda suke a baya..."

Sallamar Zaitoon ne ya hanashi magana kuma dama ba niyyar yin maganar yayi ba sbd bashi da amsar bawa Ammin.
Da yake 'kage yake da son cigaba da abinda ya kawo shi hakan yasa batare da 6ata lokaci ba ya fara aika kayan ituwan zuwa cikin sa.

Duk ba wani da'din su yake ji ba amma gudun kar Ammi ta sake complaining ya sanya shi daurewa ya cusa su a dole.

Da gamawar sa ya sake tambayar Ammi kayan tace" Ka matsa Rayyan Allah yasa dai Alkhairi..."
" Insha Allah Ammi.."

" Suna can 'dakin Safaa..kaje ka duba.."
" Tsaye ya mi'ke da hanzari sai dai tuno wani abu ya sanya shi sake duban Ammi..." Amma Ammi 'dakin Safaa ba shine wancan yarinyar take ciki ba..."
" Shine ".
" Ammi idan na tarar ta 6ata min kayan m..."
" Kar ka damu babu abinda ya ta6a kayan ka, Zaitun bata da wannan rawar kan da 'kyar ne idan tasan da zaman su a 'dakin ma..kaje ka duba drawer 'karshe da zaka ga alamun ma ba'a bude shi kwata kwata, key din sa na can saman sa ka duba..."
Tashi yayi ya fita..'Dakin gyare yake tsab sai 'kamshi dake tashi, bai wani tsaya dogon nazarin inda ta samu turare ba dan yasan Marwa ce, Ammi kanta tana siya mata turare ya sani.

Sai da yabi drawers din duk ya bi ya bu'de bai kuma san dalilin.sa nayin hakan ba,
Kayan Mufeeda ya gani wanke kuma a goge jere reras bisa tsari
sosai suka birge shi hka ma ma'abociyar gyaran, ko ba komai bai ta6a samun ta da 'kin jinin sa ba, ta kuma kula da Mufeeda tamkar ranta..."

Rufe drawers din yayi yana jin bugun da zuciyar sa ke masa.
Hakan yasa shi jingina da jikin drawern Yana dafe saitin zuciyar tasa.

Ganin kamar zai 6ata lokaci ya sanya shi.janyo side drawer ya hau ya dubo key din ya bude.

Sai da ya barbaza kayan kaf a 'kasan tiles, yana bi yan kallo, photuna da takaddu da komai da ya shafi Nadia mai muhummanci da akasin sa.

Takardar Anti- natal 'din ta da kuma kati da sauran Scan results 'din ta duk ya ware gefe ya duba su da kyau..zuciyar sa na harbawa.

Gani yake tamkar ba dai- dai idanun sa suke game masa ba.
Meyasa duk a baya bai ta6a tunanin duba cikin da kansa ba? Meyasa bai ta neman ganin takaddar Scanning d'in ta ba..?"
Gaba 'daya ji yayi komai.ya kwance masa har wani jiri jiri yake gani hakan yasa shi zama bakin gado dan tabbas zai iya kaiwa kasa batare da ya farga ba.

Ya bude ido ya rufe fin 'kirga, ya girgiza kansa yafi sau shuri masaki da tunanin ko de bacci yake har yake mafarki amma duk babu ko guda daga cikin tunanin sa da yake dai dai, abin nan dai da yake gani shidin ne.

Ashe cikin 'yan biyu Nadian sa ke 'dauke da shi a lkcn batare da ya sani ba....?

Harha'da komai yayi kawai ya cusa cikin jakar da suke ciki ya maida ya kulle drawwer yayi waje illah takaddar dake hannun sa.

Ko sake bi ta saman Ammi bai yi ba balle sashen Amrah ya sake hawa motar sa yayi gaba abinsa bai zame ko'ina ba sai unguwar Anty Madeena.

Kafin shigar sa gidan ya tsaya ya sallaci maghrib da ta 'dan 'kwace masa sannan yayi zaman azkar.

Zaitoon ko da ta dawo 'dakin ta tarar kan tiles 'din kaca kaca da 'kura ba 'karamin mamaki ya kamata ba dan tasan ba haka tabar shi ba.

Sai da tabi dakin da kallo sosai sannan ta fahimci anma shigo cikin sa.

Sanin da tayi cewar ba ita kadai ke rayuwa cikin gidan ba uwa uba zaman alfarma take ba itace mamallakiyar dakin ba ya sata cire damuwa ta gyare tsab ya koma tamkar bashi ba.

Ganin Isha'i ta gabato kawai ya tsaya har aka sallaci isha'in, bayan haka ma ya 'dan 6ata lokaci sosai wajen azkar gami da addu'o'i sannan ya fita ya 'karasa gidan Anty Madeena.

Sai dai cikin rashin sa'a sa6ani suka buga, domin basu jima da fita zuwa Shoprite ba da Abbahn su Badi'a da Anty Madeena hadda Mufeeda.

Bai ji da'din hakan ba Amma albishir 'din da yazo mata da shi baya jin zai iya tafiya batare da ya isar da shi gareta ba.

Dan hka yayi zama sa a parlon ba'ki yana jiran dawowar su, nan yake ta sake- saken abubuwa, babu abinda bai zo kansa na duk abubuwan da ke faruwa gereshi ba, yasan dole Allah na jarabtan bayin sa da komai dake cikin duniyar nan fatan sa Allah ya bashi ikon cinye tashi jarrabawan batare da ya kuskure ba.

Tsabar rashin natsuwar da ya shiga cikin 'yan kwanakin nan da baya samun bacci, zaman sa anan har bacci ya 'dan fara 'daukan sa..bacci kuma mai nauyin gaske.

Sultan da dama yake bibiya da fakon duk motsin Rayyan cikin 'yan.kwanakin sai abin ya 'kara tasiri, tun bayan tsawar da Rayyan ya doka masa ranar nan.

Sosai ya baza mutanen sa
suke lura masa da shiga da fitar sa, a yadda labari yaje wa ya fahimci dole akwai wani abu, domin shiga da fitan da yake gidan Anty Madeena yafi yawa..hatta fitan su zuwa asbiti tare da yarinya sai da aka sanar masa sai dai babu wanda yasan abinda ya kaisu, wannan dalilin ya sanya shi 'daura ayar tambaya akan Yarinyar, ba kuma zai samu natsuwa ba har sai ya tabbatar da cewa bata numfashi, Abinda ka'dai Allah ya hana Sultan fahimta game da yarinyar shine kamannin ta shi be taba tsayawa ya 'karewa kammanin ta kallo ba balle ma ya fahimci wani abu.

Sannan sun yi magana da Amrah ya kuma fahimce ta sosai, tun bayan zuwan su asbiti da Rayyan basu kara samun isashsen lkcn sa ba, gidan ma bari yayi gaba 'daya, tana kuka take masa bayani...tashin farko ya fahimci inda matsalar take, yasan babu mmk Rayyan ya gano cewa Arfan ba jinin sa bane shiyasa ya dauke musu wuta, in kuwa hakane asirin sa dab yake da tonuwa kenan, ayanzu Rayyan abinda ya sani kawai shine bashi da alaka da Arfan ya kuma yi reacting ina kuma ga cewar ya fahimci cewa yaron na sane...koma ya fahimta bazai bashi damar bayyana ta ga kowa ba.

Masu bibiyan masa diddigin Rayyan basu san cewa Anty sun riga sun fita tare da sauran iyalan ta ba dan su Rayyan suke bi, tun shigar sa unguwar kuma bai fita ba haka suma basu fita ba basu ga wani ya fita gidan ba haka babu wanda fita tun shigar sa.

Haka suka sanar da Sultan..dan haka yace kawai suyi kokari su haura gidan su banka wuta ta ko'ina ta yadda zai tashi lokaci guda kafin kowa ya farga yayi illar da suke bukata dan sam baya so Rayyan ko Anty Madeena 'dayan su ya fito araye......

Salmerh😘
[8/11/2022, 11:42 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...67*

.......Hakan kuwa akayi, lokaci guda kawai wuta ta kama ci a gidan, gateman kuwa dukan tsiya sukai masa sannan suka kulle shi cikin 'dakin sa ko motsin kirki bai iyawa.

Daga Rayyan sai Nuwaira cikin gidan, itama tuni bacci ya fara 'daukan ta dan haka bata farga da wutan da wuri ba har sai da wutar ta mamayi ko'ina cikin gidan..Lokacin da jama'ar unguwa suka farga da wutan take suka fara kawo 'dauki, a dai- dai lokacin ma'aikatan Sultan suka dulmiya cikin su kamar masu kawo 'daukin suma.

Ihun Nuwaira ne ya fargar da shi sai kuma salatin mutane da 'kauri da tiririn wuta dake ratso shi.

A firgici ya mike zai leka window yaga babu hali sbd wutar tuni ta hauro Salati ya fara ya nufi kofa sai dai ina tuni wutar ta ratso parlorn ta kama kujeru babu ta inda zai iya tseratar da kansa ma balle wani ban da ihun Nuwaira da ya ke iya jiyowa.

'Kofofin ma munafukai da jin wutar duk suka 'kara kamewa....Jikin bango ya kalla yaga babu fire estinguisher anan 'kasa, Parlon saman Anty ne ka'dai dama yake ganin akwai basu sa a kasan ba sa6anin gidan su da yake kota ina an sanya shi ko wani 6angaren.

Kuma wutar ta haura sosai abinda ma ya takaita saboda POP dake saman parlon ne shiyasa wutar ta tsaya iya 'kasan amma yasan idan wutar ta mai yawa shima 'din na iya tsagewa so yake ya samu damar haurawa saman stairs amma hakan ya gagare shi.

Ihun Nuwaira da yake faman ji yana sake rage sauti ya fi 'daukan hankalin sa sosai.

Kalle- kalle ya fara ko.zai samu abinda zai iya tallafa masa amma bai ga komai ba, 'Karfen labile da yagani ya jawo ya take da takalmin sa da yake labilen ya riga ya kama da wutar shima, da shi yayi amfani wajen kawar da abubuwan da ke cin wuta agaban sa ya tsallaka gefen da yake jiyo ihun Nuwaira.
Chapter 116 · 0% Book details