← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 120 OF 218

Sashe 120

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da dawowar Sultan bayan kwanaki biyar da tafiyar sa, Ammi ta zaunar da shi suka yi tattauna...shi kansa da farko yayi na'am da batun ko dan kar a dinga takura shi ma but jin wacce suke magana akai 'din yasa zuciyar Sultan luguden gudu, saurin canza baki yayi yace da Ammi sam Zaitoon bata dace ba, ama bar wani batun auren.gaba 'daya inda hali, taya ma za'a ce Zaitoon za'a aura masa alhali ba sanin asalin ta suka yi ba...cewar Sultan cike da bakin kishin dake ci masa zucia.

Ammi tace ni kaina ina kokonto duk da kuwa na yadda da tarbiyar yarinyar dari bisa dari, amma tsoron kowa ma nk ni a yanzu..bana so in 'debo mana abinda zai zo ya dame mu watarana...."
" Gaskia a dai dakata Ammi, inda hali ma a bar zancen gaba 'daya ni da zai fi, dama dai watace daban ba ita ba,.amma Zaitoon 'din nan sam hankali na bai 'dauke ta da auren 'dan uwa na ba...."

Zancen Sultan 'din sai ya tsayewa Ammi a zucia, domin tun ganin yadda Zaitoon ke hidima da shi yasa ta fara sakkowa kan dokin na'kin da ta hau, amma batun Sultan ya sake rikita mata tunani ta yadda hatta su Raihana sai da suka fahimci canzawar yanayin ta karaf 'daya.

Ranar ko magana batayi sosai ba...hakika Rayyan na bukatar matallafi, in dai kuma ba san zuciya zasuyi ba bai kamata suce Zaitoon tana yi masa wasu abubuwa fannin kulawa da jikin sa zuwa wasu abubuwan hakan kawai sbd yana kwance ba, bacin sun san ba muharrami 'yk agareta ba, gefe guda kuma tunanin ta yadda Zaitoon zata kar6i zancen take sai kuma ga maganar Sultan da ya wargaza mata komai.

Ko da Raihana ta tambaye ta damuwar ta bata 6oye mata ba, nan dai Rainahan ta 'dan 'kara mata 'kwarin gwiwa daga baya takaiwa Anty Madeena Zancen suka sake tattaunawa, dan tuni raunin Ammi ya fito fili...dan haka dole ne suma su sake wani yunkuri.

Dama ita Anty Madeena can Sultan haushi yake bata, bayaga haka ma yazo ya gudu Lagos alhali yana ganin Rayyan kwance rai a hannun Allah duk da haka bai damu ba yayi tafiyar sa afterall ai yasan shike yi masa komai amma yayi tafiyar sa.

Saboda irin wa'dannan halayen nasa ya sanya tun farko baya birge ta...shine har zaizo ya wani sake zuge Ammi sbd munafunci...toh shi ina ruwan sa da koma menene hukuncin da suka yanke a junan sa ai bai sjafe shi ba.
A ganin Anty Madeena kenan.
Cikin ranta tace ai in kasan wata baka san wata ba.
Ta 'karashe da jinjina kai tana mai cizon la66a.

Maigidan ta taje ta samu da batun shima yaje ya samu Alhaji Rufa'i da yake ma yanzu jikin nasa da sauki sosai anan suka shirya yadda abin zai kasance.

Anty Madeena da Raihana su biyu suka samu Zaitun har 'dakin ta suka zauna a'kasa tamkar basu ne sama da ita ta ta fannoni da dama na rayuwa da kuma shekaru ba.

Cike da laushin murya suke ro'kan ta akan ta amince da auren Rayyan ko dan kula da lafiyar sa ma, ta taimake su, ita ka'dai suke ganin dacewa tattare da ita kuma ita din ce suka fi jin yadda da amincewar su har can 'kasan zukatan su.

Hankalin Zaitoon ba 'karamin tashi yayi ba, tuni itama ta zube 'kasan tana kuka tama rasa mai zata ce da su.

Meyasa zasu bijiro mata da wannan gingimemen lamarin bacin sunsan ba abinda take nema wajen su ba kenan, me yasa sai ita? Meyasa zasu ce ta aure shi bayan sun san ba wata shiri ke tsakanin su ba, me zai hana su tuntubi wata cikin sauran ma'akatan gidan ba ita ba, shin suna tunanin zata amince tayi aure ne bada sanin ko yaddar iyayen ta ba, toh kuma ma idan ta amince bayan ya samu lpy ya matsayin auren yake...?
Ko ka'dan bata ta6a jin sha'awar hada inuwa 'daya da Rayyan ba ko cikin mafarki...meyasa yanzu..?"

Ganin yadda hankalin ta ya tashi ne, yasa Anty Madeena kamo hannun ta tana mai kwantar mata da hankali, tace kar ta damu, auren ba wai aure ne na damuwa ba, taimakon su kawai zatayi tunda tasan komai akan idanun ta Amrah ta tafi ta barshi ba sai sun maimaita mata ba...so ko bayan ya farka taga cewa bata ra'ayin auren abu mai sau'ki ne kawai a sallama mata batare da kowa ma yasan anyi auren ba balle sakin illah shaidu..."
Girgiza kanta kawai take yi..Raihana ne tace.." Yes zai zama ne kamar auren contract ko yarjejeniya kin gane, dan shi kanshi yayan ma ba'a san kar6an da zai wa auren ba but for now dan Allah ki taimaka mana, wallahi mun mk alkawarin babu wata matsala da zata kunno da har zai sa kiyi blaming auren da iznin Allah, amma zasu bata lkc nan zuwa dare tayi tunani.

Da 'kyar bakin ta ya iya buduwa tana duban Anty Madeena tana girgiza kai hawaye na sakko mata tace..." Wallahi Anty idan Yah Rayyan ya san wannan maganar kashe ni zai yi...dan Allah ku rufa min asiri ku aura masa wata ba ni ba, Anty idan ya kashe ni Mufeeda fa...wa zai kula min da ita..."
Kallon ta kawai Anty Madeena ke yi tana sake kissima abubuwa, har yau har gobe ta kasa gane wace iriyar 'kauna Zaituna ke wa Mufee ta kuma kasa gane dalilin 'kaunar.

Bata da buri a yanzu illa ta samun lafiyar Rayyan, daga nan kuma ita ka'dai tasan shirin ta.

A lokacin zata fasa duk wani 6oyayyen lamarin da suke 6oyewa ita da Rayyan, bata san wani irin yanayi Ammi Aseeya da iyalan ta zasu tsinci kansu ba in suka ji wannan labarin.

Ganin kamar Anty Madeena bazata yi magana bane yasa Anty Raihana cije da kwantar da hankali ta cigaba da fadin
" Kinga Zaitoon..ai mun waye Yaya Insha Allahu babu abinda zai faru ki kwantar da hankali kinji, ki nutsu kiyi tunani muna nan muna jiran shawarar da kk yanke..."

Daga haka suka fita suka barta ita ka'dai Anty Madeena 'dauke da Mufeeda a hannun ta, Zaitoon kuka sosai take, bakomai ke zuwa ranta ba illa Ammi, shin da amincewar ta ne, ko kuwa ita ta turo su...?
Indai hakane mai ya kamata tayi, ya kamata ta amince ne ko kuwa ta ce a a.. shin menene matsayain hallaccin su gareta, ya dace ta watsa musu kasa a ido ko kuwa bai dace ba, shin ya dace ta amince da auren nan ko kuwa bai da ce ba...?

" Taimako ne kawai Zaitoona..kuma akwai tabbacin yana farkawa zai bijirewa auren kinga shikenan daga nan zai sallame ki..."
Wata zuciyar ta ta bata shawaran haka.

After all ma da kunya a ganin ta, akwai tsananin kunya ta dubi tsabar idanun mutanen nan tace musu bazata auri 'dansu ba bacin ita kanta tasan a halin yanzu yanada bukatar matallafi akusa da shi...sai dai abinda kai kawo cikin zuciyar ta shine..shin zata iya aikin da suke so suyi auren ko kuwa, sam bata ji zata iya kwata-kwata, Rayyan fa..? Rayyan 'din Ammi, Rayyan mijin Amrah Yayan Marwa, Rayyan me cikar kamala da izzan nan..wannan 'dan 'kwalisan nan me ji da kyau me murza Naira ganin daman san nan.

Baya ga ciwo ina ita ina Rayyan a wannan duniyar? tasan har abada!...dan haka ko ka'dan ita kam bazata iya aikin da suke so tayi musun ba kuma zata fa'da musu gaskia...bazata iya auren Rayyan ba.

Yinin ranar kaf bata samu sukunin zucia ba...Marwa ce ma da taje ta dubo Yayan nata ta dawo 6angaren Ammi still bata gan Zaitoon ba tunicsai ta nemi hanyar 'dakin ta.

Hankalin ta yaso tashi da ganin yanayin Zaitoon din amma gano inda matsalar take ya sanya ta 6oyayyen murmushi.

Ita dama taso hakan tuntuni kawai babu ta yadda zata iya hadawa ne yasa ta basar...dan tasan Rayyan ba abokin wasan ta ba ne, amma taso shi da Zaitoon sosai, shiyasa sau da dama dramar su ke sata nisha'di.

Tuni Marwa tayi fuskar tausayi ta 'dora kan ro'kan da su Raihanan sukai mata, 'karshe sai ga su duk sun 'kare da kuka ba Marwan ba ba Zaitoonan ba, dan Marwa tsananin tausayin Rayyan ya kan hana hawayen ta tsayawa kusan ko wani lokaci idan har ta tuna da shi, but ganin wai yau gashi su ne suke rokon alfarmar wata mace akan ta amince ta auri Rayyan ya sa duk taji ta rasa 'kwarin gwiwar ta...Yayin da Zaitoon ke kukan ta mai sauti tana sakin ajiyar zuciya, abin yana ta6a ranta sosai...haka suka kasance kowa abinda yake sa'kawa cikin zuciyar sa daban.

Sai da suka gama kukan suka nutsu kafin Zaitoon take tambayar Marwa cewar
" Yanzu Marwa idan ban amince da wannan auren ba ya zakiji?"
" babu dadi..."
" Ammi fa...?"
" Itama hakan ne, zaku ma taga cewar kin guji ha'da jini da ita ne a dai- dai lkcn da yake matukar bukatar taimakon ki..."
" Marwa..."!
" Sincerely speeking Zaitoon ai kinsan bazan mk 'karya ba...a halin yanzu amincewar ki ka'dai kowa ke jira, wallahi zaku ma mufi kowa farin ciki idan kk amince da auren Yayah, wannan kadai idan ki kai mana wallahi kin gama mana komai..."
" Kina nufin Har Ammi..?"

" Tabbas kuwa...sai ma tafi kowa, dan zai zamana ne bata da haufi akan mai bawa Yah Rayyan kulawa koda bata kusa tunda tasan kece...karkashin kulawar ki yake har zuwa lkcn da zai samu sauki...hankalin ta zai kwanta sosai.."

" Baki san wani abu bama Zaitoon..a wannan halin fa abu na biyu da zai matukar farantawa Ammi shine auren Yayah na farkon shine ganin sa da lafiyar sa, so ki 'kiyasta cikin ranki ki bawa farin cikin nata matsayi zaki fahimci me nake nufi..."

Tsaye Zaitoon ta mi'ke a hankali ta juyawa Marwa baya, ga can window ta tafi ta dafa karfen windown tana jin wani 'ka'kkarfan kuka na taso mata amma tana danne shi...wani sabon yanayi ke sake shiganta.

Wai wannan wani irin dabaobayi rayuwa ke son yi mata batare da ta shirya ba.
Chapter 120 · 0% Book details