Sashe 46
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yasan Adam ya fishi gaskia, yasan ya fishi tarin hujjoji ya kuma ninkasa juriya da hakuri shiyasa bai ga laifin sa ko guda cikin duk irin kalaman da ya furta ba, amma me ya sha kansa ya mance da lamarin yaron sa har haka ne a rayuwa, meyasa be ta6a tunanin 'dansa zai rayu da kewar mahaifin sa ba, ina tunanin sa ya tafi ya mance da lamarin mafi soyuwar 'da guda 'daya tak da Allah ya bashi a fa'din duniyar nan? Me yasa bai ta6a mai da hankali ya fuskanci irin tarin kaunar da Adam ke masa ne yasa yake dukkan abubuwan da yake aikatawa ba, meyasa ya kasa fahimtar haushi yasa Adam ke ta guje masa da duk wani abu da ya shafe shi ba?
gashi dai ya tara dukiyar ya kuma samu soyayyar mutane, ya yi suna fin yadda ma shi ya tsammaci zai iya yi, sai dai a yanzu baya jin duk yana da bukatar su sama da farin cikin gudan jinin sa, sosai yayi nadamar komai da ya aikata tun ma kafin a haifi Adam har zuwa yau 'din dayake rungume da shi cikin jikin sa nadama duk ta baibaye shi.
Gaskiyar Adam ne, gaskiyar sa ce da ya ce yayi watsi da amanar da Allah ya bashi ya banzatar da shi.
Dukiyar banza, neman sunan banza, banda tarin zunubbai ma me dukiyar ta tsinana masa...?
Tsawon mintina biyar suna a hakan sannan ya ciro shi yana share masa hawaye shi har Adam 'din babu wanda ya iya kallon cikin idanun juna da hannuwan sa duk biyu ya dafe gefe da gefen kafadun Adam da wani taushin murya ya fara magana..." Ka daina kuka kaji, na baka dama idan kalaman da ke cikin zuciyar ka basu 'kare ba duk ka fitar da su, ka fa'da min dukkan laifi na har sai kaji zuciyar ka tayi sanyi sannan ka sarara.."
Shiru dukkan su suka yi babu wanda ya sake furta komai, 'Dan Maliki na karantar yanayin fuskar Adam 'din ne yayin da Adam yake jin lamarin ba'ko agare shi shiyasa ya kasa tsaida zuciyar sa wuri guda balle har bakin sa ya iya furta wata kalma.
"...Nasani ni'din mai laifi ne, amma hakan ba zai hanani sanar da kai abu guda zuwa biyu ba, duk da nasan ba lallai ne ka amince ba amma ina tabbatar maka iya gaskiya ta kenan, kar ka sake tunanin ni Jibrin 'Dan Maliki bana kaunar ka, sannan kar ka sake ji aranka cewa ban shirya kar6ar ka matsayin 'daa ba, wa nake da shi a duniyan kaf ban da kai Adam? Idan ban 'kaunace ka ba wa zan 'kauna ta? wallahi yadda nake kaunar ka ban ta6a jin abinda ya kai ka muhimmanci cikin zuciya ta ba, duk abinda kake tunani akaina ba haka bane Adam, taya ma zan iya wofintar da rayuwar yaro na guda a duniya, ta ya zan yi watsi da kai da duk abinda ya shafe ka gaba 'daya, wallahi Adam kullum kana zuciya ta, in samu lokacin da zan ware saboda kai ne abin ke gagarata ban kuma san dalili ba, sai da nasan dukkan bawa dama da kalan tashi jarrabawar, babu mamaki ni har kai 'din kalar jarrabawar da Allah yaso yi mana kenan, amma ka gafarce ni...duk abinda kake son ji game dani zan sanar da kai yanzun nan komai da kake bukata zaka jishi a yanzun, zauna anan ina zuwa..."
Ya 'karashe maganar da zaunar da Adam bisa 'daya daga cikin hanshakan kujerun dake palorn.
Tuni Hafeez ya fice abinsa ya basu waje, shi kansa gaba 'daya jikin sa yayi sanyi, yana matukar son yaga an samu cikakken sasanci da kyakkyawar fahimta tsakanin abokin nasa da mahaifin sa, amma bai so abin ya kasance ta wannan sigar ba, bai ta6a fatan ranar da zai ji ko ganin Adam na furta zafafan kalamai ga mahaifin nasa ba, yaso maslahar tazo cikin nastuwa sai dai wani 6arin zuciyar sa bai ga laifin sa ba, musamman idan yayi la'akari da cewa ayau 'din sun ci karo ne da abinda shi har Adam 'din basu ta6a tsammata ba haka kuma tunanin sa matsayin 'daa agare shi mawuyaci ne ya iya jurewa, bai ta6a sanin har yau mahaifin nasa na hul'da da matan banza ba amma ya gode Allah da ya ji Adam bai furta su ga Alhajin ba, bai tsammaci zai kawar da wancan batun ba dan yasan halin Adam da 'dan banzan zuciya..amma yadda yayin ya matukar birgeshi..can 'kasan ransa yake jin wani tarin farin ciki marar musaltuwa, fatan sa Allah ya tsayar da lamarin haka nan..Allah yasa wannan haduwar tasu ta zam silar shiryuwar 'Dan Maliki ta kuma zam silar samun sassauci wa zuciyar Adam.
Yau 'din da kansa yaci alwashin yiwa Hajiya Talatu albishir 'din wannan lamari, yasan zata fi kowa jin dadin jin samun sasanci da fahimtar juna tsakanin Adam da mahaifin nasa...duk da ya lura dama mahaifin nasa ya 'dan kwana biyu yana neman sasancin Adam ne ke bijirewa, fatan sa ayau komai ya kammala tsakanin su shiyasa ya fito ya basu waje.
Da goran ruwa 'Dan Maliki ya dawo da kuma glasscup a 'daya hannun sa, inda ya mikawa Adam cup 'din da nufin shi da kansa ya sa masa ruwan amma Adam bai bi takan cup din ba ya kar6i ruwan ya 6alle marfin ya kafa a baki bai cire ba sai da ya shanye tass.
Yana cire goran yake sauke sassanyan ajiyan zuciya, kadan kadan yake jin zafin da zuciyar sa ya dade yake yi masa yadan sauka sai dai a tunanin sa hakan ya ta'allaka ne da ruwan da yasha kasancewar sa mai sanyi.
Sau 'daya tak ya dubi fuskar 'Dan Maliki take ya kawar da kansa gefe cike da basarwa
" Thanks".
Yace batare da ya sake duban sa ba.
Cak ya mike tsaye jin ya 'dan samu nutsuwa, kuma baya so 'yar natsuwar da ya samu ta barshi dan haka cikin ransa ya yanke shawarar barin gidan nan take.
Juyawa mahaifin nasa baya yayi ya fuskanci 'kofar fita batare da ya sake duban sa ba, taku 'daya biyu yayi kafin ya kai gayin na uku 'Dan Maliki ya fahimci manufar sa hakan ya sa ya dakatar da shi da kiran sunan sa..." Adam..!"
Cak ya tsaya amma bai juyo ba.
" Shikenan haka zaka tafi? baka bukatar jin komai daga gare ni...?"
Juyowa yayi ya dubi 'Dan Malikin kallon da bai fi na seconds biyu zuwa uku ba ya 'dauke idanun sa.
" Zan tafi ne, I have a lots to do outside there...".
" Har sun fi ni muhimmanci...? Sun fi tattaunawar da zaka zauna kayi dani muhimmanci...?"
Kai ya girgiza masa gami da kankance idanu yace" Ko 'daya, kawai dai bana son 'karin fami ne bisa ciwon da ke zuciya ta, dan Allah kayi hakuri ina da burika da dama a rayuwa ta, matsalar dake tsakani na da kai a kullun shine farko sama da komai amma not this time..dama rokon ka ne ya kawo ni gidan nan, alfarmar ka nazo nema..."
Hannun sa ya 'dago duk biyu ya ha'de waje guda alamar roko sannan ya cigaba da fadin..." Dan Allah ka barni nima na kafa sana'ata yadda ta dace ka daina rusa min hanyoyin samu na, zan 'kara tayar da wajen sana'ata a karo na biyu, ban ta6a neman alfarmar komai daga wajen ka ba a yau ina neman alfarma a karo na farko wannan karon ka bar min abu na, shekaru na na ja batare da na fuskanci inda na dosa ba kuma ina so nima inga na kula da Hajiya ta fiye da kulawar da ta bani a rayuwa ta, hakan kuma bazai ta6a faruwa ba sai ina da sana'a, na roke ka dan Allah Alhaji..."
Daga haka ya juya batare da ya jira jin amsar komai daga mahaifin nasa ba yayi gaba.
Kallon bayan sa 'Dan Maliki ya tsaya yi ya ma kasa fa'din komai.
Wai dagaske yaron nan ya ke yi baya bu'katan dukiyar sa? baya bukatar komai daga gareshi, dagaske yake da kansa yake so sai ya kafa kansa bayan ya jima yana tara masa, toh miye amfanin neman da ya 'karashi ilahirin rayuwar sa yana yi...idanu ya lumshe cike da dakiya ya furta.
" _...Adam Shaheed Jibrin Adam 'Dan- Maliki......."!_
*Comment nd Share to other groups*
Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*
Wattpad@
Serlmerh-md
🅿️ *...29*
.........Cak ya tsaya yana jin zuciyar sa na harbawa da kai kawo jin yadda mahaifin nasa ya kira sunan sa abinda bai taba ji ba.
" Kar ka manta da cikakken sunan ka da kuma waye mahaifin ka a duniyar nan..."
"...Tun ina yaro ma ban ta6a mantawa ba balle yanzu.."
..." Well..kaje kayi sana'ar da duk kake ganin tayi maka bazan hana ka ba, amma ina sake jaddada maka cewa kai 'din jinin 'Dan Maliki ne kuma wani 6angare na rayuwar sa kar ka ta6a mancewa da wannan, ka kuma kula...".
Adam bai ce da shi komai ba kawai ya fice daga palorn bayan ya juyo ya dube shi sau 'daya, da ace yana cikin mood mai kyau babu abinda zai hana shi murmushi da jin kalaman 'Dan Maliki amma baya cikin wannan yanayin a wannan lokaci, hanyar da yasan zata fitar da shi daga gidan ma gaba 'daya ya tunkara yana jinsa wani sakayau babu nauyi.