← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 218

Sashe 9

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da karin mamaki ya zaro idanu " 'Yar ki..? ya tambaya yana me jin tamkar mashi ta caka masa a kahon zuciya.." dama kina da 'ya ne ban ta6a sani ba Zaitun?"
"Da yake bada ita nake zuwa wajen aikin ba shiyasa ba kowa ya santa ba.."
" Ya subhanallahi!"
Ya furta a fili gami da kasa 6oye mamakin sa.

Sam bai zaci Zaitun tana da yarinya ba, bai ta6a kawowa aransa hakan ba duba da irin karancin shekarun ta, amma me yasa jikin ta bai nuna alamun hakan ba, duba daya zaka mata ka fahimci zallar kuruciya tattare da ita, ko yanzun ma da ya lura bayan ta da goyo bai kawo aransa cewa goyon nata bane...me kenan? me hakan ke nufi wai?"
Yayi wa kansa wannan tambayar yana me shafo gashin gansa daga keya har mafitan gashin.
Ba ya san yarda da irin amsar da zuciyar sa take shirin basa akan yarinyar...ji yayi jikin sa duk yayi sanyi.

Sake 'daga idanu yayi ya bi bayan ta da kallo duk da cewa tayi nisa da inda yake tsaye yanzun amma bai daina hango bayan ta.

Haka ya juya zuwa inda ya tunkara yana 'daga kafafu da kyar, dama wajen Hajiyar sa zashi da yake basu hadu da safiyar yau din kwata- kwata ba bisa ga rashin kwana da bai yi a gidan ba.

Washe gari da yamma kamar wasa sai taji ana sallama daga mashigar gidan da yake itace ke farko zata fi kowa saurin jiyo duk wani motsi da ya tunkaro gidan nasu. Ko da ta leko sai taga yaro ne" ka karasa ciki mana ai daga nan masu gidan baza su jiyo ka ba..."
Tayi maganar tana mai shirin mai da kanta data leko cikin dakin ta.
Yaro kam da ya san wajen wa aka aiko sa sai cewa yayi
" Wai ana magana da Zaitun a waje.."
Abinda taji yaron ya fada kenan da ya sanya ta tsayawa cak, ba ita kadai ba hatta tunanin ta sai da ya tsaya na wasu sakanni illah bugun zuciyar ta da ya kara sauri, lokaci guda tunanin ta ya dawo sai kuma ta lula can baya can a wancan lokacin da Abbale kadai ke aikawa ayi kiran ta kamar hakan dai.

Da sauri ta sake dawo da kanta sai dai madadin lekawan wannan karan gaba dayan ta ta fito dai dai lokacin da yaron ya juya zai maida aikan ganin bai samu gamsashshiyar ansa daga wajen ta ba.
"..Baka ji ba..?"
Da sauri yaron ya waigo...sai lokacin ma ta lura ashe dan makwabtan su ne duk da ba wata shakuwa ce tsakanin ta da gidajen ba amma yau da gobe tasa tana iya gane su.
" Wa ke magana da Zaitunan..?"
Ta tambaye shi tana mai kure shi da idanu.
" Wani ne..nima ban sanshi ba".
" Je ka tambaya sai kazo ka fada min kaji.."
Kai ya yaron ya dage mata gami da juyawa.

Ita kam tsaye tayi tama kasa 'daga kafafuwan ta..tunanin ta ya kasa bata shin waye zai zo neman ta...kar dai!...kar dai!!...kai um um bana tunanin hakan, amma ai shi kadai ne nake da yakinin zai iya nemo inda nake a duk fadin duniyar nan domin shi kadai ne ya damu dani shi kadai yake min kauna da dukkan zuciyar sa...amma taya YA BUKAR zai gano inda nake...a tunani na nayi tafiya me nisan da ni kaina bazan iya kiyastawa ba.
" Wai yace Adam ne daga inda kike aiki...".
Wata shegiyar ajiyar zuciya Zaitun ta sauke da ita kanta bata san ta menene ba sai dai tana da tabbacin cewa na jin cewa ba Yah Bukar ne me neman nata ba kamar yadda tayi hasashe, 'dan takaitaccen bayanin da yaron yayi ya sanya batare da dogon nazari ba ta fahimci waye ne..kuma tana da yakinin shima din yayi hakan ne saboda tayi saurin ganewa.
" Ba mamaki Hajiya ta aiko sa".
Ta fada a fili gami da komawa ciki.

Babban Hijabin ta da tun iya zaman ta shine kadai yalwataccen Hijab data mallaka kuma take matukar ji da shi shi ta sanya kalar Navy Blue sosai ya fito mata da kalar madaidaicin hasken ta ras.

Sai da ta gyarawa Feefy kwanciyar ta ta sake lullu6e ta saboda yanayi na sanyi da ake ciki sannan ta fita cikin natsuwa take takun ta kokadan Zaitun ba rawar kai tattare da ita.
Sallama tayi da 'yar muryar ta da baya fita da hayaniya.

Saurin waigowa Adam yayi yana me sakin kayataccen murmushi.." Barka da zuwa..fatan anyini lafia?"
Ta hada duk lokaci guda dan rasa ma yadda zata tarbe shi tayi, gefe guda kuma zuciyar ta na taraddadin abinda ya kawo sa..tsoron ta daya kar Hajiya Talatu ta aiko sa da mummunan sako, sam bata so ta rasa aikin ta musamman saboda rufin asirin su ma itada Feefyn ta.

Bai amsa gaisuwar da tayi ma san ba sai ma gyara tsayuwar sa da ya sake yi karo kusan na uku kenan" Sai naga wai kamar ba'a yi maraba da zuwan nawa ba, kar dai in takura ki Zaitun dan ni har abada bana da burin shiga hakkin rayuwar ki...."
Duban ta takai gare shi a karo na farko suka hada idanu take sai kuma ta kawar da idanun ta amma hakan bai hana Adam fahimtar me ke cikin zuciyar ta ba a lokacin dan kai tsaye ya fahimci kallo ne me cike da tarin tambayoyin da ba lalle nexta iya furta su ba dan haka sai cewa yayi" Gani nayi kamar a 'darare kike irin ba a son ranki na fito da ke a irin lokacin nan ba".
" Ni..ba haka bane..me Hajiya tace ka fa'da...min?"
Tayi maganar muryar ta na rawa sosai shiyasa duk maganar tata ya kasance a rarrabe.

Sai yanzun ya fahimci damuwar Zaitun din 'karara sai ya saki murmushin sa me burgewa, wani 'dan madaidaicin bishiyar Nyim dake gaba da su kadan ya kaiwa duba cikin daddadar muryar sa yace..." Nifa ba Hajiya ta aiko ni ba, ki kwantar da hankalin ki..yarinyar ki nazo dubawa ya jikin nata yanzu..?"
Tsabar jin dadin cewa zuwan nasa bai shafi aikin ta ba ya sanya ta lumshe idanu cike da jindadin da ita kadai tasan abinta ta bashi amsa"..auu Mufeeda, jikin ta da sauqi Alhamdulillah dama zazza6i ne na hakori kuma na bata magani..."
" Masha Allahu..Ubangiji Allah ya kara sauqi.."
" Nagode sosai ka gaida gida".
Ta fada tana kokarin juyawa cikin gida.
"...Zaitun kenan!..dukkan alamu dai sun bayyana cewa bani da damar ganin Mufeeda ko..?"
Dakatawa tayi daga tafiyar da tayi niyyan yi din, sai ta girgiza kanta.." Ba haka bane ba fa wallahi bacci take yi ne yanzun shiyasa.."
"Babu damuwa in da rai ai wani lokacin zan ganta duk dama na fahimci 6oye abarki kike yi shiyasa tuntuni ban ta6a ganin ki tare da ita ba".
Wannan karan kam bata ce da shi kala ba sai sallama da take sake kokarin yi masa.
" Zan ma tafi ba sai an kore ni ba ai".
Ya ce yana murmushi tare mika mata ledan hannun sa.." saura kice min Mufeeda bata bukatar su ni kuma inyi saurin fahimtar kadan suka yi.."
" Yah Adam...!"
" Dan girman Allah Zaitun ki ansa banason jan magana".
Yadda yayi maganar ne ya sanya Zaitun 'daga hannu ta kar6a ba wai dan ranta naso ba sai dan ganin yadda yayi kicin kicin da fuskar sa.
" Allah ya bata lafiya.."
Ya fada yana me juyawa yayi tafiyar sa.

Zaitun kam kasa motsawa tayi daga wurin zuciyar ta cike da wasi- wasi.

Wannan shine farkon sabon ta da Adam da kuma dalilin sa wanda a hankali batare da ita kanta ta farga ba Adam ya shige jikin ta.
Sau da dama yakan sayi abu idan ta taso wajen aiki ya bata yace na Mufeeda ne kuma tun lokacin da yazo gaishe ta da bata da lafiya bai sake zuwa gidan su ba sai bayan wani lokaci sannan ya sake yi mata bazata, ranar kam bai yadda ya bar kofan gidan ba har sai da Zaitun ta kawo Mufeeda ya ganta, bai 6oye yabawar sa kan yarinyar ba dan ko yaro karami ya dubi Mufeeda yasan yarinyar kyakykyawa ce ajin farko.

Tun daga ranar Mufeeda ta shige ransa...hidima kuwa sai abinda ya karu, da kansa yakan siyo mata riguna masu kyau wadanda Zaitun tasan sai ta hada kudaden aikin ta na wata biyu ma kafin ta iya siyan irin rigar guda daya..takalma da komai na amfanin yara da zai fito da martaba da kyawun su Adam baya gajiya da siyawa Mufeeda su, in Zaitun tayi magana yace " Wannan yarinyar taki kalar 'yan gayu ce Zaitun barni in fito da ita, kuma ma baki so ne nima in samu ladan marainiyar Allahn nan"
Dole Zaitun take jan bakin ta tayi shiru da yake da kanta ta sanar dashi cewa mahaifin Mufeeda rasuwa yayi tun yarinyar na jinjira ta kuma kara da fadin bata san kuma ina zata samu dangin sa ba shiyasa bata neme su ba.

Ko da ya nuna mata rashin kama da yaga basa yi da yarinyar sai cewa tayi" Kamar mahaifin ta sak ta dauko har hasken sa shiyasa banbamcin kamannin su da ita ya fito fili.

Adam kam batare da wani dogon nazari ba ya yadda da batun na Zaitun domin shi tun a kallon farko da ya yiwa Zaitun yaji ta shiga ransa, ko da yazo ya fahimci ta ta6a aure har da yarinya ma kaunar da yaji yake mata kokadan bai girgiza ba sai ma karuwa da yayi.

Yasan a yadda yaga ta riki aikin nan dole tana cikin matsalar rayuwa ne shiyasa yake dan rage mata wasu abubuwan duk
da kuwa kusan kullun sai ya dage kafin take kar6an duk abinda ya kawo mata.

Ya jima da fahimtar yadda ta riga ta sadaukar da lokaci, 'karfi da jin dadin ta ga yarinyar shiyasa yake tsananin tausayin ta gami da tayata kulawa da yarinyar a fakaice.

Ita kanta Zaitunan bai bar ta abaya ba..domin lura kawai yake da ita ya fahimci abinda take da karancin sa kawai sai taga ya kawo mata a bazata in taki ansa kuma ya nuna 6acin ransa shima.
Chapter 9 · 0% Book details