← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 218

Sashe 19

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komai da yake yi cikin sanyi yake yin sa, dan shi ka'dai yasan irin halin da yake jin zuciyar sa ciki...kamar kaine ace rana guda za'a raba ka da wani abu mafi soyuwa a wajenka a zuciar ka..abin ba sauqi, balle Zaitun da ya dauki duk buri da farin cikin rayuwar sa ya 'daura a kanta, be ta6a kallon kowace mace da sunan soyayya ba sai Zaitun, akan ta ya sanin zafin so akan ta yasan 'kauna ta asali da ta boge, amma rana tsaka Hajiya na neman tarwatsa duk tubalin da ya fara ginawa.

Yaro ya aika kamar yadda ya saba kullun amma sai bai fahimci amsar da yaron ke san sanar da shi ba..." an ce wai bata gidan tun jiya...."
Abinda yaron ya sanar da shi kenan matsayin amsar aiken da yai masa.

Take yaji bugun zuciya mai tsanani.." tun jiya kuma...?"
Ya sake tambayar yaron yana mai kankance idanu cike da rashin yadda da maganar.
" Erh Hajja ce tace a fa'da maka...".
Guntuwar tsaki yaja jin cewa Hajja ce duk ji yayi ma bai yadda da zancen ba gaba 'daya, ai duk yana da lbrn yadda Hajjan ta tsani Zaitun, baya raba 'dayan biyu wani makircin Hajja ta shirya kuma.
" Amma kai kaga alamun tana gidan ne...?"
Ya sake tambayar yaron.
Sai cewa yayi.." a a ni dai Hajja ka'dai na gani kuma ita ta fa'da min..."
" Toh fa..! Kaga dan Allah koma kace wai afa'da maka inda taje..sai kazo ka fa'da min kaji?...".
Haka yaron ya koma cikin gidan, can sai gashi ya sake fitowa Hajja tafe a bayan sa da guntun mayafin ta aka...
Hango Hajja bayan yaron ya sanya Adam maida hankalin sa gareta batare da ya sake bi takan yaron ba..." aww kaine ashe...yaro ai mutuniyar taka bata nan tun jiya Hajiyar gidan tazo da kanta ta sallame ta babu kuma wanda yasan inda ta nufa..."
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un..sallama kuma kamar yaya?...ban fahimce ki ba wlh Mama..."
" Koranta Hajiya tayi daga gidan inajin dai wani laifi tayi mata.."
" Subhanallahi...wai kina nufin Hajiyata ce tazo har gidan nan..kuma ta kori Zaitun..?"
" Tabbas...".
Kansa ya dafe da hannun 'daya.
" Hajiya kin kashe ni..."!
bai san lokacin da hakan ma ya fito bakin sa ba saboda tsabar ka'duwan da yayi.. dafe kirjin sa yayi gami da zama bisa dakalin kofar gidan yana jin kamar ya fasa ihu ko zai sami sauqin zuciyar sa.

Hajja kam ciki ta koma tana mita 'kasa 'kasa" Jimin kinbabbe, santalelen yaro da kai ka tsaya lalacewa karkashin waccan banzar..."
Itakam Hajja ai barka tayi ma da faruwar wannan lamarin, dan a cewar ta an yada kwallon mangoro menene abin damuwa ban da kayi farin ciki 'kuda sun bar ka...yarinya duk tabi ta hana kowa zaman lafiya.
Shi kan sa Bbn Abdul ba karamin tashin hankali ya shiga ba da Hajjan ke sanar masa yadda abin ya kasance..." ke kuma Hajja sai kika barta ta tafi batare da kin bincika kinsan inda zata je ba?"
Yayi maganar ne cike da alhini gami da haushin rabuwa da Zaitun din adaidai lokacin yake tsaka da kaunar kasancewa tare da ita.

Wani zabura Hajja tayi tayo kansa da masifar ya yake so tayi da ita ne bacin masu gida ne da kansu suka sallame ta...ana me zata tsaida ta.

Bbn Abdul bai ko sake tanka Hajjan ba ya tafi 6angaren su yana me fatan Allah ya sake nuna mishi Zaituna a lokacin ne zai fito fili ya nunawa Hajjan cewa shifa dagaske yake son ta ba wasa ba.
Wannan shine yadda suka yi da Bbn Abdul akan Zaitunan....wanda duk Hajjan tana kan hanyar komawa gida take sake tariyowa, ai kuwa sai jan wata doguwar tsaki tayi ta fara magana a fili ita kadai..." Yarinya sai kace 'kanwar ifiritu".
Sam ta rasa itan wace iriyar yarinya ce, bayaga haka ace duk wadannan zabga- zabgan mazajen na shiga rudu saboda rashin ta?...( Adam da Bbn Abdul).

Adam sai da ya shafe kimanin rabin sa'a zaune a wajen batare da ya motsa ba hannuwan sa daya dafe da saitin zuciyar sa bai sauke ba, shi kadai yasan abinda yake ya kuma san damuwar da hakan ya haifar masa...bai ta6a kawowa aransa Hajiya zata aikata hakan ba.

Iya tunanin sa ya kure na inda Zaitunan zata shiga a fa'din garin amma bai tunano komai ba bai tuna kowa da yasan ta sani ba, gashi bata da waya taki yadda ya sai mata wayan dan acewar ta ita wa take da da har zata yi magana da shi a waya...yau ga ranar wayar ai.

Daga nan bai zame ko'ina ba sai gidan Hajiya wajen Hafez 'din ma fasa zuwa yayi gaba 'daya, 'dakin sa ya shige ya kwanta, tun yana tunani har tunanin nasa ya toshe baki 'daya..sallah ka'dai ke iya tada shi.

Ko da Hajiya ta dawo ma bai iya ya tanka ta ba, toh me zai ce mata? Abinda ya faru ya riga ya faru bazai iya dawo da lamarin baya ba, kuma yasan duk Hajiya na yin hakan ne a tunanin ta sbd ta tseratar masa da mutuncin sa..dan haka bai 'kara tada maganar ba kawai yake jinyar zuciyar sa a tsaye ko abinci ba iya ci sosai yake ba...kafin wasu kwanaki har ya zabge ya rame sosai.
Hajiya da fari share sa tayi ta fita sabgar sa a cewar ta yayi ya gama fushin da kansa ma ze sauko ne, sai daga baya kuma da kanta ta fuskanci abin fa ba fushi ne kadai da alamu hatta lafiyar sa ma da ta jima tana tattali ya samu gi6i, sai kuma taji ta damu.

_Salmerh_ 😘
[20/9/2022, 12:32 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE* 💕
*( 'yata ce)*

*Salmerh MD*

🅿️ *...12*

......Kimanin sati guda kenan Zaitun na zama cikin mabaratan bakin titi kuma har a lokacin magana be ta6a ha'da ta da ko guda daga cikin masu baran ba.

Ba burin ta tayi bara dan ta samu kudi ko wani abin ba a a kawai ta za6i zama cikin masu baran ne sbd tana ganin nan ne kawai ya dace da ita haka zuciyar ta yafi natsuwa da su...

Cikin wani kango take kwana gefe ka'dan da titin anan take rayuwar ta ita da yarinyar ta, sai dai babu batun wanka yanzun, babu batun wanki ba kuma wajen kwanciya mai da'di, baccin ma ba samu take tayi sa cikin natsuwa ba sbd tsoron kar tayi bacci wani abin ya saman mata Mufeeda ba karamin kaffa kaffa take da yarinyar ba.

Duk Zaitun ta lalace ta 'kara duhu ta zam tamkar wata zararriya, abinci kam bata rasawa sbd tana da 'dan guntun ku'da'den ta da ta6a bada hankali ta tara shi da niyyan canza musu muhalli, da shi take ta amfani yanzun duk dama ta cinye fiye da rabin sa daga zuwan ta waken zuwa yanzun.

Ta kanzo bakin titin ne ta zauna kan jakan kayan ta gefe kadan da su, bata iya barin jakan ta a gefe ne sbd tsoron kar a raba ta da kayan nata domin akwai abu muhimmi da bata san ta rabu da shi sam aciki, sau 'daya wata mata ta ta6a bata sadaka har ta Naira dari biyu wanda daga nan bata sake samin wata sadakan ba..domin a yadda ta lura ma hatta su masu baran ba sosai suke samin sadakan ba.

Ko yau din ma daga inda take zaune take iya hango wata yarinya daga can tsallake suna fuskantar inda take zaune, yarinyar 'karama ce da bazata haura shekara goma ba wacce ta kasance 'yar jagora ce ga wata mata wacce dukkan alamu suka bayyana cewar idanun ta ne basa gani duba da yadda take tsaye rike da wata sanda, lokaci lokaci yarinyar ke share hawaye.

Duk da Zaitun bata san mene dalilin kukan yarinyar ba amma haka kawai sai taji ta bata tausayi, da farko tayi niyyar basar da ita amma sai taji sam bazata iya ba..rashin nuna jin 'kai da tausayi ba halayyar ta bane ba.

Haka ta tashi rike da jakar kayan nata ta tsallaka inda suke..." 'yan mata me ya same ki ne naga kina share hawaye..."
Ta tambayi yarinyar tana duban ta cike da kulawa.
"...yunwa...nake ji..Yawuro kuma tace bata da ku'din da zanci abinci yanzu...".
Yarinyar ta bata amsa cikin shashshekan kuka.
Wannan mata me sandan ne ta zaburo da niyyan masife yarinyar nan...Zaitun da ta lura da hakan sai tayi saurin dakatar da ita..." Yi hakuri Baaba abin ai bai kai nan ba, kinsan yunwa ba kara ce da ita ba..."
" Nasani Hajiya amma cewa nayi ta'dan dakata mu samu sadaka sannan nima din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..."
Zaitun kam kalmar _Hajiya_ da akai mata la'kabi da shi shine yafi tsaya mata take ya ya dauki hankalin ta gaba daya, wai " _Hajiya_ "ta tabbata dan matar bata gani ne shiyasa, bayaga haka da ko kusanta ta da wannan kalmar bazata yi ba.
....Maganar ta ta karshe ce kadai ta shiga kunnuwan Zaitun..."... _nima 'din ai ba wani abin naci ba kawai dauriya ce..."_
Hakan ne yasa ta fa'din " ayi hakuri dai Baaba, itan ai yarinya ce...ga wannan ta sama muku abinda zaku ci kafin zuwa anjiman za'a rage kaifin yunwar ai.."
Zaitun ta 'karashe da mika musu Naira dari biyu da aka bata sadakar sa rannan har lokacin bata kashe ba ba kuma ta canza ta ba.
" Allahu Akbar..'yata angode..Allah yashi albarka ya 'kara arziki, Yah Allah ya daukaki darajar ki ya kare ki da dukkan sharri..Allah Ubangiji yayi miki abinda kikai mana, Allah ya saka miki da mafificin Alkhairi."

Cikin zuciyar ta ta amsa da Amin tana mai jin dadin addu'ar...batun yau tasan irin dadin da mutun ke tsintan kansa idan akai masa taimako musamman sa'in da yake cikin halin bukata ba, tabbas itan ganao ce ba jiyau ba.

Goyon dake bayan ta ta gyarawa zama 'dam sannan ta dauki jakar kayan ta da zuwa yanzun ko nauyin sa ma daina ji tayi, domin ya kasance mata ne tamkar abokin tafiya...duk motsin da zata yi yana nan a hannun ta.
Chapter 19 · 0% Book details