← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 218

Sashe 101

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dabara ce ta fa'do masa dan har ga Allah bai san ta yadda zai lallashi yarinyar ba, shi ba gwanin lallashi bane balle yace zai ma gwada, wayar sa ya zaro yana sake gyara ri'kon da Mufeeda tayi masa.

Youtube ya hau ya searching children Rhymes ya kunna mata...hadda 'kara sautin muryar ta yadda zai dauki hankalin ta sosai.

Ya kuwa yi nasara domin a hankali ya 'dan zamo da ita yana nuna mata wayar idanun sa na kan fuskar ta dake ji'ke da ruwan hawaye.

Wani bugawa da yaji zuciyar sa tayi masa har sai da ya sashi dafe 'kirjin sa yana lumshe idanu a hankali ya bu'de idanun ya sake sau'kewa saman fuskar ta haka kawai fa yaga fuskar Nadian sa ta wulga a kan fuskar yarinyar, abinda bai ta6a gani ko lura ba sai yau 'din ka'dai.

Sai da ya zuba mata idanu kafin ya yadda da gaske fa yarinyar na 'dan shige da Nadian sa..." Allah mai iko..." ya furta cikin zuciya
Yayin da sautin kukan Mufeeda ke raguwa a hankali tana bin wayar dake hannun sa da kallo.

Sake mi'ka mata yayi bayan fahimtar ya samu nasaran janyo hankalin ta.
Da 'kyar yayu dauriyan da harshen sa ya iya furta " Come on...take it and see your friends playing..hho..."
A hankali ta sa hannu ta kar6a tana sakin wuyan sa da ta ri'ke, shi kuma ya sake bin fuskar ta da kallo a hankali, sosai tsabtar da ake mata yake matu'kar birge shi.
Shiyasa baya shayin dau'kan yarinyar sam kuma ko can cikin zuciyar sa ya kanji tana shiga ranshi sbd wannan tsabtar...Marwa hadda 'karyar turaren yara duk take siya mata idan ta fita shopping kuma Zaitoon na mata amfani da shi, 'kamshin ta kullun mai sanyin dadi sosai Rayyan yake jin natsuwa a yadda suke zaune da yarinyar.

Abu guda ne bai so game da ita yadda yake jin bugawar zuciya indai ya sanya idanun sa cikin nata sai kuma yau da acewar sa shai'dan ya shigar da fuskar Nadian sa kan tata alhalin yasan 'karya ne babu wata ala'ka da ta gifta tsakanin su, duk da bai san dangin Nadia kaf ba amma a iya sanin sa basu da mai suna Zaitoon balle wannan da Ammi ta tabbatar masa da cewa a garin Bauchi suka hadu har ta taho da su.

Bayan shu'dewar wani 'dan lokaci data shagala da kallon Rhymes 'din daya sake duban fuskar ta ta sai kuma bai ga fuskar Nadian ba.
Hakan ne ya sake tabbatar masa da zargin sa ma cewar shai'dan kawai ya raya masa ko 'dazun ma.

Sai da ya 6ata tsawon mintina uku yana tayata kallon dan hankalin ta ya kwanta kafin ya zame a hankali ya zaga ya shiga motar ya tada ya durfafi hanyar gate.

Mufeeda sam bata ma kula da hakan ba hankalin ta naga wayar dake hannun ta ne.
Bai zame ko'ina ba sai bakin gate 'din CONCORD ACADEMY...yasan makarantar akwai tsada sosai amma tsarukan makarantar suna matu'kar birge shi ba tun yau ba, sannan professional teachers da suka san me suke yi suke aiki dasu, haka nan kawai ya tsinci zuciyar sa da bashi shawarar kawo ta CONCORD bai kuma san dalili ba, nan take kusa unguwar su Anty Madeena tsakanin su ba wata tazarar kirki bace.

Sosai hankalin Mufeeda ya 'dauku ga kallon Rhymes 'din shi kansa sai yaji baya son ma ya yanke mata, musamman sbd gudun kar ya dawo mata da kukan ta baya.

Ko da yayi parking 'din juyawa yayi yana duban ta ko 'daga kai bata yi ba ba balle tasan abinda yake yi illa ido data tsurawa wayar tana kallon tana tatta6a fuskar wayar.

Fitowa yayi ya zaga ya bu'de 6angaren da take sai lokacin ta dube shi.
Hannun sa 'daya ya mi'ka mata da nufin tazo su tafi ita kuwa sai ta kalli hannun sannan ta kalli wayar dake hannun ta.

Mi'ka masa tayi da tunanin ko abarsa yake so tunda tasan cewa dai ba nasu bane.
Bai 'ki ba ya amshi wayar sa sannan a hankali yace" Baby muje ko, we ar almost getting late..."
Yana maganar ne gami da 'dago ta ya fito da ita.

Yadda yake tsammanin tsadar makarantar ma har ya wuce tunanin sa, bai tabbatar da hakan ba sai da aka bashi list 'din expenses na skul 'din kafin ya sake tabbatarwa.

Sai dai kuma baiga laifin tsadar tasu ba bayan karance list din expenses ya fahimci komai su ke badawa kama daga Lunch box na yaro sneekers hatta da socks zasu bada kala biyu sai dai in kanaso daga baya ka 'karo ma yaron ka but same sample.

Sai da yayi sighing na acceptance kafin aka sake bashi form ya cike mata wanda shine shaidar zamtowar ta cikkiyar 'daliba a CONCORD ACADEMY.

Wannan lamarin na faruwa ne duk Mufeeda na manne da jikin sa tayi luf kai baka ce ta ta6a yin kuka akan shi ko ta ta6a gudun sa ba .

Sai da suka nemi yi mata passport kafin aka 'dan so yin daga da Mufeeda abin mamaki sai ta'ki bin kowa daga cikin su ta ma'kal'kale shi.

Rayyan murmushi yayi da ganin hakan, sam bai ta6a zaton Mufeeda zata so shi akan wasu ba, har can cikin zuciyar sa yaji da'din haka, take sai yaji wata 'kaunar ta ta ta taso masa da bai san daga ina ba.
Da kanshi ya kaita wajen passport din aka 'dauka da kalar background da suke so kafin suka dawo office din head of the school din dan cigaba da cike form 'din da ya fara.
Sunan ta shine abu na farko da zai fara rubutawa kuma bai sani ba, kallon sa ya kai gareta amma yasan itama ba cikakkiyar amsa zai samu daga wajen ta ba ya sani.

Sai da yabi sauran ya gama cikewa har wajen Guardian inda ba tare da tunani ko tantamar komai ba ya rubuta sunan sa, wajen signing na mahaifi shima ya buga signing dinsa.

Sai da ya gama cike duk inda ya dace shi yayi kafin ya 'kira Ammi a waya yake tambayar ta sunan yarinyar.
Ammi ta ce da shi sunan ta _Aisha..._
" Ammi Aisha ka'dai ai ba suna bane i mean her full name fa..."

" Toh wannan ne dai ka bari in tambayo maka Zaitoon gaskia nima ba sani nayi ba...".

'Dan 'karamin tsaki ya sau'ke yana duba agogon hannun sa.
Sosai ya shiga lokacin sa gashi yana da ayyuka masu dama agaban sa, akwai kayan da zasu yi exporting kuma bai gama saka hannu ba, gashi yau zasu yi voucher na biyan ma'aikatan su duk kuma sai ya sa hannu.

Tuno hakan ya sanya shi fara rubuta Aisha dan rage aiki kafin Ammi ta 'kira ta sanar da shi sauran sunan, dan yana kyautata zaton daga haka ya kama komai, sai dai yana fara rubuta Aisha kafin ya ankara har Muhammad ya biyo baya.

Ya ankara da hakan ne kafin ya rubuta Sa'ad ko Auta dan haka sai yayi saurin ajiye biron yana cika iska cikin bakin sa ya lumshe idanu.
Dai-dai lokacin da aka taking excuse aka gabatar da passport 'din Mufeeda da aka 'dauke ta.

Sake kallon sunan yayi _Aisha Muhammad_ ya maimaita saman la66an sa a hankali yakai hannu ya 'dago Form 'din yana mi'kawa PC da fatan Allah yasa sunan mahaifin nata da Ammi zata tambayo ya kasance Muhammad 'din ne kamar yadda ya rubuta.

Mufee ta so yin rigima lokacin da zai tafi amma da yake suna da wajen wasan yara sai suka ja hankalin ta da wannan, dama Marwa ta saba kaita irin wuraren yawo dan haka basu sha wahalar 'dauke hankalin ta da wannan ba musamman ma data ga yara sa'oin ta nata wasan su tuni itama ta zage, da wannan time 'din Rayyan yayi amfani ya zame ya bar skul din ya nufi ma'aikatar su.

Sha biyu da rabi ya ga 'kiran sabon number da yayi saving da PC wanda suka yi exchanging numbers kafin ya bar skul 'din bayan wanda ya ajiye wajen cike form.

Shaf ya mance ma da batun yarinyar sai da yaga call 'din PC.
Goshi ya dafe dagaske ya mance da ita....bai yi niyyar fita bama a lokacin dan niyyar sa sai time 'din sallar azahar kawai zai fita sbd ayyuka amma da ganin call din tuni ya mi'ke ya rusa waccan tsarin...gashi Sultam ma ya fita wai baya jin dadi da duk tara masa ayyukan duk zai yi.

Da hanzari ya dauki abinda yasan yana da bukata ya fice kiran PC na sake shigo masa yayi saurin 'dagawa domin bai samu daman daukan kira na farkon ba.

Batun yarinyar ya tunasar da shi kamar yadda ya tsammata take ya tabbatar musu da cewa yana hanya.

" Innalillahi..." ya furta idanun sa na kan Mufeeda da tazo ta rungume shi...bayan kukan da tasha tuni tayi sanyi.

Anan PC ke tunasar da shi mantuwar da yayi na rashin kawo mata abinci da bai yi ba ya dafe goshin sa, wallahi shaf ya mance ne amma bai yi niyyar barinta da yunwa ba, ayyukan dake gaban sa ne suka sha kansa..wani tausayin yarinyar ya tsarga masa ya mmayi ilahirin zuciyar sa, gaba 'daya sai yaji ya ma karaya.

Bayani PC ya cigaba da yi masa cewar amma ya gafarce su sun bata biscuit da abinsha sbd kar ta galabaita duk da sunsan haka ya sa6awa dokar makaranta amma ba yadda zasu yi ne, Nannyn su ta kawo ta tana kuka kuma lokacin breakfast ma tace bata ga tana cin abinci ba shiyasa suka bata.
Rayyan yace" bakomai.."

'Dago ta sama yayi yana sake rungume ta yake fa'din" So sorry Baby.. "
Yayi maganar yana share mata fuska da sky blue hankicin sa.

PC ne ya gabatar masa da Uniforms nata har guda biyu, ga game dress nata Blue house take, textbooks, takalmi, socks, lunch box da sauran duk tarkacen da skul zata bata...Duk sukai masa packaging.
Haka ya tattaro ta da kayan suka fito zuwa mota.
Chapter 101 · 0% Book details