Sashe 203
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanan su biyu cikin dangi suka dawo zuciyoyin su cike da kewar juna.
Kamar ha'din baki kuma sai ga Auwal ma yazo washegari wai tafiya da Mufee zaiyi, abin sai yai mata yawa...kuka ta ri'ka yi babu ko kunyar idanu ta ri'ka share 'kwalla har sai da ta bawa Innani haushi.
Yah Bukar ne ya lallashe ta da 'kyar ta bari aka 'dauki yarinyar...gani take tamkar raba su ake son yi shiyasa aka tsiri wannan tafiyar...ita kanta Mufeen kuka take tana 'kiran Mammi...Mammi har suka wuce ...ita kuka Zaitoon kuka.
Bayan tafiyar su kuwa har zazza6i sai da ta kwanta, rama kuwa kallo guda zakai mata ka fahimci irin ramar da tayi. Amma Innani ta fita hanyar ta sbd ita aganin shishshigewan yayi yawa harma ta fara bata haushi.
Babu wanda kai tsaye zai fahimci halin da Zaitoon take ciki sai wanda yayi wa sha'kuwar ta da yarinyar farin sani.
Shiyasa Innani ke ganin ai za'kewar ta ce tayi yawa, wacce ma ta haifi yarinyar ai ta tafi ta barta balle ita karere...acewar Innani.
Tunani kawai Inna tayi yau wannan idan akace za'a raba auren ta da uban yarinyar kuma su amshi 'diyar su wa ma yasan irin halin da zata fa'da...shiyasa bactun yau ba take mata addu'a da fatab dacewa.
Fatan ta kawai Allah ya yi mata za6i mafi alkhairi..inma uban yarinyar inma wani daban.
Tun bayan dawowar Zaitoon gida akalar adduar ta ya sauya.
Rayyan kuwa bai sake zuwa ba haka kuma ko a waya basu yi magana da shi ba ya share ta...
Sai da Khausar tazo ne ma take ji abakin ta cewar suma an kai musu kayan abinci sosai acan gidan kuma an sake tafia da Abban su asbiti sai dai bata san waye yasa ayi hakan ba.
Wasa wasa sai da Mufeeda tayi sati, Zaitoon duk ta rame sbd damuwa ga azumi da aka fara.
Mufee na ganin Zaitoon madadin tayi farin ciki a a kawai sai ta sanya kuka sai da tasa kowa daria.
Duk wani abu dake faruwa abakin Khausar take jin sa.
Abu guda da idan ta tuna ko da ita ka'dai ce a 'dakin sai tayi murmushi shine kasancewar Adam Shaheed matsayin 'dan uwan ta na jini, bata kuma san meyasa take jin hakan akan sa ba sosai dai abin nan ke yi mata da'di.
*****
Anyi bikin sallah lafiya sai fatan Allah ya kar6i ibadun bayin sa ya kuma samu cikin bayin sa 'yantattu.
Koka'dan Zaitoon bata ta6a neman abu ta rasa ba domin an wadata su da komai, a hakan sai abinda suke so suke ci, ita da Mufeeda, domin hatta Adam ba a barsa abaya wajen hidimta musu ba, har ma za'a ce yafi kowa tunda shi akai akai yake zuwa, ga Yah Bukar ga Rayyan ga 'yan uwan Nadia...abin ba'a cewa komai.
Sallah da sati biyu aka 'dago maganar tafiyar su Kano wai zata koma matsayin matar Rayyan akaro na biyu.
Abin sai yy mata bambara'kwai, itafa tunda taga an 'dauki lkc bai zo ba bai aiko ba bai kuma yi maganar Mufeeda ba shikenan ta saki ranta cikin yan uwa da dangin ta...kuma kusan kullum suna magana da Marwa da Ammi da wayar da Adam ya bawa Innani...kuma ko su ba sa mata maganar sa..sai dai Mufee.
Har waya ake ha'da su da Mufee suyi, suyi video call suyi voice call kuma tana ganesu.
Zaman aure da shi kuma dama ba 'kauna take ba tuntuni ma ta mance, duk zaton ta shikenan magana ta 'kare tunda bb wanda ya sake 'dago maganar, ita indai za'a bar mata Mufeeda tare da ita toh bata da damuwar komai.
Shiyasa tuni ta saki rai taci gaba da rayuwar ta ashe ta'kaitaccen mafarki take.
Baran ma da taga yanzu Alhamdulillah lafia ta samu ga Abban ta, yana gani sosai dan an masa aiki a idanu sosai..sai matsalar hawan jini da shima Alhamdulillah ya sauka sosai yanzu.. ashe wai Yah Adam ne ya fara 'daukan nawin kai sa asbiti, daga baya Rayyan ya 'karasa, sosai tayi masa godia tayi masa fatan alkhairi mai 'dorewa har 'karshen rayuwar sa...yace babu komai, ai shima Abban sa ne...hakika dan uwa dan uwa ne.
Rayyan kuwa sai dai tayi masa addu'ah kawai tunda ba ganin sa tayi ba balle ta gode masa.
Abban nasu ne yace sam sam shifa dagasje bai yadda a sake wata hidimar biki ba kawai a maida yarinya 'dakin mjin ta, shi dai Yah Bukar ba haka yaso auren Zaitoona ya kasance masa ba Amma tsarin Allah daban yake...sai dai duk da hakan zasu yi iya 'ko'karin su wajen ganin ba'a barsu abaya wajen nuna mata gata ba.
Adam ma hakan yace...domin yanzu bakin su 'daya ne da Yah Bukar tamkar dama can sun san juna..'karshe dai aka yanke babu wani taron biki da za'ayi kawai gidan mijin ta za'a mi'ka ta kowa ya bita da fatan alkhairi kawai.
Wannan magana ta komawar Zaitoon ba 'karamin tada hankalin Iyami yayi ba, ta ri'ka shiga tana fita amma ina...komai ya tsaya mata cak.
Dama ba ko da yaushe nasara ke 'dorewa bawa ba...wani sa'in ka kanyi nasara, wani sa'in ka kan fa'di 'kasa warwass...idan ka matsa kuma sai kayi gangancin da zai iya kai ka ga nadama maras iyaka.
Sun taka rawar gani fiye da zaton duk mai zato, yayin da Iyami duk jikin ta yayi sanyi ganin yadda kowa ke faman hidima da nuna farin cikin sa a fili.
Ta kasa 6oye 'kyashi da ba'kin cikin ta.
Babu kuma wanda bai nuna bajintar sa ba cikin yayyen ta, sai da suka yi mata kaya na gani a fa'da, kaya en gaske dake nuni da zallar gatan ta. Ammi kanta sai da tayi fa'da, ita aganin ta ai an riga an zama 'daya Zaitoon tasu ce ko da Mufeeda ko bb ita, dan kuwa zaman da suka yi yaci ace an bata wannan damar na yiwa Zaitoon kayan 'daki amma suka shammace ta kawai sai ganin kaya tayi.
Sai a lokacin hidimar komawan nata Babaji yazo..duk ya lalace ya rame ya zama wani firgigi da shi.
Kallon ta kawai yake amma shi kansa rasa abin da zai ce da ita yayi.
Nadama kawai yake a zuciyar sa ashe rashi babba yayi da ya rabu da ita acan baya, duk da yake ba laifin sa bane amma kacokam ya 'dorawa kansa laifi a halin yanzu.
Fatan Alkhairi shima yayi mata kawai yayi gaba.
Shi kansa uban gayyar irin taron gayya da hayaniyar ba so yake ba hakan yasa yaji da'di da wannan tsari na Yah Bukar...kuma acan gidan su ma ba wata gayyar akayi ba en uwa ne na kusa ka'dai suka hallara domin nuna farin cikin su.
Gyara sosai ya yiwa gidan sa kafin aka zuba kayan Zaitoon...abin kawai sai wanda ya gani.
Khausar sai mita take tana 'kun'kuni biki sai kace na wata gagarumar bazawara salaf babu komai.
Dije ce tace mata babu komai kar ki wani damu, a naku bikin ai sai inda 'karfin mu ya 'kare..sai mun gaji da ciwon jiki.
A hakan dai ranar wata juma'a aka mi'ka Zaitoon gidan mijin ta Kano ta dabo timbin giwa....
Ranar tasha kuka, kuka irin wanda ta jima bata yi irin sa ba, ta kuma sha fa'da da nasiha, jin ta take tamkar ba ita ba har tsoron bu'de idanu take.
Tunanin rayuwar ta kaf aranar daki daki sai da tayi, ta kuma jinjinawa 'kaddara, domin 'kaddara na gangara ta ganin daman sa wannan duniyar, a ganin ta 'kaddarar ta abar labartawa ce ga 'yan baya, 'kaddarar ta na iya zama abin koyi ko akasin haka, sai dai ita kanta bata san wani matsayi zata bawa ta kalar rayuwar ba.
Gum ta rintse idanun ta ta kasa bu'dewa...bata so ta bu'de idanu ta ganta a gidan Rayyan matsayin matar sa...meyasa sai ita?
Meyasa da ta koma gaban mahaifan ta ba'a barta ba..?
Meyasa aka sake dawo mata da 'kaddarar ta baya.
Shin ita ahaka zata 'kare rayuwar ta babu walwala babu farin ciki?
Meyasa basu zaunar da ita sun tambaye ta waye Rayyan ba kafin su dawo da ita?
Meyasa sukai dubi ga nagartar sa ta zahiri ka'dai...shin an mata adalci ko kuwa farin cikin ta ne babu wanda ya damu da shi?
A ranar tayi kuka sosai, aranar ta zubda hawaye, tayi kuka kwatankwacin ranar da ta tsinci kanta ita ka'dai da goyon jaririya babu mai mata jagora ko yi mata nuni izuwa dai- dai.
Marwa ce ke 'dan 'kara kwantar mata da hankali da kalamai masu sanyi, domin yanzu duk Marwa tai sanyi...ko lkcn da taje duba su acan garin su ma Zaitoon sai da tayi mamakin ta, baki 'daya kamar ba ita ba tayi sanyi sosai.
Dama ita ba wasu 'kawaye gare ta ba Dije ce sai Kuma Marwan da Allah ya ha'de jinin su...Dije kuwa na 'dakin mijin ta an dai yi duk wasu hidima da ita amma bata zo Kano ba tace sai wani lokacin idan Allah yaso.
Marwa tace" Kina sani inajin babu da'di Zaitoon, sai kace baki san waye Yayah ba, ba fa ba'kon ki bane shi, babu halin sa da agani na baki sani ba..toh menene abin damuwa saboda Allah...?"
Cikin ranta tace " Marwa kenan..har abada bazaki ta6a ganewa ba, bazaki ta6a fahimtar waye Rayyan ba..".
Lokacin da Marwa zata wuce Zaitoon kamar ta shi'de sbd kuka, gashi babu Mufeeda wai tana can wajen Anty zata zauna zuwa wani lokaci.
Gidan sai yai mata girma sosai...ko ada da take ji su Marwa na labarin girman gidan bata ta6a shigan sa ba sai yanzun, bata ta6a tunanin ya kai hakan ba, shiru yai mata ranar ko bacci kasawa tayi...tsoro da fargaba sukai mata 'kawanya, kuma ko motsin Rayyan bata ji ba balle ganin sa, dan bai le'ko inda ma take ba balle tasan da wanzuwar sa cikin gidan, shima baccin sa yayi, dan shi kansa rasa yanayin da yake jin ransa yayi...shin farin ciki yake ko kuwa akasin haka?"