← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 218

Sashe 92

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka 'yan uwa na kusa suka rinka zuwa gaishe ta sakamakon yanayin ta suka ce bazai yiyu tayi ta zirga zrigar zuwa gidajen su ba acikin kwanaki biyu kacal da zatayi bayan ta riga da tayi nawi.
Da yawa ma fa'dan tahowar tata suke yi idan suka ji cewa tafiyar ta kwana biyu ce, bayan sunyi zaton haihuwa ta dawo yi a gida kamar yadda wasu ke yi amma sai tace a a..yanzu laifi ne da na zo aka sada zumunchi.
" ba laifi bane amma ai da kin bari idan Allah ya sauke ki lafia sai ki zo ziyarar ki ki sada zumunchi yadda ya kamata babu mai cewa a a".

" Wannan ai lissafin Gaibu ne, mu da bamu san 'karshen yinin yau bama ballantana na gobe talkmore of bayan haihuwa yaushe zamu ringa dogon lissafi...".
Amsar da Nadia ke basu kenan kuma sosai take gamsar da su dan maganar tata tafe take da hujja 'kwakkwara.

Zuwa azahar Rayyan ya sake 'kiran wayarxta kamar yadda ya saba ko da tana gida indai shi baya nan yana office ne ko wani wajen daban yakan kira matan sa yaji lafiyar su akai- akai.

Yana fitowa daga masallaci Amrah ya fara 'kira kafin Nadia sai dai bata yi picking call fin ba sakamakon hayaniyar ba'kin da take cikin su suna ta shan hira.

Sai da yayi mata missedcall biyu kafin ya bari.
Ganin bata daukan ba dai domin shi ba gwanin jerawa mutane kira bane daya yake mai hujja ya bari.
Amma wannan karon sai yaji ya kasa samun natsuwa da Nadian bata 'dauki 'kiran ba.
Yana shiga office 'din sa ya sake gwada 'kiran layin nata yana kuma tunanin ayyukan da ke gaban sa, domin akwai wasu jerin takaddun da suke jiran saka hannun sa kuma zuwa yammaci ake bu'katar su...amma ji yake mutukar bai gana da Nadia ba bazai iya aikin ba.

Cikin sa'a wannan karon sai tayi piciking.
Tsaye yake ya kama jikin kujerar tasa cike da fargaba amma da jin ta 'dauka ya sa shi sakin boyayyiyar ajiyan numafashi yana zama bisa kujerar ya wani yi baya da ta ita ya 'dora 'kafa 'daya bisa 'daya saman Desk din dake gaban sa na office." Mrs Rayyan fushi...?"
" a a "
Ta bashi amsa atakaice.
" Toh menene...Na 'kira tun 'dazun but u didnt pick d call har kin sani cikin fargaba..".
" Bakomai, ina cikin ba'ki ne..".
" Kuma kina fushi..."!
Sai tayi shiru.
" Right...?"
" a a kam".
" Fa'da min gaskia dear."
Sai tayi shiru.
" Na sani ai, I heard ur voice ba haka na saba ji ba..ke bazaki gane abinda nake nufi bane, sam bakya tausayin kanki naga alamu..."
" Bakomai fa babu abinda ke damu na ko da na taho ma ba wata gajiyar da naji.."
" Really..?"
" Yes har aiki nake taya Umma fa..".
" Da kyau, amma ai da bambamci, that's airjourney nd this tafiyar mota ce, dole gajiyar ta bambanta, nasan dole ne zaki gaji because its 2 to 3 hrs journey kuma ki dawo aranar akwai gajiya fa dear...kuma ma kuma ma who ll massage ur legs idan kika dawo..?"
" Zan tara idan na dawo duk ka fanshe min abu na..."
" Ba ruwana, ni na saka mutun yawo ne...?"
Murmushi tayi cike da jindadi, tasan zai barta tafiyar a yadda ta fahimci kalaman sa.
" Kinsan mene..?"
" Sai ka fa'da "

" Ki tura min numbern Auwal ko kuma ki ha'da ni da shi( Kanin ta..), zan mai magana ne ya samu mota mai kyau sai akai ki zan tura miki ku'di sai ki mata siyayya amma pls ki kula kinji...?"
" Insha Allah, thanks my dear Allah ya bar min kai, Allah ya kare min kai, Allah ya baka zuri'a masu albarka ya kuma baka ikon kulawa da su"
" Ameen Ameen...Ameen Yah Rabbi..".
Ya ce cike da jin dadin addu'ar ta.
" Amma ina da sauran kudi a hannu na, kuma akwai ATM a waje na I think ba sai ka 'kara tura ku'di ba zan yi duk abinda ya dace..."
" Ban dai isa ba kike nufi..."
" Haba dai..kai kuwa ka isa har ka fi ma.."
" Toh abar ni, nima ladan nake so nasamu ai..".
" Shikenan..Allah ya 'kara arziki mai albarka.."
" Amin...thank u.."
Yana shirin yanke wayar tace" Maganar Mota kuma...?"
" Uhum ina jin ki.
" Dama nace ko za a sama min 'karamar mota a tasha sai muyi tafiyar kaga wanda ya kainin shi zai dawo dani har gida..."
" Ok ba matsala dama magabar da zanyi da Auwal kenan..Amma dai ki ha'da ni da shi'din in mai bayani da kaina nafi so sai ya tabbatar yana da sani akan driver din sosai tukunna"
Da hk suka yi sallama ta kuma tura masa numbern Auwal din sun yi magana 'karshe da kansa ya 'kara mata kwana 'daya akan wanda ya bata da farko...tayi murna sosai da jin hakan kuwa dan zata fi sakewa.

Washe gari da safe suka yi tafiyar cikin sa'a suka isa lafiya, ba 'karamin tausayawa halin da Anty Yakura ta ke ciki tayi ba, duk da suna da 'karfi amma jikin ne sai a hankali kuma ba laifi ana 'ko'kari sosai kan kulawa da ita.

Ita kanta Anty yakuran da taga yanayin cikin Nadia sai da tai mata fa'da sosai akan wannan ganganci nata duk da koka'dan cikin ba mai wahal da ita bane amma girman sa ke sawa suke gani kamar 'karfin hali take ita kuwa rass take jin kanta sai dan abinda ba'a rasa ba.

Kwanan ta guda a wajen Anty Yakura washe gari da safe suka yi musu sallama da nufin komawa Maiduguri daga nan kuma idan ta huta d following day ta kama hanyar Kano.

Salmerh 😘
[19/10/2022, 6:11 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

*Wattpad@*
_Serlmerh-md_

🅿️ *...55*

.......Tun kafin azahar yake faman neman layin ta amma wayar bata tafiya, sosai yake jin hankalin sa a tashe, ranar ko office ha'kura yayi da shi ya dawo gida musamman yadda yake ji zuciyar sa na mai zafi, fargaba ya gama cika masa zuciya, duk wani 'kwarin gwiwa tasa tuni ta bar shi.

Kwance yake a 'dakin sa har wani zazza6i zazza6i yake ji na shigan sa yayin da Amrah ke gefen sa tana 'ko'karin kwantar masa da hankali sai dai koka'dan bata ga alamun nasara ba.

'Karshe shafa kansa ta koma yi a hankali tana taya shi jimantawa.
Bayan yawan Dialled call dake wayar sa na numbern Nadia ita kanta Amrah ajiye batun kishi tayi sbd yadda taga ya koma ta gwada kiran layin Nadia fin sau goma sha biyar amma duk basu same ta ba.

Akai- akai yake 'kiran Auwal yana tambayar sa ta iso gida ne Auwal nace masa "a a" shima cab tuni hankalin sa yake atashe musamaman da yake da labarin harin da akai yau a garin na Damaturu sun kuma tuntu6i Anty Yakura ta tabbatar musu da cewar Nadia takwas ma bata same ta a gida ba.

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Auwal da Abbahn su ke nanatawa.
Umman Nadia kam tuni ta fara kuka.
Abban su ne ke kokarin kwantar musu da hankali duk da shima 'karfin hali kawai yake amma tuni lamarin ya sanya shi cikin fargaba.

Numbern drivern da Auwal ya kar6a ma yayi ta gwadawa bata tafiya.

Rayyan kam mutuwar jiki bata tashi kama shi ba har sai bayan da Sultan ya 'kira shi yake tambayar Nadia ta iso gidane.."
" Rayyan yace a a
atakaice ya masa bayanin halin da suke ciki ma yanzu haka...na rashin samun ta har ya fara tunanin bin bayan ta.

Ashe Sultan na tare da Ammi ne alokacin sakamakon labarin da suka ji ayanzu nan yasa ta saka shi nemo Rayyan 'din a waya.
Sai dai jin amsar da ya bawa Sultan ya saka ta amshe wayar tace kul kar ma ya fara batun tafia, Maiduguri har Damaturun yau ba su tashi cikin yanayi mai da'di ba, ya bari a cigaba da neman ta awaya a kuma cigaba da addu'a Insha Allah babu abinda zai samu Nadia.

Duk Rayyan bai da wannan labarin sai yanzu domin tuni ya na gida kuma basu kunna television ba.

Amma jin wannan labari shi ya sake ta'azzara yanayin sa dan hatta Auwal da yake 'kira balbale shi yayi na 6oye masa da yake tuntuni bai sanar da shi ga abinda ke faruwa ba.

Wasa- wasa har yamma babu Nadia babu labarin ta.
Kamar wasa kamar gaske sai ga labarin na neman girmama izuwa wani abu daban har wayewar safia.

Rayyan da ya kasa hakuri dole sai da Ammi ta hakura ta barshi ya tafi.
Tuni ma an riga an saka doka 48hrs a garin so bashi da damar isa har bayan wannan awannin.
Tare da Sultan zasu kuma yaso suyi tafiyar mota amma Rayyan yace sam mota 6ata musu lokaci zata yi...dole badan Sultan yaso ba sai da suka yi bi jirgi bayan cikar awanni arba'in da takwas wanda yake dai dai da cikar Nadia kwanaki uku kenan ba asan inda take ba.

A cikin tsawon kwanakin nan irin ramar da Rayyan yayi har sai ya baka mamaki, domin lokaci guda ya zabge tamkar bashi ba, bai ta6a zaton yana yiwa Nadia irin wannan 'kaunar ba sai yanzu...ji yake inama inama, inama tun farko bai amince mata tayi tafiyar ba...da yasan wannan tashin hankalin ne zai biyo ba da bazai ta6a amince mata tafiyar ba...sai dai komai nufin Allah ne..komai Allah ke tsarawa.
Chapter 92 · 0% Book details