Sashe 196
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace...kuma shi aure ai Allah ke ha'da shi ba wai iyawar mu ba, yace ka duba misali mana lkcn da take nan gida shekarar ta nawa da zancen auren Babaji? 'dan uwan ta ne amma kuma auren ya kasa yiyuwa sbd wasu 'kananun dalilan da mu da kanmu ba zamu iya ce ga irin su a zahiri ba balle har mu iya magance su..sam Allah bai bamu damar tantancewa ba...kasan dalili...?
Ya girgiza kansa.
Abba Yace" Saboda Zaitoona ba matar sa ba ce tun asali..."
" Ka duba yadda wannan auren nata ya kasance? a yadda suka fa'da kai kanka kasan mu'kaddari ne kawai da kuma shirin mahalicci...basu ka'dai ba, bashi mijin ba hatta su iyayen nasa da suka shirya shi yazo musu ne a bazata da yake Allah ya riga ya rubuta sai anyi...baka ga anyin bane ?"
Toh Bukar mu su waye da zamu ce sai mun raba abinda Allah da kansa ya shirya ya kuma ha'da shi?
" Nasani da kanka kasan cewa ba mu ke rubuta 'kaddarar mu da hannun mu ba, ko kuwa ka mance cewa kowa da kalan tasa 'kaddarar yake tafe ne a rayuwa...? Mene amfanin sakin nata da za'ayi indai an yadda da nagartar mijin nata ai rabuwar babu amfani, baya ga haka ma bb wata matsala gagaruma a tsakanin su, ba rashin ci ba, ba rashin sha ba, ba rashin kwanciyar hankali ba..ba kuma wata cutarwa ake mata ba..dan Allah Bukar abarta tayi zaman auren ta kawai sbd Allah.
Muyi mata fatan alkhairi, ka kyautatawa kowa zato..kayi mata fatan samun aljanna sanadin wannan aure bawai burin raba shi ba, dan Allah kayi hkr kaji ba wai na matsa bane kawai inaso ne..."
Shiru Bukar yy bai iya ya sake fa'din komai ba.
Ire- ire wannan maganar kusan ko wani lokaci idan zama ya ha'da shi da mahaifin nasa yake masa..kuma ya fara yi masa maganar ne tun washegarin tafiyar su Rayyan da safe daya je duba shi.
Amma shi dai har yanzu ya kasa jin amincewa.
Yana nan dai akan bakan sa na son zaman Zaitoona kusa da shi.
Iyami kuwa dake yawan musu la6e kwafa kawai take yi tana cije baki.
Kusan kullum hakan ke faruwa, haka zata tsaya ta jira wucewan Bukar ta sau'ke ruwan masifa kan Abban nasu...haka take yi masa kullum amma ya kasa canza ra'ayi, kamar yadda shima Bukar ya kasa jin aminta da batun da Abban ke zuwan masa da shi.
Ita kuma Iyami da gangan take hura masa wuta dan ya janye maganar amma yya 'kiya...wannan karan so yake ya yiwa Zaitoon adalcin da tun tasowar ta gaban sa bai ta6a yi mata shi ba dai- dai da rana guda a rayuwar ta.
Idan ta gama sau'ke masifan ta fita cikin gida sai ta 'daura da gorace gorace habaici da 'kananun maganganu...wai kwa'dayin abin dunia yasa shi nacewa kan batun...kuma indai hkne itama Khausar an fasa auren ta da Babaji sai dai ya samo mata wani 'dan birnin itama ta aura.
" Kice dama damuwar kenan?"
Sai anan ya tanka ta.
inda ya cigaba da fa'din " wannan ne kuma baku isa ba.. daga ke har mai goya muku baya din, tun farko ku ka amince har aka gama magana dan hk wannan aure kamar an yisa an gama ne".
Bai tsawaita ba yy shiru...Iyamin ke ta faman masifa da kumfar baki..ta inda take shiga bata nan take fita ba, tana ta hargagi ita ka'dai zuciyar ta ba'ki'kirin.
Abban kai kawai ya girgiza a zucia yace.." Mai hali dai baya fasa halin sa.."
'Bangaren su Zaitoon kuwa a hankali yanayin ke shiga jikin ta, tamkar su Ammi sun tafi mata da walwala da farin cikin ta haka take ji, sau'kin ta ma 'daya an bar Mufee tare da ita, kuma babu laifi tana 'debe mata kewa, amma sam ta kasa walwala...bata ta6a sanin har haka suka shaku ba sai yanzun, bata san cewa zatayi kewan su Marwa ba sai yanzu.
Ta riga ta nemi afuwan mahaifan ta kan abinda ta aikata 'daya bayan 'daya sun kuma yafe mata so sai ta rasa kwata kwata meke damun ta a zucia, amma kusan koda yaushe ji take bata da da natsuwa...fargaba take ji na yawan shigan ta...banda tsoro dake kusanto ta kusan kowace rana.
Cikin lkc 'kan'kani labarin dawowar ta da 'diyar ta ya baza ko'ina a garin, wani abu da 'karamin gari da wuya magana ke 6oyuwa.
Da yawan mutane zuwa suke domin ganin ta, yadda kuma akayi tsammani ba haka ake tarar da su ita da 'diyar tan ba, kowa sai ya ja bakin sa ya gimtse 'dai- 'dai ku ne ke fa'din" Hakika bariki tayi kyau, yawon bariki yy rana.. Zaitoona irin kyau haka..gaba 'daya ta canza ta zama wata 'yar gayu kamar ba ita ba, maganganu iri iri dai ke tasowa.
Hatta Salele mai chemist sai da yazo ya ganta, Dije kuwa ranar da tazo sabon kuka suka dasa dukkan su biyun rungume da juna.
Sai da suka sha kukan su suka gaji sannan Zaitoon ke bata labarin duk abinda ya faru, kuka sosai Dije keyi ta na faman jinjinawa 'kaddara..hakika dole aji tsoron Allah a kuma godewa ni'imomin sa.
'Dan yaron ta da bai wuce watanni bakwai ba kwance a jikin Zaitoon Mufeeda na tsaye tokare da jikin ta tana ta kumburin sai dai yabar mata jikin Zaitoon ita ta zauna...Dije tayi murmushi..." Aishatu ko kara babu? haka ke kuma kk da 'kin mutane?..gaskia baki gaji halin 'kawata ba..."
Ta 'karashe tana 'yar daria.
Murmushin itama Zaitoon tayi tana kallon Mufee tace" Halin Abban tane ai, shima bai son mutane sai ba'kin rai da mugun hali, amma yana da kirki sosai...".
" Shiyasa naga ya siye zuciyar ki da kirkin nasa ai..."
Idanu ta zaro sosai.
Dije tace" erh mana".
A a wlh...kar ki min sharri dan Allah..wancan mutumin fa!..lallai dan baki san ko waye shi bane shiyasa".
" ai ke kin san shi ko...?"
Dije ta sake tambayar ta still tana dariyar dai.
" Erh mana.."
" Toh ai bu'kata ta biya".
Shiru Zaitoon tayi bata sake tankata ba.
Amma sam maganar Dijen ya kasa barin ranta...dama tun zuwan su bata ta6a hirar sa da kowa ba, ko batun auren Innani bata ta6a yi mata ba, ko Abban ta in taje wajen sa nasiha kullum ke ha'da su ya kuma ce kar tayi wasa da addu'o'i ta nemi za6in Allah bisa komai nata na rayuwa..bai ta6a fitowa fili yace ga manufar maganan sa ba..balle Yah Bukar da har yanzu ma ba gama hucewa yy ba...gaisuwa ka'dai ke ha'da su shima 'din sama sama yake amsa ta.
Khausar ce uwar surutu da rawan kai amma ko ita idan tazo burin ta kawai ta 'dauki Mufee su je yawo da ita ne...sai kuma ta ri'ka sumbatu akan rayuwar su wani sa'in..." Adda ke kam kinji da'din ki...Allah yana son ki sosai.."
Da yake ba wani sake mata fuska take ba shiyasa hirar su bata wani fiye yin tsayi ba.
Ummaru ne abokin hirar ta shima kuma kwana biyun nan duk bata ga idanun sa ba.
Duk wani wanda ke zuwa gidan domin ta kuwa duk tasan yanayin da take tarbar su..ko bakomai ta 'karo ilimin zaman dunia..ba duk wanda ke yi maka daria ke 'kaunar ka har zuci ba...wannan karatun ta gama haddace shi ba tun yau ba, bata manta irin su Hajjaju mai 'yan mata ba...
So bata hira da kowa, duk wa'danda tasan ada bata ishe su kallo ba sam bata sake masu dogon hira dan tasan gulma ce kawai ta kawo su da 'daukan magana..toh da wa zata yi hirar Rayyan 'din...sai fa yau da ta samu Dije suka sha hirar su har suka ta6o 6angaren sa...a ranar yini sukayi suna hirar su ta bayan rabo tamkar kada su rabu da juna haka suka ji.
Shi kansa mijin Innani da farko 'kin amincewa yy da zaman su a gidan sa dan dama yana kan masifan yadda cikin kwanakin 'aka dinga yi masa zaryar ba'ki a gida..da kansa kuma sai ya sake fuska bayan fahimtar irin yadda Zaitoon ke girmama shi ga kuma Mufee da ke matukar son shi da ya 'kira ta take zuwa wajen sa tana daria, sai ma ya zamana baya iya shigowa gidan batare da ya ri'ko mata abin lasawa ba...Bayan kwanaki hu'du da tafiyar su Ammi sai ga Adam ya dawo.
Yaso tuntuni ya zo ma amma jikin Abban Hafiz 'din ne sai a hankali.
Direct gidan Innani ya wuce da yake yanzu yasan gidan ba sai yayi tambaya ba.
Yana zuwa kuwa ya ci karo da Mufee na wasan ta a 'kofan gida ita da Ummari yaron Yah Bukar.
Hamdala ya saki har a fili domin ganin tan ya alamta masa cewa zai sake ganin Zaitoon kenan..dan ba tun yau yasan halayyar Zaitoon har ma 'diyar ta ba...bata ta6a yin nisa da inda Zaitoon take.
Sai kawai ya dur'kusa gaban ta ya 'kura mata idanu, sai kuma yaga ko kallon inda yake ma batayi ba balle ta nuna alamun tasan shi.
A hankali yace" Feefy na kin manta da ni ko?..
Ko nuna alamun taji maganar batayi ba..ma'ana dai bai isheta kallo ba.
" Wai Feefy kin manta da Daddyn ki...?"
Ya fa'da cike da mamakin ta yana 'dan 'dage gira.
Shifa ala dole gani yake bata manta shi ba.
Kallon sa tayi 'kur cikin idanu sai dai madadin ta yi masa magana kawai sai ta tashi tayi ciki da sauri tana waigen sa.
Sai da ya sake doka sallama kafin Zaitoon ta fito anan ta fahimci shigowar da Mufee tayi mata baya rasa nasaba da ganin ba'kon fuskar da tayi.
" Ke de baki gaji hali ba wlh....".
Ta fa'da cikin ranta.
Ko ba a fa'da mata ba tasan wanene ke sallamar, domin ta yiwa sautin muryar farin sani tunda jimawa.
Bata so fita ba amma tana da tabbacin Innani na sallah ne a wannan lkcn dole yasa ta zum6ula babban hijabi ta fito fuskar ta babu yabo babu fallasa.
Fuskar fayau babu kwalliya...rabon ma da ko mai ta shafawa jikin ta har ta manta.. amma duk da hakan sai ta fito rass abinta da ko'daddiyar fuskar ta.