← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 184 OF 218

Sashe 184

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kanta take bawa Ameeran labari a ta'kaice na abinda ke faruwa da har yasa ta dawo gida sai dai bata fito fili ta fadi mata waye Arfan ba, ta dai ce 'yan uwan Rayyan da 'kannen sa ke neman raina mata hankali ita kuma bazata iya zama tana kallon su ba, ba ma zata iya zuva idanu ana ci mata fuska akaran banza ba, hakan yasa ta dawo gida a kwatan mata 'yancin ta.

'Yar murmushin gefen baki Ameera tayi sannan tace" ban ta6a sanin baki da wayo ko na sisin kobo ba sai yau Amra.."
Idanu ta waro akan Ameera da alamun tambaya.
Kai Ameera ta jinjina mata alamun tabbatarwa ta sake fadin tabbas Amra baki da wayo sam sam".
" akan wasu can 'yan uwan mijin ki, bama shi ba fa Amra..'yan uwan sa kk ce amma sai ki ri'ka wasa da auren ki? Shin bake ce kk ce min sun yi masa wani auren da 'yar aikin ki ba...?"
Shiru Amra tayi tana me tunanin yaushe ma ta fa'di wannan abin kunyar.

Ameera ta cigaba" Toh wlh tun wuri ki shafa kanki ruwa ki yiwa kanki fa'da, bb inda ya kai mk 'dakin mijin ki, ke in takaice mk ko yaron ki kular da zai samu gaban mahaifin sa ba 'daya yake da na wani wajen daban ba, haka kawai akan wani dangin da bama kullum kk ganin juna ba sai ki tattare ki taho gida da yaro..sai kace babu gurbin kwakwalwa cikin kanki...?"
Da sauri Amra tace
" Ke..har fa da mahaifiyar sa..?"
Ameera ma cike da 6acin rai ta cigaba
Sai kuma kiyi ai..ni dai ban ta6a ganin alamun hkan tattare da Ammi ba tun sani na da ita, matar nan tayi ne a rayuwa, kima gode Allah da ya azurta da samun irin ta matsayin uwar miji, wannan rawan kan tun wuri ki nema masa mashiga ki kama kanki...duk wanda zaice miki kin yi daidai toh wlh bb kaunar ki a ransa amma kin ga cewa batuna da kuskure ba tilasta nake yi ba, kina da ra'ayin kanki...kiyi yadda kk so..."
" Matar da ko ba'ko me yaje gidan sai ya yaba da kirkin ta balle matar dake a matsayin matar 'danta...wlh Amra ki nutsu ki san inda ke mk ciwo, kinsan yadda 'yan mata ma ke bibiyan irin mijin ki kuwa? kina sane da kalar zamanin da muke a halin yanzu ko? kina nan zaune wata zatayi mk wuff da shi sai dai ki kuma jin labarin an mk wata kishiyar banda waccan da kk barsu tare a gida...."

" Allah ya sawwa'ke Ameera dan Allah daina yi min wannan fatan, waccen ma ai tuni ina jin bb auren dan nasan ba lallai ne tayi masa ba..."
" Da yake igiyoyin auren a hannun ki suke ai dole kice haka..mjin da kk kasa jinyar sa, kk kasa zama da shi a halin jinya kika juya masa baya duk ta maye wa'dannan gurbin kk tunanin zai iya rabuwa da ita cikin sauki...da alamu kanki sam baya jaa Amra..."
Fa'da sosai Ameerah tayi mata kafin ta bar gidan.

Sosai kuwa taji fa'dan Ameera, jikin ta yy sanyi, tunani kala kala ta zauna ta yisu ta kuma ku'durta komawa gidan mijin ta aranta tun kafin ai mata sakiyar da ba ruwa, tunda Allah bai sa an tona ta wajen kowa ba.

Rayyan kuwa dama tasan halin sa mawuyaci ne yazo gidan sun musamman sbd ita tunda ba shine yace ta taho ba sarai tasan bazai ta6a zuwa sbd ita ba.

Ko da ta komawa Mummyn ta da maganar komawa masifa ta fara yi mata, akan bazata koma 'din ba gidan da ake yi mata gorin sa, gidan da ake binta da sharri, gidan babu wani mai kaunar ta a cikin sa zaman me zata je tayi a cikin su banda zaman takura.
Amra tana tura baki tace" Mummy ba fa shine yai min laifin ba, Antyn sa ce wlh..kuma kinsan sa da taurin kai da shegen son 'yan uwan sa bazai ta6a zuwa gidannan danni ba.

" Sai yaje can da girman kan sa shi ya sani, ni dai babu mai kawo min wargi har cikin gidana in 'kyale sa wlh...dan rashin kirki ko 'dansu dake tare dake ma ai babu wanda ya damu ya zo ganin lafiyar sa balle ke da dama aka raina...a fili ake nuna mk kiyayya amma sam baki ganewa...".
"...Mummy...dan Allah..."
" Ke...!
Ta daka mata tsawar da ya kusan firgita ta.
" Nace ki bani wuri bb inda zaki...".
'Kafa ta fara bugawa a 'kasa tana kuka take fadin " Haba Mummy?..haba Mummy!!..fi sabilillahi mutun da mijin shi ace bazai koma gidan sa ba haka kawai, nifa wlh ina son mijina har yanzu..".
" Sannu suda sarkin so...!ina ce kafar ki ta kawo ki da wuya ta koroki toh bazan san kinayi ba sam Amra har sai kin fito dunia kin nuna musu cewa ina son raba ki da mijin ki tunda nice naje har gidan naki na 'dauko ki...tsaban rashin zucia ma shi bai zo ko sau guda cikiyar ku ba sai kece zaki bibiye sa...".
" Ni dai wallahi ba rashin zucia bane..mutun da gidan sa ace bazai koma ba...".
Haka ta 'karaci mitar ta akan Mummyn nata bata ce da ita 'kala ba.

Ko da ta koma 'dakin ta kuka sosai tasha, cikin ranta take jin kewa da tausayin Sultan amma bata da ikon zuwa gare shi sbd gudun zargi.

Karo guda tamkar an tsikare ta ta tashi ta fara ha'de kayan ta, ba yau ta fara guduwa daga gida dan komawa 'dakin mijin ta ba amma yau 'din haka kawai sai taji bata so tayi hakan...tafi so tayi komai da yaddar mahaifiyar ta duk da bata ga alamun mahaifiyar tan na da niyyar mayar da ita ba.

Magana take so ayi aja wa kowa kunne akan ita da yaron ta cikin gidan kuma hakan bazai samu ba har sai Rayyan ya kawo kansa gaban mahaifan ta ko kuma su mahaifan nata su nemi jin ba'asin.dawowar ta amma bata ga alamun faruwar ko daya daga cikin hakan ba sam, Abban ta ne dama kuma baya 'kasar tun zuwan ta, itama Mummyn nata dawowa tayi ta tarar da ita, shi dama Rayyan ba yau tasan halin sa ba matukar ba shine yace tazo gidan da kansa ba baya ta6a biyo bayan ta ba kuma ya bari wani yy hakan.

Tun wani zuwa da ya ta6a yi mahaifiyar ta taso yi mar tijara ya yaye wa kansa bin bayan ta...ta san kuma idan shekara zatayi ba zuwan zai yi ba.

Hakan kawai kuma sai ta tsinci kanta da son komawa, kayan ta ta ha'de kaf da na yaron ta ta ajiye a gefe.

Washe gari da sassafe taje 'dakin Mummyn nata ta ri'ka yi mata kuka da magiya akan komawar , dan tasan Daddyn ta ba matsala gare sa ba shi.

Yadda take kukan ya tilastawa Mummyn amince mata amma tace ita bb inda zata je, sai dai ta 'kira mijin nata yazo ya 'dauke su zuwa dare su koma.

Hakan kuwa akayi, da komawar ta 'daki ta 'kira shi bayan gaisuwa sai ma ta rasa abin cewa.
" Baby shine tunda muka taho ko sau 'daya baka zo ka duba mu ba..?"
" Bani da lokaci ne".
" Ayyah ..Arfan ma na gaida ka".
" Ya yake?"
"Lafiyar sa 'kalau..but he is missing you badly".
Tayi maganar tana murmushi.
Rayyan bai ce komai ba.
" Baby yaushe zaka zo mu koma gida?"
" Babu rana!"
" Ayya pls mana Baby kayi hkr, i know ban kyauta ba amma Insha Allahu hkn bazai sake faruwa ba.."

Tasan bazai zo 'din ba dan tun daga yadda taji yake amsa mata magana abin bai yi mata ba domin a wani da'kile yake amsa ta tamkar bai san yin maganar.

Ai kuwa amsar da ya biyo baya bai mata da'di ba sam dan cewa yayi" Ai ni ban kore ki ba Amra, ban kuma ce ki tafi gida ba dan haka ni ban da lkcn wani zuwa 'dauko ki, kisha zaman ki ki huta a gida kawai tunda haka kk fi so...."

Tace sam ita dai zata dawo sai yace Allah ya tsare hanya.
Daga haka ya kashe kiran ya cigaba da harkokin sa.

Anyi hakan da kwanaki biyu ta dawo gidan..kuma abinda ya bata mamaki har aka kwana biyu da dawowar ta Rayyan bai nuna alamun yasan da zuwan ta ba, sai ta ga ma duk wasu lokutan harkokin sa ya canza su ba kamar yadda ta sanshi abaya ba.

Idan ya fita tun safe bai dawowa har sai ya tabbatar kowa yy bacci, kuma sannan rufe 'kofar sa yake ya wuce da keys 'din sa baya bari a shigan masa 'daki.

Wannan sabon canjin ba 'karamin ba'kanta ran Amra yy ba ta kuma rasa ta yadda zata 6ullo masa.

Shima 6angaren sa bata san tana cikin ransa ba, shi ba wai yayi farin ciki da da dawowan ta ko akasin hakan ba ba 'daya daga ciki, kawai so yake ya samu lkc yaji daga bakin ta akan Arfan 'karya guda kuma ta kuskuara tayi masa hukuncin sa bazai zama mai dadin ji ga duk wani mai kaunar ta ba.
Abinda kullum ke ransa kenan game da Amra, bayan hakan bb komai, babu wata kauna tata a hahalin yanzu aransa, baba shauki balle kewa nata da ada ya saba jji da zaran ta nisance shi.

Ai kuwa Amra ta kai kusan sati a gidan batare da sun ha'du da Rayyan ba dan 'karshe ma barin gidan yayi abinsa ya koma can gidan sa shi ka'dai yake rayuwar sa.

Ranar da ta cika sati kuma aranar ya dawo da Mufee a hannun sa ya shigo 6angaren nata da misalin sha 'daya na safe dan aranar ne ya yanke zasu Prison da Marwa.

Rashin ganin sa na tsawon kwanakin da batayi ba bai 6ata ranta kamar yadda taga ya shigo mata da Mufeeda suna daria tare ba.
Chapter 184 · 0% Book details