← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 218

Sashe 98

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sam ta rasa shi wannan wani irin marar hankali ne shi?
Wani irin mutun ne da bai da imani sam? amma Rayyan yanada zuciyar tausayi a kijrjin sa kuwa, Me yasa baya iya bambance tsakanin babba da yaro? yarinya kamar wannan har abin ka mayar abin gabar ka ce...miye ribar da zaka tsinta idan ka cutar da ita.

Kukan Moopy da Ammi ta jiyo ne ya sanya ta saurin saukowa a rikice tana salati cikin zuciyar ta hakama ma'aikatan gidan duk suka fito domin abin ya faru ne a palon dake 'kasa kuma duk kukan Moopyn ya kara'de ko'ina.

Sanin da Ammi tayi cewar kukan Moopy tafiya yake dana Zaitun ya sanya ta 'kara hanzari...cikin zuciyar ta take ayyana Allah yasa ba Rayyan bane sanadi.

Tun kafin ta sau'ko kuwa ta hango su zaune 'kasan tiles. Zaitun rungume da yarinyar tana kuka itama...ga wata mai aikin tana 'ko'karin amsar yarinyar daga hannun ta amma Zaitoon ta kasa bata dama, ri'kon sosai ta yiwa yarinyar tana aikin kuka itama.

A rikice Ammi ta 'karaso gaban su tana tambayar Zaitun abinda ya faru.

Yanda take faman lumlumshe idanu hawayen ta masu kauri na sauka ka'dai idan ka duba ya isa ka fahimci cewa har cikin zuciyar ta take jin zafin wannan lamari.

Da farko ma rasa amsar da zata bawa Ammi tayi da 'kyar ta harha'da kalamai a bakin ta furta" Fa'duwa tayi Ammi..."
Wani hawayen mai 'kulle zuciya na sake sau'ko mata.

'Ko'karin kar6ar ta Ammi tayi dan har a lokacin Moopy kuka take yi sosai...ga mamakin ta sai ji tayi Zaitun ta sake matse ta jikin ta tana jin kukan na ratsa mata har 'kwa'kwalwa da jinin ta.

Gani take kowa ma yanzu baya kaunar 'diyar ta ita ka'dai ke son abin ta shiyasa ta kasa bawa Ammin ita.
Ji tayi ta tsani kowa ya ra6e su domin ta lura mutane bazasu ta6a canzawa ba..kowa mugu ne idan akan Moopy ne.

Da 'kyar da lallami ta sakewa Ammi ita sai dai me ganin yanda bakin Moopyn ya kumbura sintim ga jini ya sanya bata ma san lokacin da ta saki shash- sheka ba.

Da gudu ta tashi ta shige 'dakin su ta turo 'kofar bazata iya ganin yarinyar cikin wannan yanayin ba.

Kuka take yi sosai na tausayin yarinyar ta...bata jin har abada zata iya yafewa wannan bawan Allahn da har ya iya sanadin da jini ya fita jikin yarinyar ta...wallahi na tsaneka a duniyan nan, mugu kawai, azzalumi, marar tsoron Allah....
Ta furta a fili.
Sam bazan iya cigaba da zama da kuba, idan na zauna na san wataran gawar Feefy na zan tsinta ka kashe min ita.

Cike da rauni take wannan kukan ta gama yanke shawarar bar musu gidan su, sam ta kasa fitowa ta sake ganin wannan jinin a jikin Mufeedah, bazata iya jurewa ba.

Ammi kam da ganin yanayin fuskar yarinyar ta furta subhanallah...wannan irin fa'duwan haka..dole Zaitun tayi kuka.
Wanda bai kai haka bama yasa Zaitun kuka balle wannan"

Da 'kyar Ammi ta lallashi Moopy tayi shiru bayan ta goge jinin dake bakin ta sannan ta tashi ta koma 'dakin ta ita a kafa'dar ta, mayafi ta 'dauko da makullin mota ta fito.

Bata ko bi ta kan Zaitun ba kawai tayi hanyar waje.

Driver take da niyyan sawa ya kaisu asbiti cikin sa'a sai ga Rayyan ya fito daga part 'din sa.

Ganin Ammin sa ya sa ya tunkari inda take yana sussunkuyar da kansa domin yasan dole yanzun ma zata yi masa fa'da tunda da kansa yasan abinda ya aikata ga yarinyar da yake gani kwance saman kafa'dar ta.

Yana isowa bata ma bari yayi magana ba ta yi saurin fa'din" Yauwa Babana kaimu asbiti pls ko kuma ka kaita kawai..fa'duwa tayi bakin ta ya bugu da tiles..kaga yanda ya kumbura har zazzafan zazzabi ya shige ta, uwar ma na can tana kuka zanje in lalla6a ta..duk abinda ake ciki sai ka sanar dani now pls".
Ta 'karasa maganar da mi'ka masa yarinyar ta juya batare da ta jira jin komai daga bakin sa ba.

Shi kam mutuwar tsaye yayi yabi ta kawai da idanu, har sai da ya daina ganin ta, shifa natsuwar sa da ya nema ya rasa ne ya sashi fitowa da niyyan barin gidan sai gashi kuma abin ya juye ya koma masa...meyasa kullum sai shi Ammi ke jangwalawa yarinyar..?

Jiyake tamkar ya yadata a 'kasan wajen yy tafiyar sa amma Ammi tafi 'karfin hakan agareshi.

A hankali ya sau'ke idanun sa kan fuskar yarinyar sai yaji wani 'kif 'kirjin sa ya buga da 'karfi, babban abinda yasa yake 'kara tsanar ta kenan, kullum hakan yake ji daga sun ha'da idanu da ita ya tsani hakan kuma shi a rayuwar sa, ya tsani abinda zai takura shi ajiyan zuciyan sheshekan kuka da tayi take saukewa cike da rauni idanun ta a lumshe na bacci, fuskar gaba 'daya tayi ja ga bakin ta da ya kumbura sintim dashi har kamannin ta ya sauya.

Yasan da ace idaun ta biyu da babu abinda zai sata amince da shi har yatafi da ita wani wurin...amma da yake tana bacci har damar kare mata kallo ya samu.

A hankali ya kafe idanun sa wajen bakin ta take yaji jikin sa ya yi sanyi sosai da ganin yanda bakin yayi...yasan bai kyau ba, amma me ne yasha kanshi har haka?
Jinin da ke gaban pitch rigar ta ya kalla a lokacin ji yayi tsigar jikin sa duk ya tashi..." Muhammadu baka kyauta ba...."
Ya tabbatarwa kansa.

'Dan tattare goshi yayi ya juya da ita a hannun sa..Moopy kam tuni anyi baccin wahala bata masan hannun wa take ba da tuni ta tara masa jama'ah dan ta tsane shi itama balle ta ganta a 'kirjin sa.

*Drop ur comment*

Salmerh 😘
[22/10/2022, 6:27 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...58*

......James ya yafito da hannun sa, ya kuwa taho da gudun sa dan cika umarnin ubangidan sa, Rayyan Key ya mi'ka..." muje Hospital plz..."
Abinda kawai yace da shi kenan ya juya ya shiga motar James driver ya jasu suka bar gidan zuwa asbiti yayin da Rayyan ke rungume da Feefy tsab ajikin sa ko 'kyan'kyamin jinin da ya 6ata mata riga ma bai yi bai kuma san dalilin sa na jin hakan ba.

Sai da suka hau titi kafin James yace" Sir which hospital...?"
Kallon sa Rayyan yayi" Wanne kuwa James ban da YOUHEAL...
YOUHEAL zamu, dama na kwana biyu ban le'ka su ba.."
Kai kawai James ya ka'da ya tunkari Youheal Hospital.

Direct wurin Fawwaz abokin sa yace a wuce da ita dan tun shigowar su aka amshe yarinyar a hannun sa ana ta mi'ka masa gaisuwa musamman likitocin da suka yi aiki 'kar'kashin sa.

Kafin ma ya iso ga Fawwaz 'din tuni ya duba ta, tunda kuma yaji ance Rayyan da kansa ya kawo yarinyar yasa bai wakilta kowa ba da kansa ya duba ta zuciyar sa cike da tsantsan mamaki, domin banda tsagwaron kamanni babu abinda ya gani tattare da yarinyar da kuma Rayyan.

Ko lokacin da Rayyan ya 'karaso ya tarar yana aikin bai 'akarsa gare su ba bayan sallama wurin zama ya nema yana fadin" likita bokan turai...sannu da aiki..."
" Yauwa INFINITY CEO.." Wata isashshiyar daria Rayyan yayi yana gyara zaman sa yace" Ya aikin?"
" Mun gode Allah, baka.'ki mu ba..muna nan muna ta fafatawa..."
With smile on his face yace " da wanne zanji ne Fawwaz kai baka ganin kokari na ma kenan..?"
" Wani 'ko'kari bayan sai bayan month kafin ake ganin ka YOUHEAL yau 'din ma nasan badan Babyn nan ba da bamu isa ganin ka ba..."

" Hmm kai dai nutsu kayi aikin gaban ka nima wani waje zani yanzun..."

Fawwaz bai furta komai ba kawai ya mi'ka masa yarinyar yana sake duban fuskar ta.
Shiru ya ratsa office 'din har zuwa lokacin da Fawwaz ya kammalla ha'da injection zai mata...har a lokacin bacci take ganin allurar ne ya sanya Rayyan duban fuskar ta..for d first time yaji tausayin ta ya tsarga masa sosai har cikin jinin sa...lumshe idanu yayi a hankali ya kuma bu'de su nan take...cikin zuciyar sa ya ayyana rashin kyautawar sa.

" Gyara ta ayi mata allurar ko malam".
Fawwaz ya fa'di yana duban sa amma sam babu fara'a saman fuskar sa, a tunanin sa Rayyan 6oye masa cewa yana 'diya yayi shiyasa ya 'dan ji haushi kadan.

Gyara ta yayi ta yanda za'ayi mata allurar batare da wata matsala ba ya kuma yi mata ri'ko mai kyau dan yasan da 'kyar idan tana iya jure injection dan yasan irin rainon da uwar ta ke mata ko 'kwai albarka...wannan kam itama uwar da kanta ya aka 'kare balle 'yar da ta kasance rainon ta.

Ai kuwa ana sanya allurar sai ta yamutsa fuska ta saki 'karamin kuka tana rungume shi da fa'din Mammy...zuciyar sa yaji ta tsinke sosai, sai yaji babu da'di harda lumshe idanun sa.

Sai da aka cire allurar kafin ya bu'de idanun sa yana jera mata" So sorry Baby ya isa ko?"
Yana lalla6a ta gami da 'dan buga bayan ta har tayi shiru ta koma baccin ta, ga mamakin sa batare da ta damu ba.

Yana duban Fawwaz yace" Da uwar ta na kusa kuwa da kun kwashi drama...bama najin an ta6a yi mata injection fa".
Yana murmushi ya 'karashe maganar yana duban Fawwaz wanda shima murmushin yayi gami da yi masa duba irin mai cike da tarin tambayoyin nan.

Gira 'daya Rayyan ya 'dage yana mai cigaba da fa'din" Ai inajin bazata ta6a yadda ka 6ula mata jikin yarinya a idanun ta har haka kuma ta iya jurewa ba...".

'Yar dariya Fawwaz yayi da son jan magana yace" kace kai dai Disney gaba 'daya ne a gidan ka kana shan drama abinka...ya sunan Babyn ta ka?"

Ido ya 'dan zaro gami da kya6e baki yana duban gefe dan bai masan me ze ce da Fawwaz ba sam bai san takamamme sunan yarinyar ba har ga Allah.

Fawwaz kam da abubuwa ke ransa da yawa manta waccan tambayar ma yayi ya sake jefa masa wani da fa'din" Wai dama kana da yarinya har haka Rayyan shine ban ta6a sani ba ko dai 'diyar Raihana ce?"
Chapter 98 · 0% Book details