← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 218

Sashe 129

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bata ce da shi 'kala ba illa" Hmm" da tace kawai ta mi'ke, tea ta ha'do masa mai zafi mai kuma kauri ta kawo masa.
Bazai iya ri'kewa da hannun daman san ba hakan yasa ta ri'ke a hannun ta tana bashi abaki ka'dan- ka'dan yake sha ko rabin sa ma bai sha ba yace ya isa, duk yadda tso ya 'kara Rayyan 'ki yayi.

Ammi sai tayi murmushi...dama tasan halin sa idan bai da lafiya sai a hankali...koma mata yake tamkar wani 'dan goye.

Yana murza hannun sa mai ciwon da 'daya hannu mai lpyr yace
" Ammi yarinyar nan..wai meyasa take yawan shigowa nan ne..ban so ni...i need privacy bana san ana yawan takura ni.."
" Wace wai...kake magana akai ne..?"
Ammi ta tambaye shi tana ajiye mug 'din dake hannun ta duk da ta fahimci wa yake nufi amma bata so ta nuna masa kai tsaye.

" Wai Amrah kake nufi..?"
" a a Ammi..wancan yarinyar...".
" Wai Zaitoon..?"
Ammi ta tambaye shi tana mai 'ko'karin saka idanun ta cikin nasa.
Da kai ya amsa ta yana kawar da kansa gefe tamkar yasan mai Ammi ke da niyyar yi.
" Toh in dai wannan ce ai a halin yanzu baka da privacyn da ya zarta ta..."
Ta bashi amsa cikin nuna halin ko in kula da maganar.
Kallon sa ya dawo da shi gareta Ammi tayi saurin jinjina masa kai domin tabbatarwa.

Sannan ta 'kara da fa'din..." Ina nufin a halin yanzu Zaitoon mata take agare ka, an kuma aura maka ita ne sbd ita ka'dai na yadda ta kula min da kai, ita ka'dai zuciya ta ta yadda in barwa amanar ka na kuma yabawa 'ko'karin ta matuka...domin kyautatawar da tayi maka a lokacin da baka da lfy kake kwance abin a yaba mata ne..."

Tun bata kai ga rufe baki ba ya zaro idanu yana duban Ammi.

Kai ta sake jinjina masa sannan ta cigaba da fa'din" Burina kaima ka 'kauna ce ta ka kula da ita, buri na zaman ka tare da ita ya kasance na har abada ne, hakan ka'dai ne zai baka damar saka mata abinda tayi mk domin a yanzu ko kace zaka sallame ta ni bazan goyi bayan haka ba, idan kace ku'di kuma ba yadda ita zata yi ta kar6a ba..."
" Ammi ko bazata kar6i kudi ba a dai nemi wata hanyar amma banda batun aure Pls.."

" Me kk nufi wai Muhammad? kana ga kamar zanyi maka za6in da zai cutar da kai ne, ko kuwa kana gani kamar zan ha'de baki da ita in cuce ka ne...?"

Idanu ya lumshe bai kalli Ammi ba bai kuma bata amsar komai ba, bai ma san ta yaya Ammin zata fahimce shi ba..hannu ya sa ya ringa shafa goshin sa da yatsun sa biyu.

Jin Ammi ta saki 'karamin tsaki ne ya sanya shi saurin bu'de idanu ya kalle ta a tsaye ya ganta ya kuma fahimci shirin barin 'dakin take sai yy saurin fadin" Ammi dan Allah ki..."
Hannu ta 'daga masa sannan tace" Kar kace min komai..daga tashin ka bazaka sani gaba da abin 6acin rai ba..kai baka da tunani ne hala...?"
Shiru yayi yana jin babu dadi cikin ransa.
Ammi ruwa ta kawo masa ajiye sannan ta matsar masa da magungunan sa tace" kasha magani.

Daga haka ta fice ta bar masa dakin Rayyan ya bita da idanu.
Ya rasa wani irin hukunci ne wannan.
Wai ma shin wani irin hali ya shiga ne da har za'a 'daura masa aure batare da ya sani ba..ina Amrah da ita bazata kula da shi ba har sai an 'daura masa aure da yarinyar nan.
Kimanin mintina sha biyar ya 6ata kafin ya tashi ya 6alle marfin ruwan sannan ya sha magungunan sa yana sha yana jinjina tsadar su.
Gefe guda kuma damuwar dake cikin zuciyar sa daban.

Sosai jikin sa yayi sanyi 'kalau..shi mamakin Ammin tasa ma yake yi..ita Ammi saurin yadda ne da ita baya ga haka me yasa zata yi haka? yarinyar nan fa haka kawai muka ganta, babu wanda yasan dangin ta yan uwan ta balle asan daga inda ta fito talk more of asalin hallayar ta, wace ita, duk babu wanda ya sani, abu mafi muni da ba ze taba barin shi yin zaman aure da ita bama shine rashin sanin hanyar da tabi har rikon 'diyar sa ya dawo hannun ta.

Sai dai ya riga ya 'dauri aniyar bincikan ta tunda jimawa.

Sosai yake da bukatar magantuwa da Anty Madeena amma yafi so abin ya kasance iya tsakanin su ne.

Ajiyar zuciya ya sauqe mai karfi..wai Zaitoon yanzu matar sa ce kenan..?
Ya tambayi kansa, ya sani 6angaren hallaya kam ta ciri tuta domin da kansa ma ya yadda da yarinyar 100%..yasan bata da wani mugun hali da za'a 'kita sbd shi...amma ai shi baya da ra'ayin aure ma kwata kwata ma a rayuwar sa balle ace auren ta.

Salmerh😘
[30/11/2022, 2:22 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...75*

.......Baya ya koma ya kwantar da bayan sa jikin gado yana sake zurfafa tunani, shaf sai ya mance da cewar 6oye kansa yake, ya kuma manta cewar da Ammi ta fita bai kuma rufe 'kofar ba, bazata kawai yaji an turo 'kofar gami da sallama ciki- ciki.

Da sauri ya 'dago kansa gami da bu'de idanun, duk da yake tun kafin ya 'dago idanun ya fahimci wanene, dirowar bazata da yai masan shiyasa shi 'dagowa a gaggauce, nan kuwa idanun sa sukayi arba da babban aboki kuma aminin sa wato Dr Fawwaz, 'dan 6ata rai yayi yana komawa dan daidaita kwanciyar sa.

Yayin da Dr Fawwaz ya waro idanu sosai yana kallon sa gami da nuna shi da 'dan yatsa ya ma rasa kalmar da zai furta.
Da 'kyar bakin sa ya iya tattaro abin fadi har ya furta sunan" Rayyan".
" What..?
Ya tambaya a dake batare da ya dube shi ba.
" ....Wai kaine nake gani ahaka ko kuwa idanu na ke min 'karya....?"
'Karamin tsaki Rayyan yaja na neman magana ya kuma watsa masa harara yana mai juya mai baya yace..." A a ka manta...kanka kake gani haka ba Rayyan ba....!"
" Yah Subhanallah..."
Fawwaz yace out of excitement...ai da gudu ya tafi gare shi ya rungume shi sosai yana sakin hamdala gami da daria bayyananniya....

Ture shi Rayyan ya fara da hannun sa 'daya mai lafiyar yana fa'din" Kai...kai..wai miye haka ne, 'karasar dani kake so kayi kome...?"
Fawwaz ko ta kansa bai bi ba balle ya ya fahimci abinda yk nufi, farin cikin da ke cin sa ya rinjaye komai a lkcm.

Sai da ya gama bayyana farin cikin sa gami da godiyar sa ga ubangiji kafin ya fara zolayar Rayyan wai shegen kaya wannan irin nisan tafiyar da kayi duk kabi ka sa hankulan mu sun tashi fa, gaskia ka shirya sai mun ci tarar ka"
" Wani karon in zan tafi ai tare zamu kwantar da hankalin ka...!"
Hannaye Fawwaz ya 'daga da sauri yana fa'din " A a...a a bawan Allah rufa min asiri ban gama ha'de guzuri na ba tukunna...".
" Matsorracin banza..."
Cewar Rayyan...yana 'yar daria,
Fawwaz yace" naji dai...ai da gaskia ta,...Ya jikin naka toh, yau dai an hutar da bayin Allah daga damuwar zucia da ta zahiri..."

'Ko'karin zama Rayyan ya yayi yana bawa Fawwaz umarnin rufo 'kofa da hannun sa yk fa'din" Ni kuma sai da na 'kwammaci ban ma tashin ba sbd damuwar da na tarar...".
" Damuwa kuma...kamar wace iri..."
Cewar Fawwaz da ke dawowa daga rufe kofar idanun sa akan Rayyan.

" Kassarani da kuke son yi mana..dan na san komai gudunmawar ka ya faru...".
'Yar daria Faweaz yayi gano abinda yake nufi yana zama gefen sa yace" Kanka ake ji kuma yanzu..".

Nan Rayyan yai masa takaitaccen bayani akan yadda yake jin hannun nasa.

Atare suka yi aikin duba hannun atare da taimakon junan su, nan kuwa gano inda matsalar take sun kuma fahimci mafita 'daya gare su in dai ana so hannun ya dawo daidai kamar da toh sai an sake yi masa aikin gyara karayar dake a hannun.
Rayyan yace sam shi dai ba yanzu ba tukunna, ya kuma ro'ki Fawwaz akan dan Allah ko Ammi ta bu'kaci su koma asbiti yasan 'karyar da zai mata ya waske, yasan da zarar anje asbiti sai an ri'ke shi shi kuma bai son zaman can dai- dai da ta yini guda ne wai da sunan jinya.

Sun sha hira sosai da Fawwaz kafin suka rabu kowa zuciyar sa na masa da'di da ganin 'dan uwan sa..a bakin Fawwaz ma yaji wasu abubuwan da shi bai san da zaman su ba, kamar tsawon lkcn zaman da yayi a kwance, yanayin jinyar sa, auren su da aka 'daura da Zaitoon a masallacin Uthman bn Affan da ke nan cikin unguwar ta su da irin hidimar da ta yi ta faman yi masa..da dai sauran abubuwa.

Sosai ya sake tsunduma cikin yanayin zurfafa tunani.
Ko yaso hana kansa tunani abin gagarar sa yake, a yanzu babban damuwar sa 'diyar sa ne, yadda zai bayyana wanzuwar ta ga kowa shine damuwar sa, ko ciwon hannun sa bai dame sa kamar yadda lamarin Mufeeda ke damun sa ba...burin sa a kullum shine yaga ya 'yantar da 'diyar sa ta dawo 'diyar sa a zahiri, ta kuma rayu tamkar ko wani 'da a gidan mahaifin sa, yana so ya gatanta ta ya 'daga darajar ta fin wanda akayi mata abaya.

Burin sa kenan a halin yanzu sai dai kafin hakan yasan dole ne sai ya tuntu6i Zaitoon yasan ta yadda akayi komai ya faru.
Tuno kalmar zargin da yai ta jifan ta da shi abaya..yasashi jin babu dadi sosai cikin ransa, hakika bata cancanci wannan kalmar daga gareshi ba... _Astaghfirullah_ ...
Ya furta saman la66an sa.

Koda ya tuno sunan da yasha jifan Mufee da shi fili da zuciyar sa kuwa idanu yayi saurin rintsewa yana gyara kwanciyar sa.
Chapter 129 · 0% Book details