Sashe 138
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shiru Rayyan yayi ya rintse idanu..abin ya masa bazata ya kuma yi masa girma da yawa...sam bazai iya baude baki yace ya za6i daya daga cikin su ba.
Dake wayar na handsfree ne yana iya jiyo tashin kukan Zaitoon ka'dan'dan kuma itama tana iya jin maganar sa dan zaune gaban ta wayar ga6a 'daya.
Cikin ranta banda rokon Allah babu abinda take faman yi, tasbihi take ga mahalicci akan ya kawo musu mafita.
Wani fizgowa da aka yiwa mufeedah yasa itama take ta tsanyara kuka tana fa'din" Mam..mi".
Gami da mikawa Zaitoon hannu.
Da 'karfi Rayyan ya sake dam'ke idanun sa bayan jin hakan, yayin da sautin kukan Zaitoon ma ya 'karu duk suna kokarin tarwatsa masa kwanya, kukan ko guda daga cikin su baya son ji a halin yanzu.
Rokon su Zaitoon ta fara nan take tana fadin" dan girman Allah ku daina yi mata irin hakan wallahi amana ce a wurina kuma nasan sai Allah ya tambaye ni akanta, ku taimaka ku bar min yarinya ta kada ku raunata mu..."
Yadda take maganar cikin kuka ko.da zuciyar ka babu imani dole sai kaji tausayin ta amma mutanen nan tamkar ma ba da su take ba.
Ko bi takan maganar ta ta babu wanda yi, yayin da idanun Rayyan tuni suka bu'de ya waro su sosai, ji yake tamkar ya ga kansa agaban su a wannan lkc...amma yasan babu hali.
Tsaye ya mi'ke kan 'kafafun sa dai- dai lokacin da kunnuwan sa suka jiyo masa magana ta cikin wayar"... tambaya ta 'karshe gare ka Dr Rayyan...ka za6a ka kuma sanar da mu wanda kk so ta rayu cikin su dan dole ne sai mun 'dauki ran 'daya sannan ka fanshi ran 'dayan da dukiyar ka kafin abin ya kewayo kanka kaima...".
Tsayuwar da bai shirya yinta ba bace ta kama shi, amma jin jiri na son kayar da shi bayan tsayuwar ya sa shi ba komawa ya zauna yana jin bugun zuciyar sa na hauhawa, zuciyar sa yake jin tamkar zai faso kirjin sa ya fito.
Kuka Zaituna ta cigaba da yi sosai bisa gwiwoyin ta, wanda yake iya jiyowa daga inda yake, tana kuma yin sa ne a tsananin galabaice gami da wahaltuwa, da 'kyar maganan ta ke iya fita take fa'din" Dan Allah ku bar min 'ya ta ta rayu, ku kaiwa Ammi ita, nasan ita ka'dai zata kula min da ita, na yadda ni ku kashe ni dan Allah..ku bar mufeedah ta ta rayu ..."
Babu wanda ya kula da maganar ta sai" muna sauraron ka da suka fa'da da alamu ba maganar Zaitoon suke da bu'katar ji ba face ta Rayyan.
Amsar sa ka'dai suke da bukata.
Shi kansa Rayyan rasa amsar basu yayi, shin wannan wani irin iskanci ne.
" Nawa kuke da bukata dan Allah ku sanar dani...zan baku ko nawa ne amma ku sakar min su gaba daya...".
" Ba bu'kata Alhaji...ri'ke ku'din ka zasu yi mk amfani daga baya wajen fansan ran 'dayan daka za6a daga cikin su, ka daina 6ata mana lkc, mukan yi komai ne bisa tsari kuma ina tabbatar maka da cewar yanzun nan kana za6a zamu idasa aikin mu mu 'dora da abinda ke gaban mu, idan ka bada hadin kai a yau ma 'dayar da ka za6a zata iya dawowa gareka, idan kuwa kayi taurin kai zaka tsinci gawawwakin su ne gaba 'daya a saman babban titi a yashe..za6i naka ne Babban gaye...."!
Ya 'karashe da muryar sha'kiyanci.
Wani dake can gefe ne ya matso ya fizge wayar yace da Rayyan..." Starting from yanzu zuwa 10 mins...idan baka za6a ba toh ka tabbatar mun lashe wasan....".
Yana gama fa'din hakan ya yanke 'kiran.
Waje 'daya Rayyan ya 'kurawa idanu, meyasa tun farko bai yi tunanin zama ready kan bin diddigin yan iskan nan bane? meyasa hankalin sa ya 'dauke ga hakan.
Gashi yanzu duk wani dogon jan lkc da zai yi babu wani amfani, lkc ya riga ya 'kure masa, yaushe ya bi diddigin su yaushe ya sa aka shirya masa troop yaushe aka je inda suke 'din duk cikin mintina goma? kuma ya tabbata ba tausayi ko tsoron Allah gare su ba a yadda yaji muryoyin su, daga yanayin da ya jisu ya tabbatar da cewar ri'ka'k'kun yan iskan gari aka tara.
Cikin hanzari ya danna kira wata lamba, umarni ya bayar bayan an 'daga kiran kan layin da aka 'kira shi last...
Har ya fara jero musu numbobin wayar sai kuma wani tunani ya fado masa, ta iya yiyuwa numbern bazai sake amfani a wajen su ba, a yanda ya fahimce su.
Wannan tunanin yasa shi camza shawara kan cewar kawai a bibiyi nashi layin, duk wani kira da ya shiga ko ya fita har zuwa lkcn da zai basu umarnin dakatawa.
Wata number ya sake 'kira yayi wasu takaitattun bayanai duk kan lamarin.
Sam bai zauna ba, sai safa da Marwa yake yana faman danna waya hankali tashe.
Kafin ya gama kiraye kirayen nasa sai gani yayi mintina biyu kacal suka rage cikin goman da suka basa.
Video call ya 'kira amma kiran bai tafi ba, sai ya 'kira voice call nan ma haka bai tafi ba...cikin hakan yaga kira da wata sabuwar numbern batare da wani nazari ba ya 'daga ya sata a speaker.
Sai ji yayi sun she'ke masa da wata iriyar dariyar mugunta.
Tsabar takaici ma kawar da wayar yayi saitin fuskar sa yana mai jin ra'dadi a zuciyar sa... sa fuskar sa kuwa tamkar bakin ha'dari idan ka dube shi...ya so su ja wasan zuwa wani lkc amma tuno yadda duk ya rasa 'yan uwan sa da mahaifin sa cikin 'yan 'kalilan din lokuta ya sanya ji aransa cewar bazai sake wasa da wata dama da tazo masa a rayuwa...hakan yasa ya kawar da wannan tunanin...abu ne guda biyu da yasan dole indai ba wani ikon Allah ba dole zai daya ya faru gare shi...har can cikin ransa baya so ya rasa ko guda cikin Zaitoon ko Mufeeda amma bashi da lkc...sun shirya kafin suka tunkare shi sun kuma yanke lokacin ba wadatacce ba.
Har ga baya so ya sake rasa wani nashi makusanci ta hanyar kisan gilla aganin sa hakan ya isa, baya so ya fara zargin kansa cikin lamarin da sam bai ta6a tunanin faruwar sa ko da cikin mafarki bane, amma sai gashi a halin yanzu bashi da iko ko damar sauya musu tunani kamar yadda bashi da damar dakatar da su, basu jin roko ya sani da wallahi ko ro'kon su zai yi akan su bar masa su duk araye ya famshe su da ko da kaf din dukiyar sa ne...bashi da damar dakatar da su sai dai ya mi'kawa Allah, yana ji kuma yana gani, yana kuma rokon sa akan ya ku6utar masa da su gaba 'daya.
" Ya akayi ne 'karamin Alhaji?!
Yaji muryar 'daya daga cikin su ya doki kunnen sa.
Takawa ya fara ya nufi jikin window ya tsaya yana hangi harabar gidan sai dai ba anan zuciyar sa take ba, tana can wani wuri me daban da shi iansa bai san ina ne ba.
He wish a gaban sa suke wannan isakanci da duk sai ya tabbatar yaji musu rauni da hannun sa.
"...wa ka za6a..wa kuma za'a kashe...?"
Hakan da yaji suka fa'da masa yasa shi tabbatar da cewa basu da niyyar sauya ra'ayi.
Hannun sa mai.ciwon ya 'dago ya dafe kargen windown da shi bai san kuma lkcn da yayi hakan ba, kamar yadda sam bai tuna cewar hannun ciwo yake ba balle ma yaji zafin ciwon.
" Sakanni talatin suka rage maka ka za6a..bayan wa'dannan sakannin kuma kawai ka tsumaye mu motsin mu na gaba..."
Tambaya ta 'karshe Mr CEO wa ka za6a...?"
Rayyan cike da sanyi da kuma rawar muryar da sautin ta ke fita masa da 'daci yace" Ku bar babbar kawai...".
Dariya suka she'ke masa da ita gaba 'daya kamar dama jira suke ya furta hakan.. shi kuwa ya rintse idanu, wannan shine ga 'koshi ga kwanan yunwa, kenan yanzu ma ya sake rasa damar cigaba da gani gami da rayuwa da gudan jinin sa a duniya kenan..?"
Zaitun kuwa na jin abinda ya fa'da ta zabura ta na nufo wanda ke ri'ke da wayar tace" Dan Allah ku rufa min asiri, kar ku biye shi ku bar min 'diyata araye, wallahi dama baya 'kaunar ta ko ka'dan, mugu ne azzalumi idan kasa aka kashe min 'yata wallahi bazan ta6a yafe mk ba kuma bazan barka ba sai na kashe ka kaima da hannu na...mugu kawai...."
Ta 'karashe da sakin kuka tana mai dur'kushewa bisa gwiwoyin ta cikin yanayi mara dadin gani, gwanin ban tausayi sosai tunda Zaitoon take aryauwar ta duk da irin gwagwarmayar da tayi bata ta6a galabaita irin na wannan lkcn ba.
Gwiwa ta fara ja tana 'kara ro'kon su tana kuka, dan Allah kar ku kashe ta, ni na yadda ku kashe ni, amma ku kaimin Mufeeda wajen Anty Madeena ko Ammi...dan Allah..."
'Daya cikin su ne ya doka mata tsawan tayi musu shiru.
Amma Zaitoon taki bin umarnin sa.
Bindiga ya 'dago take Zaitoon ta ha'diye wani mugun miyau tana duban cikin idanun sa da shi kadai take iya hangowa... kirjin ta take faman nunawa tana kuma kokarin harha'de kalaman ta da tuni suka watse a kwanyar ta... sake rungume Mufeeda da 'dayan hannun ta tayi yayin da 'dayan hannun take toshe bakin ta da shi.
" Ni k..kashe ni..dan Allah kar ka ka kashe min yarinya ta ka ...barta... ta rayu...".
Bata gama rufe baki kunnuwan ta suka ji 'karar fitar harsashin da bata san takamamme inda ya sau'ka ba.
Hakan yasa ta sakin wani 'ka'k'karfan ihun da yayi amsa kuwa yabi iska take ta fadi a wajen sumammiya.
'Kit Rayyan shima ya kashe wayar yana mai mayar da idanun sa ya lumshe...
Tunda kunnuwan sa suka jiye masa 'karan bindigar bai sake sanin ina tunanin sa suke ba, bakin sa bai sake iya furta komai ba ji yayi yayi masa nauyi, haka kwakwalwar sa bata sake fahimtar abinda ke faruwa da shi ba balle wayar da ke hannun sa, yana nan tsaye tamkar an dasa shi idanun sa na hango down stairs kamar me nazarin wani abu...amma tunanin sa na can wani wuri.