← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 218

Sashe 47

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A bakin gate ya tarar da Hafeez tare da gate man yayin da sauran securities 'din Alhajin ke gefe suna sha'anin su.
Bai ce da Hafeez komai ba shima da ganin sa kawai ya taso suka fice yana wa gate man 'din sallama..daga haka suka bar gidan ma gaba 'daya inda suka bar 'Dan Maliki cike da zullumi da nadama matsananciya, sosai jikin sa yayi sanyi, raunin da bai ta6a fuskanta bace ta ke shigan sa a wannan lokaci, ji yake tamkar ya sulale ya 'dora hannu aka yayi ta ihun ta6argazar da yayi ta aikatawa, abu 'daya da a kullun yake gode Allah akai shine da bai tsaya duban halayyar sa ba ya bashi yaro nagartacce mai zuciya irin Adam.
Babu ta yadda halayyar su tayi kama, shi'din tamkar kishiyar halayyar sa ya kwaso, babban abinda ya birge shi ga Adam 'din shine yadda koka'dan dukiyar sa basu dameshi ba, burin sa kawai ya tara nashi da gumin sa.

Daga gidan Maliki basu zame ko'ina ba sai gidan su Adam Shaheed nan ma direct 6angaren sa.
Hafeez ne yasa hannu ya bu'de 'dakin da suka shiga kuma ya maida ya rufe harda saka makulli.

Adam kam kan kujera ya zauna yana dafe goshin sa, kadan kadan yake jin kwanciyar hankali na shigan sa, sai dai yasan mawuyaci ne ya samu kwanciyar hankalin gaba 'daya, wancan abin da ya gani ya kuma yi kokarin dannewa can kasan zuciyar sa bazai ta6a barin sa ya samu cikakken farin ciki ba.
" Meyasa ne?
" Why Alhaji?
" Da wannan shekarun?
" Kuma yaran cikin ka..?
Hafeez ne da ya taho kanshi ya tsaya ya dakatar masa da tunanin da fadin..." kasan me nake ji kuwa...?"
Dago idanu yayi gami da bude su akan Hafeez 'din tare da lumshewa ya kuma budewa nan take alamun ina jin ka.
Hafeez da ya san ma'anar hakan sai cigaba yayi da fa'din..." Ji nake tamkar in ta dukan ka har sai ka suma"!
Hafeez ya furta cike da jin haushi.
Waro idanun yayi kan fuskar Hafeez da alamun tambaya amma bakin sa ya gaza furta wata kalma.
"...ka bani haushi sosai, meyasa ka kasa tauna kalaman ka, ka kasa sassauta furuci da sautin muryar ka gare shi? Meyasa zaka sashi agaba kana furta duk abinda yazo bakin ka? Kaman ta mahaifi yake agare ka ne, ka manta cewar shine aljannar ka.."
Ran Hafeez dagaske ya 6aci sosai da yatsa ya nuna Adam sannan ya cigaba da fadin" bari in fada maka wani abu Adam wallahi duk lalacewar masa tafi kashin shanu daraja, duk tsiya mahaifin ka ne, duk lalacewa da mugun halin sa mahaifi yake a wajen ka, nasan kuma kasan girma da darajar da iyaye suke da shi a wajen mu iyaye iyaye ne hara abada ba'a ta6a canzawa tuwo suna, kayi maza ka nemi yafiyan sa kafin lokaci ya kure maka ina fada maka".
Ya karasar da daga murya.

Adam Maida idanun sa yayi ya rufe sannan ya bude su kan fuskar Hafeez ganin yadda ya dauki zafi ne ya sashi bu'dan baki da 'kyar ya fara magana..." wai duk wannan zafin ran akan maganar nan ne?
Hafeez harara ya banka masa batare da ya furta komai ba.
murmushin gefen baki Adam yayi sannan cikin sigar lallashi yace" ka kwantar hankalin ka zanyi duk abinda kace amma ba yanzu ba, for now ka barshi nasan ban kyauta ba amma dole tasa nayi hakan, ya rayu ne kaf din rayuwar sa babu mai fada masa gaskia a yanzu kuma da nake da damar hakan bai kamata in yi wasa da wannan damar ba..."
Shiru yayi na dan wani lokaci yana jin tukuki cikin ransa amma ya zai yi ya zam masa dole ne ya nema masa rufin asiri.
Sai da ya kawar da kai gefe tamkar bazai yi magana ba sannan a hankali cike da rauni ya 'kira sunan Hafeez.
Duban sa yayi gami da sauraron abinda yake son fada masa.
" Hafeez nasan kai amini kake a wajena dan tabbas ka wuce aboki musamman a yanzu da muka yi tarayya wajen ganin abu guda, Hafeez ina rokon dan Allah abinda muka gani gidan Alhaji..."
Bai ma jira ya karasa ba ya tare shi da fadin" kar ka damu kasa a ranka tamkar batare da ni kaje gidan ba, I promise u...u won't regrets trusting me..".

Ajiyar zuciya Adam ya sauke ko ba komai matakin nutsuwar da ya 'dan samu ta kara hauhawa.
Ya yadda da Hafeez kwatankwacin yardar da ya yiwa kansa, ya zame masa dole ne ya kare mutunci da martabar 'Dan Malikin duk da yasan ba lallai ne ya iya hakan ba, duba da cewar wanda ya gani ne kadai ya sani bai kuma san farkon lamarin ba balle karshen, baya shakka kan Hafeez dan ya masa farin sani, yasan shi din mutun ne mai kwatantata rikon amana iya iyawar sa..yasan indai ta wannan bangaren ne bazai samu matsala da Hafeez ba koda kuwa bai kara tada zancen ba amma da yake mutun akace shiyasa ya sake jaddadawa gami da rokon sa ya rufa wa mahaifin nasa asiri yadda dunia take ganin sa matsayin mutum mai mutunci da kyautatawa wanda hakan yasa jama'a kaunar sa lets it be....

*****
Tun daga wancan rana Jibrin 'Dan Maliki ya fara kokarin ganin ya gyara mu'amalar sa da ubangijin sa, ya kuma fara gyara dukkan wata 6araka dake cikin rayuwar sa gaba 'daya.

'Bangaren Adam kuwa tun da ya bar gidan Alhajin suka yi.magana da Hafeez bai sake tattauna al'amarin da kowa ba hatta da Hafeez 'din kuwa, sai ma killace kansa da yayi ya daina fita ko'ina, wannan karon ma jinyar zuciyar sa yake faman yi a 6oye batare da Hajiya Talatu ta sani ba.

Hafeez ne kamar yadda yayi alwashi, shi ya labarta mata komai, ba 'karamin mamaki kuwa tayi ba ganin shi Adam 'din bai sanar da ita ba, hatta da shi kansa 'Dan Malikin bai ce da ita komai game da ha'duwar su da Adam Shaheed 'din ba.

Tayi farin ciki sosai da fara wanzuwar shiri tsakanin Adam 'din da mahaifin sa.
Ita kanta bazata so ganin Adam na fama da kewar mahaifin nasa ba bacin yana nan a raye.
Sai dai itama bata ce da shi komai ba kawai ta zuba masa idanu dan ganin gudun ruwan sa.

Shi da kansa ganin killace kan bazai masa ba kawai yasa ya sake harha'da 'yan ku'da'den sa ya tada wajen sana'ar tasa da zummar yin fito na fito wannan karon da duk wanda ya sake yun'kurin hana shi rawan gaban hantsi.

Sosai ya sake ja baya da komai da ya shafi mahaifin nasa, hatta Hajiyar sa ma yanzu ba sosai suke samun zama tare ba, 'kunci ya yiwa zuciyar sa yawa, sau da dama ya kanji tamkar Jibrin 'Dan Malikin badluck yk ga rayuwar sa sai dai baya barin wannan tunanin yin tasiri a zuciyar sa, dan yasan koma ya yake dole mahaifin sane, koma me ya zama a duniyan nan dole ne ya kira shi da suna mahaifi, kuma yana 'kaunar sa bawai baya yi ba kawai rashin sha'kuwa da fahimta ne tsakanin su, in ya tuna hakan ma da wuri yake istighfari ya kawar da batun a ransa, yana kuma 'ko'karin yi musu addu'a shi har da mahaifiyar sa kowa da tashi kalar addu'ar...yana kuma fatan Allah ya bayyana masa Zaitun cikin kowacce sallar sa dan ita ka'dai ce macen da zuciyar sa ke tsananin muradi a kaf fa'din duniyar nan.

Tsawon sati uku bai sake ji daga 'Dan Malikin ba, yayin da shirin sa na wajen sana'ar sa duk ya kammala har ma ya fara kasuwancin sa na Bunburutu, sai dai abin sai a hankali jarin bai kai wanda ya karye abaya karfi ba a hakan ma sai da Hajiya Talatu ta saka masa hannu kafin ya daidaita.

Hankalin sa ya fara kwanciya damuwar sa ta fara raguwa yayin da 'kuncin dake zuciyar sa yake sulalewa a hankali, sosai yake jajircewa wajen tabbatarwa zuciyar sa cewa shi'din namiji ne, baya ga haka da tuni ya kwanta jinya a asbiti...amma Alhamdulillah duk wani nawi da yake ji a 'kirjin sa yanzu da sassauci sosai sai dai abinda ba'a rasa ba.

'Bangaren 'Dan Maliki ma yana ta 'ko'karin shirin sa a 6oye batare da shi Adam ya sani ba wanda yana yin komai ne da taimakon Hafeez daya fahimci amintacce ne ga Adam Shaheed 'din.

Ashe duk ba wannan ne mugun ji da gani da zai kuma yi ga mahaifin nasa ba...kwatsam 'karar su Zaitun a kotu ta bayyana da bai ta6a zaton sake ganin ta cikin sauki haka nan ba, yana farin ciki da murnar ganin Zaitun yaje kotu da zummar ganawa da ita, domin ko kowa bai yadda ba shi dai yana da ya'kini 'kakkarfa cewa Zaitun bazata aikata abinda ake tuhumar ta dashi ba, yaushe ma tabar shi, yaushe ma ta rabu da shi da har za'a ce ta fa'da irin harkan nan sam bai ji ya yadda da mummunan zargin da ake mata ba.

Zaitun batada burin tara dukiya, kudi sam basa gaban ta, yasan halin ta sarai burin ta a kullun Mufeeda ne, burin ta ta samawa yarinyar farin ciki, yasan mutun me 'karancin shekaru irin ta me kuma irin wancan burin mawuyaci ne ta sanya rayuwar ta cikin ha'dari saboda son dukia kawai, sosai ya ci burin sake magantuwa da mahaifin sa kan Zaitun 'din dan yasan yana da yadda zai yi kotu ta wanke ta.
Kwatsam sai ga wani tashin hankalin kuma ya bayyana gareshi jin sunan mahaifin na sa ya fito cikin manyan masu 'daukar nawin laifiin a bazata.

Tuni raunin sa ya bayyana 'karara, taya zuciyar sa zai iya 'daukan duk wannan nauyin? mutane biyu ne masu matukar muhimmanci da daraja a zuciyar sa sama da kowa, amma baya da ikon taimaka musu ta ko'ina, bashi da dama, banda nawi babu abinda zuciyar sa ya karu da shi...nawin da yake farin ciki da sulelalewar sa daga kirjin sa sai gashi tashin farko yayi dawowar lokaci guda tamkar saukar aradu.
Chapter 47 · 0% Book details