Sashe 147
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kansa ya shafo yana sake 6oyayyan huci, du'kar da kansa ya sake yi sosai sannan yace " Baffah wallahi..ina jin shai'danu ke firgitata cikin bacci...tana yawan firgita sai ta yi ta kuka abin ya jima yana damun ta to na sanar da Baffah tun kwanaki nama yi zaton zai same ka da maganar ne bansan bai sanar da kai ba..."
Kai Baffah ya jinjina da mamaki yace" Ita Zaitunar shai'danu ke firgitawa shine kuma yayi biris da maganar..?"
Shiru Bukar yayi..sai shi Baffa Liman 'din ne ya cigaba da fa'din...Ni dai bansan wani irin mutum ne Ahmadu ba, yanzu ko wani abin ne daban haka zai yi shiru akai bazai sanar min ba har sai abu ya lalace ko...".
" Ayi ha'kuri Baffah ina jin mantuwa ce yayi".
Cewar Bukar da ke sake yin 'kasa da kansa, sam bai san cewa Abban nasu bai sanar da Baffah Liman ba da ba zai ma zo ba..dama da Baffan ya fa'da ne to da tuni kawai zai masa kan maganar amma yanzu kam sam bazai iya ba, sai dai ya koma ya sake tunawa mahaifin nasu 'kila zai zo ya masa bayanin dalla-dalla tunda shi yasan komai akai.
Cikin zuciyar sa yake wannan tunanin da kansa a du'ke...amma sai yake ga kamar hajan kuma ba mai yiyuwa bane dan sarai yasan waye mahaifin sa yasan halin sa kamar yunwar cikin sa, abu ne mawuyaci ya iya zuwan musamman sbd ita.
Mahaifin su bai wani damu da damuwar su ba, bai damu da 'kuncin su ko farin cikin su ba, bai damu da duk halin da zasu tsinci kansu aciki ba, shi dai bai san me yake damun Abban na su ba amma halin ko un kula da yake nuna musu abin na damun sa arai sosai, ace mutum tsakanin ka da iyalan ka daga abinci sai abinci baka damu da jin damuwar su ko kuma tsaya musu kan lamarin da ya taso musu ba, to ma bai damu ba balle idan ka sanar da shi yy maka maganin damuwar ka...kullum gari na wayewa ya bar gida sai kuma yamma zai dawo babu damuwar sa da sanin ya kuka kwana balle ya kuka tashi, shi kansa idan yana so ya ha'du da shi su gaisa sai dai idan sun fito daga masallaci idan kuma basu ha'du masallacin ba sai dai ya taho gidan sassafe tunda duru-duru.
Shiyasa yake matu'kar tausayin 'kanwar tasa Zaituna, domin ita bata da kowa agidan, sai Allah, bata da wanda zai jata a jiki yaji damuwar ta sai shi kadai, bata da wanda zata zauna tayi hira da shi kaf cikin gidan sai shi ka'dai.
Shiyasa shakuwar su ta ninka ta kowa.
Dan ko can wajen mahaifiyar ta ma da take zuwa Iyami ta sa mahaifin su ya hana ta zuwa kwata-kwata da mummunar doka akan hakan kuma...in ba rashin imani da tausayi ba menene wannan haka, yarinya da mahaifiyar ta araye ace kuma an shiga tsakanin su kar su yi zumunci, wannan zamanin mace na da tsayayye akanta ma ya aka 'kare ballantana kuma babu wanda zai jata ajiki yaji damuwar ta....
Maganar Baffah Liman ce ta katse masa dogon tafiyar da yayi
"...Kana jina ko Bukar..?"
Saurin gya'da kansa yayi.
Baffan ne ya cigaba da fa'din.." Ka turo min ita Zaitunar da kanta zaifi kasan sharri na shai'danu ai babu dadi...amma banda abu na irin na Ahmadu ai bai kamata yy shiru kan hakan ba...kai de ta shi kaje ka cigaba da hatkokin ka..Allah ya shi albarka ka turo min ita da Allah ko zuwa gobe ma..."
" Insha Allah Baffah zan turo ta...Allah ya 'kara girma.."
" Amin Amin Buba ka gayar min da mahaifiyar taku..ina wannan gagaren kuma sarkin surutu Ummaru?"
Murmushi Bukar yayi yana saka takalma yace" yana nan duk lafiyar su kalau Baffah"
" Toh madallah...Allah yai muku albarka ya tsare mana ku".
Yana amsawa da Amin ya bar Baffah Liman 'din zuciyar sa cike da neman wata mafita.
Ai ya riga yasan halin Zaituna ko tazo babu abinda zata iya cewa Baffahn nasu domin ko shima lokacin da ta gaya masan wayon ta da saura yanzu kam ko ya tambaye ta sai de kawai tace masa mafarkin nayi.."
Kwanakin nan kam ma sai dai kawai tayi ta zabga uban kuka bata fadin komai, Iyami kuwa na jinta duk da yake ta riga tasan matsalar amma bata ta6a nuna damuwar ta akai ba sai de ta kya6e baki,
bai san ko dan cewa ba ita ta haife ta bane oho.
Allah ma ya taimaka babu wani bare da yasan labarin dan ko ita Zaitunar ya hana ta fa'diwa kowa baya ga hk da yanzu yasan ana can ana ta yama'di'di da su a gari bacin bb wanda ya fi karfin Allah ya jarrabce shi da makakamanciyar ta...cuta ce ya kuma san tabbas tana da magani, yasan addu'a ce kan gaba shiyasa ya fara koya mata addu'o'in tsari daga shaidanu tun a farko kuma Alhamdulillah yasan zuwa yanzu ta haddace su.
Yana kan tafiyar ya yanke shawarar abinda yaga yafi masa arai...dan hk washe gari kashe ranar yayi gaba 'daya ya bar san'ar sa ya nufi cikin garin na Maiduguri dan niyyar neman mafita wa 'yar kanwar tasa...domin ba zai iya zuba idanu yana ganin ta cikin damuwa koda yaushe ba da wanne zata ji ma.
Da yake Maidugurin ba ba'kon sa bane can ya saba harkokin sana'ar sa ba tun yau ba yana kuma da wani aboki shi yy masa jagora zuwa wajen wani babban malamin sunna...anan ya samu cikakken bayani kan abinda ke damun Zaituna wato namijin dare...sosai yayi masa bayani ya kuma fahimce shi, daga 'karshe ya bashi addu'o'i a rubuce masu yawa, ya hada masa hadin magani da musulunci ya bamu damar amfani da su duk yayi masa bayanin komai, 'karshe kuma wani 'kullin magani ya bashi wanda zata na shafawa a jikin ta idan zatayi bacci.
Godiya sosai yayi wa malamin barin ma da yaki kar6ar ko sisin sa yace in sun sake haduwa zai ansa, haka ya dawo gida jikin sa sanyi kalau sakamakon jiyo sirrin mafarkin kanwar tasa da yayi.
Sosai lamarin ya karya masa zuciya, Zaituna nawa take da har hakan zai ringa faruwa da ita, suma aljanun basu mata adalci ba sam aganin sa, Zaituna yarinya ce mai natsuwa da kuma kamala, sam bata da rawar kai uwa uba ma'abociyar suturta jiki ce ita, bacci wannan da haijabin ta take yinsa kuma ko cikin gidan bazaka ta6a ganin kanta bb hijabi ba...Sallah ma baya ta6a wuce ta duk da yasan ba wani karatun addini mai zurfi ne da ita ba amma ko a ina zai yi shaidar Zaituna kan riko da addinin ta....karatun allo dukkan su suka yi wajen wan mahaifin su wato Baffah Liman, amma babu laifi yasan sun san kan addinin su.
Shidai Bukar yayi sau'ka har sau biyu amma Zaituna bata yi da nisa ba dan kwata- kwata bata fi izu biyar ba..amma Alhamdllh duk da hakan yasan tana sau'ke hakkin addinin ta dai dai gwargwado, to me ya kawo mata wannan matsalar kuma? gashi sam shi bai da sani akan hakan, shiyasa tun da shekaru biyu kenan da suka wuce ta sanar da shi irin mafarkin da take cewa wani mutum yana danne ta a bacci tayi masa bayanin abinda yk yi mata, ta kuma ce ita tsoro yake bata sosai, a yanzu kuma sai salon abin ya canza domin tace masa idan mutumin ya danne ta kuma da safe sai taga wani abu a jikin ta.
A lokacin yayi mamaki sosai..amma hakan bai sa ya 'daga hankali ba domin ba akai akai take yin irin mafarkin ba, wani lokaci har sai ya manta ma sannan take ce masa tayi...da kansa ya ringa koya mata addu'o'in da zata ringa yi..kuma Alhmdllh duk wadanda ya koya mata ta iya su.
To da abin ya dame shi shine ya samu Iyami da zancen ita kam sai ta kya6e baki tace to ita ina ruwan ta ita tasan inda ta yayibo aljanun ai..
jin kalmar aljannun da Iyami ta furta ne yasa abin ya tsaya masa aransa hakan yasa ya tunkari mahaifin sa da maganar inda yayi masa bayani dalla-dallah, abin mamaki sai yy biris da maganar tamkar ba abin damuwa bane aka sanar da shi..
Shima kansa har ya fara mantawa da batun sai gashi kwanaki bai fi wata biyu ba ya same ta tana kuka ko da ya nemi jin abinda ke faruwa sai tace masa mafarki tayi.
Ido ya zaro sosai yace mafarkin kike wa kuka 'kanwata?"
" Yaah ni dai bana so bansan yadda zanyi ba"
Yace baki yi addu'a kafin ki kwanta ba ko. .?"
Tun ma kafin ya rufe baki ta bashi amsa da fadin" Wallahi Yaah nayi ban ta6a mancewa ba ko sau 'daya, kuma ina yin alwala kullum..."
" Masha Allah, toh kar ki damu kinji kanwata, Insha Allah watarana duk zaki daina su tun da muna addu'a babu fashi..zamu yi ta rokon Allah ya yaye miki yasa ki daina yi kinji.."
Ranar da kyar ya samu ya kwantar mata da hankali...shiru shiru kuma abin ya lafa sai jiya ya sake samun ta kuma still Mafarkin ne...so abin ya dame shi gaskiya kuma yasan Zaituna bata da wanda zai tsaya mata sama da shi, tunda an riga an shiga tsakanin ta da mahaifiyar ta dole shi'din ne dai....
Da dawowar sa ko gidan sa bai shiga ba ya wuce gidan mahaifin sa dan yiwa Zaituna albishir 'din ya samo mafita sai dai ko da yazo bai same ta gida ba wai sunje barka da ganin wajen jinjiri gidan Babaji...
Bukar baiyi mamaki ba sam dan sarai yasan halin 'kanwar tasa da tsananin son yara musamman 'yan jirajirai...
Gidan sa ya koma ya yi wanka ya ci abinci ya huta sai dare ya dawo bayan yy sallar maghrib ya shigo, kan wata yagaggiyar dadduma ta ya same ni na sallame sallah ina zaune shiru kamar me tunani... Ya kuma san bai wuci batun mafarkin ne ke raina ba har yanzun.