← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 114 OF 218

Sashe 114

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Madeena tace abarta mana, yarinyar da tuni ta saba da su ta sake tana wasan ta, makarantar ma tuni ta saba da ita, tace Badi'a bazata ji dadi ba idan aka dauke ta wallahi.

Ammi tace itama uwar dan baku san halin da take ciki bane...ai tayi hakuri ma.

Anty Madeema tace kai Hajjaju..ku dai kuce kuna son adawo muku da 'diyar ku ne kawai amma nan din ma ai duk gida ne.."
" Erh munji adawo da ita duk wannan hakurin baku gani ba?"
Ammi tace tana murmushi.
" Bari dai toh in gani in zai yiyu zuwa gobe sai asan ya za'ayi ko zuwa jibi ma..."
" Allah ya nuna mana dan Allah a kokarta munyi kewar ta sosai..."

Duk wayar a handsfree akayi shi, kuma wannan wayar da taji shi ya sanya zuciyar ta cikin walwala sosai har ma idan ka dube ta lokacin da take bacci murmushi zaka gani kwance saman fuskar ta.

Tun bayan jin maganganun Amrah da Sultan, bata sake jin kanta cikin farin ciki kamar yau din ba.

Tun cikin dare Anty Madeena ke neman layin san amma baya shiga, so take ta sanar da shi batun test din su danta lura tunda ya samu Arfan ya mance da batun Mufeeda...
aganin Ammi fa..

Rayyan nan kan kujerar ya Kwana, tun tasowar sa har girman sa bai ta6a yin kwanan takura irin wannan rana ba, amma ji yake zuciyar sa tafi natsuwa fiye da ace yana gida 'kar'kashin inuwa guda da Amrah, baya so fushin sa ya haura level 'din da bazai iya controlling fushin sa ba dan zai iya illata both Amrah da Sultan din.

Sallah kadai ke tada shi.
Da dare kuwa kwana yayi sallah yana rokon Allah gafara, rayuwar tasa tsoro take basa ayanzu, ta ko'ina baya samun sassauci.
Ta ko'ina illata masa zuciya ake.

Baccin da bai yi da daren bane ya rinjaye sa da safe shiyasa sai da yakai har kusan sha daya sannan ya farka.

Sai da ya watso ruwa sannan yazo ya zauna wayar sa 'daya da yasan yafi huldar family da shi ita ya kunna, Ammi yake son kira amma ga mamakin sa yana kunna wayar 'kiran Sultan ne ya fara shigowa, haushin hakan ya sanya shi sake rufe wayar ya kife ta ya tafi izuwa ga 'kananun kayan sa ya sanya a jikin sa.

Bai sake bi takan wayar ba har sai daya dawo daga sallar azahar da ya fita masallaci, sannan bai dawo akan kari ba dan sai da ya wuce Shoprite ya siyo kayan da yasan zai bukata anan na 'yan kwanki...

Anan nema daya ga hada- hadar mutane ta yawaita sosai ya tuna ashe fa daf ake da kama azumin ramadan...shaf ya mance.

Ammin ce dai still acikin ransa.
Hakan yasa da dawowar sa ya sake kunna wayar sa tasa, dan manufar ta karu masa.
So yake ya sanar da ita inda yake gudun kar ta shiga damuwa, baya ga haka yana kuma so ya tunasar da ita adadin kudin da za'a fitar dan rabawa mabu'kata kayan abinci da suka saba kowace Ramadan.

Wannan karan ma yana kunna wayar kiran Anty Madeena ya shigo masa.

Sai dai bai 'ki 'daga nata 'kiran ba duk da ba hakan yaso ba.
" Sannu isashshe..sai yanzu kaga damar bude wayar? meyasa kake son kashe dukkan wayoyin ka ne Rayyan sai ayi neman ka baza'a samu ba...?"
" Wlh Anty bana jin dadi ne..."
Ya bata amsa da sanyin murya.
" Subhanallah...ya jikin..kuma fa gashi ina son ganin ka, kaga Ammi da Zaitoon sun matsa adawo musu da yarinyar nan gashi har yau ka kasa tsayar da lokacin da ya kamata muje asbitin, kuma nafi so ayi komai a kamamala cikin lkc 'kankani ta yadda babu wanda zai zargi wani abu...in da hali ka daure muje ko zuwa bayan la'asar dan Allah...".

Hannun ya cusa cikin gashin kansa ya shafo wannan ha'da shi da Allahn da Anty Madeena tayi yasa shi amince mata bisa dolen sa.

" Toh Anty Insha Allah zan yi kokari in zo sai muje..."
Daga haka suka yi sallama...Ya kira Ammi...gaba daya hankalin ta tashe yake tun jiya take kiran sa har yau din amma shiru, dole hankalin ta ya tashi tana tsoron abinda ya faru abaya ya sake faruwa gare shi shiyasa duk ta shiga tashin hankali.

Ga Marwa bata shigo gidan ranar ba balle ta taya ta jimantawa sai Zaitoon kadai, Amrah kuwa yaron ta kuka yake yawan damun ta da shi itama ba nutse take ba.

Tana zaune zaman zullumin inda yake da abinda ya same shi taji wayar ta na 'kara, da sauri ta kai duban ta ganin shine ya sa ta 'daga da sauri.
" Rayyan?..haba Rayyan..ina ka shiga haka ne...?"
" I'm sorry Ammi...ina gidana ne..."
" Shine bazaka fada min ba kuma ka kashe wayoyin ka Rayyan, hankalina ya tashi sosai wlh..."
" I'm sorry Ammi kawai na bukaci hakan ne but zuwa dare zan shigo Insha Allahu..."
" Ok...pls kar ka sake min irin hakan kaji duk inda zaka ko wani abu ka sanar dani dan Allah.."
" Insha Allah Ammi...".

Bai yi niyyar zuwa ba amma jin yadda Ammi ta rikice da jinsa ya sanya shi dole yayi skipping maganar kayan Ramadan har sai yaje, dan ya lura ganin sa ne kadai zai iya sanyaya zuciyar Ammin sa.

Sultan kuwa tunda ya 'kira Rayyan ya kashe masa waya zuciyar sa ke tafarfasa, gaba action 'din Rayyan 'din sun dagula lissafin sa, dama yasan na'ura sosai, so kawai bin diddigin Rayyan din yayi ya kuma yi nasarar gano inda ya ke amma bai sanar da Ammi ba, haka shima bai je ba.

Ko ta 'kira sai dai yace mata yana kan bincikawa.
Shirin sa kawai ya cigaba da yi a 6oye batare da kowa ya sani ba daga shi sai Allahn sa sai kuma mataimakan sa.

Rayyan kam kaya ya canza ya fita zuwa gidan Anty Madeena dan zuwa yanzun shi kansa yana so koma mene akai shi 'karshe ya gaji da walagigi da saka rai da ake masa akan yara...bai sani ba ko bashi da rabon samu ne alhali Allah ya daura masa kaunar su...basu wani 6ata lokaci ba suka fita zuwa hospital, tun kafin zuwan su ya kira Fawwaz ya sanar da shi ya tabbatar masa cewa yana hospital.

Tun isowar su da yaga Anty Madeena ya kuma ga Mufeeda zuciyar sa ya bashi wani abu, ganin yanayin Rayyan bai bashi mamaki ba domin yasan dama fin haka ma za iya gani tun ranar da yaga yarinyar yaji cewa akwai wani abu.

Salmerh😘

[3/11/2022, 9:16 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...66*

........Bai manta dalili da kuma yanayin da suka rabu a jiya ba.

Gaisar da Anty Madeena yayi yana me duban Rayyan dan sosai tausayin abokin nasa ya tsaya masa arai tun a jiya.

Anty Madeena ce tayi masa takaitaccen bayanin abinda take so ayi.
Ya kuwa kallo RAYYAN a firgice yana me mi'kewa, shi dama ya ta6a zargin hakan, ba kuma yaji aransa cewar zargin nasa ll totally go.in vein hakanan kawai ba, amma dayake Rayyan bai bashi 'kofa ba yasa dole ya watsar da batun.

Rayyan daya san dole da jin maganar Fawwaz zai dube shi sai ya ki 'daga idanu ya kalle shi balle su ha'da idanu...ji yake tamkar Fawwaz din na 6ata mai lokaci, 'kage yake da son jin 'karshen sakamakon...ba dan ba zai iya ta6uka komai ba da ko sauraran wani ma bazai yi ba da kansa zai yi komai.

Fawwaz da kansa ya ja jinin su duka yayin da Mufeeda dake rungume jikin Anty Madeena ta saki kuka jin yadda allura ya 6ula mata jiki.
Sosai Anty Ta rungume ta yayin da Rayyan ya zuba musu idanu.
Ji yake tamkar yaje ya kar6e ta ya lallashe ta sbd yadda kukan ke ratsa masa zuciya...amma baya so Anty taga kamar ya za'ke da yawa...amma da ace zai bi umarnin zuciyar sa da tabbas hakan zai yi.

Fawwaz tsaye ya tsaya kan 'kafafaun sa a Lab 'din har aka yi komai aka gama, duk da yake sun zone kusan za'ace a 'kurraren lokaci amma yadda Rayyan ya shiga damuwa yana fatan wannan sakamakon ya wanke masa dukkanin bakin cikin dake cikin zuciyar sa.

Tun da ya fito da sakamakon yake sakin hamdala gami da murmushi ya nufo office 'din sa da sassarfa, ji yake tamkar wani babban kyauta akai masa.

Hakika Allah gwanin baiwa ne kuma sarkin sarakai, Allah mai kyauta da 'kari, ya hana ka wani abin ya kuma baka wani a lkcn da bak zato, sai gashi ya dawo ma Rayyan da farin cikin sa a lokacin da yake tunanin ya rasa ta.

Da zuwa bai ko kalli inda Anty Madeena take ba ya nufi Rayyan ya mika masa Papers 'din fuskar sa kumshe da yalwataccen murmushi, yayin da ya tsurawa Rayyan idanu dan ganin nashi yanayin.

Idanu Rayyan ya zuba akan Papers din tunda ya fara karantawa da ya fahimci abinda suka 'kunsa kawai sai ma ya kasa 'karasa karatun ya tsura musu idanu...sai ya ma rasa shin nazartar rubutun yake ko kuwa irga yawan su, bai ta shi sanin 'kwalla ke bin 'kuncin sa ba har sai da Fawwaz ya dafa shi.

A lokacin ya 'dan motsa kansa sai kuma ya 'daga kai ya kalli Fawwaz dake tsaye kansa da rinannun idanuwan sa, Kai Fawwaz ya jijjiga masa..." Hamdala ya kamata kayi ba kuka ba Dr...ka godewa Allah da ya nufe ka da fahimtar haka tun kafin 'diyar ka ta dulmiya cikin dunia batare da ka san da zaman ta ba, baka ma gode Allah ba da ya sake dawo maka da ita gaban idanun ka ta rayu gaban ka, karkashin inuwar ka da dukiyar ka duk da kuwa baka san cewa jinin ka bace...?"

Karo na farko tsayin ranar ya saki murmushi, murmushin da ya fito tun daga zuciyar sa ya kuma kore masa dukkan 'kuncin da yake jin sa ciki lokuta 'kalilan baya.

A hankali ya sau'ke idanun sa kan cinyar Anty Madeena, Mufeeda ce, yarinyar Zaitoon, hakika ita din jini na nace, 'diyar ciki na....
Chapter 114 · 0% Book details