← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 218

Sashe 81

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kawar da kansa gefe yayi batare da ya sake furta komai ba.
Hannun sa ya 'dago ya dubi agogon sa sai kuma ya saka yayi waje.

Nayi tsayuwar fin mintina ashirin bayan fitar ban iya na sake motsawa ba, tunani na ma sai ya hargitse gaba 'daya.
" Me ma na fa'da ne?"
Na tambayi kaina a fili.
A hankali duk abinda na fa'da masa suka fara dawo min.

Ro'kon Allah nake Allah yasa ban furta abinda zai zame min matsala anan gaba ba.

Tsabar shiga ru'du ban ma san lokacin da ya bar gidan ba, sai uban sara da kaina yake.

Tuno wani abun ya sani fita da sauri na fito harabar gidan...wajen ajiyan motoci na duba ga mamaki na motar bata nan.
Wani sara naji kirjina ya min.
Kar dai bawan Allahn nan bai 'dauki shawara ta ba..?"

Wata zuciyar tawa ce ta amsani da fadin..." baki fa'di abu da 'kwakkwaran hujja ba taya zai 'dauki shawarar ki..?"

Innalillahi amma ai ni na gani da ido na, naga mutum 'karkashin motar sa sannan kuma ya fito yayi 'yan dube dube kafin ya 6acewa gani na.
Sai da safiyan nan ne ma dana zurfafa tunani naga yanayi da zubin sa kamar 'daya daga cikin ma'aikatan sa ne, duk da bawai sanin tsab nai musu ba amma yau da gobe ta wuce wasa.

Ciki na koma jiki na sanyi 'kalau, ba 'karamin haushi ya bani ba, amma hakan bai hana ni nema masa kariya wajen Ubangiji ba.
Sai da na kammala aikina tsaf kafin na baro sashen da tunanin makomata.

" Shiyasa kika ga duk jiki na yayi sanyi, Wallahi Marwa inajin tsoro sosai sam hankali na ya kasa kwanciya ban kuma san dalilin ba...".

Ga mamakin ta sai taga Marwa tayi dariya sannan tace" Ba mamaki tsoron hukuncin da Yah Rayyan zai miki ke jefa ki cikin fargaba...".

Idanu na bu'de ina duban ta.
" Ban ga fa kin tsorata ba Marwa? Bakya tsoron abinda zai iya samun yayan ki...?"
" Ni kuwa nake ji Zaitoon, ba ma ka'dan ba..sai dai nasan a kowani lokaci Allah yakan bamu kariya ne saboda isar sa ya kan kuma sawa wani abu ya riske mu wanda zamu koka da shi wannan ma saboda isar sa ne.."
Sosai na gamsu da bayanin ta duk da hakan sai naji ina son tunatar da ita sharri irin na 'dan Adam da kuma amfanin kiyaye wasu abubuwa kafin faruwar su baya ga haka ma ina jin shakka kan zancen da muka yi da shi, kar ya fassara ni ta wani 6angaren ko kuma ya tuhume ni akan sa.

" Amma Marwa....."
Da sauri ta tare ni.
" Kar ki wani ji kin damu, ina dai kin sanar da shi kuma kin tabbatar ya jiki..?"
Da kai na amsa ta.

Kuma kin tabbatar ya saurari abinda kika fada...?"
Wannan karan ma da kai na bata amsa.
" Zai kiyaye..Insha Allahu babu abinda zai samu Yah Rayyan...".

Cikin zuciya ta na amsa da Allah yasa.
Yayin da a fili kuwa na jefa mata tambayar..." Amma dama kuna da makiya ne da suke yi muku zagon kasa a rayuwa..?"

Kai Marwa ta jinjina gami da fa'din sosai ma, baki da labari ko...?"

" a a...ban sani ba wlh amma daga abinda ya faru jiyan nan na fara zargin wani abu, kuma tsoro ya cika min zuciya..."
Murmushi Marwa tayi...idanun ta na cikowa da 'kwalla.
Da sauri ta dafe kanta da duk hannuwan ta biyu a 'ko'karin ta na son 6oye yanayin da ta shiga.

" Kiyi hakuri idan tambaya ta ta bata ranki ne Marwa, ba nufi na in 'kona miki ba..".
Na fa'da cike da sanyi bayan fahimtar halin da Marwa ta shiga.

Tsawon mintina biyu muna ahakan duk 'din mu babu wanda ya sake fa'din komai kowa abinda ke cikin zuciyar sa daban.
Bangare na ni kam mamaki da da nadamar tambayar da nayi mata nake, yayin da Marwa ke alhini da tunano abubuwa masu dama da suka shu'de cikin rayuwar su.

'Bangaren Rayyan kuwa, da fitar sa wajen motar ya tunkara ya 6ata tsawon minti guda yana 'karewa motar kallo.

Jiya da yamman aka wanke masa ita gata fess da ita kamar yadda ya barta.
Mamakin abinda Zaitoon ta fa'da masa yake sam ya kasa tantance manufar ta balle yasan gaskiya take fa'da ko a a.

Shiga yayi ya dudduba cikin motar bai ga wani ba'kon lamari da zai sa mishi zargi ba.
Ya kunna ta ya gwada komai da yasan rashin su na iya kawo barazana ga rayuwar sa amma bai ci karo da komai da ya dangancin hakan ba, dalili kenan da yasa shi tabbatar wa kansa cewar may be mafarki tayi ba gaskiya bane abinda take fa'da, ko kuma idanun ta basu gane mata da kyau ba.
Batare da damuwar komai ba ya tada motar ya yi gaba abinsa.
Ko da ya isa ga mai gadi tsayawa yai yayi masa tambayar ko akwai abinda yake zargin faruwar sa daga daren jiya zuwa wayewar safiyar yau ya tabbatar wa Rayyan cewa babu komai.

Ya sake tambayar su Huzaifa aka tabbatar masa da cewar basu shigo ba rabon su da gidan tun jiya da yamma.

Kansa ya jinjina gami da harba motar yayi gaba.
Tuni ya watsar da al'amarin cikin ransa ya sawa ransa cewar shirme ne kawai na mata ba komai ba..ko kuma gani take fadin irin wannan maganar zai sa ta samu fada a wajen sa ne oho..

Ba 'karamin gudu yake shararawa bisa titin ba Allah Allah yake yaga ya isa ma'aikatar saboda shigewar lokaci ya tabbata yanzu haka ana nan dakon isowar sa.

Yana cikin sharara gudun kwatsam sai ya hangi wani dattijo agaban sa yana dogara sanda da nufin tsallaka titi a cikin gari irin kano da wannan safiyar da jama'ah duk ke tururuwar tafiya bakin ayyuka da wajajen sana'ar su, ya tabbata ba 'karamin kuskure bane barin wannan dattijon ya tsallaka shi ka'dai.

Sai da ma ya iso ya fahimci ashe ba tsufa bace tasa mutumin nan dogara sanda ba face rashin isashshen lafiya ta ciwon 'kafar sa ta dama.

Yana isowa kusa da shi ya taka motar ya tsaya sannan ya fito da 'dan hanzari ya kama hannun sa yana fa'din Baba, ina zaka je haka da safiyar nan? titinnan yayi girma ka tsallake bayan ga yawaitar ababen hawa".
" 'dan nan Magani zan kar6owa 'diyata a wancan 6angaren yau ta tashi da masassara ne ga shi dama lafiyar ba ta ishe ta ba shiyasa na yanke shawar zuwa da kaina".
" Subhanallahi Allah ya rufa asiri baba".
Yace cike da tausayin mutumin nan.
Shi ya ya yiwa masa jagora suka tsallaka sannan ya ciri 5k ya bashi yace ya 'kara akan ku'din maganin.

Yana kawar da idanun sa daga kan tsohon zuwa bakin titin da nufin samun damar tsallakawa idanun sa suka sau'ka akan wani abin al'ajabi.
Motar sa ke fidda wani bakin haya'ki sosai kamar wacce ake 'kona taya ajiki abin mamaki kuma ta 'kar'kashin motar hayakin ke fitowa.

Har hankalin mutane ya fara dawowa kan motar, kafin yayi wani yun'kuri kuma lokaci guda wuta ta tashi da motar tamkar dai tashin Bomb.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..."
Ya furta a fili yana duban motar da cikin 'kan'kanin lokaci da faruwar lamarin amma tuni ta fita a kammanin ta ta yadda bazata iya 'kara amfanuwa ba.
Abin kamar al'amara kamar cikin mafarki.
Lokaci guda maganar Zaitoon ya dawo masa.
Kansa ya dafe yana komawa baya ya jingina da jikin wata motar da ta parking daura dashi sakamokon abinda ke faruwa.
Duk yadda aka so tsaida wutar da ke ci cikin motar abin ya faskara ana ji ana gani motar nan tayi 'kurmus.

Abinda ya fara zuwa masa shine " da fa yanzu da shi cikin motar nan...Yah Subhanallahi.."
Dattijon nan da shi ka'dai ya san cewa motar tashi ce shine ke ta bashi 'kwarin gwiwa a tunanin sa Rayyan ya shiga ru'du ne sbd asarar motar da yayi.
Sa6anin tunanin Rayyan da ya tafi gurin tantance faruwar lamarin da ma'kasudin sa.
Baya so ya zargi kowa duk da yake har gobe bashi da wanda zai zarga 'din kuma har zuciyar sa baya so ya amince da zancen Zaitoon a ganin sa zai zama ne tamkar rashin tawakkali.
Abin dole cikin biyu 'daya ne.
Amma yafi bawa zuciyar sa tabbacin duk faruwar lamarin shirin ubangiji ne.
Hatta zancen Zaitoon bai yadda ya kama zuciyar sa sama da hakan ba.

Allah ne ya 'kaddaro ya kuma tseratar dani na ku6uta batare da nasan hakan zai faru ba.

Abinda ya tilastawa zuciyar sa rikicewa kenan.
Ko lokacin da 'yan kwana- kwana suka iso tuni mota kam ta gama 'konewa.

Bai 'kira kowa dan ya tallafa masa ba kamar yadda bai 'kira kowa ya sanar wa faruwar lamarin ba...hatta Ammi kuwa.

Yana shirin taran adaidaita yaga gilmawar mota ta gaban sa a slow sakamakon 'dai'daikun mutane dake wajen har yanzu duk da kuwa yawa sun riga sunyi nasu waje amma still da mutane.

Baya ka'dan motar da dawo bayan har ya shiga Adaidaitan suka ji 'karar horn da 'karfi, duk 'din su duban su suka kai wajen.
" Fawwaz "
Ya furta saman la66an sa.

Fitowa Fawwaz yayi da sauri shima Rayyan ya fito daga adaidaita.
Fawwaz 'din ne ya mi'kawa mai adaidaitan Naira 'dari biyu..hankalin sa na ga Rayyan da bai ma tanka sa ba sai motar Fawwaz 'din daya nufa.

A hanya yake bawa Fawwaz labarin duk abinda ya faru a wajen ba 'karamin mamaki Fawwaz yayi ba..sai dai 'karshe hamdala kawai yake ta zubawa ga mahalicci da ya ku6utar masa da aboki.
Sai da ya sau'ke shi a office 'din su kafin ya wuce asbiti wajen aikin sa.

Duk da yake ba'a nitse yake ba sannan ya makara sosai amma duk hakan bai hana shi shiga meeting 'din dan zantawa da bakin nasa ba.
Ya kuma yi 'ko'karin yin komai bisa tsari da natsuwa yadda ya kamata.

Ammi na can Abuja labari ya riske ta na abinda ke faruwa wanda ta samu labari daga bakin wani abokin 'dan ta marigayi Muhammad Kabeer.
Chapter 81 · 0% Book details