Sashe 121
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cike da raunin murya ta fara magana ta yadda Marwa zata ji ta...." Ammi ta 'kaunace ni ta 'yanta ni, Ammi ta bani gata, ta bamu dangi tai mana sittira ta faranta mana ni da Mufee na, Ammi ta zame mana garkuwa ni har 'diyata a lkcn da bamu da duk wannan ni kuwa me nake da shi? me na mallaka da zan saka mata da shi baya ga in ganta cikin farin ciki..farin ciki me dorewa na. har abada, wallahi Marwa matu'kar Ammi tayi na'am za kuma tayi farin ciki toh nima na amince, sai dai bisa shara'di 'daya...."
Marwa da gudu tazo ta rungume ta out of excitement hawayen farin ciki na sulalo mata ita kanta Zaitoon 'din ma hakan ne...tuni kukan ya 6alle mata...ba kowa take tunawa ba illah Yayan ta, tasan bata kyauta ba, a yau ta yankewa kanta hukunci batare da sanin sa ko amincewar sa ba.
" Dan Allah fa'da min, fa'da min shara'din dan Allah Zaitoon..."
" Hannu takai ta na share mata hawayen take cewa" dube ki sai kace wacce akace mk lafiya zan bawa yayan kin..."
Da sauri Marwa ta kawar da kanta tana murmushin farin ciki tace
" Bar min hawaye na, bar min su su sauka iya san ransu, a yau dadin su nake ji fiye da komai dan tafiya suke min da kullin dake cikin zucia ta, after all ma ai ke ma hawayen kike, ni dai fa'da min shara'din naki dan Allah yanzu..."
" Da zarar ya samu sau'ki zai sallami auren dan inaso ko bayan sallah babba ne in koma gaban iyaye na kuma bana so su san da wani batun aure akaina...."
Marwa bata ce komai ba sai sake rungume Zaitoon da tayi, lkc guda kuma ta sake ta tayi waje da gudu cike da tsantsan farin cikin da bazata iya misalta shi ba, dan farin ciki ne na cikar burika da dama dake ranta.
Da Ammi ta fara cin karo itama rungume ta tayi har Ammi na firgita ta kuma ce..." Kai Marwa ke meyasa kullum baki sanin girma ne pls..?"
" Ammi guest what...".
Tayi maganar tana 'yar tsalle.
" Toh fa..kede fa'da min kawai Allah yasa alkhairi ne dai, yanzu na baro wajen Rayyan da sai ince ko shine ya farfa'do da kike irin wannan murnar"
Ammi ta 'karashe maganar da rauni.
" Ammi shima Yayan da iznin Allah zai farfado ai muna masa addu'a ba dare ba rana..."
" Toh menene fa'da min...".
Ammi tayi maganar tana mai kokarin cire Marwa cikin jikin ta.
" Zaitoon ta amince da auren Yayah, yanzun nan ta sanar da ni, tana ma can kuma tana kuka na barota...".
Karaf a kunnen Raihana.
Ta kuwa kasa 6oye farin cikin ta itama.
Yayin da Ammi ta 'dan bu'de idanu akan Marwa.." Bangane ba Marwa, dama waya fa'da mata da har ta amince 'din...?"
" Bansani ba wallahi Ammi, amma dai inaga su Anty ne.."
" Toh ba dole tayi kuka ba, wama yace musu su sanar da ita, sun mata caa aka kam ba dole shakkan su yasata ta amince ba, ni na aiki wani daga cikin su ne ko kuwa nace musu na amince da batun auren..."
" Ba haka bane fa Ammi, ni sai ita ne fa muka yi maganar kuma tun 'dazun nake wajen ta wallahi babu wanda ya tilastata ra'ayin ta ne na kanta, kuma tace sbd Allah da kuma ke, amma bisa shara'di..."
Nan ta zayyano wa Ammin yadda sukayi.
Ammi rasa abin cewa tayi...da baya da baya ta koma kan kujera ta zauna tana sakin ajiyar zuciya mai zafi da har wani jiri jiri yake sata ji.
" Marwa 'kira min ita please..."
" Ammi baki ga halin da take ciki bane, ki bari zuwa gobe sai kuyi magana da ita".
Washegari a 6angaren Rayyan suka ha'du, kallo 'daya zaka yiwa Zaitoon ka fahimci bata kwana cikin yanayi mai dadi ba.
Hakan yasa Ammi jin tausayin ta ba 'dan kadan ba...ta kuma kasa sakewa a a yau din dan sai take jin tamkar ta za'ke da yawa ne duk da yake su ne suka bu'kaci tallafin ta.
Bayan ta kammala aikin ta tana niyyar tafia Ammi ta dakatar da ita.
Ammi bata yi 'kauran baki ba ta tambaye ta ta kuwa amsa ta cike da dakiya.
" Zaitoon kiyi hakuri kinji..nasan baki da ra'ayi kan maganar da su Raihana suka je mk da ita amma bazan 6oye mk ba nayi matu'kar mamaki da jin amincewar ki wanda nima naji abakin Marwa, Zaitoon in babu wata damuwa ko zan iya sanin dalili...?"
_Salmerh_ 😘
[16/11/2022, 11:59 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
*Wattpad@*
_Serlmerh-md_
🅿️ *...70*
......." Saboda Allah na amince Ammi da kuma ke...."!
Zaitoon ta bata amsa cike da dakiya domin in dai zata biyewa zuciyar ta, yadda take ji da banda kuka babu abinda zata sawa Ammi a wannan lkcn, sai dai dole ne ta bawa kanta 'kwarin gwiwa bisa abubuwa masu dama, ba dan komai ba sai dan kawai taga bata karya zu'katan wa'danda suka mutunta a rayuwa ba, taga cewar ta rama alkhairin da suka yi mata da wani alkhairin ko da bai kai wanda su suka yi mata ba.
A ganin ta Ammi tafi 'karfin komai a wajen ta musamman ma a yanzu da ta tabbatar tana da bu'katar taimakon nata da gasken gaske.
" Zaitoon kar ki biyewa su Raihana ki takurawa zuciyar ki akan abinda kika san ba ra'ayin ki bane, aure wa Rayyan ba wai dole bane kawai sbd wasu dalilai ne da na tabbatar akwai auren da babu shi babu abinda zai canza shi, sai dai kasancewar auren na iya sau'ka'ka al'amura ba ma ka'dan ba, kar ki tilastawa zuciyar ki dan nima ba wai na sa auren nasa araina sosai bane...".
Kai Zaitoon ta girgiza tana kallon gefen Ammi tace.." Ammi in dai har su Anty Raihana da Anty Madeena da kansu zasu same ni har 'dakin da nake zaune kan wata magana toh na tabbata mai muhimmanci ne, kuma akwai dalili kwakkara da zai sa su nemi taimako na, Ammi ban manta ku 'din su waye agare ni ba balle na iya juyawa maganar ku baya, Ammi kiyi fatan alkhairi tsakanin yin sa ko barin sa Allah ne zai bayyana mana, nima din ta 6angare na hakan ne, bazan kuma gushe ina neman za6in Allah ba har sai naga abinda ya tabbatar min...".
" Zaitoon ki fahimce ni, bana so a takura mk ko shiga hakkin ki akan wannan maganar koka'dan asan wace ke na kuma wasu daga cikin ra'ayoyin ki duk da ba kowanne ba amma ina da tabbacin baki da ra'ayin wani aure dai dai da 'kwayar zarra cikin ranki..toh mene amfanin sa...?"
Shiru Zaitoon tayi tana duban gefe ban da sara babu abinda kan ta ke mata amma bata so tun yanzu Ammi ta gama fahimtar rikitar yanayin ta balle ta cigaba da tuhumar kanta bisa tursasawar da ta ganin sun mata bayan tasan Ammin sai tafi kowa farin ciki idan ta amince da auren Rayyan kawai 6oyewa take cikin ranta.
Ammi ce ta cigaba da fa'din..." Ki 'kara zurfafa tunani kinji 'diya ta, idan kin tabbatar zuciyar ki tayi na'am da batun ina tabbatar miki da cewa sai na fi kowa farin ciki akasin hakan ma bazan ta6a ganin laifin ki ba Zaitoon..."
Wasu siraran 'kwallan da suka zubo mata tayi saurin sharewa cikin ranta ta ayyana" _Anzo wurin_ !...dama tasan hakan ne kamar Ammi tasan menene cikin ranta adaidai lkcn.
Tana mai 'kakalo murmushi a zahiri ta furta" Ammi na gama tunanin fa shiyasa ma na yanke shawara kuma har zuciya ta, ba wannan ba Ammi ko wani abin ne daban da ya fi wannan girma matu'kar bai sa6awa addini ba Insha Allahu zan iya mk shi Ammi indai har zai sa zakuyi farin ciki da faruwar shi, domin kun min fiye da yadda zan iya yi muku a duniyan nan...ba kuma zan yi sbd abinda kukai min bane kadai Ammi, ba kuma sbd kunyar kar in ce a a kuji babu da'di ba ne, zan yi ne kawai sbd Allah da manzon sa, baya ga haka ma Ammi kin manta na 'dan lokaci ne ba wai na har abada ba Insha Allah ba wata matsalar da za'a samu daga 6angare na na kuma yi mk al'kawari zan yi fiye da yadda kuke tsammani daga gareni da iznin Allah Ammi.....".
Cike da farin cikin da ke fitowa tun daga zuciya Ammi take fa'din " Nagode..'diyata, nagode sosai Zaitoon Ubangiji Allah yayi mk albarka ya albarkaci rayuwar ki data zuri'ar ki, Insha Allah nima nai mk alkwari da zaran Rayyan ya samu lafiya hankula suka 'dan kwanta zan bincika mk iyayen ki zan kuma fahimtar da su su kar6e ki ke da 'diyar ki a yadda 'kaddara ta gina ku, Insha Allah za ki rayu cikin farin ciki tsakanin 'yan uwa da dangin ki tamkar kowa...".
" Allah yasa..!Nagode Ammi..."
Yadda Ammi tayi farin ciki da wannan lamari kar ku tona zuciyar Raihana, Marwa da Anty Madeena, banda sauran 'yan uwa da suka zo daga wasu garuruwan domin duba jikin Rayyan din, suma da zarar sunji labarin abinda mahaifiyar Amrah tayi sai suji babu dadi, gashi Raihana da Anty Madeena sam basa rufe maganar da gangan suke bayyana ta ga kowa sbd a 'kalubalanci lamarin a kuma yi saurin amincewa da batun Zaitoon.
Kamar wasa sai magana ta tsaya akan ranar Friday bayan sallar Juma'ah za'a 'daura aure.
Alhaji Rufa'i ne zai yi wakilcin Rayyan while mijin Anty Madeena shine ya bada auren ya kuma kar6i sadaki.
Sultan jin zuciyar sa yake tamkar zata yi bindiga sbd takaici.
A ganin sa sai ma da batun auren ya taso gadan- gadan yake ganin wani kula da kaffa- kaffa da akewa Zaitoon da 'diyar ta...abin sosai yake ta6a shi dan hatta Marwa daina ganin fara'ar sa tayi cikin kwanakin.