← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 207 OF 218

Sashe 207

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan yakai kusan karfe tara kafin ya dawo, Mufee ya samu itama 'din nata 'kananun kuka wai Mammi, 'dan zaman da sukayi a gida garin su Zaitoon su ka'dai ya 'kara 'karfafa sha'kuwar su, ita nan Mufeeda wai har ta fara mance mutane.
Tana ganin sa kuwa ta taho wajen sa da gudu ta rungume shi..koda ya 'dago ta luf tayi ajikin sa tana sauke ajiyan numfashi, sosai ta bashi tausayi.

Ya riga yasan damuwar ta dan haka cikin ransa yake tunanin mafita.

Bahijja ya 'kira yake tambayar ta inda wani chocolates ta kawo masa dan shi babu abinda ya riko.
Anty najin haka tace" Rayyan za'kin nan fa...ban fiye son ana bata ba gaskia?"
" Ba abinda zai mata Anty".
Tace" Toh..Allah yasa".
Kafin akawo din ne suka samu daman gaisawa da Anty.

Yana bu'de mata Mufee ta dago tana duban hannun sa jin karan ledan..sai da ya sa mata abaki kafin ya bata sauran a hannun ta.
" Abbah..?!
Yaji dadi sosai da sunan da ta 'kira sa da shi.
Hakan yasa shi amsa ta cikin tsananin farin ciki yace" Na'am.. Mamana ".
Tace" Mammi.."!
" Ita kike so?"
Sai ta 'dage kanta sama.
Murmushi yayi haka ma Anty itama murmushin tayi inda ta 'kara da fa'din" ai Mufeeda badai kulafucin uwa ba..na jima ban ga yaro irinta ba gaskia".

Kusa da kunnen ta ya ra'da mata" zanzo in kaiki wajen ta kinji mamana amma ba yau ba..".
Yasan ba fahimtar sa zatayi ba dan haka bai damu da amsawa ko rashin amsawar ta duk da yake Mufee sai da ta dage masa kai sama alamun ta amsa din.
Kafin ya bar gidan ma har tayi bacci ajikin sa, Bahijja ce tazo ta 'dauke ta zuwa makwancin ta.

A hankali tayi mata shirin baccin gudun kar ta farka dan ranar Mufee rigima take ji da shi...abinda ta yini musu da shi kenan.

Sun 'dan tattauna da Anty kafin ya bar gidan, daga nan kuma gidan Ammi yayi shiyasa sai da ya kusa kaiwa tara kafin ya dawo.

'Bangaren ta ya fara nufa dan duba lafiyan ta da yake dama duk abinda yake tana nan zaune cikin tunanin sa...cikin rashin sa'a sai yaji 'kofan a rufe.
Baiyi mamaki ba dan yasan halin ta, babu mamaki har tayi bacci ne.
'Bangaren sa ya wuce ya watsa ruwa yayi shirin baccin sa kafin ya tattaro wayoyin sa da duk wasu 'kananun abubuwan da yasan zai bukata ha'de da spare key ya dawo 6angaren.

Koda ya shiga 'dakin wani ni'imtaccen kamshi yake da ya matukar shiga masa zuciya.

Mayar da 'kofan yy ya kulle sannan ya 'karasa ciki.

Sai da ya kunna AC bisa sassau'kan yanayi kafin ya isa bakin gadon wayoyi biyu dake hannun sa ya fara direwa sannan ya danja mayafin kannata zuwa 'kasa kadan.

Bacci take amma yanayin baccin kana gani kasan ba cikin natsuwa tayi sa ba.

Hannu ya kai ya dafa goshin ta nan yaji babu sauran zazza6in..wani sanyi yaji cikin ransa.

Zama yy ya dan duba sakkoni kafin ya ajiye wayoyin ya bi lafiyar gado.
Haka nan kawai yau 'din yaji bazai iya barin ta ita ka'dai kamar jiya ba.

Ta6a mata abin rufa da yayi ya sata farkawa.
Tayi tunanin ko haka nan kawai ne ko kuma itake ta6a abinta, amma sai taji kamar alamun mutum kusa da ita..gashi 'dakin babu haske sai na compound da ke 'dan dimming ka'dan a 'dakin.

Hakan sai ya sake ta azzara tsoron dake ranta, sosai ya tsanan ta, musamman dayake dama a tsoracen ta kwanta.
Hannu takai domin tabbartawa tunanin ta nan kuwa taji dai tabbas mutum 'dinne.
Shikuwa yayi luf yana ji da ganin duk abinda take yi.

Matsawa tayi baya da sauri ta bude baki ta saki ihu.
Abin yai masa bazata duk da yake ba lallai ne ya iya dakatar da ita ba amma da sam bazai bari tayi ihun ba, domin sam babu da'di ihu da wannan daren sai azaci ko wani abin yai mata ko kuma ya cutar da ita.

Kafin ta samu damar sakin ihu na biyu Rayyan yayi wani zazzafan yun'kuri ya dawo kusa da ita ya ri'ko ta.
Hakan sai ya sake firgitata...bu'de baki tayi da iya 'karfin ta zata saki wani ihun jikin ta na 6ari sosai..without any doubt kawai Rayyan ya rufe mata baki da nasa.

He can feel yadda jikin ta ke 6ari da son 'kwace kanta...amma ta kasa...sosai firgicin ta ya tsananta.

Ka'dan ya rage ta sume masa kafin ya samu da 'kyar ya sanya hannun sa cikin nata ya ha'de musu yatsu waje guda.
Tuni yaso shagala cikin yanayin amma mutsu mutsun da take ya hanasa, shi kansa natsuwar ta yake da bu'kata a wannan halin ba abu daban ba.

Ganin kamar abin na neman fizgar sa ne ya shi sakin ta ya rungume ta sosai cikin jikin sa.
" Miye hakan wai, ki nutsu mana, bana son wannan firgicin sam..."!
Ya ra'da mata cikin kunnen ta yana shafa bayan ta.

Da jin muryar sa tayi lakwas sai ma lokacin ta tabbatar shi 'dinne da gasken gaske.
Amma kawai sai ta saki kuka mai sauti.

Rayyan bai hana ta kuka ba, dan atleast tayi kukan fin na mintina biyar yana sauraren ta rungume da ita illah shafa bayan ta da yake yi a hankali.

" Toh ya isa haka nan..."!
Ya furta bayan ya tabbatar ta 'koshi da kukan cikin wata disashshiyar sautin da fitar ta ya matu'kar yi masa wahala dan sai da yayi da gaske kafin ya iya bu'de bakin sa.

Abu ne da bai wani faru cikin niyya ba, coincidence ne, dan shi sam be zo 'dakin ta da niyya ko fatan samun wani abu daga gare ta ba, amma faruwar abinda ya farun sai ya kusan birkita masa asalin yanayin sa.

" Kiyi shiru please..."!
Ya sake furtawa ciki- ciki.
Dole ta rage sautin kukan dan ita kanta ayau tayi matu'kar mamakin sa.

Rayyan sam baya hana mutum kuka, if u intend to do it dama yake baka kasha kukan ka son ranka..amma sai gashi yau yana dan tausan ta akan kuka dole ta tsagaita.

Sosai take jin haushin sa bisa faruwar abubuwa biyu zuwa uku amma hakan sam bazai hana ta fahimtar canzuwar furuci da kalamai da yanayin sa ba.

Motsi tayi 'kakkarfa da niyyan raba jikin ta da nashi amma yaki bata wannan damar sai ma sake rungumata da yy zuwa cikin jikin sa.

Saukan zazzafan numfashin sa da take ji saman wuyan ta ne ya sa ta 'kara yunkurin janye jikin ta.
Wannan karan bai hana ta ba amma bai bari space 'din da ke tsakanin su yy fa'da'da ba.

Da sauri ya kamo hannun ta cikin nasa..." Matsoraciya kawai".
Yace atakaice.
Bata ce komai ba kawai tayi 'kasa da idanun ta.
" Kinci abincin?"
Da kai ta amsashi.
Saura magani kenan.."
" Nasha...".
Ta ce da shi ciki ciki.
" Kin tabbatar..?"
Bata amsa ba sai ma 'dago kai da tayi ta dube shi ta kuma mayar da kan 'kasa.
" Jikin ma naji ai da sau'ki ko.."
Tace" Umm...bana jin komai".
" Bakya jin komai sai rigima ko?".
Tayi shiru.
Yace Allah ya 'kara afuwa..."
Saman la66a ta amsa da" Ameen...".
Yace" koma baccin ki toh sai ki samu natsuwa..dan nima kaina ba 'karamin firgita ni kk yi ba a yau".
Yana fa'din hakan ya sakin mata hannu.

Yana kallon ta gyara ta kwanta ya rufa mata mayafin kafin ya juya 'daya bangaren ya 'dauki
wayar sa, rasa me ma zai yi da wayar tasa yayi ayau dan kawai scrolling ya ri'ka yi yana dawowa daga 'karshe kawai ya ajiye wayar yana mai sakin ajiyar numfashi.

Kamar wasa daren ranar sai bacci ya gagare sa, abu ne da ya jima bai faru gare shi ba, dan ko da ace ya tsinci kansa cikin wani yanayi ya kan yi masa wahalar daidaita kansa koda kuwa ace yabi hanyoyin da yasan sukan kawo masa sassauci..ayau din kuma baya jin bin wadancan hanyoyin, haka kawai yake ji aran sa ayau yana tare da sassaucin sa kusa da shi ba bukatar wani kuma.

Kamar wasa bacci ya gagare sa, rungumar da yawa Zaitoon ne ya matu'kar tsaye masa arai ya kasa mantawa.

Wannan yanayin yake so ya sake jin sa ciki koma fiye da hakan, juye juye ya riqa yi har tsakiyan dare.
Da 'kyar bacci ya 6arawo ya sace sa.

Lokacin da yazo ya farka ba 'karamin mamaki yayi ba da yayi tozali da fuskar ta kusa da tashi fuskar, bu'de idanun sa ke da wuya da fuskar ta yy tozali, idanu kawai ya zuba mata batare da mamakin ta ya hakan ya faru ba dan yasan bacci ne, da ace tasan tana kusa da shi da tuni ta matsa gefe.

Bai yiwa kansa ba'kin ciki ba ya kalle ta son ransa 'karshe hannayen sa 'ya 'dago ya fara zagaye lips 'din ta a hankali.

Sosai yake birgesa ba tun yau ba..haka nan kawai ya tsinta kansa da son kusan ta kansa gare su.

Cikin bacci kawai taji abinda ke faruwa, duk zaton ta mafarki ne so bata wani damu sosai ba, balle da tasan kafin tayi bacci hakan ya faru sai tayi tunanin ko shi 'dinne yake dawo mata.

Sai da taji yanayin na neman canza salo sannan ta dawo hankalin ta amma ina ta riga ta makara, domin ya yi nisan kiwon da muwuyaci ne waigowar sa.

Duk 'ko'karin da tayi wajen ckwace kanta abu ya faskara kawai sai ta saka masa kuka.

Abanza..domin kuwa Rayyana bai ma san ta nayi ba.
Burin sa kawai yake da mura'din cimmawa, kuma awannan lokacin ji yake idan bai samu abinda yake so ba zai iya shiga wani hali.

Tasha kuka, shi kansa ya sani, domin ba 'karamin galabaitar da ita yayi ba, duk da yake kuma is not her first time amma sai da ya jin mata ciwo.

Shi da kansa ya tallafa mata ta gyara jikin ta sannan ta sake kwanciya hadda juya masa baya kawai sai yayi murmushi.

Daga baya kenan yarinya.
Ya fa'da cikin ransa yana murmushin jin dadi.
Chapter 207 · 0% Book details