← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 218

Sashe 103

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ma Moopy, dan tana ganin sa da ta gama 'kare masa kallo bayan ta tabbatar shine sai ta fara mi'ka masa hannu tana kya6e baki.

Nuwairah kam Anty Madeena ta kalla sai ta ce da ita kaita wurin sa.."
Tuni Moofy ta fara kuka ganin kamar Baza'a kaita wurin san ba, ana bata shi ta rungume shi tsam tana 'kara volume 'din kukan ta...shima rumgume ta yy sosai a jikin sa yana jin wani iri cikin zuciyar sa..." Mam..mie.! Mammie!!
Ta fa'da da alamun son ganin ta kawai take yi.

Jikin sa sanyi 'kalau yy cikin ransa ya jinjina irin wannan 'kaunar, lalle ya 'dauki alhakin bayin Allahn nan, Itama uwar ya tabbatar tana can ta fice hayyacin ta ita kuma wannan ta makalkale shi da tunanin zai kaita wurin Mammie...

'Yar murmushi yayi yace" Aiki Jaa..."
Wannan fari ne, jan na zuwa daga baya...
Kallon ta yayi da alamun tambaya sai ta 'dora da" Cire rigar jikin ta ka gani..."

Kallan Antyn yayi amma ganin yanda ta saka serious face ya sanya shi yin kamar yadda tace.

Rigar ya cire yana 'dan lalla6a ta da fa'din" Mamin ki kk so ko Baby...bari I wld take u to her...pls stop crying Mammies Angel..?"
Ita kam sai ajiyar zuciya take saukewa.

Yana gama cire rigar Anty Madeena tace" Kalli gefen cikin ta..."
Dubawa yayi amma baiga komai ba..sai ya 'daga kai ya kalli Anty yace" me yake faruwa ne Anty banga komai bafa..hala ciwo taji...?"

" Duba dai da kyau zaka gani..".
Sai ya kalli 'dayan gefen nata...kasa 'daga idanun sa yy akan wurin a hankali ya kai hannu yana shafawa Muphy kam jikin sa ta kwanta har yanzu tana sau'kar da ajiyar zuciya..'kasan ma'koshi ya furta " Ikon Allah...".

Ba wannan ka'dai ba Rayyan, yanzu kai baka lura da kamannin yarinyar nan da kai ba, dubi fuskar ta pls..bakin ta hancin ta hatta idanun ta irin naka ne..ni kaina ban ta6a lura da hakan ba sai yanzu..Rayyan kar ka 6oye min dan Allah ka gaya min gaskiya..".

Kai ya girgiza yace" Wallahi Anty bb wata ala'ka ta jini tsakani na da wannan yarinyar baki ga mahaifiyar ta ba ban san taba, ban taba ganin ta ba wlh sai a gida kawai da Ammi ta kawo ta...".
" Sam ban yarda ba Rayyan...dole akwai wani abu..ko kai ko Sultan...ba dan Kabeer ya jima da rasuwa ba da sai ince har da shi tunda kammnnin ku 'daya ne da gaba 'daya..."

Shi kam ido ya zuba mata yana kallon ta bama fahimtar ta yake yi sosai ba, shi kansa yy mamakin wannan lamari...sak fa irin nasa wannan ba'kin abin..inba ikon Allah ba waye ya isa yy haka, da ace shi me neman mata ne da sai yace shine yy cikin yarinyar amma yasan ba haka bane sam bb mata a tsarin rayuwar sa, especially matan banza ya tsane su, ya tsani duk mai irin harkar ma, me zai yi da wasu mata can har ya 6ata lokacin sa wajen su bayan Allah ya hore masa abinda zai yi aure ya kuma kula da rayuwar su ya kuma bashi damar ajiye 'dai 'dai har guda hu'du me zai yi da wata mace daban a waje?...amma shi kansa yayi mamaki, meyasa yake dan ganin kamannin Nadia tattare da yarinyar? musamman dazu da zai fito da ita daga gida har sai da hakan ya doki zuciyar sa.
......Fawwaz da ya fa'do ransa ne ya sa komai ya tsaya masa cak, kardai dagAske shima abinda ya lura da shi kenan har yake zargin ko 'diyar sa ce ko ta 'yan uwan sa , babu shakka, amma ai shi yasan babu komai, kuma ma in dai hakan ne dagaske mecece ala'kar sa da su, shifa haka ya gansu tare da Ammin sa, da dantashi ne ma da tuni sun bar gidan tun farkon zuwan su, me ma zai sa ya haifi 'diya kuma ya bari ana yawon bara da ita, ko da ace bata hanyar aure ya haifa ba baya jin zai iya bari....

'Dagowa yayi ya kalli Anty Madeena data tsura musu idanu, gani kawai take taMkar Mufeedan tsagin jikin sa ne, yadda yarinyar ta rungume shi ba kowa bane zai iya shakkar fa'din cewa shi'din mahaifi yake agare ta...muryar Rayyan ya dakatar da ita daga dogon tunanin data fa'da.

" Anty ku fahimce ni mana, babu komai babu wata ala'ka tsakani na da su wlh Anty, kawai ikon Allah ne, kinsan yafi gaban hakan, fiye da hakan ma sai ya aikata ba abin mamaki bane, haka fa Fawwaz yaso ya 6atan rai lastweek...sai da na nuna masa 6acin raina kafin ya bar zancen..."

" Kai kuma da yake kai sauna ne har abin alfahari kaek ganin ka aikata da nuna masa 6acin ran naka ko...?"

Dagowa yayi ya kalle ta sai ta cigaba" Erh mana.. me ze hana daya fa'di hakan baka sa kai ka bincika ba, inma ka tabbatar da cewa kaine sarkin wawnnci ba, ai ko ba da kanka ba sauran 'yan uwan ka fa....?"
.." Haba Anty...!"
Ya zaki ce haka? wauta ce dan ban kula da maganar ba..?"
" 'Kwarai kuwa ai inda ba 'kasa nan ake gaddamar kokawa, kuma in ba anga alamu ba za'a fara fadin hakan ne.."
" Anty bayan nasan babu wata ala'ka da zai kawo hakan mai zai sa in damu kaina ko in takura kaina da wani bincikawa...ni 'din nan ne dai kuma nasan bamu da wata ala'ka, ban ta6a sanin yarinyar nan ba sai da nazo gida na tadda Ammi ta kawo ta...Allah ne shaida ta...."

Shiru Anty Madeena tayi tana duban sa.
Amma meyasa sam zuciyar tata kasa yadda cewa basu da ala'ka, dole akwai wani abin dai...
Ta tabbatar wa kanta.

Tuni Mufeeda tayi bacci ajikin sa, hakan yasa ya fahimci yinin ranar kaf batayi baccin ba.
Ya kuma fahimci Anty Madeena basu bata drop din da zai sata baccin ba kamar yadda ya fa'da.

A hankali ya kwantar da ita gudun kar ta farka ya tashi kawai yayi waje ko sallama bai yiwa Anty Madeenan ba.

Ko da ya isa gida direct 6angaren sa ya wuce har akayi maghrib kuma bai shiga 6angaren Ammi ba.

Da suka gaji da jira ne Marwa ta bawa Ammi shawarar ta6o shi a waya, ita kanta 'kage take da ganin yarinyar..." Can't wait to see this cute baby in her school uniform..."
that's what Marwa keep saying throughout the day..duk damuwar da Zaitoon take ciki ita bashi ne gaban ta ba...dan tasan ko giyar wake kullum Rayyan kesha bazai kwatanta abinda Zaitoon ke zaton zai aikata ba, me akayi akayi Mufeeda da har zai zalin ta, babba ma Rayyan ba kowa yake da lokacin tankawa ba balle Mufeeda.

Tasan duk abinda ke faruwa tsakanin su coincidence ne da kuma sakawa arai da Zaitoon tayi...Babban abinda ke damun zuciyar ta kuma shine rashin yadda da yake hana ta sakewa da mutane...ciki kuwa har da Rayyan...kuma babban abinda ya fara haifar musu da sa6ani kenan...sai dai zata yi 'ko'kari ta daidaita wannan kafar Insha Allah.

'Karan wayar sane ya yanke masa tunanin sa.
Ammi ce, ya kuma san abinda zata tambaya, hakan yasa kawai ya shuri silifas 'din sa ya yayo 6angaren ta.

Da sallamar sa ya shigo Ammi da Marwa suka amsa yayin da Zaitoon ta dube shi da jajayen idanuwa tana le'ko bayan sa, ji yayi daria na shirin 'kwace masa a yadda ya gantan tamkar ganyen paw- paw da ruwa ya gaza masa, yasan cewa an yini aikin kuka ne yau din.

Zama yayi yana amsar gaisuwar Marwa, me kike a gidan nan har yanzu baki tafi gidan ki ba...?"
Yace yana duban ta.

" Yah Sultan nake jira.."
Ta bashi amsa tana yin 'kasa da kanta.

" Har yanzu bai dawo ba ne...?"
Ya sake tambayar ta.
" Erh Yayah...".
" Anya kuwa, ki dai je ki duba, tun kusan 12 ya bar office fa wai baya jin da'di inaga ma yana can gida fa ke kuma kinyi zaman ki anan baki san wani hali yake ciki ba...."
" A a fa Yayah munyi waya yace min zuwa 8 zai shigo mu wuce".

Shiru Rayyan yayi da tunanin ko Sultan 'din bai sanar da ita bane gudun kar hankalin ta ya tashi.

Ga Ammi ya maida hankalin sa ya gaida ta amsa ta kuma 'kara da fa'din.." Nace wai ko makarantar yini da kwana aka kai mana yarinyar...?"

Kansa ya dan shafa ya na jin bai kyauta ba da bai zo ya sanar da su ba tun daowar sa gidan...shaf ya mance ne da hakan kwata- kwata bayan zafin da Anty Madeena ta 'kara masa..." abin mamaki yanzun ma sai naga baka shigo da ita ba ko wajen Amrah ka baro ta...?"
Cewar Ammi tana masa kallon mamaki.

" Ohh no tana can fa na mance ne, tana wajen Anty Madeena tun da azahar,...".

Wani sassanyar ajiyar numfashi Zaitoon ta sau'ke da har sai da yasa duk suka kalle ta sannan Rayyan da Ammi suka 'dauke kansu suka cigaba da magana.

" Toh haka muka yi da kai ne? duk kabi ka tayar mana da hankali a banza, kuma ma ai sai ka 'kira ka sanar da ni amma kayi shiru ina ta 'kiran wayar ka kuma baka responding...".

"afwan Ammi ban kyauta ba na sani amma sharrin mantuwa ne, Insha Allah gobe zan sa adawo da ita gida immediately when they are off...."
" Da dai yafi kam...ya batun makarantar toh...?"
Ammi ta fada tana gyara zama dan sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta.

" An gama komai nd they offer her everything suna can gidan..."
" Masha Allah...Allah ya saka da Alkhairi yayi maka albarka..ka jini shiru batun suna k, shirme tayi min ai caa tayi wai asaka Aisha Zaitoon Kyari...shirme fa shiyasa ma kaga ban kuma 'kiran naka ba..."

Da mamaki yace Aisha Zaitoon kuma, mance sunan uban tayi ne ko me...?"
" Wai ita hakan tafi so asaka mata.."
Ammi ta 'karasa da duban Zaitoon da kanta ke 'kasa yayin da Marwa ke 'yar daria da jin yadda suka yi da Ammi dan a time 'din bata shigo ba shiyasa bata sani ba.
Chapter 103 · 0% Book details