← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 218

Sashe 63

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi kam daga baya ma wata mai aikin ta sa aka nema mata dan taya Zaitun aiki dan ganin kamar Zaitun 'din yanzu aikin yawa yake mata ga kuma kula da yarinya da a koda yaushe zaka gansu tare.

Kuma ko wani irin aiki take yi ko ma wa take yiwa aiki to kuwa da zarar taji kukan Mufee zaki ga ta bari ta tafi da sauri...Ammi kam inda sabo da riga ta saba da wannan 'dabia na Zaitun hakan yasa ta daina damuwa da komai dazata gani daga gareta ta game da yarinyar ta.

Salmerh 😘
[26/9/2022, 8:05 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...39*

........Hawowa yake cikin takun sa mai matukar birgewa da tafiya da hankalin duk mai kallon sa, tafiyar sa cikin natsuwa yake yin ta, tun da ya fara haurowa ya lura da yarinyar da bama tasan da tahowar sa ba, ba 'karamin mamaki yayi ba ganin ta bakin stairs ita ka'dai ayau 'din, iya sanin sa da 'yar gwal 'din nan ba kasafai zaka ganta ita daya batare da uwarta ba, da wuya ne ma idan uwar tasan cewa ta iso har nan dan ya lura tafi bawa yarinyar muhimmanci fiye ma da kowa da cikin rayuwar ta, sai dai tunda ya ganta saman Ammin yasan cewa uwartata ma na nan kusa da ita dan a yadda ya fahimce ta bata iya yin nisa da yarinyar sosai, shi kam kallon ta yake yana jinjina kyau irin na yarinyar, sai kuma akayi dace ta yi sa'ar uwa mai son farin cikin ta da son gyara mata jiki, domin tun da yake ganin yarinyar be ta6a ganin ta cikin yanayin da ba shine ba..kullum tsab zaka ganta cikin kayan ta masu 'daukan hankali.....

Bai ma gama wannan tunanin ba Mufee ta 'dago ta kalle shi bayan ankarewa da tayi da mutum na tahowa kusa da ita sanadiyyan 'karan takun sa da taji.

Ai kuwa take ta gigice ta fara kyabe baki tana 'daga hannuwa sama kamar mai 'daukan nata na a kusa da ita ne da alamun 'kage take sosai ta bar wurin kafin ya cimmata, cikin rashin sa'a sai ta zame tayo baya, step biyu ya rage masa ya hauro amma ganin yarinyar na shirin gangarawa yasa shi take su a taki 'daya caraf ya riqo hannun ta hakan ya taimaka wajen hanata fa'duwa.
Hakan ma gaba 'daya ya faru ne cikin sakannin da a'kalla baza fi biyu zuwa uku ba, shikan sa bazata abin yai masa, bai zaci faruwar hakan ba, yayin da Moopy ta sake razana jin ta ya riketa fin ma razanar da tayi abaya da ganin sa, hakan ne ya sanya ta sakin kuka mai 'karfi.
Rintse idanu yy yana jin ihun nata na neman hargitsa masa kwalkwalwa...yau ka'dai yaji tashin hankali har ransa saboda kukan yarinyar nan...lokaci guda tunanin yadda zai lallasheta tayi shiru yazo ransa amma ya rasa me zai mata.

A hankali ya sau'ke idanun sa a kan fuskar ta yayinda yake jin bugun zuciyar sa na 'kara tsanantawa..wanda yayi dai-dai da fitowar Zaitun da gudu daga bedroom 'din Ammi....
Turus taja ta tsaya ganin 'diyar ta a hannun sa cike da mamaki ta zuba masa idanu tama kasa kasa 'karasawa inda suke.
Ganin yadda ta ritsa shi da idanu ya sa shima 'din kallon ta, fuskar sa babu yabo babu fallasa bazaka ta6a fassara yanayin da yake ciki ba.

Ido cikin ido suke kallon juna kowa da abinda yake sa'kawa cikin ransa gefe guda kuma kukan Mufeedah na tashi har yanzu bata da alamun tsagaitawa...tuni idanun Zaitun sun cika da 'kwalla har bibbiyu take ganin sa banda tu'ku'ki da zuciyar ta ke yi, dama ta sani tunda taji kukan Mufee tasan bakowa bane sai shi.

Tsawon mintina biyu suna kallon kallo da shi ko zuciyar sai lokacin ma Moopy dake ta faman zillewa tana son barin hannun sa ta lura da Zaitun dake tsaye can nesa ka'dan dasu, hakan sai ya 'kara mata kaimi wajen son barin jikin nasa tare da fa'din Mam...my..., Mam...my cikin kuka sosai tana mi'ka hannayen ta ga Zaitun.

Shi kam bai wani damu ba sai ya 'dage gira 'daya ya 'daga 'kafa ya taho a hankali zuwa gaban ta yana fa'din" Kin wani tsaya kallo na..so kike sai ta toshe min kunnuwa da ihunta kafin ki kar6e ta dan mugunta ko?"
Bata ce dashi 'kala har yanzun kallon sa take tana mamakin abinda yai wa yarinyar.

Mi'ka mata Mufeedahn yy gaba yana sake fa'din " amshe ta ko in sake ta ta fa'di.."
Da sauri Moopy ta bar jikin sa ta cakume jikin Zaitun 'din tana rage sautin kukan ta itama tana duban Rayyan.

Zaitun ma sai ta rungume ta 'kam tana sake bin shi da kallon tuhuma har da waigawa, kamar bazai yi magana ba amma ganin irin kallon da take binsan da shi yasa shi batare da ya jiyo ba ya furta" Dan Allah kar ki cinye ni....zamewa zatayi na tare ta".
Daga haka ya tura 'dakin Ammi da sallama ya shiga.

Ita kam rintse idanu tayi sai lokacin kuma hawayen ta suka gangaro...tana tsaye a wurin yazo ya sake giftata ganin Ammi bata 'dakin ya kuma ji motsin ruwa a bayi dole yasan kuma zata bu'kacy privacy idan ta fito shiyasa kawai ya fito da niyyar jiran ta a parlourn 'kasa.

Sau 'daya kawai ya kalle ta ya 'dauke kansa, baki ya kya6e ganin yanda ta rungume 'yar yarinyar tamkar zata maida ta cikin ta
" Wannan kam ina jin tafi kowa sanin zafin haihuwa".

Abinda ya fa'da kenan cikin ransa dai-dai lokacin da ya isa bakin matakalar benen yana kya6e baki.
Wannan karon kam da 'dan hanzarin sa ya sau'ka ba kamar yadda ya hawo ba.

Zaitun cire Moopy tayi daga jikin ta itama dur'kusawa tayi gaban ta tana bin jikin yarinyar da kallo wai ko zata ga gurbin ciwo a jikin ta amma bata ga komai ba.

Har rigar ta sai da ta 'daddaga amma bata ga komai ba, hannun ta ta kama duka biyu tana 'dan ja baya Moopy na biyo ta nan ma taga tafiyar yarinyar normal ne ba wata matsala ta tabbatar kafar ta bata ji ciwo ba, haka kuma ba marin ta yayi ba bata kuma ga alamun bugu kan skin 'din yarinyar ba.

Sassanyar ajiyar zuciya ta sau'ke mai 'kunshe da jin da'din ganin ba cutar mata da yarinyar yayi ba...'kwafa tayi cikin zuciya ta furta" Allah ya taimake ka wallahi da kaga yanda ake ramuwa".
(Su Zaituna manya, ni kwa nace me zaki iya yiwa Mr Rayyan ne).

Dama tun ba yau ba tayi alwashin duk ranar da ya sake sa mata yarinya kuka to kuwa sai ta rama mata duk abinda yai mata babu ruwan ta da wani girma da mulkin sa, tunda bai san tausayi ba bai san yaro ba itama haka bazata 'daga masa 'kafa ba..ya maida mata yarinya tamkar tsarar sa abokiyar gaban sa haka kawai.

Dan ta sake tabbatar da babu abinda ya samu yarinyar madadin ta 'daga ta sai ta kama hannun ta suka koma 'dakin Ammi tana mai sake lura da yanayin tafiyar ta.

Suna shiga Ammi da fitowar ta kenan daga bayi ta saki murmushi tace" Kishiya ta ya ido da hawaye kuma?" dan ita Ammi bata ji kukan Moopyn ba sam kasantuwar tana bathroom ne.

Amsa Zaitun ta bata da fa'din" Wallahi Ammi Fa'duwa tayi".
" Ayyah fatan bata ji ciwo ba?"
" Ina ga dai kamar bakomai".
" Toh Masha Allah..Allah ya rufa asiri..ya kare min kishiya ta farin cikin Mamin ta".

Murmushi Zaitun tayi gami da fa'din" Ameen Ammi".
har cikin zuciyar ta taji da'din wannan addu'ah ta Ammi shiyasa take bata daraja tamkar ta mahaifiyar ta.

A duk lokacin da ta shiga firgici musamman akan Moopy to yanayin ta gaba 'daya ke sauyawa, sai tayi kyau, idanun ta su zama wasu lumsassu kafin hawayen ta ya sau'ko gashin idanun ta ne ke fara ji'ka da ruwan hawayen ta a hakan zaki ga tana zaro idanun musamman idan tana zargin wani da ta6a mata 'yar ta haka zata ritsa ka da ji'ka'k'ku kuma lumsassun idanun ta tana binka da kallon tuhuma, ko da bata tanka ba toh wannan kallon ka'dai ya kan isar da sa'kon zuciyar ta.

Yanayin ta a wannan lokacin sosai yake tafiya da imanin sa, har ya kan gaza 'dauke idanu akan ta...ya ringa jin bugun zuciyar sa na da'da 'karuwa kenan akanta nd bai san dalilin hakan ba, shi dai kawai tsintan kansa yake da shiga wani yanayi akan yarinyar.

Shiyasa sau da dama ya kan firgita mata yarinya batare da sanin cewa da gangan yayi ba sai ta saki kuka, ita kuwa uawar son 'ya ko a ina take ko me take yi da zaran ta ji muryar Moopy zata taho a gigice dan ganin abinda ya same ta.

Haka zata zo ta ritsa shi da idanu shi kuma yana enjoying kallon ta bata sani ba, bazata yi magana ba haka shima ba zai yi ba, cikin zuciyar ta kawai take jin tsanar sa na 'kara ninkuwa cikin kowani dakika musamman da ya sako mata 'ya agaba kamar abokiyar gaban sa.

Shi da kansa daga baya yazo ya fara jin haushin kansa kan hakan sai ya fara kwa6an kansa yama daina shiga sabgar su kwata kwata.
Ya ma manta da wanzuwar su cikin gidan gaba 'daya balle har wani abu ya ha'da su.

Wasa- wasa watannin Zaitun kusan hu'du yanzu suna a gidan Ammi, ba ta da matsalar komai yanzu duk da yake Marwa sun sake yin wata doguwar tafiya da mijin ta sati shida kenan yanzu bata da wata abokiyar hira bayaga Raleeya, sai ko wani lokacin Ammi, amma hakan bai rage ta da komai ba dan bata da wata matsala a yanzu babu shiga sabgar su.

A bakin Raleeya take ma jin ceea ashe tun auren Sultan da Marwan basu yi zaman watanni uku mai kyau a Kano ba, yawon 'kasashe suke tafiyar su suna hutawa.

Kwata- kwata Sultan baya bawa ma'aikatar ta su muhimmanci sai dai duk da hakan salaryn sa bai samu tangar'da dai- dai da rana guda ba.
Chapter 63 · 0% Book details