← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 167 OF 218

Sashe 167

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanda ya yadda da ni ya yadda ni wanda kuwa akasin hakan yake a zuciyar sa shima bazan tuhume shi game da hukuncin da zuciyar sa ta riga ta yanke masa domin akwai hujja ta zahiri yadda hujjar ta tafiyu ne kawai bambanci.

Fatana kawai shine Allah ya bamu dacewa.

Na kan yawaita tuno kalaman Dije agare ni na 'karshe, ina matukar kaunar Dije domin itan aminiya ta ce ta gaske,
Mun rayu da Dije ne tamkar 'yan uwan jini, nasan ba dan bin umarni ba Dije bazata ta6a juya min baya ba.

Bazan manta ba kwanaki ta aikowa da Aishatu hula a 6oye kuma na tabbata babu wanda ya sani, na kuma matukar jin dadi da wannan sako na Dije domin hakan shi ya sake alamta min da cewa tana nan tare da ni, ganin juna ne dai ya haramta gare mu amma muna nan cikin zu'katan juna.

Ina yawan kuka idan na tuna lkcn da Nadia ta barni, idan na zauna tariyo tun farkon ha'duwar mu zuwa 'karshen rabuwar mu kuwa da shashshe'kan kuka nake 'karasar da tunanin, na rasa wannan wace iriyar 'kaddara ce tamkar a shirin drama.

Gashi abin tamkar danni ya faru duk yazo ya cushe min ni ka'dai, wanda ya tafi kam ya riga ya tafi ai sai dai addu'a ta rage tsakanin mu, kuma har yau 'din nan bana gajia da yiwa Nadia shi cikin kowacce sallah ta.

****
Kwanaki biyar kacal da tafiyar Yayana kasuwancin sa mijin Inna ta ya dawo daga doguwar tafiyar da yayi, dama yaso yazo kafin sallah amma Allah bai yi ba sai yanzun, tun da yadawo gidan babu fara'a a fuskar sa domin ko gaisuwar da nai masa bai amsa min ba...haka ma ta Innata.

Ko da ya fita ya dawo kuwa bansan me yaji ko ince aka sanar da shi ba amma cikin hassala ya fara masifa 'karshe ya kore ni daga gidan sa.

Yace sam shima gidan sa babu makwancin shege wanda ya haife ni ma ya kasa zama da ni a gidan sa sai shi ne da aka rainawa wayo za'a zo a tare masa agida..sam bazai yadda ba, yace wanda muka yi da bai sani bama bai yafe ba...yace shi ba 'dan iska bane da zai tafi yawon nema ana nan ana ciyar da karuwai daga cikin dukiyar sa..badan wani abu bama kotu zai kaimu sai an biya sa, ran Innata ya 6aci sosai amma ya zam min dole na bar masa gidan sa.

Ni kaina hankali na tashe nake jin sa amma ganin yanayin Innata ya sa dole na danne nawa na kwantar mata da hankali...sannan na 'dora da fa'din zan koma wurin Abban mu in sake bashi ha'kuri ko zai ha'kura duk da nasan mawuyaci ne ma ya ha'kuran, ni da aka haramta min ko kallon 'kofar gidan toj da wani 'kafafun kuma zan iya sa kaina a cikin sa...?

Haka na tattare kayana kaf cikin jakar da Inna ta ta bani zucia ta fal da tunanin inda zan saka rayuwa ta...Allah ka dube ni...ka kawo min mafita mai 'dorewa.

dama kayan nawa ba wasu masu yawa bane dan haka basu wani bani wahalar 'dauka ba, 'karamin jakan Nadia dake wuri na ma ban barshi ba na sanya shi can 'kasan kayan nawa...goye Mufeedah nayi a bayana na lullu6e ta da hijabin dake kaina, cikin ko wani da'ki'ka 'kaunar ta nake ji yana sake ratsa ni har cikin jini na...tausayin ta nake ji sosai sbd maraicin ta, sannan kaunar da nake yi mata na tabbata sbd an haife ta kan idanu na ne, nasani a yanzu Mufeeda bata da wani dangi sama da ni toh idan na guje ta hanun wa zata fa'da?.
Ni har ita a yanzu Allah kadai ne gatan mu.

Dama a rayuwa dole sai an ha'kura da wasu abubuwan sannan ake samun daidaituwar wasu...fatana a kullun Allah ya bamu dacewa dunia da kiyama.

Ko hauka nake bazan ta6a iya taka 'kafata gidan Abbah na ba dan nasan halin sa da kafiya..hakan yasa na nufi gidan Yayana da tunanin zan sami muhalli a can tunda nasan tun farko duk cikin yaran Iyami shine yafi 'kauna ta, ko tafiyar nan da zaiyi ma sai da yaje ya bani ku'di yace in ri'ke a hannu na kafin ya dawo.

Naso naki amsa sbd hidimar da yake yi akan mu ni da Mufeeda bazai fadu ba amma ya nuna min 6acin ran sa...hakan yasa dole na ansa.

Sam banyi mamakin irin tijjarar da Azeemah tayi min tayi min a wannan ranar ba, dan nasan tun farko dama ba shiri muke yi da ita ba balle da batun yarinyar nan ya bayyana sune kan gaba wurin nuna min kyara da tsana.

Buga kirji tayi tace min babu wanda ya isa ya zauna mata da 'dan shege cikin gida ganin yanda take hargagi take 'ko'kari tara min jama'ah yasa hawayen da tuntuni nake dannewa suka fara bulbulowa.

Gyara goyo na nayi da kyau sannan na 'dauki jaka ta ina hawaye na fita daga gidan ko ganin gabana da kyau bana yi..sam a lokacin ban yi tunanin sake zuwa wurin kowa ba dan nasan bakowa ne zai kar6e ni da wannan 'kaddarar ba domin ko wurin su Yaaganan mu naje nasan dole sai an samu bambancin ra'ayi ta iya yiyuwa ita zaman ta na yar uwa ta ta kar6e ni amma 6angaren mijin ta kuwa bani da tabbaci babu mmk shima ya min kwatankwacin na mijin Inna ta ko ma fin haka..Baffa Liman kuwa dama inada labarin yafi kowa 'daukan zafi kan batun, kusan ra'ayin su 'daya ne da Iyami tamkar a takadda guda suka karanta abinda ke cikin zu'katan su.

Kausasan kalamai naji su babu iyaka, anci min zarafi sau ba adadi an kuma muzanta ni sau da dama amma ban ta6a jin sun cire ni cikin natsuwa ta irin na yau ka'dai da nake neman rasa inda zan tsoma rayuwa ta ba.

Ban kuma mance tsauraran kalaman Abbah akaina ba, Abbah na Allah ya isa ya min ga koda kallon gidan sa ne balle kusanta kaina ga dukkan wanda ya kasance jinin sa ne..badan komai ba sai dan kawai na shafi yarinyar, toh ya zanyi? Bani da ikon mayar da 'kaddara ta baya da wlh na mayar da ita ta yadda bazan je jejin bama balle har na hadu da Nadia balle akai ga batun Mufeeda.

Amma Abbah ya kasa fahimta ta..kuskure ne da ya riga ya faru, da ace kafin ha'duwa ta da Nadia Abbah ya fa'di hakan da ko hauka nake bazan ta6a ha'da jiki na da ita ba, amma meyasa sai da abinda ya faru ya riga ya faru Abban zai gina doguwar katanga tsakanin mu, bayan yasan ban isa na maida 'kaddara ta baya ba, meyasa zai ce hatta ni baya da bu'kata bayan ni 'din jinin sa ce.. ina Abban mu yake so naje a wannan duniyar da ke da matu'kar girma da fa'di.

Muurmushi mai ciwo nayi..tuno matsayin Abbah na a wuri na, mahaifi na yake, kuma abin alfahari na ne shi, hawaye ne masu zafi ya 6ul6ulo min tare da tuno Inna ta...inna ta bata ta6a nuna min kyara ko tsangwama ba akan yarinyar nan, domin da idanun ta taga gawar mahaifiyar yarinyar, tun a lokacin taso mu bayar da ita amma nace a a dan ban manta batun uwar Mufeedah ba da tace min ta iya yiyuwa ko yarinyar ta shiga hannun hukuma 'kila baza'a sada ta da asalin dangin ta ba, babu mamaki ta fa'da mugun hannu ko kuma ta rayu cikin gidan marayu alhali nasan tana da asali ni kaina bazan so faruwar hakan ba tunda nasan tana da dangin ta can wani wuri masu matu'kar so da 'kaunar ta tun kafin a haife ta.

Haka kawai Nadia taji ta yadda da ni, sam bata ji 'dar ba wurin barmin amanar 'diyar ta ba, duk kuwa da cewa bata san ko ni 'din wacece ba, to ni kuma me yasa bazan kar6a mata ba, sam bazan iya bari a a tozarta 'diyar ta ba tunda hakan mahaifiyar ta ta guje mata tun farko...da bayan hannu na goge hawaye na ina mai sunkuyar da kaina tare da gyara ri'kon da nayiwa jakar kayan mu.
Daidai da motsin da mufeedah tayi a baya na, 'dayan hannu na na kai 'kar'kashin ta ina jijjiga ta..cikin raina" Na 'dauka mata al'kawarin kulawa da ita, nayi al'kawarin sadaukar da duk farin ciki na saboda ita...daga yanzu zan 'dauka ta ne tamkar bani da kowa a duniyan nan sai ita, itace jina da gani na, itace sanyin idanu na..itace tsagin jiki na kuma jigo na...Hamma na ka yafe min ban yi hakan saboda ka kasa ba, ban yi hakan saboda farin cikin kaina ba face dan farin cikin wannan baiwar Allah marainiya da ke bayana, zan jure komai daga yanzun nan, zan iya komai da 'karfi na saboda kawai inga na gyara rayuwar Aishatu na.

A yanzu na gama yadda cewa in aka 'dauke mahaifa na bani da wani masoyi sama da Yayana...Bazan ta6a gajia da maimaita cewawa gami da jinjinawa Yah Bukar ba, domin shine madadin uwata a gidan mahaifi na, shine malami na, shine yayana kuma garkuwa ta...shi ya koya min dukkan add'uo'in da na iya saboda in ringa bawa kaina kariya da su, ya min al'kawarin nema min maganin matsalar da ke damu na tun kafin faruwar wannan lamarin kuma Alhamdulillah burin sa ya cika...duk safiyar da yazo ya tarar da ni ina kuka ya kan zauna ya saurari damuwa ta zai ji matsala ta kuma ya fahimce ni...daga nan sai ya jero min kalaman kwantar da hankali ya kuma 'karamin 'kwarin gwiwar cewa insha Allahu watarana zan daina, matu'kar zan ri'ki tsoron Allah da ta'kawa da gaskiya, in kiyaye dokokin sa, in kuma ringa yin ibadu na yadda ya kamata da kanshi zai kawo min sau'ki.. Hamma na shiya koya min addu'ar safiya da maraice...ya kuma koya min wacce kafin nayi bacci zanyi, shiga ban 'daki da fitowa da kuma idan zan sanya tufafi na...sai gashi a yau kwatsam 'kaddara mai girma tana neman raba ni da kai jigo na, ina 'kaunar ka Hamma na Insha Allahu watarana zan dawo, zan dawo sbd kai ka'dai da mahaifiya ta.
Chapter 167 · 0% Book details