← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 218

Sashe 133

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanun sa ne ya sau'ka akan 'kofan 'dakin Amrah sai ya kasa kawar da idanun sa.
Tsam yayi da ransa tunanin sa na canza salo daga na Zaitoon zuwa na Amrah.
" _Sultaan...Amrah..._"
Ya furta 'kasan ransa.
A hankali ya saki 'kofar sa ya nufi 'dakin Amrah bai tatar da shi da lock ba hakan ya sa ya wuce ciki kawai.

Tsaye yayi yana 'karewa 'dakin kallo, sosai yayi 'kura, yasan kuma ba komai ya kawo hakan ba face da'dewar da yayi mamallakin sa bata nan.

Gaban ya tafi ya tsaya yana 'karewa shirgin ta dake jere saman mirror 'din kallo yana jin wani bugun zucia akai akai na mamayar normal hrtbeat din sa.

Baya so ya tuno komai, baya so ya tuno irin rainin hankali da cin amanar da bayin Allahn nan ke yi masa.

Under his roof, kuma da igiyar auren sa...abin ya munana sosai kamar yadda yake kuntata masa zucia a duk lkcn da zai tuna cewar 'dan ma da yake tunanin ta haifa masa shima ba nashi bane na Sultan ne.
" Sultaan fa, Sultan dake matsayin 'kani a wajen sa, Sultan mijin blood sistern sa, Sultyn Ammin su da take yi masa kirari da shi kafin abashi auren Marwa...

Wani jiri- jiri ya fara ji na shirin 'diban sa hakan yasa ya dafe bango numfashi ya fara saukewa a hankali yana tunano da me ya ragi Amrah a duniyan nan...ta ina gaza mata.

Sake 'dago idanu yayi ya sauke kan mirrorn nata, nan idanun sa suka sau'ka akan wani wristwatch.

Wristwatch 'din da ko.ba'a fada masa ba yasan na wanene..domin da kansa ya siyo a Dubai wani zuwa da yayi.

Sultan ne da ya gani yace masa yana so ya kuma bashi, ya gani a hannun sa ya kai sau uku bayan ya bashi 'din sai kuma yanzu gashi a 'dakin Amrah.

Wani 'kwarin gwiwa ne yaji ya shige shi.
Kan 'kafafun sa ya tsaya a har lkcn yana jin bugun zuciyar sa bai koma daidai ba.

Gaban madubin.yaje ya tsaya ya tsurawa agogon idanu batare da ya ko gwada kaiwa hannun sa ba.

Hannun sa mai lafiyar ya cusa cikin aljihun wandon sa 'kafafun sa a 'dan bu'de, yayin da idanun sa suka koma jajaye sosai jijiyan kansa suka fito.

Tun daga yanayin tsayuwar sa zaka fahimci ba dai- dai yake ba balle idan kaga fuskar sa da ta riga ta gama bayyana yanayin sa.

Wani kishi mai zafi yake jin na taso masa, tsawon wani lkc ya 'dauka yana tarayya da matar da bata san darajar kanta ba balle auren ta.

Tsawon wani lkc ya 'dauka ana yaudarar sa da ha'intar sa.
Rayyan ya da'de gaban madubin Amrah kafin ya bar 'dakin batare da hannun sa ya ta6a daidai da allura cikin 'dakin ba.

'Bangaren Zaitoon kuwa ko data farka sosai tayi mamakin irin baccin da tayi, domin har gari yayi haske kafin ta tashi ahaian ma still tana jin idanun ta da nawi.

Mufeeda dake gefen ta kalla da alamu ta jima da farkawa tana ta wasan ta kawai batare da ta takura ta ba.

'Ko'karin tashi zaune tayi sai taji duk jikin ta nayi mata ciwo tamkar an mata dukan tsiya.

Ba 'karamin mamaki tayi ba da jin hakan.
Koda ta gwada yin yunkurin farat 'daya sosai taji babu dadi ajikin ta har tsayuwar na neman gagarar ta.
Tayi mamakin abinda ya same ta kwarai da gaske, me ya kawo hakan meke faruwa duk bata sani ba.

A daddafe ta samu ta shiga bathroom ta cire kayan jikin ta tsab sannan ta tsaya 'karewa jikin ta kallo a gaban madubi..sbd yadda take jin jikin tan har na neman zarta tunanin ta.
Ko'ina ciwo yake mata hatta Boobs 'din ta.

Tuno wani abu yasa ta komawa ta jingina tana me dafe kanta sai hawaye shar suka gangaro.

" Wai har yanzu...?"
Ta tambayi kanta tana mai toshe bakin ta da hannun ta 'daya.
Kuka sosai Zaitoon tasha a bayin nan kafin ta ha'da ruwa mai zafi tayi wanka ta gasa jikin ta tana mai tunano rayuwar ta baya, sai dai ai dacan baya koda ta tashi ta tsinci kanta cikin irin yanayin nan bata jin ciwon jiki kamar wannan.

Haka ta gama wankan ta kuma yi wankan tsarki kamar yadda aka koyar da ita tun a baya..sannan ta fita ta gabatar da sallah.

Tana so ta tashi ta yiwa Mufee wanka ta shirya ta cikin shigar makaranta amma sam ta kasa yin hakan, jikin ta take ji babu 'karfi sosai.

Asali tun abaya takan yawaita yin mafarki kuma ta tashi ta ganta cikin wani yanayi amma ai an da'de sosai da ta daina, meyasa yanzu kuma?
Shin addu'o'in ta ta sun raunata ne ko kuwa mene..?

Tunani take yi sosai tana mai share hawaye, ita kadai tasan takaicin da take ji, ita ka'dai tasan 'kuncin da irin wannan abin ke jefa ta.

Ko abaya yayanta ka'dai ke sauraranta har ya kwantar mata da hankali, ayanzu kuwa wa ze maye mata gurbin sa, wa take da shi da zai saurari damuwar ta? Babu kowa.

Taso koda ka'dan ne ta tunano mafarkin nata amma ta kasa, kwata'kwata jin 'kwa'kwalwar ta take acushe.

Abu 'daya zuwa biyu kawai take iya tunowa.

Tasan ta shiga gyarawa Rayyan gado amma batasan yaushe ta dawo nan ba...toh ma indai ba tunanin ta ya 6ace bane ai dai tasan bata baro 'dakin ba bacci ya 'dauke ta, in kuwa hakane ya akayi ta ganta a 'dakin ta kuma...sosai abin ya 'daure mata kai.

Tana cikin wannan tunanin taji an turo 'kofa..da sauri ta 'daga idanun ta...nan tayi arba da Rayyan fuskar sa babu yabo babu fallasa, dan tuni ya kori duk wani 6acin rai da tunanin abinda ya shafi Amrah aransa, yace bashi da lkcn 6atawa wajen tunanin wa'danda basu san ma inda yake musu ciwo cikin jikin su ba balle su san na wani.

Idanu ya tsura mata ya kasa kawar da kansa.
Zaitoon kam kokarin mi'kewa tayi tana me share hawayen ta...amma jin zogi sosai yasa ta fasa mikewan ta koma ta zauna sai ga wasu sabbin hawaye.

Gira Rayyan ya 'dage yana duban ta yace.." Kuka...?"
Zuciyar sa na tsinkewa kar dai ta gane abinda yai mata.

A hankali ya tako ya isa gefen gado ya zauna yayin da Zaitoon ke daga gefen sa sai tayi 'kasa da kanta sosai.

Hawayen ta share tana me harha'do kalaman bakin ta ta furta masa" ina kwana, ya jiki..?"

Rayyan bai amsa ba kawai ya zuba mata idanu.
Ita kuma ta kasa kallon shi, gani take tamkar da ya ha'da idanu da ita zai fahimci damuwar ta.

" Me ya faru wai? Me ya same ki..?"
Ya tambaye ta a ha'de duk da bashi da tabbacin samun amsar ta yayin da ta wani 6angaren zai iya cewa ya ma fita sanin ainihin masar tambayoyin nasa.

Shiru Zaitoon tayi bata ce komai ba illa sautin kukan ta da ta yakara karfi.

Rayyan shiru yayi yana duban ta cikin ransa yake jin babu da'di, sosai yake ganin rashin kyautawar sa a fili, sai yanzun yake ji dama ya sani bai biyewa zuciyar sa ba, da yasani da be bi da ita da wannan hanyar ba.

Bai ce tayi shiru ba kamar yadda bai rarrashe ta ba illah Mufeeda da ya tashi ya 'dauko ya 'daura saman cinyar sa.

Sai da ta yi kukan ta son ranta ta fara tsagaitawa kafin ya sake maimaita mata tambayoyin.
" Ban ..jin...dadi ne...".
Ta bashi amsa a rarrabe.
" Subhanallah sannu, ina ke mk ciwo...?"
Tace" Ko'ina...".
" Kamar...?"
Sai tayi shiru tana me sake dukar da kanta.
" Toh kin sha magani ne...?"
Girgiza kai tayi alamar a a.
'Kasa ya 'dan yi da muryar sa tamkar wanda bai son wani ya jisa yace..." Wanka fa...? Kinyi...?"
Ta 'dage kanta sama alamar" erh.."
Yace" Wanka me kyau na tsarki...?"
Da sauri tayi 'kasa da kanta cikin gwiwoyin ta tana me jin wani iri da tambayar tasa, hawayen ta kuwa tamkar 'kara tuttu'do su ake yi, sai dai can 'kasan ranta tana mamakin yadda akayi yasan matsalar ta da har yake tambayar ta akan tsarki...waya sanar da shi ta ya akayi ya Sani? Ai ko yayan ta Habu da ada yake sanin damuwar ta ba haka nan kawai bane, ita ce ke sanar da shi da kanta.

" Baki ce komai ba..."
Ya sake jefa mata wata tambayar.
" Nayi..."!
Ta bashi amsa da muryar kuka a kuma cike da 'kosawa da tambayoyin sa.

Wani ajiyar zuciya ya sau'ke yana mai mayar da kallon sa ga Mufeeda, dama shi damuwar sa makomar ibadar ta ne, amma tunda ta fahimta har tayi wankan ai shikenan...sai dai shi kansa yayi mamakin yadda har akayi ta fahimci abinda ya faru cikin sauki hakanan, ba sai an bashi labari ba a halin yanzu ya san wace ita balle ya budi baki yace ta san hakan ne sbd ta saba aikatawa...in ma ya furta hakan yasan bai mata adalchi ba.

Toh in ma ta fahimta 'din yaji but wa take zargi aranta...?
Ya tambayi kansa.
Sam bai so ta zarge shi, aganin sa ai girman sa fa'duwa zai yi a idanun ta in dai hakane.

Toh kuma wa zata zarga in ba shi 'din ba, tunda tare suke su biyu a part din.
Ai bama ita kadai ba kowa ma idan yaji labarin abinda ya faru daga bakin ta shi zai zarga.

Amma a zahiri bai ga alamun tana zargin sa kan lamarin ba...toh wa take zargi aranta kenan..?"
Kansa ya kulle sosai.

Zaitoon ma kantan kullewan yayi da tunanin ta yadda ya san abinda ya faru da ita, sam ko kadan cikin ranta bata ji tana zargin kowa ba tunda tasan kanta batun yau ba...wannan tunanin.shine ya 'dan tsagaitar mata da kukan da take cike da mamaki a hankali batare da ta 'dago ba tace" Amma...."

Sai kuma tayi shiru.
" Amma me...?"
Ya sake tambayar ta cike da kulawa.
" Feel free to talk kar kiji kunya ta kinji...kin manta kece sama dani yanzu...I'm ur patient remember?...so amma me? tell me..."
Chapter 133 · 0% Book details