← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 218

Sashe 80

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_Haka kawai yau na yanke shawarar zuwa aiki na da nake yi a 6angaren Amrah duk da kuwa har yau 'din nasan bata dawo gidan ba, kuma rabo na da yi musu aiki tun batun satan nan da akayi kwanaki, idan ban manta ba kwanaki goma sha tara kenan yanzu, amma zan yi hakan ne kawai dan in samu damar ganawa da Rayyan ba dan komai ba, duk da nasan mawuyaci ne ma ya saurare ni._
_Duk da nasan dai matukar Allah ya riga ya tsara wa bawa abu toh kuwa wani bawa bai isa ya dakatar da faruwar lamarin ba, amma muna fatan faruwar alkhairi ne kowace wayewar safia wala alla yun'kurin mu su kasance mana garkuwa idan Allah yaso...._
_Da wannan tunanin na sake samun 'kwarin gwiwar 'kaddamar da nufi na, Knocking bakin parlorn nayi amma shiru ba'azo an bu'de min ba, tsawon mintina ina tsaye ji nake tamkar in koma amma kuma 'kafafuna sai suka kasa motsawa duk da kuwa zuciya ta ta riga ta bani umarnin in ha'kura kawai nayi tafiya ta._
_A hankali na sake 'daga hannu na danna bell din ina lumshe idanu da fatan nasara._
_Bayan kamar da'ki'ku hamsin sai kawai na yanke shawarar juyawa, wannan karan 'kafa ta batayi min nawi ba, amma daga yadda nake tafiyan zaki fahimci ba a son raina nake tafiyar ba...kawai dai naga alamun ba lallai ne a bu'de min kofar ba...bazan samu ganin sa ba kenan..ba mamaki ma baya 'dakin kilan yana wajen motsa jikin sa kamar yadda ya saba duk safiya, amma ai lokacin barin sa wajen tuni ya gota...duk wannan tunanin ina yinta ne cikin zuciya ta yayin da idanuwa na ke kafe kan motar da na tabbatar akayi abu 'kar'kashin ta._

_Ka'dan ya rage nayi nisa da bakin 'kofan naji alamun an bu'de ta, haka kawai na saki ajiyan numfashi._
_Waigowa nayi muka ha'de idanu, sanye yake da dogon wando mai kauri na ba'kin jeans da singileti fari, fuskar sa babu yabo babu fallasa...sai kuma naji kwarin gwiwar da suka yo min rakiya duk sun zagwanye..Allah ya bawa Rayyan kwarjini, kyau da cikar kamala gashi mutum ne mai matukar natsuwa._

" _Kin tsaya kallo na bake ke sallamar bane..._ ?"
_Ban bashi amsa ba illa takowa da nayi na dawo baya step uku dake nan wajen tamkar dakali da zaka fara takewa kafin isa ga barandar Parlorn nasa kafa na fara takowa a hankali idanu na na 'kasa._

' _Kofar ya saki ya koma ciki batare da ya rufe ta ba_ .
Cikin ransa ya furta..." " _Tamkar wata mumina_ "

_A hankali na tura na shiga, ban wani yi yawo da idanu na sosai a palorn ba kasantuwar yana a ciki shima can gefe bisa kujerar dinning da yake 6angaren ba wani babba sosai bane ba so daga inda nake ina iya hango shi kuma shima yana kallo na._
_6angaren sa ne tun na zamanin samartakar sar sa kuma ko lokacin da aka daow da Amrah gidan ba ai masa gyaran komai ba._

_Sau 'daya dana dubi parlon na tabbatar baya samun isasshen gyara yadda ya kamata dan babu takamman mai zuwa ya kula da tsabtar sa._
_Shi da kansa Rayyan yake komin sa tun bayan tafiyar Amrah dayaga Zaitoon bata zo aikin ba bai sake gayyatan wata dan yi masa aiki ba, haka kuma itama bai neme ta ba sbd yasan dole ne taji babu da'di bayan sharrin sata da Amrah tayi mata...sannan itama Ammi fushi tayi ta ki sake tura musu mai aiki domin acewar ta bazata ringa mika yaran mutane ana binsu da sharri ba._
_Ban iya 'daga idanu na dube shi ba kawai nace" Yayan Marwa Barka da safia"_
_Bakin sa kawai ya motsa sai numfashin sa da ya fito da sautin murmushi, dan har ga Allah furucin nata ya basa daria, bata ta6a yi masa suna ba tun zaman ta gidan sai yau kadai yau din ma..." Wai Yayan Marwa.."._
Ya sake nanatawa cikin ransa.
_Dama nasan bazai amsa ba..ba yau ya saba min irin hakan ba._
_Kitchen kawai na wuce dan fara aiki na duk da nasan ba shine ainahin abinda ya kawo ni ba, amma yadda naga 6angaren ya canza ya zam min dole in canza masa yanayi..." An aiko ki ne hala..?"_
_Ya jefa min tambayar yana sipping ruwan tea dake cikin wata mug a hannun sa._
_" Aiki nazo yi kawai"._

_" Fa'di gaskia ke dai, ai kin me zakiyi bacin kin riga kin korar min mata..?"_
_Ya yi mata tambayar yana kawar da kansa gefe a kokarin sa na 6oye murmushin da ke saman fuskar sa domin yasan dole zata waigo._
_Ai kuwa da sauri na waigo._
_" Ni kuma na koreta...?"_
_Na tambaya da idanu na waje sosai._
Kai ya jinjina min kawai ya mike ya nufi dakin sa.

_Kalaman san nan sai suka 'kara sanyatar min da jiki na..kaddai dagaske gani yake ni 'dince na korar masa mata, bazan manta ba haka kwanaki ya ta6a furta min ranar da ya dawo dani gida._
Idan da gaske ni din ce ya _zanyi yi..Allah ma bazai barni ba fa._
_Sosai na sake tsorata...haka na fara aikin cike da rashin natsuwa amma dai hakan bai sa nayi abinda ba shine ba._
_Ina tsaka da aikin har ma na mance batun da ya kawo ni ina ta tunanin Amrah da tausayin ta sosai musamman da nasan cewa tana da juna, kamata yayi ace tana tare da mijin ta a wannan halin amma hakan bai samu gareta ba._
_Ina tsaka da tunani kawai naji alamun anbude bude kofa...nasan lokacin fitar sa office ne yayi._
_Take komai ya dawo min lokaci guda._

_Da sauri na dawo bakin kitchen 'din na tsaya ina gani yana nufar 'kofar da zata fitar da shi amma sai na rasa 'kwarin gwiwar tunkarar sa, ta ina zan fara yi mai bayani ne ban sani ba._

Shima daf da zai fita ya kamar yasan ina kallon sa sai ya waigo...ga mamakin sa Zaitoon ce, kuma shi take kallo.
Gira ya 'dage mata duk biyu da alamun tambaya cikin idanun sa.
" _Wani abun kike so ne_ ...?"
Na tsinkayi muryar sa yana fa'din hakan.
Da sauri na girgiza kaina ina maida dubana izuwa 'kasan tiles.
" Ko nii...?"
Ya sake fa'da yana nuna 'kirjin sa da hannun sa 'daya.
Take sai kuma ya juya gaba daya ya fuskance ta.
" Ohh na gane...kin korar min mata sai kuma kizo kina kalle mata miji ko, ya miki ne ki fa'da...?"
" _Ko ka'dan, banga abinda zai min ko ya birge ni tattare da shi ba..."_
Na bashi amsa cike da kwarin gwiwar da nasan iya baki ya tsaya, duk da inajin fargaba, rashin ha'duwar mu kwanakin da suka gabatan nan yasa nake ganin sa daban da baya a yadda nake ganin sa da kuma yadda mu'amalar mu take kasancewa.
" Kin tabbatar...?"
" Fiye da zaton ka...".

'Yar murmushi yayi kawai ya juya batare da sake fa'din komai ba..taku biyu yayi uku naga alamun kamar dagaske tafiyan zai yi hakan yasa na budi baki da 'kyar nace..." In baka shawara...?"

*Drop ur comment*

*From the writter of CAPTAIN ABBAS & NOORUL (Haske na)*

_Salmerh_ 😘
[16/10/2022, 9:03 am] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...50*

......" In baka shawara?"
Cak ya tsaya da tafiyar duk da kuwa naga alamun cikin hanzari yake kasantuwar shigan lokacin da ya riske shi ya kuma haifar masa da makara, yana da ba'kin da zasu gana da wannan safiyar ne shiyasa kuma hanzarin nasa ya sake ta'azzara.
Ban jira ya juyo ba na 'dora da fa'din " Kar ka hau motar nan taka yau ka fara bincika ta tukunna...".
Cikin tsanaki ya juyo ya dube ni cike da tsananin mamakin jin kalaman baki na, yayin da zuciyar sa ke sake shiga ru'dani amma ya basar.

Yayin da ni kuma nayi 'kasa da kaina dan bana san 'kwarin gwiwa ta ta barni.

" Hakan shawara ce...?"
Da kai na bashi amsa alamar" erh".

".. _Bisa wani dalili kenan?_
Sai kuma ya girgiza kansa ya canza maganar da fa'din" _I mean hujja_ ...?"

Shiru nayi, na rasa ma me zance masa ne.
Da gaske ya kamata ace ina da hujja kafin bashi shawarar saboda gudun abinda ka iya zuwa ya dawo amma..amma ai hujja ta tanadaddiya ce, tabbbas ina da hujja amma shin idan na fada zai fahimce ni ko kuwa..?"
Na tambayi kaina.

Toh ma idan bai fahimce ni ba rayuwar waye take cikin ha'dari..? shine!
Idan bai 'dauki shawara ta bama kansa ya yiwa ba bani ba.
Wata 6arin zuciyar tawa ta ayyana hakan.

Sai dai bazan so faruwar hakan ba sam, ko bakomai shi jinin Ammi ce, bazan so ganin ta cikin 'kunci dai- dai da 'kwayar zarra ba, kuma na tabbatar duk ranar da akace babu shi na tabbatar Ammi sai ta shiga wani hali.

" Ni dai dan Allah.."!
Na tsinci la66ana na motsawa wajen furta hakan cike da marairai ta batare da na shirya ba.

Kallo na ya tsaya yi batare da ya furta wata kalma ba.

A hankali kamar bansan maganar nace" ka canza masu kulawa da ku.."
Bansan meyasa ba amma haka kawai naji zuciya ta bata amince da su ba, duk da bansan inda 'karshen maganar zai tsaya ba amma ni dai inaji araina in fa'da masa koda hakan zai iya sanadin tawa rayuwar ne, zan yi ne saboda Allah da kuma Ammi.

'Dan ha'de rai Rayyan yayi da alamun wani sabon mamakin kuma, sai dai maganar tata ya hana mamakin nasa bayyanuwa.

Wai.. _masu kula da kai..._
me yarinyar nan ke nufi?

Tana nufin su Huzaifa zan canza ko me?..
Ya tambayi kansa.
Yaushe ma na basu damar bibiya ta, yaran da a yini bai fi mu hadu sau biyu ba, gidan ma yaushe suke shigowa sam bai amince da cewar su bayyana kansu matsayin masu bashi kariya ba, a ganin sa babu kariyar da tafi ta mahallici, amma duk da hakan bazai watsawa Ammi kasa a idanu ba kamar yadda ta bukata, hakan yasa ya barsu a matsayin da suke kai ake kuma biyan su.
Chapter 80 · 0% Book details