← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 158 OF 218

Sashe 158

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da yasan gari ba lafia amma ya kasa ha'kura ya zauna a gida, baya iya yin mintina ashirin batare da ya fito ya duba wai ko Zaituna ta dawo ba.
Hankalin sa duk ya gama tashi haushin iyami yake ji sosai bata ta6a yin abinda ta matu'kar bashi haushi irin na yau 'din ba.

Daga 'karshe kasa ha'kuri yayi ya kamo hanya da niyyan zuwa duba ni, Goni ma da ganin hakan ya biyo bayan sa duk da ba wani hutawan kirki yayi ba, ya riga ya sawa ransa cewa zai dubo ni so bai damu da duk wani abinda zai biyo naya ba.

Tun daga nesa muka fara jiyo karan tahowar motoci sai dai hakan bai sa mun dakata da tafiyar ba kasancewar tun farko ma motoci na wucewa da dugu dan mamallakan motocin na gudun ceton ransu ne, kamar dai ita wannan matar da nake tare da ita, duk tunanin mu ya raja'a ne akan masu gudun ceton ransu ne shiyasa bamu yi yun'kurin dakatawa da tafiyar ba.

Muna daf da hawa saman titin muka 'dan dakata dan motocin su wuce da yake da gudun su suke tahowa..sam bamu fahimci ko su waye ke cikin motocin ba kamar yadda bamu san manufar fitar su ta ranar ba, ashe 'yan ta addar ne suka dawo dan komawa ma6oyar su..amma tun daga inda suka fara tafiyar basu barin duk wanda suka ci karo da shi, harbi suke saki da sun hango mutum, namiji ne ko mace yara ko manya babu ruwan su.

Salmerh😘
[2/1/2023, 10:23 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...89*

.......Cak numfashin mu ya tsaya dukkan mu muka yi suman tsaye sakamakon 'karar harbi da muka jiyo tun kafin su 'karaso inda muke.

Duk cikin mu kuwa babu wanda ya iya 'daga koda 'dan yatsan sa ne balle muyi yukurin guduwa, tsayuwa kawai muka cigaba da yi idanuwan na bin titin da kallo..idan ka ganmu zaka yi zaton an shanye jinin jikin mu ne tsaye nan inda muke.

Mota ta farko Bus ce ta wuce, sai wata golf, ta ukun ma golf ce daga nan sai helux fara kuma duk muna ganin mutanen dake cikin motar, motar da ta 'kara kunno kai ita ma helux ce amma ba'ka, ta bayan ta ma bakar helux ce mutanen ciki tsaitsaiye da bindiga a hannuwan su, nan muka yi ido hu'du da mutum biyu dake cikin motar suna fuskantar mu da bindiga a hannun su, kusan ko wani 6angare akwai wa'danda idanun su ke kallon wurin kuma suke ankare da duk wanda zasu gani.

'Karar harbi muka ji daga 'daya 'bangaren wanda muka tabbatar mutum suka gani suka harba, ni kam idanu na 'kyam na ware su ina duban masu bindigan illah bugun zuciya ta da ya 'kara tsanani ji nake kamar zai faso 'kirjina ya fito.

Matar ce dai ta rintse idanu da 'karfi hawaye masu zafi suka gangaro mata, da sauri ta kuma bu'de idanun ta sai taga already wannan farar helux 'din ta wuce ba'ka ce yanzu saitin mu ita kuwa ba gudu take yi kamar sauran ba.

Kafin muyi wani yun'kuri sai gani muka yi 'daya daga cikin su ya saito mu da bindiga, wani bushshshen yawu na ha'diye, wanda na tabbatar ko ma'kogorana bai wuce ba.

Matar ce ganin ana shirin harbin mu tayi 'karfin halin tura ni bayan ta ita kuma ta kasance a gaba tana sake rungume 'danta a 'kirji.

Bazata batare da mun shiryawa hakan ba kawai muka ji 'karab harbi, 'karan harbin da ya gigita min kwanya yasa na daina jin komai na wucin gadi.

Harbi na farko ta kan jaririn dake hannun Nadia ya shiga ya kuma fita ya ratsa ha'karkarin ta sai dai bai shige can ciki ba.

Idanu tayi saurin rintsewa tana karanto Innalillahi wa inna ialihi raji'un a fili..cike da galabaita, ban san abinda ya faru ba, ban san cewa harbin gare mu ya taho ba amma jin tana innalillahi yasa da sauri na ri'ke ta musamman ma jin yadda ta kame wuri guda, ina kokarin fitowa daga bayan ta tayi saurin rike min riga ta baya da 'daya hannun ta..da karfi ta rike ni ta kuma tokare ni ta yadda motsi ka'dan idan nayi 'kasa zata yi duk bansan meke faruwa ba, ajiyan numfashi na sauke wanda yayi daidai da sake jin saukan wani harbin a gefen cikin ta, wannan karon kam gaba 'daya tayo baya ta kwanto jikina, bani da karfin iya 'daukan nawin matar da kuma kaina hakan yasa muka yi baya nuka fa'di 'kasa gaba 'daya...Nadia na salati, jaririya kam na jin yanda muka fa'do sai ta tsanyara kuka dan ita ba haka ta saba jin tana rayuwa cikin mahaifiyar ta a gigice ba, sai kuma akayi rashin dace ta fito dunia ne adai dai ga6ar da kowa ke neman tsira da ransa

Yanda matar ta danne ni ne ya sa na kasa cire kaina daga 'kar'kashin ta da wuri ga kuma kukan jaririyar dake ratsa min ko'ina a jikina...kukan take yi kamar ranta zai bar jikin ta, ni kuma gaba 'daya sai hankali na ya tashi ganin abubuwa na neman tsarwatsa min kwakwalwata, me ke faruwa ne har alkcn ban sani ba.

A gigice kawai na tashi zaune daidai lokacin da motocin 'yan ta addan suka 'karasa wucewa da alamu sun 'kare kenan..kan matar sai ya zama na akan cinya ta yake hakan yasa na zuba mata idanu a rikice nake tambayar ta ko lpy.

Dafe cikin ta kawai tayi da 'dayan hannun ta wanda 'dazu take rike ni da shi, a hankali idanun ta ke lumshewa hawaye masu sanyi na gangarowa ta gefe da gefen idanu, har yanzun kuma jinjirin na rungume da ita bata sake shi ba.

Jini da na gani yake malala daga jikin ta ne ya matu'kar gigita ni, take na kai hannu bakina na saki kuka jikina ya fara rawa sosai...da rawar murya nake ro'kon ta akan ta taimake ni ta ta shi dan ni ban san yadda zan yi da su ba.

A hankali matar ta 'dage hannun ta kan cikin wanda duk ya 6aci da jinin harbin da aka yi mata.

Hannu na ta kamo ta rike cikin nata hannun tana duban fuska ta take murmushin 'karfin hali.

Sai da ta lashe la66an ta kafin tace"...Zaitoon"!
Ban iya na amsa ta ba sai idanu na dake turereniyar hawaye na zuba mata na ma kasa fadin komai " Nasan ke 'yar halak ce, kamar yadda yarana suke 'ya'yan halak..."

Ido ta lumshe cike da galabaita tace" Na baki ita kinji, na baki Aisha halak malak ki kula min da ita ki bata tarbiya mai kyau kamar yadda akayi maki kinji...daga yau Aisha 'diyar ki ce...
Cikin jakata akwai ku'di sai dai ba yawa akwai katin banki na aciki zaki iya amfani da shi..kiyi ha'kuri dan Allah, ni ba niyya ta in saki cikin matsala ba, ba niyya ta in shiga rayuwar ki in cutar da ke ba amma Allah yafimu sanin kowani sirri, nasan Allah ne ya ga daman ha'da ni dake, ko bayan bani kimin wannan uzurin kinji 'kanwata, duk halin da zaki tsinci kanki a ciki karkiyi tunanin dan mugunta na saki..bani da yadda zanyi ne..amma babu mamaki ki ha'du da..."
bata 'karasa ba sai kuma tayi shiru.
Ni kam banda kuka babu abinda nake yi, kuka nk hadda sheshsheka sosai jikina yayi sanyi.

Idanun ta ta lumshe sannan tace" Ina jin zafi sosai.., 'kirji na yana min zafi sosai Zaitoon..".
A hankali sosai tayi maganar amma dayake kanta na kan cinya ta ne hakan yasa naji abinda ta fa'da.

Hijabin kanta ta nayi saurin cire mata dan dama ba wani sauka mata yayi sosai ba kasantuwar bashi da girma.
Kalle-kalle na fara da nufin samun abinda zan yi mata fifita tunda tace zafi take ji, sai dai ban ga komai ba a kusa da mu ba, Allah ma ya taimake ni zuwa lokacin yarinyar ta tsagaita da kukan da take yi tayi shiru.

Dogon numfashi Nadia taja cike da 'karfin hali ta juya ta kalli 'diyar tan dake hannu na sai kuma ta kalle ni da tun 'dazun nake tsiyayar da hawaye.

" Ki bar kukan mana.."
Ta fa'da da sanyin sauti mai cike da rauni.
Hatta idanun ta bazaka yi zaton tana iya ganin abu ahakan da su ba yadda duk suka zama lumsassu.

Cikin 'karfin hali ta sake bu'de baki ta furta" Tashi..ki kaita Inna tayi mata wanka sai ki kawo min ita in ganta kinji?"
"...toh..toh..mutafi tare mana".
Nace da rawar murya ina kokarin 'dago mata kanta.
Tace
" A a kije ki dawo tukunna..ina nan ina jiran ku baki ga naji ciwo a ciki na ba, sai na huta tukunna zan iya tafia..kuje ku dawo...".

" Ba ciwo ba ne..sune suka ji miki ciwon da bindigar su...kuma Insha Allah baza suyi 'karshe mai kyau ba, Insha Allahu su ma sai anyi musu fiye da yadda sukai mk..."

Baki na ta toshe min sai na 'karashe maganar da kukan tausayin Nadia.
" Mance da su...kiyi ta yiwa 'diyar ki addu'a yafi kin ji...nima idan ta girma kice mata ina son ta ina 'kaunar ta..."

Kai na fara juyawa da sauri..." Bani ce zan fada mata hk ba ai ke ce Hajia, kece zaki fada mata ina kaunar ta sosai...".
Murmushi tayi, murmushin da sai daga baya na fahimci cewa na 'karfin hali ne.
" In hkn toh yi sauri kuje ku dawo ina jiran ku ...."

Da jin hakan sai na fara yun'kurin mi'kewa a hankali na sau'ke kan ta daga jikina ban mike ba sai da na 'dauki jinjirar na kuma rungume ta sosai a jiki na, ina shirin mi'kewa sai naji Nadia ta riko hannu na da idanu ta mika min karamin jakan ta ban yi musu ba na amsa na gyara rikon yarinyar da kyau ta yadda babu wanda zai ganta a hannu na.

Haka na wuce ina tafiya ina sake waigowa domin itama Nadia idanun ta akan mu yake, ta zuba mana idanu tayi tana kallon su har muka 'dan yi mata nisa da inda take sannan ta maida idanu ta lumshe tana kallon sama.
Chapter 158 · 0% Book details