← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 218

Sashe 41

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A kan zuciyar ta take jin Hafsat dan ita ka'dai ce danginta take ji a kaf fa'din rayuwa, kauna da burin ganin farin cikin Hafsat shine mura'din ta a ko wani lokaci, ace kuma yau ga wannan Hafsat 'din 'dauke da ciki a jikin ta bata jin akwai wanda zai kaita kaunar cikin nan koda kuwa mahaifin cikin ne.
Son dunia Hjy.Talatu ta 'dora wa cikin nan kamar a jikin ta yake, banda tausayin Hafsat din daya sake cika mata kirji, tana ji dole ne a wannan ga6ar tayi wani abu dole ne ta tsayawa Hafsat wajen ganin ta samu 'yan cin ta, bazata sake bari Jibrin ya cutar mata da 'yar uwa ta kyale ba, duk yadda taso 6oye kauna da farin cikin bayyanar cikin Hafsat din sbd tsanar halin Jibrin amma kasa jurewa tayi.

Manya ta ha'da da maigidan ta da yake babban mutun ne shi mai kuma dattako ta ha'da da manya daga cikin dangin mahaifan su inda ta sanar da su halin da Hafsat take ciki.
An zauna da Jibrin an yi masa fa'da an kuma nuna masa kuskuren sa ya amince tamkar gaske ya kuma basu haku'ri gaba 'daya, hatta ita Hafsat din sai da ya bata hakuri da kansa batare da wani yace ba, amma suna dawowa gida ya kama Hafsat ya jibga son ransa ya mata dukan tsiya, dukan da yasa hatta cikin jikin ta sai da ya fita duk wai sbd karar san da takai.

Hajiya Talatu ba 'karamin bakin ciki tayi da faruwar lamarin ba taci alwashin sai ta kai 'karar sa ga hukuma a hukunta sa amma maigidan ta ya hana ta, acewar sa tsakanin mata da miji ba'a shiga, ciki kuma Allah ke bada shi idan yaso zai 'kara basu wani aduk lkcn da yaga dama, batun duka ne dai sai da aka sake masa magana dan sai da Hafsat tayi sati kwance a gadon asbiti kafin ta 'dan warware..kowa baiji da'din lamarin ba.

Daga asbiti Hajiya Talatu gidan ta ta wuce da ita wasa-wasa sai da Hafsat ta shafe watanni hudu bata koma gidan ta ba, duk yadda Jibrin ya nuna damuwar sa Hajiya Talatu kallo bai ishe ta ba, karshe mijinta ne da Jibrin ya biyo ta hannun sa ya sa dole badan ta so ba ta maida Hafsat 'din 'dakin amma da 'kwakkwarar kashedi ga Jibrin ya kuma amince.

Comment
Share
Vote
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...26*

.......Haka tayi ta lalla6awa, shima Jibrin 'din sai ya 'dan canza kamar gaske, ya kan 'dan bata kulawa ko da bana kirki bane ya dai fi baya da yake babu kulawar gaba 'daya, ya kuma daina kawo mata gida da 'yan mata ya rage tsawon dare da yk yi ya kuma sassauta time din da yk dawowa, taba ce dai bai daina zaman sha a parloun ba amma bata kulashi, haka in ya gama zata tattare tsab ta sanyawa 'dakin turare faman da ta tayi kenan har zuwa lokacin da Allah ya sake bata wani cikin watanni bakwai bayan fitan na farko.

Wannan karon kam Hajiya Talatu sai ta tsaya tsayin daka tana kula da ita, kusan kullun sai ta zo gidan in ma bata zo ba takan kirata a waya taji ya take karshe ma data ga hankalin ta yaki kwanciya ta nemi Hafsat din ta dawo gidan ta har zuwa lkcn da zata haihu amma Jibrin bai amince ba dole ta hakura da batun domin bata da ikon tilasta shi.
Lokacin da cikin Hafsat ya 'dauko tsufa a daidai lokacin harkokin Jibrin suka sha kansa, sanadiyar za6e da ya gabato, shi kuma yana 'daya daga cikin na hannun daman wani 'dan takarar ne a wancan lkcn, sam Hafsat ta rage yawan ganin sa, sai tayi wasu kwanaki ma bata sashi a idanun ta ba, kuma bata da bakin tanka shi.

Ranar wata Laraba tatashi da nakuda cikin rashin sani ta cigaba da harkokin ta na cikin gida batare da bawa abin muhimmanci ba.

Kafin fitar Jibrin a gidan ne sai abin yaso yai mata tsanani ta nemi ya kaita asbiti amma yace mata ta 'dan daure dai bari yaje wani 'dan taro ana jiran sa ne zai dawo.
Da haka yasa kai ya fice a gidan batare da damuwar komai ba balle ya damu da halin da ya barta a ciki.

Sosai abin ya damu Hafsat, gashi bata da ko sisi a hannun ta, wayar ta ma rabon ta da kati har ta mance balle ta kira yayar ta Talatu ta sanar da ita halin da take ciki.

Cikin sa'a kuwa daidai lokacin da take gab da galabaita a dai- dai lokacin Hajiya Talatu tayi kiran ta kamar yadda ta saba a kullun dan jin lafiyar ta, da 'kyar ta iya amsa wayar maganar ma sai ta gagare ta yi sai nishi da take saukewa kasa kasa.

Hajiya Talatu ma da jin yanayin da ta ke hankali tashe ta fara shirin tahowa.

Cikin sa'a kafin isowar ta wata makwabciyar su ta shigo gidan dan duba ta dayake tana zaman mutunci da kowa, so kafin ma Hajiya Talatu ta iso har matar ta taimakawa Hafsat, ba daman zuwa asbiti a lokacin dan haihuwar ta riga ta taho gadangadan ne.

Tare suka taimaka mata ta haifo 'dan ta namiji kyakykyawa dashi me kama da mahaifiyar sa sak har hasken ta bai bari ba.

Ta galabaita sosai dan hk koda suka gyara ta suka ce asbiti zasu kaita a duba lafiyar su tukun na.

Suna niyyar tafiya asbitin jini ya 6allewa Hafsat cikin lokaci kankani kuma ya galabaitar da ita ta fita hayyacin ta gaba 'daya, da gudu Talatu tayi waje ko zata sama musu abin hawa at same time tana kiran wayar Jibrin amma baya 'dagawa...ta 'kira numbern mijin ta shima ya bar wayar a mota ya shiga meeting.

Da 'kyar ta samo mota ta dawo gidan da gudu-gudu sauri- sauri tana fa'din kamata mu tafi asbitin na samo abin hawa.

Duk yadda makwabciyar Hafsat taso yi mata bayani kasa fahimta tayi tace sam suje asbiti ita dai bata ji ta ydda ba, taya zata wani bata numfashi sai dai in doguwar suma tayi dan haka ita dai su je asbitin.
Abin yazo ne gaba daya cikin 'kan'kanin lokacin da duk cikin su babu wanda yy zato.
Hajiya Talatu da ta kasa yadda sai da suka dangana da asbiti kafin, acan aka tabbatar musu da cewar already ma ta rasu, dan zuwan su asbitin ma ko ciro ta cikin motar ba ayi ba aka duba aka kuma sanar da su dan haka suka juyo gida, Talatu ji take kamar tayi ta ihu tana fada musu cewar Hafsat din ta tana nan a raye bata mutu ba amma tasan ko ta fada karya take, mutuwa dole ce akan kowa kuma kowa nada nashi lokacin..a karo na biyu ta sake rasa makusanciyar ta.

Fa'din irin tashin hankalin da Hajiya Talatu ta shiga ma 6ata lokaci ne, ko kuka kasawa tayi, gaba 'daya jin ta take tamkar itama ba a duniyar take ba ido kawai ta kurawa gawar Hafsat 'din ta kasa ko kyaftawa, yayin da sabon jaririn dake hannun makwabciyar Hafsat din yake ta tsanyara kuka tamkar yasan meke faruwa.

Karshe Jibrin sai zuwa yy ya tadda Hafsat sam6al a kwance amma wai babu rai tattare da ita.
Ido ya kura mata kamar zai ce tashi amma bb dama, kokadan bazaka iya bayyana halin da yake ciki ba.
Haka akai mata suttura aka kaita gidan ta na gaskia.

Tun daga lokacin rikon Adam da Jibrin yai masa hu'duba da sunan mahaifin sa ya dawo hannun Hajiya Talatu, dan a cewar ta bazata sake yin sakaci karo na biyu ba, sosai ta 'kullaci Jibrin duk da tasan mutuwa dole ce amma a ganin ta da gudunmawar sa wajen rashin Hafsat da tayi.

Sosai ta tattara so da kaunar da take yiwa Hafsat ta 'kara kan wanda take yiwa yaron ta ha'da masa gaba daya, kulawa take bashi tamkar kwai, gaba 'daya ta baibaye rayuwar sa da farin ciki da 'kauna.

Sau tari ba 'karamin mamaki Jibrin ke bata ba, dan yana iya shafe watanni biyu 'kwarara koma fin hakan batare da yaji ko ganin yaron ba, bai damu da komai da ya dangance sa ba, ko maraicin da yaron ke ciki Jibrin baya dubawa, haka kuma 'daya daga cikin halayyar sa bai canza ko guda ba sai ma abinda ya karu tamkar dama fili yake jira ta bashi, duk abubuwan da yy abaya sharan fage za'a iya kiran su.

Dama ba wasu dangin sa Hajiya Talatu ta sani ba mahaifiyar sa ce ka'dai kuma itama bayan auren sa da Hafsat Allah yy mata rasuwa, ko wajen rasuwar Hafsat basuga kowa nasa ba.

Bata tsinke da al'amarin Jibrin ba har sai da taga ana neman shafe shekaru biyu Jibrin bai zo ganin 'dan sa gudan jinin sa ba bai kuma kira a waya yaji lafiyar sa ba..ba 'karamin mmk tayi da hkn ba, bata ta6a tsammanin abin nasa har zai iya shafan gudan jinin sa ba, tun daga lokacin ta tsinke da al'amarin Jibrin ta kuma 'daura aniyar kulawa da Adam muddin ranta.

Adam bai ta6a sanin yana da wani uban ba baya ga maigidan Hajiya Talatu har ya cika shekaru biyar da haihuwa sannan watarana Jibrin 'din yazo tamkar daga sama ya fa'do.

Ko kallo bai ishe ta ba, ba ta dai hana shi ganin 'dansa ba amma itakam bai ga idanun ta ba balle har ya samu sakin fuskar ta, dama maigidan ne ya shigo da shi, ko daga Adam din ma bai samu sakewa ba dan ba sanin sa yayi ba shima 'din ko a photo kuma bai ga laifin yaron ba.
Chapter 41 · 0% Book details