← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 218

Sashe 126

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

......Tunanin Zaitoon ya tsaya ne dai- dai da tsayawar numfashin ta, tsaye ta mike cak numfashin ta na kokuwa da juna wajen fita sbd al'jab, cike da mamaki ta zaro idanun ta waje sosai, sake maido da duban ta tayi kan gadon ganin wayam babu kowa.

Take ta sake kallon sa akaro na biyu domin tabbatarwa idanun ta, Rayyan ne ko kuwa wani mai kama da shi ne....?

Tsam ta tsaida idanun ta akansa, yayin da yai mata duba 'daya kawai ya 'dauke idanun sa daga kanta.
Rayyan ne ya fito daga bayin dagaske ba wani ba.
Ta tabbatar wa zuciyar ta hakan.
Cike da tsananin mamaki take duban sa, shi kam cigaba yayivda tafiyar sa da take da 'kyar kuma a dur'kushe tamkar wani dattijon da 'karfi da lafiya sukai masa 'karanci, hannun sa na hagu dafe a cikin sa yake tafiyar kuma a hankali.

Jikin sa farar singlete ce da bakin dogon wando..kallo 'daya zakai masa ka fahimci irin muguwar ramar da yayi..tamkar ba Rayyan da tasani abaya ba.

Cike da mamaki Zaitoon ta ringa binshi da idanu sam bata san har haka aka samu cigaba ba...kuma har zuciyar ta taji tana taya Ammi farin ciki da samun sauqin 'dan na ta ko ba komai alamu sun nuna cigaban lafiyar yafi na baya tunda gashi da 'kafafun sa...yayin da gefe guda kuma kanta take tayawa farin ciki, domin alamu sun nuna ta kusan samun 'yancin kanta itama.

Sai ma ta rasa shin wazata gayyato yazo yaga abin da idanun ta ke gane mata, ko kuwa ihu zata yi dan bayyana farin cikin ta, Amrah..kai a a...Marwa...Marwa tana gidan ta yanzu haka, Anty Madeena ta tafi, haka ma Anty Raihana...sannan bata da waya balle ta kira wanin su...da ace ma tana da wayar da Ammi zata fara yiwa wannan albishir din ayanzu.

Dan rasa abin yi kawai sai tsurawa maganin dake hannun ta idanu amma tunanin ta baya tare da shi sam, sau 'daya idan ka.kalli fuskar ta zaka hasko wannan kwantaccen farin ciki dake tasowa tun daga zuciyar ta...murmushi ya kasa barin fuskar kwata- kwata.

Sai da ta rintse idanu ta bude su akan hannun ta tana mai sake kallan maganin domin bazata iya sake duban inda yake ba.

Shima maganin bazata iya gane komai ba, amma data tsaida idanun ta akansa sai ta kasa tuno me irin kalar shi cikin magungunan da Ammi ke bashi, wannan kalar sa yellow ne, cikin wa'dancan kuma babu yellow, takaddar jiki kam bazata iya tantance su ba amma kalar maganin ba zai 6ace mata ba dan sau tari da ita ake basa...abu guda daya da har yau bata iya yi masa ita ka'dai shine goge masa jikin sa, inma zata yi toh sai dai in goge masa iya inda yake waje ne, misali kamar saman kafa'dun sa hannayen sa da 'kafafuwan sa.

Shima 'din tun ranar da taga irin ba'kin tabon da Mufeedan ta ke da shi a jikin sa bata 'kara ba...dan da zarar ta gani sai taji zuciyar ta na tsinkewa da 'karfi gami da fargaba.
Dr Fawwaz ke masa sauran.

Bazata manta ba ko ranar ma Dr Fawwaz din yasa ta zama, inda yace lallai ta zauna taga yadda yake yi sbd ta koya da kanta ba sai sun ta jira azo a gyara masa jiki ba.

Bata ce da shi komai ba kawai tayi murmushi.
Hakan kuwa ta tsaya sai dai kusan rabin tsayuwar tata kaita a 'kasa yake...lkc lkc ta kan 'dago kai ta kalle su sai ta kuma sunkuyar da kanta, a lkcn cikin sa Dr Fawwaz ke goge masa da wiper dake hannun sa.
Har ta sunkuyar da kanta sai kuma take ta sake 'dagowa dan tabbatar da abinda idanun ta suka gane mata.

Madadin taji fargaba sai taji murmushi ya kubce mata.
Cikin rai ta ayyana irin na Moopy na.."
Har ila yau dai ga wani abin da kuka yi tarraya kansa kai da Moopy na bayan yanayin hallitar lips 'din ku.

Ko bayan fitar Dr Fawwaz kasa nutsuwa tayi, sai da ta sake 'daga singlete 'din sa ta zubawa ba'kin circle dake gefen cikin sa idanu.

A hankali ta kai hannu ta shafo shi..tana murmushin mugunta, har hasko yanayin fuskar sa take yadda zaiji idan ya ji cewar wannan abin ma Mufeedan ta nada irin sa.
Kamar an tsikare ta kuma ta cire hannu gami da mikewa tsaye..sakamakon wani faduwar gaba da taji.

A waNcan lkcn Mufeeda na can makaranta...sai lkcn tashi ya kusa take zuwa ta taho da ita gida...amma hakan nan ranar kasa zuwa tayi sai dawo mata da yarinyar driver yayi shi ka'dai.

Tun kuma ranar bata 'kara yadda taga abin ba sbd fargaban dake ziyartar ta.

Ko yanzun ma tuno wancan ranar da tayi yasa ta saki wata 6oyayyar ajiyar zuciya gami da murmushin mugunta ta cigaba da bin maganin da idanu.

Zuciyar ta fal farin ciki ta shiga bayin da ya fito ta tsabtace shi, duk tasan ba wani datti gare shi ba dan ba kowa ke amfani da shi ba duk da hakan kusan kullum takan tsabtace shi.

Tana yi tana tunanin ta yadda zata yiwa Ammi wannan kyakkyawan albishir 'din gashi ita ba waya ba bata kuma san ranar da zata dawo ba.

Sai dai ko in sun hadu da Marwa tayi mata albishir din ita kuma ta tayata isarwa ga Ammi.

Baiwar Allah kusan kullum sai ta sashi agaba tayi ta kuka da hawaye, sosai take son 'dan ta amma ma'kiya sun musu katanga.

Lokacin da ta fito abayin sai taga ya koma ya kwanta kamar yadda ya saba kullum duk yadda akayi yanzun ma babban uzuri ne ya tashe shi, to ko tsawon wani lokaci ya 'dauka cikin wannan halin oho, tsawon wani lokaci ya 'dauka yana tashi da kansa yy wa kansa abu batare da ta sani ba, ko kuwa dai yau ne farko...duk bata da amsa.

'Kofar fita ta nufa fuskar ta cike da murmushi yayin da hannun ta ke rike da na Mufeeda.

Rayyan tsurawa bayan yarinyar idanu yayi, yana jin wani sassanyan yanayi na shigan sa, sai ma ya rasa albarka zai sawa Zaitoon ko kuwa mai zai mata.

Kamar tasan zai bukaci ganin 'diyar sa a yau din nan ta kuwa zo masa da ita...ji yake tamkar ya janyo yarinyar ya rike ta a wurin sa gudun kar wani abu ya saman masa ita.
Sai dai hakan ma ya gode wa Allah daya 6oye wa kowa ita, ya gode Allah da bai yi azar6a6in bayyanata tun san da ya fahimci cewa jinin sa bace ita, da yanzu a zaman jinyar sannan bai san me zai faru gare ta ba,...Alhamdulillah, Alhamdulillah kawai yake ambata cikin ransa.

Zaitoon har ta kusa fita sai kuma ta dawo da baya, gaban gadon nasa taje ta tsaya ganin ya sake maida idanun sa ya lumshe amma tasan ba bacci yake kamar na baya da basu da tabbacin ranar farkawar sa, sa6anin wancan yanzu da kansa ya kwanta ba kwantar da shi akayi ba, za kuma a iya tashin sa ya tashi ba kamar baya ba... kuma sarai yasan da wanzuwar ta a cikin 'dakin sai dai sam bai nuna alamun hakan ba.

Magani ya kamata yasha first amma bata san ta yadda zata mai bayani ba..batasani ba ko zai bu'kaci wani abin daban bayan maganin.

Take sai ta diririce tama rasa mai ya kamata tayi.
Ashe dai dama 'karyar sakewa take a 'dakin nasa ashe dan baya cikin hayyacin sa ne yasa take sakewa.

Gashi yau Dr Fawwaz ya makara dan bata ga alamun zuwan sa ba sam.
Babu mamaki ma sai yamma zai shigo, 'kila wani uzuri ya ri'ke shi.

Da 'kyar ta saisaita sautin muryar ta a hakan ma muryar na rawa kanta a'kasa tafara fa'din.." Kayi hakuri...dama an wa Ammi 'kiran gaggawa ne yau da sassafe ta wuce Maiduguri amma ga wannan magungunan ta aiko wai kasha...".

A hankali ya bu'de idanun sa ya tsayar akan maganin da ta 'dago tana nuna masa...koda ace kullum idanun sa a lumshe suke amma hakan bazai hana shi gane kalan nashi maganin ba, balle ma tunda yaji tace wa'dansu sai ya ji bai yadda da maganin ba, ledar maganin ya kalla sannan ya sake bin hannun ta da kallo da ke rike da magungunan.

Sai yaga kuma gashi an cire takaddar jikin wasu dan kar agane wani irin magani ne ma kenan.

Shiru yy bai tanka mata ba illa maida idanun sa da yayi kan Mufeeda kallon sakan hudu yai mata ya sake maida idanun ya rufe su.

Ji suka yi ana nocking 'kofar lkc guda... da mamaki ta kalli 'kofar dan tasan bayan shigowar ta bata kulle har da key ba.

Kallon juna suka yi ita da shi lokaci guda, hakan yasa shi mi'ka mata hannu, maganin ta bashi da 'dan jan jiki ya tashi zaune dan har yanzu yana jin jiki ciwon jikin sosai

File 'din sa dake kan side drawer ya bu'de da yake ciki da biro, amma babu damar ya yagi 'daya daga cikin takaddun domin duk bisa tsari suke.

Zaitun kam binsa da idanu kawai take cike da tsananin mamakin sa, yayin da farin cikin da ke mamayar ta yake rinjayar mamakin a hankali.

Kansa ya dafe sai kuma yayi saurin kamo hannun ta har ta firgita sai kuma taga bai bi ta kan firgicin nata ba, rubutu layi guda yy mata cikin tafin hannun ta while ana cigaba da bugun 'kofan daga waje.

Yana gama rubutawa ya ajiye biron ya koma ya kwanta kamar ba shi ne ya tashi zaune yanzun ba.

Zaitun sai da ta sake duban sa kafin ta dubi hannun ta inda yy rubutu da mamaki, me hakan ke nufi kenan?
Ta tambayi zuciyar ta.

Bugun 'kofar da aka sake yi gami da ambatar sunan ta ya sata saurin ankarewa domin idan kunnuwan ta basu yi mata karya ba sautin muryar Ammi taji ta 'kira yi sunan ta.

Zuwa tayi ta bu'de tana sakin ajiyan zuciya tace.." Ammi har kin dawo? ina cikin bathroom ne ina aiki wlh banji bugun ba..."
Ta 'karashe maganar da sakin ajiyan zuciya mai sanyi...gami da jinjina karyar da ta gamawa shirgawa.

" Bakomai..."
Ammi tace tana mai bin ta da kallo sama zuwa 'kasa.
Chapter 126 · 0% Book details