← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 218

Sashe 50

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Ya isa haka nan!, kukan nan ya isa"
Ta furta cikin ranta cike da bawa kanta 'kwarin gwiwa.
" Mene ma ribar shi?"
Ta sake tambayar zuciyar ta.
Bude idanu tayi ta sauke su kan Mufee dake wasa da 'dan 'karamin kwalin waya da bata san ko wacce iri ba ce ba ta dai tabbatar da kwalin waya ne duba da ganin hoton wayar da tayi a jiki, daga hannayen yarinyar fuskar ta maida duban ta har kullum kaunar ta sake ninkuwa mata yake a zuciya ita da kanta tana mamakin kanta lokuta da dama.

Daidai da rana guda bata ta6a ji yarinyar ta ishe ta ba, bata san meyasa ba, duk da irin tarin qalubale da ta fuskanta amma bata ta6a jin sa6anin 'kauna game da yarinyar ba..ko meyasa?
Wani 6ari na zuciyar ta ne ya bata amsa da fa'din.." Saboda ita 'din marainiya ce.."
" Tabbas hakane!
Ta tabbatarwa kanta.
" Mufee na marainiya ce..ni kuma uwa ce zan kuma zame mata uba da kowa data rasa a duniyan nan...".
kusan kowani lokaci alwashin da Zaitun ke ci kenan ko bata furta a fili ba takan ayyana cikin ranta ta kuma tabbatarwa ranta cewar tabbas zata iya.

Kwanan ta biyu cikin gidan bata samu matsala ta kowani fanni ba, babu wanda ya takura ta ko ya shiga rayuwar ta, babu wanda take hira da shi sai Mufee duk da yake dama ita ba gwanar surutu ba ce amma haka kawai sai taji zaman shirun ya ishe ta, bata da matsala wajen abinci sbd sau uku ukun nan kullun ake bata abinci Hajja Ladi ke wannan hidimar wanda ta tabbatar bisa umarnin Hajiyar gidan ne.

'Bangaren Mufee ma bata samu matsala da ita ba dan tana cin duk abinda ta bata yanzu ko da babu yawa, dan har ayanzun Mufee ba cin abincin kirki take ba, 'dan banzan za6e ne da yarinyar, kuma in abu bai mata ba bata ta6a cin sa shiyasa a cewar Zaitun har yanzu bata da kumari tana nan 'karama da ita amma matukar zata ga yarinyar cikin walwala da kuzari hankalin ta kwanciya yake ta mance da duk damuwar da take ciki, sam ita bata ta kanta ma.

Sai dai kuma tana jin bazata iya zaman gidan nan ba, bata son takura ko damuwa yanzu a rayuwar su bata son karin wata matsala makamanciyar wadda ta fito cikin ta kwanaki 'kalilan baya...aiki take so tayi burin ta taga ta fara tara ku'din mota dan hankalin ta ya fara komawa gida, burinta kafin cikar lokacin da ta 'debar musu na komawa ga ahalin nata ya zaman ace tana da isashshiyar ku'din motar da zata kaisu ba tare da wata gargada ba.

Duk da yake har cikin zuciyar ta taji ta yadda da matar da ta dauko tan amma ai tun ranar da ta kawo ta ta fita bata sake ganin ta ba balle tasan matsayin zaman ta tare da su.
Shiyasa wasi- wasi ya kasa barin zuciyar ta, ta riga ta yanke cikin ranta cewar barin gidan shine maslaha a gare ta da ma rayuwar ta.

Sai dai wani 6ari na zuciyar ta na jin shakka, wancan daren tsoron faruwar makamanciyar sa take, tana tsoron mummunar 'kaddarar da zata iya fa'da mata tunda ta jima da lura rayuwar ta cike take da 'kaddarori masu matukar yawa, amma duk da haka tana matukar so da 'kaunar mutuncin ta, tana kuma iya 'ko'karin ta wajen kare shi..a kullum fatan ta shine Allah ya bata kariya ta wannan fannin, ya basu ikon cinye dukkan jarabawar su batare da sun cutar da wata halitta tasa ba, ba kuma tare da sa6a wa umarnin sa ko keta haddin islama ta kowacce fanni ba.

Ko cikin dare bacci na yanke mata dalilin tunani da damuwar makomar ta da kuma kaddarar ta ta gaba, fatan ta kawai shine Allah ya sassauta mata koda wata kaddarace yasa komai yazo mata da sauqi..bacci 6arawo ne yayi gaba da ita batare da ta sani ba sakamakon 'karancin bacci da take fuskanta a kwanakin shiyasa kusan duk lokacin da ta samu natsuwa ta zauna shiru bacci ke kawo mata hari.

Duk launin idanun ta sun canza, har kuma a yanzun ramar ta na nan sai manyan idanuwan ta da suke farare tas, tsawon mintina da basu haura bakwai ba da baccin nata taji Mufee na kokarin shiga jikin ta dole ta bude idanu tana jin baccin cike a idanun ta, gyara kwanciyar yarinyar tayi cikin jikin ta ta rungume..." _Bacci cikin natsuwa 'yan mata na_ ...".
Ta ra'dawa Mufee cikin kunne a sanyaye tana sake rufe idanun ta dan baccin sosai take ji.

Da irin wannan lokacin kawai ta ke samu ta yi bacci wanda dududu baya wuce na awa 'daya baccin yake sakin ta gaba 'daya sai kuma dare in tayi sa'a ko kuma washegari da irin wannan lokacin..misalin karfe goma ne na safia zuwa sha daya dai ko sha biyu na rana zuwa bayan Azahar.
Kamar dai yau 'din daya kasance bayan azahar 'din ne.

Bata aikin komai, illa hidimar kanta da ta 'diyar ta da ta riga ta saba da su, sai muhallin su da a koda yaushe yake tsabtace bata ta6a barin aga datti ko min 'kalilan 'din sa a inda take zaune.
Wannan kuwa asalin dabi'ar ta ce tun ma tana gidan mahaifinta ta tsani datti.

Ko da ta tashi a baccin sallah taji ake 'kira wanda ta tabbatar na la'asar ne, ba 'karamin mamaki tayi ba ganin yau 'din baccin ta yayi nisa sosai.
Koda tayi sallar tunani ta fara na ko tabi shawarar Raleeya ne da tace ta ringa fita tana shan iska, sosai taji yau 'din dai bari ta gwada, hakan yasa tayi zaman jiran Mufeeda har ta tashi a baccin sannan ta watsa mata ruwa suka fito tana jikin ta.

A hankali suke tafiyar kamar bazata taka 'kasa ba, bata san meyasa take jin ragaggiyar fargaba cikin gidan nan ba sa6anin gidajen da ta zauna abaya, in ka 'dauke gidan Hajiya Talatu da tasan zaman ku'din hayar da ta biya tayi babu inda ta zauna babu fargaba sosai cikin ranta sai wannan gidan.
Tasan kuma bakomai bane face kamala, sakin fuska da karamcin da ta lura mamallakiyar gidan ke da shi.

Can ta samo su Raleeya zaune a babban Parlon gidan suna sauraran maimaicin labarai da ake yi 'karde hu'du na kowacce yammaci, har a yanzu babu wata sakin fuska da take samu daga Hajja Ladi sai dai ga Raleeya abin ba haka yake ba.

Dan haka barka da hutawa tai musu a jimlace sannan itama ta zauna 'diyar ta rungume da jikin ta.
Raleeya ce ta yi kokarin kar6ar Mufee amma ta noke sai ma sake rungume Zaitun da tayi.
'Yar dariya Raleeya tayi tana mata tsiyan kyiyuya da take har Mufee ta fara dariyan itama saboda wasan da Raleeya ke mata.

Ganin haka yasa dukkan su sakin fuskar su illah Hajja Ladi da ko kallo ma basu ishe ta ba.
Ji ma take da tana da iko da tada su a parlorn zata yi tace su koma inda suka fito amma tasan Ammi bata lamuntar abu irin hakan matukar taji labari kuma bazata kyaleta ba..bata ta6a ganin mutun mai karrama 'dan Adam irin baiwar Allahn nan Ammi ba.

Tuna hakan yasa ta ja karamar tsaki ta tashi a parlon ta bar su da Raleeya, sosai take jin tsanar Zaitun haka kawai har cikin zuciyar ta.

Kallon suka cigaba da yi ana ta bada kanun labarai sai dai da turanci ake labaran Zaitun ba fahimta take ba, amma jin sunan garin su ya fa'do cikin labaran yasa ta bada hankalin ta sosai har aka lula cikin labaran.

Bata iya fahimtar komai ba sai dai lura da Raleeya tayi ta bada hankali ga labaran yasa take 'dan tofa nata itama, bawai dan tana tunanin Zaitun 'din bata fahimta ba ne a a kawai dai dan 'karawa zaman shirun nasu armashi.

Sosai jikin Zaitun yayi sanyi kur ta kurawa Tv 'din idanu..har Raleeya na iya hango hoton Tvn cikin idanun ta saboda yadda suka cika taf da ruwan da ta hana su sau'ka, sai walwali da suka 'karawa idanun.

Duk 'kwa'kwar ka bazaka ta6a fahimtar inda hankali da tunanin ta ya dosa ba, amma ita ka'dai tasan halin da ta shiga a wannan zaman.

Sosai take jin gudun jinin ta na 'kara sauri akan nada, haka ma bugun zuciyar ta, tayi 'ko'karin ri'ke hawayen ta gudun kar Raleeya ta gani amma bata san tuntuni sau'ka suke ba sai da taji Raleeya na fa'din..." Subhanallah...Zaitun kuka kuma...?"
Firgigi tayi tana duban Raleeya tamkar wacce zata gano wani abu daya danganci garin nasu akan fuskar ta.
" ...Da tausayi kam ni kaina naji babu dadi amma ya zamu yi? Addu'a kawai zamu cigaba da musu Allah ya saka musu ya bi musu hakkin su, wa'danda aka kwasan kuma Allah ya ku6utar da su...yankin Borno ai suna cikin tashin hankali sosai, dole a tausaya musu".
Cewar Raleeya cikin raunin murya tana dauke 'yar 'kwallar da ya sakko mata da yatsan ta.
_(Allah Ubangiji ka 'kara bada kariya da tsaron ka duk jihohin mu da ke fuskantar tashin hankali da barazanar 'yan ta'adda Allah ka kare mana dukkanin al'ummar mu..Ameeen)_
Kawar da idanu Zaitun tayi zuwa wani 6arin.
" Kenan dagaske abinda take tunanin ya farun shi ya faru...?"
" Yah Allah...Ya rabbil Izzati, ya Zul arshil majeed Yah Raheemu Yah Rahman ka kare min mahaifa na, 'yan uwana da ma dukkan musulmi..."
Tunanin ta tsayawa yayi jin cigaba da maganar da Raleeya tayi...." Haka ma fa kwanaki a kan hanya aka ringa yiwa mutane kisan gilla, wlh wai yankan rago an zubda jinin musulmi sosai ko labari bana son inji anayi saboda yadda abin ya munana, shiyasa yanzu da yawa ke fargabar tunkarar hanyar Borno abun bb dadi sam..."
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.."
Ta maimaita yakai sau uku.
Tana so ta bu'di baki ta tambayi Raleeya yaushe akayi hakan amma bakin ta duk taji ya mata nauyi.
Ido kawai ta waro kan fuskar Raleeya.
Chapter 50 · 0% Book details