← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 175 OF 218

Sashe 175

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yadda jami'an tsaro ke tsaye tsayin daka kan Sultan abin gaba 'daya ya gigita Ammi, kuma har lkcn babu Rayyan bb dalilin sa...basu sani ba ma shi tuni ya wuce Lagos, hannun sa kuwa tun bayan da ya bigi Sultan da ya dawo gida daga kai Marwa asbiti ya kama hannun ya ja sosai ya mur'de shi sbd zogin da yake mishi daga cikin hannun tun daga ranar bai sake tunawa cewa hannun sa na ciwo bama balle ya hana shi wasu al'amuran sa.

Kwanan Sultan biyu aka sallame shi, sai dai ga mamakin Ammi division aka wuce da shi tana ji tana gani aka tisa 'keyar sa.

Tabi bayan su ita da Anty Raihana da wata Hajia Zahra dan sanin ma'kasudi da kuma neman belin sa amma abu ya faskara dole haka suka koma gida rai bb dadi, kafin komawar su kuwa Anty Madeena ta wuce gidan ta dan tace bama zata zauna ba balle Ammi ta fahimci tasan wani abu duk da yake ita kanta Anty Madeenan ba komai ne Rayyan ya sanar da ita ba.

Allah Allah take akawo 'karshen komai a raba su da jarabbaben yaron nan da har Marwa ke son 'daurawa kanta cuta sbd shi.
Da kyar suka samu ta dawo daidai sai da Anty Madeena tayi mata tatas tukunna take cewa ke baki ji da kunnen ki abinda Rayyan 'din yace bane, matar sa ya ta6a masa taya bazai bige shi ba, ko ya 'dauka kowa ma irin Amra ne dangin akuyoyi, kuma da kanki kinsan ai Rayyan ba zai aikata hakan sbd son zuciyar sa kawai ba, dole sai da wata kwakkwarar dalili, inba haukan ki bama abinda ya kamata ki damu da son sanin sa ba shi ne gaban ki ba sai wani can dan iska maci amana kk damin kanki ki damu mutane akan sa...? toh wlh ki kiyaye ni tun kafin ki 'kureni in sassa6a mk cikin gidan nan, wawuya kawai wacce bata san ciwon kanta ba....".

Sosai ta 'kara shiga 'dimuwa domin Anty Madeena ta ankarar da ita wani abu da ada bata zurfafa tunani akan sa ba, kuma ma bata ta6a zargin hakan ba sam, nd babu shakka tana matukar kyautatawa Rayyan zato tasan bazai yi haka nan kawai batare da wani dalili ba..amma ai bugun yayi yawa, dole sai ta warware ta shiga tunanin abinda ya ha'da Rayyan da Sultan har aka kaiga wannan gandun gashi 'karshe a hannun hukuma Rayyan ya dam'ka shi an kuma nemeshi an rasa shi.

Ta kan zauna jigum cikin su amma ba umm ba um-um sai dai idanu kawai, Zaitoon da Raihana kadai ke 'ko'karin kwantar mata da hankali, a hakan Zaitoon idan ta ke6e kuma ita kanta kukan take sosai domin gani take duk itace silar komai.

In kaga Marwa na 'dan fara'a toh Mufeeda na tare da ita ne, da ita kadai take 'dan hira har ta biyewa shirmen ta wani lkc.

Kwanaki biyar ana cikin wannan halin duk sun rasa meke yi musu da'di, duk yadda Ammi taso bu'de bakin aljihu dan ta samu belin Sultan abin ya faskara, har tsoro Rayyan ya fara bata yanzu.

Wai wannan hauka ne ko kuwa kishi? tana yawan yima kanta wannan tambayar da ita kanta bata san amsar ba, duk tunanin Ammi kan ta6a matar sa da yace Sultan yy ne ka'dai, kuma in dai kan hakane ai bai kamata ya ja maganar har haka ba hadda hukuma, hukumar ma zazzafa indai ba wai dama da kwai wata a 'kasa wanda ita bata sani ba.
Tunanin Ammi kenan kusan ko da wani lic, ta kuma so ganawa da shi Sultan 'din amma bata samu damar hakan ba.
A yanzu kam ta gama fahimtar yanayin tafiyar da duniya take yi dama rayuwar gaba 'daya.

Kai zaka haifi 'da ko 'ya da cikin ka amma watan watarana sai ya fi ka 'karfin iko da nuna isa, dan gashi zahiri taga misali ganin idanun ta akan ita da Rayyan.

Ko da ya dawo daga Lagos 'din kuwa bai je gidan san bama talkmore of gidan Ammi.

Hotel ya kama yayi zaman sa yana mai cigaba da harha'de hujjojin sa na shiga kotu, dan ba 'karamin nasara ya samo a wannan tafiya tasa ba.

Yayi amfani da salon aikin sa na lauyoyi ya kuma samo duk hujjojin da yake bu'kata wa'danda suka shafi Companyn sa na can Lagos 'din dama wasu daban,..wannan karan da kansa yake so ya tsayawa ahalin sa, baya so ya wakilta kowa shi da kansa yake so ya bayyanawa dunia waye Sultan su gani, ba kuma dan baya son shi ko kuma dan ya tsane shi ba, badan komai ba kawai sbd 'yan baya da kuma Sultan shi kansa, so yake rayuwar Sultan da kuma hukuncin da za'ai masa ya zam darasi ga duk wani maci amana da kuma mai burin aikata irin hakan agaba..so yk Sultan yasan cewa yayi kuskuren da dole hukunci ya hau kansa..gagarumin darasi yk so ya bari wa 'yan baya.

Kwatsam kawai lbr ya iso Ammi akan za'a shiga kotu ranar litinin mai zuwa wanda yyi daidai da kwanaki hu'du kenan masu zuwa daga lkcn da taji.
Wannan lamari yafi komai tada mata hankali fiye ma da abinda ya faru abaya..abin ya mata bazata domin bata tta6a zaton hakan ba.

Wai duk menene wannan, menene Rayyan yake nufi, Sultan 'dan ta ne kamar yadda yake 'danta, meyasa bazai iya yafe masa 'dan wannan abin da yai masan ba har sai ya dangana da hukuma 'karshe kuma kotu...meyasa bazau zo gida a zauna ayi magana ba, tunda wannan issues din na gida ne, bai kamata wani dan karamin family issue yasa ka rufe ido kai ta tafka rashin mutunci ba...watarana kai ne da kunya a tunanin Ammi kenan.

Tabbas kuwa hakan ne, sai dai kuma bb mamaki rashin sanin takamammen abinda ke faruwa yasa Ammi tunanin cewa wannan abin family issue ne kadai.

Ranta ya 6aci sosai musamman idan ta tuna daina ganin Rayyan da tayi cikin kwanakin sam, duk kuma wani wuri da tasan zata same shi taje bb shi, gidan sa, office, asbiti, Infinity duk bb shi, hatta abokan sa ta tuntu6e su bb labarin sa.

Anty Madeena kam ko ajikin ta tamkar ma bata san meke faruwa ba kwata- kwata, gidan ya sake zama shiru kace gidan mutuwa ne, ba Raihana ko Zaitoon ba, ba Marwa ba kar ma Ammi taji lbr hatta tsirarun ba'ki dake gidan suma bb wanda yake cikin yanayi mai da'di...ko.Mufee da ke 'yar mitsil a gidan sai da ta fahimci gidan ba daidai yake ba sbd walwalar kowa da ta daina gani.

'Karshe Anty Madeena 'dauke Mufeeda tayi dan acewar ta basa bata kulawar da ta dace sbd wani 'dan iskan yaro can da bai san mtunci ba baza'a illata musu lafiyar yarinya ba.

Ammi har rama tayi sosai, idan ka ganta sai ka tausaya mata cikin kwanaki 'kalilan.

Ana gobe za'a shiga kotu Ammi ta rasa ta yadda zata sami Rayyan kawai taje ta siyi fili a gidan Talebijin aka mata cikiyar sa da kuma babban kashedi kan shiga kotun nan, wannan abu shi yaja ra'ayin mutane da dama kan zuwa kotun dan ganewa idanun su irin shari'ar da har ake kashedi akanta.

Da yawan mutane kuwa da suka saurari jawabin Ammin fatan su kar ma ace Rayyan ya gani balle ya 'ki zuwa kotun burin su a gudanar su kuma gani da idanun su abinda ke faruwa.

Salmerh😘
[24/8/2023, 4:26 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...97*

.......Yadda kuwa jama'a suka yi fata da buri hakan ne ya faru.
Yayin da da yawan su suka kwana da burin zuwa kotu a wannan ranar...gaba 'daya hankalin jama'ah sai ya raja'a akan shari'ar Rayyan duk da shi ba hakan yaso ba, ita kanta Ammi bata san maganar da tayi tamkar sake janyo hankalin jama'a tayi kan shari'ar tasa ba kasantuwar tayi abin ne bisa zafin rai cike kuma da jin haushi, sa6anin yadda taso a janye ma gaba 'daya sai salon abin ya canza zuwa ga 'kaguwa ga sauraran wannan shari'ar.

Ammi bata san hakan ba har sai washegari da idanun ta ya gane mata yadda jama'a ke ta tururuwar zuwa, kanta daurewa yy da farko sai da ta nisa kafin ta farga da kato6arar da tafka.
Haushi kuwa ya kara cika ta.

'Bangaren Marwa da Zaitoon sun kwana ne cikin yanayi na tsantsan damuwa da rashin sukuni banda kuka babu abinda suke yi har wayewar gari.

Anty Raihana da Ammi kuwa bazaka iya ma bayyana ainahin yanayin da zu'katan su ke ciki kai tsaye ba, Anty Madeena kadai ke cikin farin ciki marar misaltuwa, ganin cewa burikan ta na cika a hankali 'daya bayan 'daya batare da ta 'daga hankalin ta ko abin ya fito daga gareta ba.
Chapter 175 · 0% Book details