← Book details Binteee Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 218

Sashe 45

Binteee Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adam sam baya amincewa da zancen Hafeez, karara yake karya ta shi dan shi bai ta6a hango alamun kauna tattare da mahaifin san agare shi ba, yakan iya jero hujjoji kan hakan kwarara da shi kansa Hafeez 'din idan yaji bakin sa mutuwa yake yi dole yayi shiru, yasan ba laifin kowa bane face na 'Dan Maliki domin da ya kula da shi da duk hakan bai faru ba, duk da hakan baya fasa kwantar masa hankali da wasu kalaman duk da yasan ba wani tasiri suke yi ga Shaheed 'din ba amma hakan bai sa yy 'kasa a gwiwa ko daidai da rana guda ba tun ma basu kai hakan a shekaru ba har kawo lokacin da mahaifin nasa ya fara kokarin daidaita tsakanin sa da Shaheed 'din bai kyale shi haka nan ba, iya kokarin sa yana yi wajen ganin ya bada gudummuwar daidaituwar alaka tsakanin su amma har ayanzun Adam gani yake tamkar da wata manufa kawai mahaifin nasa ke neman su sasanta babu wata kauna da yake masa ta 'daa da mahaifi.
Amma ba zai iya 'kyale shi ba, ba zai iya tsayawa yana ji yana kuma gani Adam 'din na furta muggan kalamai ga mahaifin nasa ya 'kyale shi ba, yasan cewa ya samu ilimi daidai gwargwado dan baya ga 6acin rai babu abinda zai sa Adam furta wasu kalaman sai dai ma yayi fa'da da nasiha ga wanda yaji ke 'ko'karin furta su.

'Dan Maliki dake tsaye shima hannun sa da ya mari Adam da shi ya ke bi da kallo ya kasa fahimtar me ma ya aikata ne? Me yasa ya mareshi ne...? did i suppose to slap him?
Why should I...?
" just because yace ka kashe shi da hannun ka ne kaji haushi har ka maresa.
Wata zuciyar sa ta amsashi.

Marin Adam yayi amma sai yake jin zafin hakan sosai cikin zuciyar sa, bisa dukkan alamu kuma sai ya lura tamkar farin ciki marin ya saka Adam ciki...abu ne da ya kamata ya sosa masa rai ganin tun da yake yaro bai bada wata gudummawa da ta dace agare shi ko kwara guds ba bai sauke hakkin sa da Allah ya dora masa ko guda ba amma sai gashi da girman sa tashin farko sai tsarabar mari ne ya biyo baya abin mamaki sai yaga abinda bai ta6a zato daga Adam 'din ba.
Murmushi yake yana shafa wajen marin at same time kuma kwalla cike a idanun sa.
Shin me hakan ke nufi? har haka Adam ke kaunar sa a zuciyar sa ne ko yaya? tsawon wani lokaci ya 'dauka yana cutar da zuciyar yaron bai sani ba, me yasa ya kasa fuskantar halin 'kunci da kewar da Adam ke ciki tsawon lokaci? shin me ma ya 'dauki hankalin sa ya manta da lamarin sa har haka ne...?

Duk cikin zuciyar sa yake wannan tunanin yayin da a zahiri ko inda Adam yake dur'kushe bai iya ya yayi wa kyakykyawan kallo ba, nawi da kunya gami da tsananin haushin kansa ne suka cika shi.

Salmerh😘
[20/9/2022, 12:34 pm] Author...🖊️: 💕 *BINTEE*💕
*( 'Yata ce)*

Wattpad@
Serlmerh-md

🅿️ *...28*

.......Idanu Adam ya lumshe wani zazzafan hawayen na sake 6ul6ulo masa, batare da ya bu'de idanun ba ya cigaba da fa'din..." tun ina saka rai akan watarana zaka zo gare ni ka nuna min kauna da kulawa kamar yadda naga ake bawa sauran mutane kamata har nazo na fara fahimtar so na ne kawai baka yi shiyasa baka ta6a damuwa da lamari na ba, baka ta6a tuna cewa ka bar marayan yaro a hannun wata mace ba, baka tunanin yaro na yana rayuwa cikin duniya ban san halin da yake ciki ba, baka damu da lafiya ta ba, ci na ko sha na duk ba sune gaban ka ba, baka damu da ilimi na ba baka damu da yanayin tarbiya da halin rayuwa da zan iya fuskanta ba, baka damu da amanar da Allah ya dam'ka maka akaina ba, dukiyar ka ka'dai ce agaban ka, burin ka kawai shine ka tara arziki, kayi rayuwar ka duk yadda kake so batare da tuna cewa Allah na ganin ka ba, shin baka jin kunyar duk abubuwan da kake aikatawa ne Alhaji? Meyasa ka za6i wannan hanyar wajen salwantar da ni dama dukiyar ka batare da tsoron Allah ba? batare da tuna cewa ni har dukiyar taka duk 'din mu amana Allah ya baka ba?
Ka wofintar da ni ka barwa duniya ni ka za6i wa'dansu daban suka maye maka gurbi na, kuma na tabbata da mahaifiya ta na raye bazata ta6a yin watsi da ni da lamari na kamar yadda kai ka aikata ba, sau da dama na kan tuhumi kaina da zamtowa 'daa agare ka a mafi yawan lokuta na kan ce dama ba kai Allah ya za6a min matsayin mahaifi ba dan na tabbatar kai kanka baka shirya kar6a ta matsayin 'daa a lokacin da Allah ya azurta ka da samu na ba, sai da kaga na girma? Ciwo na ya ri'ka? 'Kunci ya gama mamaya ta? na gama gwagwarmayar rayuwa ta, na bar dukkan 'kalubale da na fuskanta abaya, karfi na ya fara kawowa na fara mantawa da damuwa da rashin ka kusa dani, lokacin da na fara burin gina rayuwa ta da halali na a lokacin ne zaka ce zaka tallafi rayuwa ta..? ka 'dauka ni 'din bani da zuciya cikin kirji na ne..? shin inada laifi ne idan nace bana bukatar komai daga gare ka? Alhaji ka bani amsar tambaya ta ina so in ji amsa ta daga bakin ka ne shin inada laifi ko guda anan....?".
Ya 'karashe maganar yana jin 'karin nawi cikin kirjin sa saboda rarrabuwar numfashi daya fara fuskanta, maganar ma da 'kyar ya 'karasa ta amma dan 'karfin hali ya dage sai yayi, inda ya 'karashe da wara idanu kan Alhajin yana faman dafe 'kirji sakamakon tari da ya sarke shi.
Hafeez da ya fahimci yana jin jiki da sauri ya iso gare shi yana kokarin kwantar masa da hankali, yasan dama lafiya ba isan Adam din sosai tayi ba amma taurin rai irin na Adam har na bashi tsoro wani lokaci, duk yadda yake da dauriya ji yadda yake dafe kirjin sa da gani kasan bisa dole yake hkn, ya da'de yana fama da ciwon zuciyar da babu wanda yasan farkon sa sai Allah mahalicci.

Hannun sa da Hafeez ya kama yayi saurin fisgewa..." ka barni Hafeez, ka barni in tambaye shi abinda ya da'de yake damu na cikin zuciya ta, ban ta6a ganin halitta mafi tsananin son kai irin wannan mutumin ba ka bar ni in tambaye shi ya bani amsar tambaya ta.."

" Haba Adam! haba dan Allah baka ganin halin da kake ciki ne baka ganin yanayin kane? kar fa ka manta condition da kake ciki fa..."Cewar Hafeez ga Adam cike da kulawa.
" Ba wannan ne damuwa ta ba Hafeez, please let him answer my question, ya tsangwami rayuwa ta, ya hana ni fuskantar rayuwata, shi lokacin da ya fara tashi rayuwar waye ya taka masa birki, ko akwai wanda ya ce lallai lallai dole shi zai za6a masa sana'ar yi ?"
Idon Hafeez cikin na Adam yake masa kallon rashin jin dadin kalaman sa, kai ya girgiza masa gami da lumshe ido yayi kasa da kansa.
Sosai Adam ya fahimci Hafeez dan ba sanin yau ke tsakanin su ba, sani ce mai cike da fahimtar da juna ya kuma san Hafeez da zuciya 'daya yake 'kaunar sa.
Shima 'din 'kasa yayi da nasa kan yana mai zazzafan numfashi yayin da Hafeez ya cigaba da fa'din.." Bana jin da'din kalaman naka Adam, please mu koma gida...".
Ya 'karashe maganar ya tallafo hannun Adam da nufin mi'kar da dashi.

'Dan Maliki dake tsaye ne yayi saurin dakatar da shi da 'daga masa hannu gami da fa'din"...Kaga barshi yayi maganar sa, barshi ya amaryar da duk abinda ke ransa, na cancanci kowace irin magana ce daga gare shi a yanzun matukar zai sa ya fuskance ni, kuma shima na tabbatar hakan zai fi sama masa sauki a zuciya..".

Shiru Hafeez yayi illa jinjina kai da yayi yana duban Adam 'din.
Bai damu da duk irin maganganun da suka wanzu tsakanin Hafeez da 'Dan Malikin ba illah sake maida duban sa da yayi ga 'Dan Malikin ya cigaba da fa'din" Ina da ciwo a zuciya ta wanda na kamu da shi duk ta dalilin damuwar ka ka ta6a sanin hakan..?
Tsam 'Dan Maliki yayi da ransa idanun sa kir kan Adam 'dun cike da al'jabin.jin furucin sa.
Haka ma Hafeez duban abokin nasa yake babu ko kiftawa
" Tsawon lokaci ina 6oyewa Hajiyata ciwo na gudun kar hankalin ta ya tashi saboda ita ka'dai gareni a duniyar nan da ace ka damu dani duk da na san kaddara ta kenan amma da ka nuna min kauna kana tunanin hakan zai faru da ni ne..? damuwa ta kullun 'kara yawaita take kamar yadda shekaru na suke karuwa kowacce rana, damar sanin dalilin ka na barwa dunia ni har yau na kasa sani, dan Allah Alhaji yau ka'dai gani agaban ka ka sanar da ni meyasa baka kauna ta? Laifin me nai maka a rayuwa da ka tsane ni ka tsani ganin farin ciki na? ka za6i gani na cikin kewa da 'kuncin zuciya da damuwa tsawon lokaci? Shin laifi ne dan na kasance 'daa agare ka ka sanar dani....".

Kasa bashi amsa ko guda daga cikin tambayoyin nasa 'Dan Maliki yayi illa tahowa da yayi a hankali yana jin 'kafafun sa tamkar bazasu iya 'daukar sa ba, 'dago Adam yayi ya rungume sosai cikin jikin sa a karo na farkon kaf 'din rayuwar su, kowa 'kwalla yake zubdawa, rungumar da rabon da yayi masa tun ranar da aka haife shi yazo ya tadda mahaifiyar sa ta koma ga Allah bayan ta haifa masa shi, wani 'kauna da tausayin Adam ke ratsa masa dukkan ga6o6in jiki wanda bai ta6a zaton yana masa irin sa ba sai a yau 'din.
Chapter 45 · 0% Book details