Sashe 7
Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuwa yanzun Mufeeda nada watanni hudu cif ne da haihuwa tuni ma tafara koyon zama haka tsab ta gama gane Zaituna duk da bata kiyuya amma kaunar da take nunawa ga Zaitun ta musamman ce...kuma a yanzun ne Zaitun ta fara shawarar canza mata abinci a karo na uku.
Dan bayan Madara da ta fara bata Maman Abdul ce ta fara bata shawaran ta hada mata da ceralac daga lokacin da ta cika watanni biyu zuwa yanzun da take da wata hudu.
A yanzun kuwa tayi tunanin fara bata kila shima zai taimaka wa yarinyar, dan har ga Allah yadda taga yarinyar tata 'yar fiyot babu girman jiki abin baya mata dadi..shiyasa ta dage take aiki tukuru dan ganin ta kula da ita sosai amma duk kokarin ta a kullun gani take tamkar ta gaza.
😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'Yata ce)*
*Salmerh MD*
🅿️...5
....Adam shi ya fara koyawa Mufee kiran sa da Daddy dan acewar sa da izinin Allah karkashin inuwar gidan sa Mufeeda zata taso shiyasa gwamma ta saba tun yanzu.
Ya jima da fallasawa Zaitun asirin zuciyar sa sai dai har yau din nan bai samu gamsashshiyar amsa daga wurin ta ba, yayin da Zaitun ke tsananin mamakin Adam, kokadan bata ga dacewar su ba, Adam kyakykyawan matashi ne 'dan gayu ga ilimi ta kowani fanni yana da shi. Sau da dama ma takanyi mamakin yadda yake cinye musu lokacin sa wajen ganin ya faranta musu ita da yarinyar ta dan farko ma kokadan bata sake masa fuska sai da Maman Abdul ta dage kafin ta dan fara sakewa sai gashi Adam ya shigar da haske cikin rayuwar su sosai suka canza ita da 'yar ta batare da tasan takamamman lokacin ba.
Adam shike dora mata karatu da kansa kullin idan yazo yakan bata hadda kuma Alhamdulillah tana kokarin ganin ta kawo haddan ta adaidai.
Yaso ta shiga Islamiya tun yanzun amma yace baya so ya dakatar mata da aikin ta tunda yini take amma da zarar sunyi aure dole ne ya sata a amakarantar Islamiya hadda boko.
Ba karamar rawa Adam ya taka cikin rayuwar Zaitun ba shiyasa a yanzun take matukar girmama al'amarin sa.
Hajja tasha yada musu habaici bayan ta ta6a binsa har kofar gida watarana da ya zo bayan Zaitun sun shigo gida.
Zaitun dai bata san me Hajjan tace da shi ba amma tasan ba magana me dadi bace..abin mamaki Adam ko dis maganganun Hajjan basu dadashi ba ganin hakan yasa Hajja ringa sakin habaici idan ta ganshi bai ta6a daga ido ya dube ta ba..." Sau 'daya tak ya ta6a bata amsa inda yace"..Mama ai ita kaddara babu kan wanda bata iya sauka kuma in ma abinda kike tunani kan Zaitun hakan yake ai ni ne da kaina nace naji na gani babu wanda ya tilasta ni.."
Daga ranar bai sake tanka Hajjan ba har ta gaji da ganta ta sarara masa.
Ita kuwa da tasan halin Hajjan tasan ba sabon abu bane indai akan ita da 'yar ta ne.
Adam ya nuna musu zallar kauna ya fito musu da martabar su ya kuma nuna wa duniya cewa su din wasu ne masu daraja, su din mutane ne masu matukar muhimmanci a idanun sa.
Ita kuwa a ganin ta me zatayi ta sakawa wannan bawan Allah da ya wuce ta bashi dama wajen ganin ya cimma muradin sa.
Baban su Abdul kadai ne damuwar ta a yanzu, kuma ko da wasa ko cikin mafarki bata tunanin zata iya aikata abinda yake nufin ta da shi, gashi da zarar ya tafi kamar tsungulin sa ake acan din yake sake dawowa gida, ada kafin zuwan ta gidan kamar yadda Mmn Abdul ta ta6a bata labari tace yakan shafe akalla watanni uku, hudu zuwa biyar bai zo gida ba amma ta lura tun zuwan da yayi ya ganta a gidan sai komai ya canza daga 6angaren sa, dawowa yake duk bayan wata guda, tsaraba kuwa daga ita har Mufee baya wuce su.
Yayin da ta 6angaren Zaitun gwanin tan nasa bai ta6a birge ta ba, bata san dalili ba kam amma har cikin zuciyar ta ta tsani taga yayi musu wani abu makamancin kyauta ko wani abu ta tsani komai da zai fito daga hannun sa.
Baban Abdul shine mutun na farko a tarihin rayuwar Zaitun da ya nuna kaunar sa ga Mufee wanda hakan bai birge Zaitun ba, bata kuma sanya shi cikin layin masoyan ta ba.
Maman Abdul kuwa da ta riga ta gama fahimtar inda mijin nata ya dosa sosai take mamakin sa ganin cewa abin nasa har na cikin gida bai bari ba.
Sau da dama ya kan siyo abu dangin sitira, kayan wasa ko kuma kayan tea ya bata yace ta kaiwa Zaitun din kuma bata ta6a jin haushin hakan ba duk da cewa ta san dalilin sa nayin hakan, amma kuma bata ta6a jin haushin Zaitun kan lamarin ba saboda ta riga da ta san da wa take zaune.
Tsoron ta daya kar wannan mugun halin nasa ya kai shi ga janyo musu abin kunya watarana, dallilin kenan da ya sanya kawai saboda ta canza tunanin sa yasa da kanta ta bashi shawaran auren Zaitun din duk da tasan abu ne mai matukar wahala Zaitun ta amince da shi, ko Adam ma da yaya ta amince masa ballantana Bbn Abdul, gefe guda kuma ga Hajjah ma tasan ko sama da kasa zasu hade bazata ta6a barin sa ya auri Zaitun din ba domin ita datake zaune dasu itace tasan adadin irin kiyayyar da Hajjan ke musu.
Maman Abdul bata yi mamakin irin tsantsan farin ciki da mijin nata ya nuna ba sakamakon wannan shawara da ta bashi...sosai ya kasa 6oye farin cikin sa.
Ido kawai ta rika binsa da shi cike da mamakin sa, da farko wasa ta dauki lamarin amma ganin yanda ya kar6i zancen ya sanya itama dole tunanin ta ya canza nan take...aganin ta bata da wata hanya ko mafitar da ya fi mata wannan din a yanzu, domin Allah ya riga ya hada su hadda rabon haihuwar 'ya'ya..baya ga addu'a da kullun take faman yi tana mika kukan ta ga mahalicci dole ne kuma ta tallafo shi ta wani 6angaren in har hakan ba zai zame musu matsala ba baki 'dayan su..idan auren sa da Zaitun alkhairi ne tana fatan Allah ya tabbatar musu da shi in kuwa sa6anin hakan ne Allah ubangiji ya canza musu da mafi alkhairi.
Ta riga da ta gama fahimtar waye Zaitun, ba tun yau tasan halin ta ba ta kuma fahimci asalin dangantakar dake tsakanin ta da Mufeeda, Zaitun ba ta da wani mugun halayya da zai sa aki ra6ar ta saboda shi dan haka bata da matsala da ita matukar zai kula ya daidaita adalcin sa tsakanin su ita me goya masa bayane cikin ko wani irin hali.
Baban Abdul bai yi kasa a gwiwa ba wajen bayyanawa Zaitun kudurin sa da soyayyar da yake yi mata da kwarin gwiwar sa musamman da yake ya gama samin license din ne daga wajen Matar sa Rahama ( Mmn Abdul)..Zaitun kam maganar tasa ya matukar tada mata hankali.
Ta yama karamar kwakwalwar Baban Abdul take tunanin ita zata iya auren mijin Matar nan?
Mace mafi karamci agare ta mace mafi kyautatawa sai a wayi gari kuma ita Zaituna ta tashi daga matsayin makwabciyar ta ta koma Kishiya...inaa bata fatan faruwar hakan har abada.
Daren ranar kaf bacci kaurace wa idanun ta yayi, bayan kukan da ta sha da tunani ta karasa wayan garin ji take komai ma a baibai yake zuwa mata ita.
Da yake Baban Abdul kamar a matse yake wajen ganin ya auri Zaitun din hakan yasa bai 6ata lokaci wajen sanar da mahaifiyar sa ba wato Hajja duk da cewa bai ji koda furuci guda daga bakin Zaitun din ba bai kuma san inda zuciyar ta ta fuskan ta ba amma zumudin da yake ciki ya kara bashi kwarin gwiwa da kyautata zaton zata amince dan shi duk zuwan da Adam ke yi ma basu ta6a haduwa ba balle yayai tunanin yana da wani rival.
Ranar kuwa yaga tijara wajen Hajja, da asuban fari lokacin da yaje gaida ta ya sanar da ita kudirin nasa wanda a lokacin kowa na gida babu wanda ya fita ciki kuwa hadda Zaitun.
'Karan hargagin Hajja ne ya maida hankalin Zaitun ga wajen kawai sai ta dafe kanta dai dai lokacin da kunnuwan ta suka tsinkayi muryar Hajjan na fadin..." sai kace da suna Saratu aka yanka min ragon suna, wlh koda mata sun kare a duniyan nan bazan ta6a amincewa ka auri Zaituna ba...kai ko da bayan raina ne ma ban amince ka aure ta ba, kai baka da hankali ne shin? baka ganin abinda ke tare da ita ne ko kuwa kasan dalilin da ya sa ta tsamo jiki daga cikin 'yan uwan ta zuwa nan...wlh ka kiyaye ni Ibrahim tun wuri ka dakatar da wannan zancen kafin in ci maka mutunci a gidan nan...".
Bata ji me Baban Abdul din ya fada ba illah muryar Hajjan da take sake jiyowa kasa kasa" Banda lalacewa ta zamani dubi 'yar yarinyar nan da har a yanzun tan ma bai wuci ace tana jikin mahaifiyar ta ba amma shine hadda goyon shege..ni an gaya maka da ace ina da dama da tuni ban jima da sallaman ta daga gidan nan bane, kawai dan bani da damar hakan ne amma ina dalili mutun ya gama biye biyen titi da kwararo kai kuma kazo ka zauna da shi salon ya gur6ata maka zuri'a in ba lalura bama me zai sa in amince da hakan, kai kuma dayake gaula ne shine wai har ka abin aura anan, toh ahir dinka wallahi Ibrahim har abada bada yawuna ba...".
Duk da cewa har cikin zuciyar ta kalaman Hajjan suka soke ta kokadan basu mata dadi ba amma ta wani 6angaren na zuciyar ta ji tayi kalaman sun faranta mata.
Tun kuwa da taji kalaman Hajjan sai ta dan ji natsuwa, ko ba komai yanzu tasan maganar auren zai sha ruwa tunda Hajja mahaifiya ce dole kuma ya bi maganar ta.