Sashe 2
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba karamin farin ciki jin hakan ya sata ba bata kuma yi kasa a gwiwa ba wajen nuna amincewa da godiyar ta a fili.
Nan ta sake rokan matar akan ta taimaka mata da neman inda zata zauna na haya in zata samu nan kusa saboda itan bakuwa ce bata da wurin zama.
Wani banzan kallo matar tayi mata cike da rainin hankali ta sake binta da kallo daga sama har kasa sannan ta tsaida idanun ta kan fuskar ta..." Ya sunan ki...?"
" Zaituna"!
Ta bata amsa tana me hadiyar yawun tsoron irin kallon da matar nan tai mata.
Ita ba saba irin rayuwar nan tayi ba...bata saba neman alfarmar kowa ba.
Ko da take gida bata daukan rainin hankali, bata roko bata kallon abin wani taji ya birge ta bata ta6a neman komai a wajen kowa ba illah mutun daya tak kuma shi din gudan jinin ta ne.
Sai dai ayau kam tana jin dole na ta jure komai, dole ne ta jure kowani irin hali da ta tsinci kanta tunda har ta kai wannan ga6ar dole ne ta kaskantar da kanta ta nemi alfarma badan kanta ba, badan jin dadin ta ba badan farin cikin ta ba sai dan yarinyar da ke goye abayan ta.
"...Akwai wajen zama nan kusa sai dai bana tunanin zaki iya biya, ni kuma ba aiki na bane 6atawa kaina lokaci wajen nemawa mutane muhallin zama musamman dan zaki yi min aiki ba...kije kawai zan sa a duba min wata daban dama already na yi magana..."
Ba karamin bugu zuciyar zaituna yayi ba jin kalaman matar nan da adan kwana biyu da tayi tana rayuwa kusa da wajen ta fahimci suna da ake kiran matar da shi shine Hajia Talatu...Hajia Talatu mai abinci.
Da rawar murya ta fara fadin "...Hajia ki fada min kudin Insha Allahu idan bai fi karfi na ba zan biya..."
"...Yama fi karfin ki, kama gaban ki kawai bana son shirme.."
Hajia ta fada a tsawace.
Dan ta fara gajiya da magana da yarinyar.
Sosai jikin Zaituna ya fara rawa, tunani take idan tabar nan sai kuma ina zata nufa...?
" Dan Allah Hajia ki saurare ni, ni dai in zan samu wajen zama inda bazai takuramu ba wlh zan iya biya koda hakan na nufin in rasa na sakawa abaki na ne, ki fada min nawa ake biya Hajia Insha Allahu zan biya kuma..."
" Dubu ashirin da biyar ne daki ne daya..."
" Zan biya Hajia..."!
Zaituna tayi saurin bada amsa tana me sauko da kullin kayan ta gaban Hajiyan.
Wani banzan kallo Hajiyan tayi mata gami da fadin kin kuwa ji me na fada ko..?"
" erh Hajiya zan iya biya ko yanzu ma..."
Kai Hajiyan ta girgiza gami da fadin sam sam ban yadda da ke ba baiwar Allah...zan mafi kyautata zaton sata kika yi daga inda kike cewa kin fito...maza ki 6ace min da gani kafin in tara miki mutane ai miki bugun 6arayi yanzun nan.."
Ta karashe maganar tana me bada umarni ga wata mai mata girkin abincin daga can wajen dafa abincin, dan ita bata aikin komai sai bada Umarni kawai ga ma'aikatan ta.
Kukan da Zaituna ta sanya ya dawo da hankalin ta gareta take tayi kicin kicin da fuska tana duban ta.
" Mayya ce ke kam hala?"
kai Zaituna ta girgiza da sauri alamun a a .
" Toh tashi ki bar wajen nan nace..."
Sum sum ta tashi ta tafi tana share kwalla...jikin ta duk yayi sanyi.
ta rasa dalilin hajiya nakin amincewa da ita kan batun hayar nan, shin ba ita tace zata biya dakanta bane, ko de Hajiya naganin kamar bazata iya biya bane.
Ta san hakan ne babu tantama ita da kanta tasan hakan, dan kafin wannan lokacin ita kanta bata taba tunanin zat iya rike kudi kwatankwacin jaka biyar bama amma kaddara ta fi karfin komai.
Ba karamin matsuwa tayi da son samun wajen zaman nan ba musamman ma dan ta samu ta watsawa jikin ta ruwa, a matukar takure take ainun da zaman wajen bishiyar nan.
Ga yarinyar ta ma da rashin wankan da take fuskan ta yake sata kananun kuka yanzun sosai hakan ke damin ta.
Karo na farko kenan da taji tayi nadamar barin gida.
Take kuma sai wata zuciyar tace mata toh ko kina gidan ma a ina zaki zauna da yarinyar nan.
" Innalillahi wa inna ilaihiraji'un..." Allah ka sassauta min, yah Allah ka bayyana min abinda yafi dacewa dani.
Kuka sosai tayi tana tuno abubuwa da dama, masu dadi da akasin hakan, sosai take jin rauni tattare da ita.
Ranar kwanan Rumfan mai kayan miya ta sake yi...washe gari kuwa da sassafe ta sake yiwa Hajiya Talatuwa sammako.
Duk ta rame ta fita hayyacin ta kamar ba ita ba.
Gaishe da Hajiyan tayi tana me silalo da siraran kwalla.
Gani tayi Hajiyan ta tsaya kallon ta duk da bata san meke cikin zuciyar ta ba amma ga dukkan alamu rahamar da ke kan fuskar Hajiyan na yau ya 'dara na jiya sau adadin da bazata iya kididdigewa ba.
Cike da marairaita ta fara fadin
"...Hajiya dan Allah kiji tausayi na, wlh tun da nake ban ta6a satan ko gudan Naira na wani ba haka wannan kudin ma da nace zan biya hayan da shi ba kudin sata bane Hajiya wlh kaddara ce ta sa na bar inda nake inaso in dan sarara ne kafin wani dan lokaci in koma gida..wallahi ke kadai naji zuciya ta yadda da ita..dan Allah Hajia ki taimaka min na miki alkwarin bazan ta6a baki kunya ba..."
"..Baiwar Allah ya ma kika ce sunan ki...?'"
Hajiyan ta tare ta tun ma kafin takai karshen maganar ta.
Cike da zakuwa ta amsa Hajiyan da fadin.
" Sunana Zaituna Hajia".
Kinga bawai kin nema miki nayi ba gani nayi kinyi karama gaskiya Zaituna, kinyi karama sosai ace kin kama daki kina zaune ke kadai kamar ydda nake tunanin bazaki iya biyan hayan ba amma in zaki iya ni ai ba ruwa na..kasuwanci ne kawai kuma babu daga kafa .."
" Insha Allahu Hajia zan iya biya ni dai dan Allah ki taimaka min.."
Bata sake ce da Zaituna komai ba kawai ta dago wayar ta kira wani wanda sai bayan ya isi ne Zaituna ta fahimci cewa shine wanda zai mata jagora zuwa inda zata zauna din.
Tare da shi suka je ya bude dakin dakansa sannan yayi mata bayanin gidan da ya kasance bayan layin inda Hajia ke saida abincin ta ne...
Sake jajjada mata kudin hayar mutumin yayi take kuwa cikin kayan ta ta ciro kudin ta biya hayan zuciyar ta cike da farin cikin samun matsuguni.
Sosai kuwa gidan yayi mata tsab da shi...daki ne daga farkon gidan sai wasu dakunan daga can ciki wanda ta fuskanci da mutane ma a cikin su...sai bayin su guda biyu na wanka daban na bahaya daban.
_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️....2
.......Cike da zumudi ta shiga dakin can kasan zuciyar ta take jin wani irin kwanciyan hankali, sai dai fayau da taga dakin bayan shigan ta ya sanya mata tsinkan zuciya, ashe da sauran rina a kaba, ta zaci komai ya kammala kenan tunda ta sami dakin, shaf ta mance da cewa bata da komai na amfanin yau da kullun.
Take gadon ta dake a can gida ya fado ranta sai tayi saurin girgiza kai cike da karayar zuciya.
Duk da tasan cewa shima din ba wani gado ne na kirki har na azo agani b amma ko ba komai yayi mata amfani tsawon shekaru wanda ko a yanzun haka da take tsaye cikin wangamemen dakin nan da zata budi ido tagan sa anan gaban ta sai tafi kowa jindadi.
Dakin malale yake da lafiyyan siminti, ga kofa ma mai kyau haka ma windown dakin babu penti kam amma hakan bai sa taga rashin kyan dakin ba musamman da tasan cewa ya dinka nata na can gida.
Matsalar ta daya ne da taji yafi damin ta bata da komai na amfani ko kuma wanda zata rika yiwa yarinyar ta shinfida da shi kuma bazata iya kwantar da yarinyar haka nan kan simintin dakin ba musamman ma dayake a yanzun ana cikin yanayi ne na damina.
Bata ta6a zaton abin zai iya kaiwa har haka ba, sai yanzun idanun ta suka fara raina fata, yanzu ne ma tafara ji aranta cewa meyasa ta aikata hakan.
Ban dama Allah ya dube ta ya tsaida ruwa a iya kwanakin da tayi tana kwanan layi da bata san ya zata yi a wancan lokacin ba, amma da ikon Allah ko digon ruwa dis bai sauka ba sai ma zafi da take kyautata zaton na nunan gero ne.
Jakan tan kawai ta ajiye ta sake fitowa harabar gidan da ya kasance matsakaici, zai yi wahala ace mutun yayi uzurin sa cikin gidan har ya gama batare da gani ko jin motsin kowa ba saboda rashin wadataccen fili da gidan ke dashi sai dai in ya kasance masu rayuwa cikin gidan basa kusa ne.
Cikin kankanin lokaci ta karewa gidan kallo babu laifi yana da kyau da kuma tsabta dai dai gwargwado dan kuwa ko kusa ba ta isa ta hada wannan gidan da can gida da ta baro ba.
Wata kofa dake gefe da nata dakin kadan tabi da kallo ganin sa garkame da katoton kwado bata yi wani dogon nazari ba wajen fahimtar cewa mamallakan dakin basa sa nanne ko kuma shima din layin haya yake da ba a riga an shiga ba tukunna duba da cewa nata dakin ma sai da ta zo kafin aka bude shi gami da bata makullin.
Sallama tayi cikin sassanyan muryar ta daga bakin 6angaren da tun dazun take dan jiyo motsin mutun amma sai taji shiru ba'a amsa mata ba.
Sallaman ta sake rerawa wannan karan da dan sauti tayi shi..can ciki taji an amsa mata bayan wasu dakiku kuma wata mata mai matsakaicin tsayi ta fito.
" a a bakuwa ce ma..barka da zuwa ga gurin zama nan zauna."
Tayi maganar tana daidaitawa Zaituna kujera daga gefe kadan sai kuma ta koma bakin kofar dakin ta ta zauna.