← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 218

Sashe 58

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana biyu da sallamo 'Dan Maliki yace ga garin ku nan, sai kiran Adam akayi aka sanar da shi yana tsaka da tunanin ta yadda zai dau mataki kan ciwon mahaifin nasa.

Sosai ya rikice ya fita hayyacin sa, bai ta6a zaton Alhajin zai tafi cikin kwanaki kalilan ya bar shi a duniyar nan ba...amma ba yiwa Allah gyara.

Shi kenan yanzu ya zam cikakken maraya ba uwa ba uba duk Allah da ya fisa sonsu ya dauke su.

Duk abinda ake so Adam ne yayi wajen dawo da Alhaji gida dan yi masa suttura da sallah Adam kasawa yayi sam ya kasa bawa kansa wannan kwarin gwiwar, da 'kyar da taimakon Hafeez komai ya kammala aka sada Alhaji 'Dan Maliki da gidan sa na gaskia.
Shikenan littafi ya rufu, Rakib da Atid sun gama aikin su, fa'di tashin duniya duk sun 'kare, numfashi ya tsaya cak, bugun zuciya ya tsaya, wahalhalu, jindadin dunia da walwala duk babu su, rayuwa kenan.

*( Allah Ubangiji ka ji'kan dukkan musulmai da suka riga mu gidan gaskia, Ya Rabbi ka kai haske 'kabarin su, Yah Allah kasa mu da muke rayen karshen mu yayi kyau, Allah ka bamu dacewa dunia da lahira, Yah Allah kasa mu cika da kyau da imani, kasa mu mutu muna jero kalmar Shahada Amin Yah Rabbal Alamin...)* 👏

_Salmerh_ 😰
[23/9/2022, 1:35 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...36*

.......Bayan da aka gama komai, zaman makoki ya kare kafin Adam ya 'dan sake, domin ranar da akai addua'n bakwai an yi nasiha sosai musamman ga Adam kan tawakkali da imani da kaddara.

Ya kuma fahimta ya rike ta hannu bibbiyu, yasan cewa kowa lokaci daman yake jira, mutuwan nan dole ce.
Abu guda dake sanyaya masa zuciya ma shine rabuwa lafiya da suka yi da mahaifin nasa, domin har ya koma ga Allah yana sakawa rayuwar sa albarka da fatan dacewa.

Wannan kadai idan ya tuna yakan kara masa karfin gwiwar cigaba da walwalar sa kamar baya, addu'a ce dai bazai fasa yi masa ba har 'karshen nasa numfashin, duk da bai da tabbacin yana da tsawon rayuwa shima.

Washe garin da akayi bakwai ya shirya shi da Hajiya Talatu da Hafeez da a cewar sa shima baza'a barshi a baya ba da shi za'a yi wannan tafiyar, haka suka yiwa Jahar Yobe dirar mikiya, ba'a kwan da su ba aka tashi dasu, ba'a san da zuwan su ba sai ga su, ba'a san da wanzuwar su ba ma a duniyar suka bayyana gare su kamar shigar mashi.

Farko gidan sarkin garin suka nufa da da bincike da komai aka gano dangin mahaifin nasa da ba laifi suna da yawa ga kuma karamci irin na dattawa.

Anan suka samu lbr ashe 'Dan Maliki tun yana yaro ya gudu ya bar garin, karatun almajiranci aka sanya shi sai kuma ya kasance malamin na da saurin hannu ga zafin duka kusan duk dukan da zai musu in dai da dorina ce toh sai ya fasa mk jiki.

Abin yana kona rana 'dan Maliki gashi kullun duk dole ne musamman idan baka kawo hadda daidai.

Da wani dare bayan sun tashi karatun dare 'Dan Maliki yasha dorina har sai da ta masa shati biyu ya damtsen hannun sa, 'daya ya fashe hadda jini 'daya kuwa bai fashe ba duk akan aya 'dayan karshe suratul Taghabun da bai kawo ba.

A zuciye ya bi bayan malam har turakar sa ya kwada masa dutsi aka ya gudu abinsa ya bar garin ya bar malam cikin azaba da tsiyayar jini har sai da akai masa dinki aka.
Cike da azaba yana dafe goshin sa yake fadin" Kai Jibrila ramuwa kazo kayi, ni ban isa in hukunta ka ba kenan, 'dan iskan yaro shaidanin banza, insha Allahu sai ka gani ai, sai ka bi dunia ka lalace...".

Sosai wannan lamari ya sosa ran Malami har ya yiwa 'Dan Malaki mugun baki kasantuwar sa mai kanbun baka sai kuwa bakin sa ya kama 'Dan Maliki.
Duk da duk da wani mai imani yasan cewa komai sai da nufin Allah, amma mun kuma san cewa littafi ko hdithi bai 'karya ta Kambun baka ba, ha'ki'ka Kambun baka gaskiya ne.

Koda aka nuna wa Adam Malamin murmushi kawai yayi suka gaisa a mutun ce dan Malamin ya tsufa jigif amma still tabon na nan a goshin sa bai 6ace ba.

Tun kuma fitar 'Dan Maliki wancan lokacin bai sake dawowa ba har sai da ya 'dauki shekaru masu yawa sannan ya waiwayo gida, a lokacin tuni mahaifin sa ya rasu saura mahaifiyar sa da kishiyoyin ta, su uku ta haifa 'daya ta rasu 'dayar kuma tayi aure cikin fulanin tashi sun kuwa tashi da ita har yau ba ita babu labarin ta, sai shi ka'dai, hakan yasa ya 'dauke mahaifiyar sa ya tafi da ita.

Tunda kuwa da ya 'dauke ta bai sake waiwayen kauyen ba har ya koma ga mahaliccin sa.
Duk yadda zan misalta muku yanayin tarin farin cikin da Adam ya tsinci zuciyar sa a ciki bazaku fahimta ku misalta da kanku.

Abu ne da ya jima yana muradi sai a yanzun Allah ya nufe shi da shi.

*****
Tun shigowar Rayyan gidan ta fahimci a yanayin da yake amma ta basar, tana kitchen taje daukan ruwan sha ta hangi.bayan sa ya shigo sai da ya zauna a parlour ya'dan huta kafin ya tashi ya 'karasa bedroom 'din sa.

Baki ta kya6e sam bata jin yau zata iya yi masa komai da yake da bukata, gaba 'daya ma jinta take tamkar wata marar lafiya tsabar wahalan da Sultan ya gana mata ayau din.
Tarasa mecece matsalar sa da Rayyan a rayuwa, abinda ya mata yau din ta fahimci kamar duk huce takaicin sa yake yi akanta da bashi da wata hanyar sai ita, ba yau tasan halin sa ba, duk lokacin da ransa ya 6aci da Rayyan akan ta yake sauke duk fushin sa sai ya tabbatar ta jikkatu kafin yake barin ta.

Kamar dai yau ma haushin sa ya sauke mata yana kananun surutai bata kuma san mene ya hada shi da Rayyan din ba.

Ga kuma Rayyan cikin yanayin da sam bazata iya da shi ba kuma.
Dan shima din ba sauqi ne da shi ba har yama fi Sultan, matukar tace zata jarraba kusanta kanta gare shi kuwa tana jin sai dai a 'dauki gawar ta a yau ba sai gobe ba.

Tuno yadda Sultan ya lalata mata aikin gyaran da ta kwana biyu tana kaffa kaffa ya sata jan tsaki hadda 'yar 'kwallar ta, ta tabbatar ba zallan jarumtar sa da ta sani bace, dole akwai abinda yasha da gangan dan kawai ya wahal da ita.
Hawayen nata kuma sai ya kasa tsayawa.

Sai data tabbatar ya shige 'dakin.sa ya rufo sannan ta fito ta koma 'dakin ta itama.

Rayyan da tun shigowar sa ya ji gidan shiru ya sa direct ya wuce 6angaren sa, sai da ya watsa ruwa ya huta kafin ya tashi hannun sa rike da wayar sa ya nufi dakin Amrah...gajiye sosai yau yake jin kansa hutu sosai yake bukata bana wasa ba.

Luf take kan gado lullu6e da bargo har kanta, ganin hakan ya sa shi 'karasawa wajen ta cike da mamaki dan yasan ba lafiya ce zata sa Amran cikin wannan yanayin ba.

Musamman ma dan ganin bata zo ta rungume shi kamar yadda ta saba duk sanda ya dawo gidan ba, a hankali ya 'karasa gare ta dan tabbatar da lafiyar ta.
" Amrah lafia..?"
Ya tamabaya yana tabbata saman wuyan ta zuwa fuskar ta cike da kulawa.

Kuka kawai ta tsinke masa da shi tana mai mayar da kanta bisa cinyar sa da ya lankwasa ya zauna bakin gwadon 'kafar sa 'daya akasa.

" Baby zazza6i ciwon kai, ko ina ma ciwo yake min ajiki na..."
Ta 'karasa da rungume shi sosai ajikin ta tana sake sakin wani kukan shagwa6an.

Dagaske Rayyan yaji jikin ta da zafin zazza6in.
Amma bai iya yace komai ba.
Sai da ta gama kukan taja ajiyan zuciya kafin yana shafa bayan ta yace" Very sorry..".
'Dan lumshe idanu tayi ta dube shi tana gyara kwanciyar ta ajikin sa.
"...Tun yaushe ya fara miki?".
" Tun safe fa Baby".!
Ta bashi.amsa cike da shagwaba.
" nd baki kira kin sanar da ni ba, kuma ai munyi waya 'dazun baki sanar da ni ba why..?"
" I'm so sorry Baby, ban san ina tayar ma da hankali ne fa...".
" Come on, wani tashin hankali kuma Amrah? akwai tashin hankalin da ya wuce zaman ki cikin ciwo ne..pls kar ki sake irin hakan kinji..?"
Kai ta gyada masa ana mai sake narkewa a jikin sa.

" Alright..let me get some drugs...ko Clinic zamu.?"

Da sauri ta girgiza kanta alamar a a.
Bai ce da ita komai ba kawai ya fara kokarin mi'kewa yana cire hannun ta dake cikin nasa itama ta 'daga kanta data aza bisa cinyar sa.

Har yaje 6angaren sa ya samo mata maganin da ruwa bata yi motsin kirki ba tsoro take kar ya gano ta.

Koda ya kawo da kansa ya bata tasha sannan yace zai je sallah itama kar ta koma sbd maghrib ta gabato zai je ya dawo.

Fitar sa yasa fargaban Amrah 'karuwa, ta rasa ma wani tunani zata yi ayau in ta bari Rayyan ya ra6e ta ai bata jin zata tashi araye ayadda take jin jikin ta.

Wlh sultan ya cuce ta ba 'dan kadan ba.
Ta raya a zuciyar ta cike da jin haushin sa.
Sai ma bayan fitar Rayyan da ta gwada tashi zuwa bathroom ta fahimci illar da yai mata, tafiya wannan da kyar taka ta yi.

Sosai ta sake gasa jikin ta fin wanda tayi 'dazu, sai kace yau tafara sanin 'da namiji..."

Ta 'karashe da jan tsaki.
Kafin ya dawo tayi sallah sharp- sharp ta koma ta kwanta kar ma ya dawo yagan ta da 'kafafunta yayi zaton ta samu sauki dan haka ta sake komawa tayi luf.

Shi kam daga masallaci 6angaren Ammi ya nufa..sai da ya shafe kusan mintina talatin acan kafin ya dawo 6angaren nasa.

Abinci ya tambayi Amrah taci tace erh..dan bama tajin cin komai ayau 'din in ba yazam mata dole ba.
Chapter 58 · 0% Book details