← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 218

Sashe 73

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Marwa tayi.
" lallai, dan baki san waye Yah Rayyan ba ne yarinya, haka fa yake, ko nima haka yake min har gara yanzu amma da nima har bansan gaida shi baya magana, baya doguwar magana, ko ada da Safaa ka'dai yake doguwar magana kafin rasuwar ta bayan rasuwar ta kuma shike nan, sai ko Yah Sultan da Ammi amma yanzu Alhamdulillah ai ya canza, kawai ke ce da baki fahimce shi ba..amma yana amsawa ko da da kai ne ko ido..."
Cike da mamaki Zaitun ta dube ta.." Da kai ko ido..?"
" Yess..."
" Toh sai kace ban da abinyi sai in tsaya gaida shi yana amsawa da ido da kai bacin ga ayyuka nan cunkus a 6angaren Ammi da suka isa in 6ata lokaci wajen yin su...?"
Dariya sosai Marwa tayi tana fa'din..." Ke Yayana ne fa, my one nd only brother haka yake, shifa da kike gani ba kamar kowa yake ba, komin sa na daban ne..."

Baki Zaitun ta kya6e tana kawar da kai.." Ke dai ke ganin hakan.."
" Kema watarana zaki fahimta, baki san tarihin gidan mu ba ko, baki san asalin labarin ahalin Late Alhaji Sa'ad Muhammad Auta ba ko..?"

Salmerh😘
[10/10/2022, 10:12 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...45*

........" Baki sani ba shiyasa kike fadin haka...".
" Toh Marwa taya zan sani bacin ba'a sanar da ni ba..?"
" Hakane...amma Insha Allahu in na samu dama zan baki labarin gidan mu, labarin ahalin mu ma gaba daya".
" Allah ya bada iko, nima zanso ji Marwa.."

'Yar daria Marwan tayi tace" Sai.na samu isaahshen lokaci".
Da haka suka 'karasa rakiyar Marwan suka juyo gida.

*****
Hutu sosai Zaitun ke samu a yanzu da yake Amrah bata gari tayi tafia, aikin ta ba wani mai yawa bane, Rayyan ma 6angaren Ammi yake zuwa cin abinci...shiyasa suke samun zama susha hirar su sosai duk ranar da Marwa ta samu shigowa.
Kusan za'a iya cewa yanzu bata da wata matsala a gidan nan, babu abinda aka tsawwala mata a kansa.

Ko Rayyan ma ba shiga sabgar ta yake ba, koda wani aikin ya kai ta 6angaren sa sai dai bisa kuskure abu yake hada su, kuma yawanci ma akan Mufeeda ne, ta jima da fahimtar cewa asali shi ba me shiga sabgar mutum bane kawai dai itan ma rashin fahimta ke sawa suke samin sa6ani.

Rayuwar sa yake yi batare da ya shiga sabgar kowa ba haka shima baya bari a shiga tashi sabgar da garaje.

Ko doguwar magana ba koda yaushe yinta ba sai ta kama, da Ammin sa ko 'yan uwan sa ne idan kaga yanayi, sai ko matar sa Amrah.

Tun zuwan ta gidan ta fahimci halayyar sa wanda daga baya ya dan kara wasu abubuwa kadan sa6anin.na bayan har yake iya doguwar magama musamman idan akan su ne, ada tasan mugun sanyi ne da shi, baya da hayaniya...ko magana ze yi da 'kyar yake harha'dawa..(baki ji ba..)
idan kina kusa da shi kika kuma ji ya furta hakan to ki san cewa da ke yake magana wataran kuma ( Ji mana)
shine abinda yk furtawa ko kuma...(nace ba)...duk sanda hakan ta ha'da ku toh abinda ze biyo baya shima takaitacce ne..coffee, ruwa, ina Ammi? Amrah fa? Marwa ta shigo ne..?
Sune abinda ze iya tambaya wurin mutum baya ga hk komin sa da kansa yake baya jira ya saurari kowa ko kuma jiran ayi masa.

Baya da fa'da koka'dan, amma idan ka 'kure shi abin ba ze ma kyau ba, baya shiga sabgar da ba ta ha'da hul'da da shi ba...ita dai tsawon lokacin zaman ta a gidan su bata ta6a ganin yayi doguwar magana ta tsayin mintina ba...sai dai in akan su ne.

Likita ne shi, kuma Barrister ne, CEO ne a companyn mahaifin sa da ya mutu ya bari...farko kafin girman sa Rayyan bashi da burin da ya wuce ya zama 'daya daga cikin manya manyan Alkalan 'kasar Nigeria tamkar dai mahaifiyar sa, burin.ya shahara ta fannin alkalanci, hakan yasa da gama secondary school 'dinsa a lokacin shekarun sa goma sha shida ne ya nemi cigaba da karatun sa fannin LAW amma hakan bai samu gare shi ba, mahaifiyar sa da kanta ta za6a masa karatu 6angaren likitanci, mahaifin sa ne yayi jagora wajen nema masa gurbin karatu a India kafin cikar sa shekara ashirin da ashirin da 'daya kuwa har ya kammala inda ya fito da sakamako mai matukar kyau, mahaifin sa be yi 'kasa a gwiwa ba wurin sake fa'da masa ilimin likitancin sa inda ya sake nema masa gurbin karatu sai dai wannan karon a anan 'kasa Nigeria yayi karatun..yana matashi mai 'karancin shekaru ya zam cikakken likita wanda ke da matu'kar kwazo da 'kwarewa bisa aikin sa.

Rasuwar mahaifin sa ya sashi sha'awar dawo da muradin sa aikin Lawyer bai yi 'kasa a gwiwa ba kuwa ya fara aiwatar da 'kudurin sa, dai- dai lokacin da aka fara shirye shiryen auren sa gadan gadan.

Matar sa ta kasance likita ce itama dan tare suka yi karatu a India da ita, bambancin kawai ita ta samu fita Indian ne ta hanyar scholarship yayin da shi kuma 6angaren sa ba hakan bane ba.
Tare suke aiki da wani abokin sa mai suna Fawwaz kasancewar sa 'dan abokin mahaifin sa ne kuma asbitin ta mahaifin Fawwaz ne.
Nan ya fara aiki kafin yazo ya 'dan ja baya yayin da kuma ya cigaba da gudanar da karatun sa a gefe guda.

Ya ha'da karatun sa na aikin Lawyer yana da shekaru 29 da haihuwa ya kuma zama cikakken Lawyer kamar yadda yake da muradi...wanda sai lokacin da yake tsaka da karatun kafin Ammin sa tasan batun ta kuwa yi masa fa'da sosai amma ya kwantar da kai ya bata hakuri bai kuma sanar da ita dalilin karatun nasa ba.

A time 'din da yake cigaba da karatun nasa already babban yayan su Kabeer ya cigaba da gudanar da kasuwancin mahaifin su kuma komai na tafia dai dai da yake dama shi harkar kasuwancin ya za6a kamar dai Sultan da shima yafi so ya karanci fannin kasuwancin.

Amma wani dalili ya sanya Sultan tafiya training na soja da yake an tsaya masa bai yi wahalar samu ba sai dai tun ba'a yi nisa ba shima ya ajiye aikin suka cigaba da gudanar da kasuwancin su tare, duk da Sultan 'din ba sosai yake bawa harkar muhimmanci ba amma ahakan sosai Rayyan ke.jin dadin ganin sun hade kansu sun kula da komai nasu atare.

Wani lokacin Rayyan is nice amma wani lokacin kam ba'a gane kansa Haka yake tamkar wani mai aljannu.

Komai na Rayyan me kyau ne kama daga halittar sa zuwa tsarin rayuwar sa, tamkar shi da kansa yake za6awa kansa komai cikin rayuwa.
Haka abubuwa suka cigaba da tafiya har zuwa wani 'dan lokaci.

*****
" Haba 'diyar albarka, kibari in kama mk ko biyu ne mana, nima ba kin yi min ba ko so kike ki sake yi min wani?"
kai ta daga sama alamar erh.

" amma fa kan nawa ya fara ciwo Moopy baza'a barni in huta haka ba.."?
Kafa'da Moopy ta no'ke Zaitun sai tayi murmushi toh shikenan zo kiyi min in kin gama sai in 'karasa miki naki kema".
Tayi maganar tana gyara kwanciya gaban yarinyar
Cikin ranta take ayyana" Moopy na rigimar ki yawa ne da ita wallahi".

Haka suke shashancewa lokuta da dama wajen yin kitso, dan sam Moopy bata 'kaunar kitso a rayuwar ta har yanzun, amma idan Zaitun zata zauna gaban ta tace _yi min kitso_ toh shikenan ta gama siye mata zuciya an ringa jagwalgwala kan kenan, da haka da 'kyar da dabara take samu tayi mata nata kitson da a kullum baya haura guda hudu zuwa shida in yayi yawa takwas zuwa goma ne, sai dai ta kanyi 'ko'kari wajen ganin ta canza masa style wanda ze birge duk wanda ya kalla.

Ammi kam da ta kasa ha'kuri sai da ta tambaye ta me yasa kitson Moopy kullum baya wuce haka dan indai ba Marwa ce ta sa akai mata kitso mai kyau ba toh kuwa kullum haka kan nata yake, ita kanta ma ba kitson take so ba balle ta damu da na 'diyar ta.
Zaitun sai ta yi murmushi tace" Ammi ai hakan ma da 'kyar da dabara muke yi fa..yarinyar nan bata 'kaunar a ta6a mata kai sam..."
" Ke kuma bakya iya yi mata abinda bata kauna ko?"

Murmushin ta 'karayi tana fa'din" Ba haka bane fa Ammi..kawai dai kukan ne bana so...."
" Haba Zaitun ai tsakanin ki da Moopy kam sai dai ni in bada labari ma wasu amma babu abinda ban sani ba...".
" Hakane Ammi..".
" Kamar dai wata 'diya ta da ta rasu shekarun baya, tun tana 'yar 'karama itama haka take bata 'kaunar ata6a mata kanta sa6anin 'yar uwar ta Marwa da ita kuma ko sau nawa zaki ware ki kitse mata bazata yi kuka ba, har suka girma haka suke da bambanci ta wannan 6angaren amma hakan bai sa daidai da rana guda na biye mata ba, har ciwo Safaa take 'kir'kira duk lokacin da ta tabbatar ranar zuwa Saloon 'din su ne, amma ahakan zan tura ta wani lokaci ko bayan anyi kitson sai tayi zazza6i, Yayan su ne ya roki adaina yi mata kawai ana gyara kan sbd bata so amma dan tani ahakan zata saba...ai mace sai da ado, mace 'yar kwalliya ce kuma hakan bai samuwa sai da gyara".
" Hakane Ammi, Allah ya ji kan su da Rahama, Allah ya gafartawa dukkan musulmi..".
" Ameen Yah Rabbir raheem..Amin 'diya ta...".
Cewar Ammi sannan ta cigaba da fadin" Ni inaso inga anyiwa Mufeeda kitso irin me kyau da ake yiwa yaran nan idan babu damuwa, kinga akwai wajen da Marwa ke kaita sai a kaita ayi mata mai kyau acan..."
Chapter 73 · 0% Book details