← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 150 OF 218

Sashe 150

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yah Bukar wani tsagi ne na jikina, sosai nake jin sa a zuciya ta nake kuma alfahari da kasancewar sa 'dan uwa agare ni...bana haufi dan yasan abu makamancin hakan bazan kuma damu ba idan da bakin sa ya sanar da wani dan nasan yana da dalili kwakkwara, amma ni sam bazan iya labartawa ba.

Ban ji haushin sa ko wani abu na daban ba domin nasan bazai ta6a yin wani abu da yasan zai cutar da ni ba.

Ina son shi da duk zu'riar sa, duk dama matar sa Azeema sam ba 'kauna ta ko guda a zuciyar ta, soaai take biyewa Iyami take nuna min tsana da 'kyama a fili.

Har na bar wajen wan mahaifin nawa ban iya furta komai ba domin daga 'karshe da kansa ya sallame ni ganin bani da niyyar magana illa kuka da nake masa.
Ban kuma san manufar zuciyar sa kan hakan ba domin bai furta min komai ba.

Yah Bukar bai ta6a sanin 'kiyayyar da Azeema ke nuna min ba haka nima ban ta6a sanar da shi ba dan bana son na tarwatsa masa farin cikin gidan sa, domin nasan halin Yayana, abune mai sau'ki yaci mutuncin Azeema akaina.

Ummaru kam da ya kasamce 'dan Yah Bukar na farko Allah ya ha'da jinin sa da ni, kuma nima ina 'kaunar yaron sosai...sau da dama da shi nake zuwa unguwa...ko Khausar bai damu da ita kamar yadda ya damu da ni ba.

Sun kasance su hudu ne Iyami ta haifa, Yah Abubakar shine Babba, sai Yaagana, Goni da kuma Khausar, ni kuwa ni ka'dai mahaifiya ta ta haifa kuma tun ina da shekaru ta shida suka rabu da mahaifi na...nayi zaman zawarci na shekara kusan hu'du kafin ta auri mijin ta na yanzu, wanda shi kam duk matan sa 'kin zama suka yi da shi saboda fitinar sa ga kuma rashin haihuwa, duk da ma Alhamdulillah yana da rufin asirin sa ba laifi amma rashin haihuwar san kan hana mata zama da shi, 'diya 'daya tak Allah ya bashi kuma daga ita bai sake samun rabon haihuwa ba, ita ma 'diyar tasa mahaifiyar ta rasuwa tayi tuni kuma ya aurar da ita.

Yana da uban fitina irin wanda idan ya ha'du da maras ha'kuri sati guda baza su iya yi atare wuri guda ba.

Da haka mahaifiya ta ke ha'kurin zama da shi...bashi da kowa agarin domin kasuwanci ya kawo shi garin har ya zama 'dan gari ya fara fita fatauci zuwa wasu garuruwa, har can kudu ba'a bar shi abaya ba, yana zuwa ko'ina harkar sana'ar sa ta saida Shanu, kuma ba laifi yana samu gaskiya dan mahaifiya ta bata nemi komai ta rasa ba na dai- dai bu'katan ma'abocin rayuwar karkara, bansani ba ko gani da sanin hakan ne yasa Iyami ha'da tuggun da aka hana ni zuwa gare ta gudun kar ta 'dauke min wasu 'dawainiya ta.

Nikam bai wani dame ni sosai ba domin tun dama can ba wani sha'kuwa ne tsakani na da ita ba...da farko ma Abba na bai hana ni zuwa wurin ta ba, har kusan bayan auren ta da shekaru uku, har ma wani lokacin na kan kwana acan, amma tun daga lokacin da aka bada aure na ga Babagana shikenan aka kuma yi min katanga da mahaifiya ta shekaru hu'du kenan yanzu sai dai mu ha'du a wani wuri idan ana taro ko wani abin daban, gashi 'karin abin haushi bansan ko mutun guda daga cikin dangin ta ba..na jima da fahimtar cewa ba wani damuwa da ita suka yi ba shiyasa babu wanda ya ta6a zuwa wajen ta dan ganin ya take ko kuma ya rayuwa ke juya mata, hakan yasa nima na cire su cikin sabgar rayuwa ta.

Rayuwa ta kawai nake yi yanda Allah ya 'daura min na.kuma taso a cikin ta, sam ban saka damuwar komai arai na...a yanzu na gama fahimtar sam ba na gaban mahaifina, ba na cikin lissafin sa sam, na 'kara fahimtar hakan ne a lkcn da na ji ciwo a ciki na..sai gashi yanzu ma kusan kwanaki shida kenan ni da shi bamu ga juna ba, kuma ko da wasa bai damu ya nemi inda nake ba balle sanin halin da nake ciki, ni kaina na damu sosai da rashin haduwar ta mu, ko ba.komai mahaifi yake a waje na da nake matu'kar bu'katar albarkar sa, duk yadda na so ko da safiya ce mu hadu in gaida shi abin ya faskara domin kafin na tashi a bacci ya bar gida.

Kuma ko da mun hadun na gaida shi amsawa ka'dai yake yi ya kawar da kansa abin na min ciwo sosai.

Sai fa idan abin kafa doka ya taso sannan yake za'kal'kawalewa ya rattafo min shara'di da dokokin sa ha'di da mummunar kalmar sa ta Allah ya isa da na fahimci ni ka'dai yake yiwa ita...sai dai ban damu ba, mahaifi na kuma dole na ne na yi masa uzuri.

Dije ce ta sanar da ni ai mutane cewa suke wai Iyami mallake Abban mu tayi da asiri...ni dai a lkcn ban fahimci kan zancen sosai ba balle in san manufar ta, baya ga haka itama a bakin mutane ta ji, kuma na tabbatar hasashe ne ba gaskia ba...sai dai yau da gobe ya wuce wasa, da farko ban sa zancen a raina ba amma yadda lokaci guda naga Abba na mantawa da ni cikin gidan, sannan abubuwa na sauyawa zuwa wani yanayin da ba shi na saba gani ba ya sani na fara kokonto a zucia ta, da kaina na fara zargin wancan maganar, a hankali kuma na fara tabbatar wa zuciya ta ita...duk da yake bani da tabbaci amma dukkan alamu sun bayyana hakan.

Dalili kenan da ya sanya na lafta masa uziri har cikin zucia ta, ina kuma yi masa addu'a da fatan lkcn da zai tuna wacece ni da matsayin da Allah ya bani na zamowa 'ya agare shi yayi saurin zuwa, wallahi badan Yayana ba da bansan yanda zanyi da rayuwa ta ba, Allah kadai nake da shi sai kuma Yayana, shine fa suttura ta takalmi na idan ya mutu shine, sabulun wanki na shi, shike tunawa da cewa muhalli na babu fitila ya kawo tocila, haka idan ya fahimci babu batiri da kansa zai siya ya kawo min dan yasan ni ba tambayar sa zanyi ba, Yayana shike zama ya binciki matsayin ilimi na ya kuma 'daura min.akan wanda nake da shi.. duk dama ba boko nake yi ba tuni na barshi, amma Yayana bai bari na batare da ya tunatar da ni muhimmancin ilimi ba musamman karatun Alkur'ani mai girma ba, shine ka'dai me zama yaji damuwa ta shine farin ciki na wanda zan gani inji cewa erh ina da 'dan uwa a dunia, shine ya sa nake jin kaina erh nima.wata abace a duniyan nan, duk sauran 'kannan sa da suke uwa 'daya basu sona basu 'kaunar gani na sam hakan bai sa ya zuna idanu yana gani a wulakantani cikin gidan ba, Yah Bukar bai ta6a yi min wani abu dan ya cutar da ni ba sai dai ya 'kare ni da shi...'yan uwa na kuwa nima ban damu da shiga cikin su ba sbd basa kaunar gani na tare da su.

Lokacin da labarin cewa Yah Bukar zai fara sana'ar sai da dabbobi zuwa Maiduguri da sauran jihohi ya riske ni, ba 'karamin tashin hankali na shiga ba, Allah ya sani bana so yai nesa da ni domin shi ka'dai ne mai kulawa da ni da damuwa ta...nasan idan baya kusa da ni ba 'karamin gararin rayuwa zan shiga ba.

Sai da ya zauna dani sosai ya lalla6ani ya taushi zucia ta da kalaman kwantar da hankali sbd sam na kasa daina zubda kwalla sbd tafiyar tasa.

Daga 'karshe mun rabu da ina mai yi masa addua da fatan nasara a ko'ina.

Haka zai je yayi kusan sati ko sati biyu sannan ya dawo...nasara ta farko da ya fara samu gaba na yazo ya baje ta ya nuna min cike da farin cikin sa nima ina taya shi, yace insha Allahu sai ya bawa kowa mamaki a lokacin aure na tunda yanzu sana'a ta kar6e shi, shi dama a yanzu baya da burin da wuce yaga ya aurar da ni lafiya 'kalau..ya kuma fitar da ni kunya ya bawa mara'dda kunya...Alhamdulillah kuma da alamu Allah nason shi da Alkhairi yana kuma son ya cika al'kawarin da ya 'daukan ma kansa.
A cewar sa.

Ni kam ban iya nace masa komai ba illa murmushi..zo kaga zuciya ta fal murna Zaituna zata yi aure ta haifi jinjiri itama...burina fa ka'dai kenan ni, sai dai wannan burin ban bari koda wasa na ya san da shi ba..daga 'karshe addu'ar cigaba da samun nasara na ringa zuba masa, da ya tashi tafiya kuwa har yimin kyautar Naira 'dari hudu cikin ku'din da ya samo.

Ido na zaro sosai ina kallon ku'din nace" Yaa me zan yi da wannan ku'din har haka?"
Yace ki ajiye a wurin ki idan bana nan ki ringa siyan abu da shi.
Nace a a
Yace" zaki 6ata min rai 'kanwa ta..ni 'din ne ban isa nayi miki abu ba ko kuwa me kk nufi...?"

Hakuri na bashi gami da yi masa godiya sosai sannan ya tafi...sai dai me...wallahi ni ban 'kara sanin inda ku'din nan suka yi ba cikin 'dakin, sama ko 'kasa sam ban ga ni ba, ranar ma sugar nayi niyyan siya Iyami ta bani koko ba sugar shine na tuna da ku'din na duba ai kuwa ku'di yace ba dai ni ba....
Ban zargi kowa ba haka kuma ban saka damuwar ku'din araina ba da yake dama ba saba ri'ke su nayi a hannu na ba.

Salmerh 😘
[25/12/2022, 11:19 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...85*
Chapter 150 · 0% Book details