Sashe 185
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Take tayi kici kucin da fuska, ta tsani yarinyar tsana mafi girma da muni, ita kanta bata san iyakar kiyayyar da take mata ba..duk ta tasan a tatsuniyoyin da suka zayyano kwanaki sun ce wai itan 'diyar sace jinin sa, ita kanta ta ta6a hasaso hakan, amma tabbattuwar maganan bai gamshe ta ba sam har zuwa yau.
Tana zaune a Palor tana shayar da Arfan suka shigo...wai duk uwar biyayyar karyar da nake yiwa mahaifiyar sa cikin kwanakin nan sakamakon da zan gani kenan .?"
Ta ayyana aranta.
Idanu ta lumshe ta bude su da sauri jin kamar hawaye na shirin zubo mata.
Bata so ta nuna gazawar ta tun yanzu...hakan yasa ta nemo dauriya da dasawa zuciyar ta.
Shi kansa sai da yayi turus da ganin ta a Parlon dan sam ya ma mance da ita a gidan kwata- kwata, gashi Amra bade iya tsara kwalliya ba...'yar gayu ce ta 'karshe.
Basarwa yayi daga sallama bai 'kara ba ya sa kai kawai yana 'kokarin wucewa ciki.
" Sannu da shigowa Baby".
Tayi dauriyar fa'da tana mai mi'kewa tsaye tana gyara ri'kon Arfan a hannun ta.
" Uhum..".
yace a 'kasan ma'koshi..
" Hala tafia kayi babu sanarwa Baby".
Yace " Ina nan..babu inda naje..".
" Kuma sai ka....."
" Pls ban san doguwar magana..akwai wani abin ne daban...?"
Yayi maganar yana dakatawa.
" Kaima kasan akwai shi...magana nake so muyi dan Allah....".
Wani kallo daya waigo yy mata sai da yasa duk wasu maganganu da 'kwarin gwiwar da ta tattaro arcewa.
Wani yawu ta ha'diye mai kamar 'kaya tana rarraba idanu a'kasan tiles.
Shi kuma ya cigaba da tafiyar sa zuwa ciki batare da ya damu da jin maganar tata ba.
Bai da'de ba ya sake fitowa Mufee biye da bayan sa, dalilin hakan ma yasa tafiyar tasa ta zam very slow sbd ita baya so yy nisa ya barta.
Har a lkcn Amra na nan Palorn sai dai wannan karan zaune take ta rafka uban tagumi bata zaci fitowar sa yanzun ba, hakan yasa da fitowar tasa ta sake mi'kewa tsaye cikin hanzari amma ko kallon inda take ma bai yi ba balle ya tanka ta har suka 'karasa ficewa daga 'dakin.
Da gudu ta nufi window tana le'ken sa tamkar yau ta fara ganin sa, ko kuma ya canza mata ne oho, wani zazzafan 'kaunar sa ke sake ratsa mata dukkan ga6o6in jikin ta.
Raihana ta riga ta wuce tun jiya dan acewar ta ita kam bata ga me zata je yi a wurin Sultan ba, hakan yasa Marwa ce ka'dai da Zaitoon suka shirya tafiyar.
A can bakin motar sa ta hango su yayin da shima Rayyan ya nufi can bayan ya 'dago Mufee a hannun sa ganin tafiyar ta ta shiga masa lkc take.
Yana isa ya bu'de baya ya sanya Mufeeda suna 'ko'karin shiga ya wani ha'de rai yana duban su.
" Me ke nan haka...?
Ya tambaya yana mai rufe 6angaren da ya sanya Mufeedan batare da duban inda suke ba.
Lkcn da yake zagawa dan shiga mazaunin driver yace da Zaitoon " ki koma gida".
Turus suka yi dukkan su, sai suka rasa cikin.su da wa yake...ita Marwa tasan cewa a yau din da kansa ya kira wayar ta tun sassafe ya sanar da ita ayau zasu je ta kuma san ba 'dabi'ar sa bace sa6a alkawari dan haka mawuwaci ne idan da ita yake, tunda ko yanzun ma shine ya aika ta fito yana da abin yi a gaban sa.
Uban ta mayar kan Zaitoon, adaidau lokacin da Zaitoon ma ta dube ta suka kalli idanun juna...sarai Zaitoon ta fahimci da ita yake a idanun Marwa...kenan 'yan uabnci za'a nuna min..?"
Ta ayyana a zuciyar ta, har ranta bata zaci zai mata wannan rashin kirkin ba da ko da Marwa tace tare zasu je baza ma ta yadda ta shirya har ta fito ba.
Bacin haka ma 'kage take sosai da son fitar nan itama ko dan sbd Marwa ma yadda taga ta damu...tana matukar 'kaunar Marwa, tana son farin cikin ta.
Tunda taji lbrn abinda ya faru take tsananin tausaya mata.
Irin kukan da tasha bazata iya tuna ranar da ta yishi sbd wani can ba.
Yadda wani 'kullutun ba'kin ciki ya turnu'ke ta yasa hatta hannun ta ma kasa 'dagawa tayi.
Dama baya take da niyyar shiga ba gaba ba, Marwa ce zata zauna a gaban so ita kanta Marwan ma kasa 'karasa shiga motar tayi duk suka tsaya saroro tamkar an dasa...
" Kina 6ata min lokaci Marwa"!
" Abinda ya sake shiga kunnuwanta kenan take ta dawo saiti.
Da rawar murya ta ce " Yayah dan Allah ka barta muje man.....".
" Idan baki shirya zuwa ba u can go back home Marwa...ni inada abubuwan yi agabana masu yawa kin sani..."
Tana tura baki ta shiga ta zauna...sai ga hawaye shar sun gangaro tayi saurin goge su, dan tasan bb amfanin su, shi kafin ya fada ne wahala, amma idan ya furta ihun ka banza ne... cikin ranta take jinjina ba'kin hali irin nasa, ada idan Zaitoon ta fa'di haka 'karyatawa take amma zuwa yanzun ta fara fahimtar gaskiyar ta ne ba sharri take yi masa ba.
Da shigar ta ya tada motar yaja suka yi gaba ya bar Zaitoon a wajen ko a kwalar rigar sa, duk kuma hakan ya faru ne akan idamun Amra dake le'kowa ta windown parlon ta.
Mufee ganin sun fara tafiya Zaitoon bata shigo ba..ta kya6e fuska tace" Mammi tana waigawa bayan ta.
Da kansa ya lalla6i yarinyar ya ha'da ta wayar sa sannan ya ci gaba da tu'ki...Marwa ko nuna alamun tana jin su ma batayi ba.
Ba Zaitoon ka'dai ba hatta ita Marwan 'kwallan take shawarewa na takaici lkc zuwa lkc kuma ko a jikin sa...ko duban inda take bai yadda yy ba, sun gama tsara tafiyar su yazo ya wargaza musu komai, kuma ai dai Ammi ce ta tsara a tafi da Zaitoon din...amma sam Marwa bata jin yin wata doguwar magana...haushi kuma yasa ta'ki yi masa bayanin komai.
Zaitoon kam da gudu ta koma ciki tana kuka sosai, bata yadda Ammi ta ganta ba ta shige 'dakin ta tana kukan da ita kanta bata san na menene ba.
Cikin masu aikin Ammi 'daya taje da sauri ta same ta ta sanar da ita a yanayin da Zaitoon ta shigo domin ita taga fitan su tare da Marwa ta kuma ga shigowan ta ita ka'dai.
Abin yaso ya firgita Ammi sai dai tuno wani abu yasa har ta mi'ke sai kuma ta koma ta zauna, umarni ta bawa mai aikin akan taje ta dubo mata su Marwa na nan ne ko sun wuce.
Amsar da ya dawowa Ammin shi ya sa ta 'dan murmusa...biyo bayan fahimtar abinda ya faru.
Waya ta 'dago ta 'kira shi...sai da ya kusan katsewa sannan ya 'daga da sallama...kasantuwan wayar na hannun Mufeeda ne.
Cikin ransa ya ayyana" Nasan za'ai haka.."
Ammi tace " Me ka yiwa 'diya ta Rayyan?"
Ta fa'di hakan bayan ta amsa sallamar tasa yace" Babu abinda nai mata Ammi, ina hanya zan kaita".
" Ba Marwa ba su nawa nace maka zasu je dama?".
Wata makirar murmushi yy bai ce komai ba.
" Wani laifin tayi ne da zai hana aje da ita?"
Sai sannan yace" a a Ammi, kawai bazata je bane.."!
" a wani dalili..?"
" Haka nan kawai Ammi.."
"Ka kyauta ai..kai baka da buri ko da yaushe sai san ganin ka hargitsa min yara ka sanya su cikin 'kunci ko..?"
" Kiyi ha'kuri Ammi...ina tu'ki ne"!.
Tace" Adawo lapia..".
Daga haka ta yanke "kiran fuskar ta yalwace da murmushin da na kasa fahimtar kona mene.
Da hannu ta bawa mai aikin umarnin tafia bayan ta 'kare wayar..bata kuma yi yun'kurin tashi wai dan zuwa duba Zaitoon ba dan tasan dole zata ha'kura tayi shiru da kanta ma tunda ba yau tasan halin sa ba..inda sabo a gidan ita yakamata tafi kowa sabo da bau'da'dden halin Rayyan.
Amra tuni ta fito ta nufo 6angaren Ammi 'kage da son sanin kanun labarin, burin ta kawai taji inda zasu je da aka 'ki tafia da Zaitoon sai Mufee ka'dai.
Domin ita dai hotunan faruwar lamarin kawai ta gani bata san komai akai ba..erh mana hotuna, tunda ko kalma guda bai fada kunnuwan ta ba.
'Bangaren Rayyan kuwa ya shirya zuwa da Mufeeda ne badan komai ba sai dan kawai ya nunawa Sultan cewa tafin hannu baya iya kare rana, sannan duk abinda Allah ya so sai ya faru, ya rayu tsawon lkc da 'kiyayyar su a ransa, da ba'kin ciki da 'kyashin kar yaga gudan jinin su a dunia musamman ma shi, sai ga shi Allah ya 6oye masa sani, bacin tare duk suke rayuwa da jinin nasa bai tashi bayyana musu ita ba sai adaidai lkcn da shi kansa ma fafutuka yake da tashi rayuwar balle ya iya cutar da wasu.
Ga 'diyar shi nan da cikakkiyyar lafiyar wacce ta rayu cikin kariyar ubangiji bai kuma bawa kowa damar cutar masa da ita ba...
Ko da Amra ta isa 6angaren ba ciki ta shiga ba tana isa parlon 'kasa ta ci karo da mai aikin nan na sakkowa daga saman Ammi.
" Barka da shigowa ranki ya dade..".
Tace da Amra cikin girmamawa.
Bata amsa ba sai ma tsayawa da tayi
Gaban ta...tace" Ina Ammi..?"
" Tana sama"
" Marwa fa..?"
Sun fita da Yayan ta da Mufeeda.."
" Ita kuma uwar Mufeedan fa..".
" Tana can 'dakin ta da kuka ma naga ta shigo inaga 'kin zuwa aka yi da ita shiyasa....".
Murmushi Amra tayi..tana 'dan waigawa take sake tambayar
" Toh dama ina sazu...?"
" Wajen mijin Hajia Marwa...".
Idanu Amra ta 'kwalalo, take wannan murmushin ya 6ace 6at..tace" kin tabbatar..?
" Erh Hajia, ai tun jiya ma suka so fitan Allah bai yi ba shi Alhaji Rayyan 'din bashi da lkc sai yau..."
Juyawa kawai Amra tayi ta fita, ita kuma mai aikin ta kya6e baki, dama shegen surutu gareta tamkar aku...sai dai sam bata da munfunci ita.
Da sauri Amra ta koma 6angaren ta 'karamar jakar ta kawai ta 'dauka da key 'din mota sai mayafi ta fito...gaba 'daya ta daburce, ta rasa me yk yi mata da'di.